Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

HIJABI LULLUBIN MUSULUNCI (2)


Mu'assasar Al-Balagh


Me Ya Sa Hijabi Kawai?

Muna fatan an fahimci irin bayanin da muka yi dangane da bambancin da ke tsakanin hijabi (kange-wa) irin wadda aka dauka a zamanin jahiliyya danga-ne da mu'amalolin mace, da kuma hijabin da Musu-lunci ya dauka a matsayin garkuwa da zai kare mace daga zalunci da tozarta kimarta da wasu wawaye ke yi.
Abin da ya saura kawai shi ne mu yi bayani kan babban dalilin da Musulunci ya dogara da shi wajen tsara wa mace wani irin tufafi daidai da yadda Allah Ta'ala yake so ga bayinsa.
To don saboda bayani kan wannan babban dalili ko manufa, ba tare da tsawaitawa ba, bari mu ambato wadan-nan abubuwa:
Da farko, akwai mahanga guda biyu dangane da mu'amala tsakanin namiji da mace:
Mahanga ta farko tana ganin mutum yana iya saduwa (jima'i) da kowace mace a cikin al'umma, kuma yin hakan ba zina ba ce.
Mahanga ta biyu kuwa, ta takaita 'yancin jima'in mutum ga matar da suka yi aure ne kawai, kana in ba tare da aure ba, to ba shi da 'yancin saduwa da wata mace.
Wannan mahanga ta farko irin ta ce a halin yanzu ake gudanarwa a Turai.
Sannan mahanga ta biyu kuwa ita ce mahangar Musulunci dangane da mu'amala tsakanin mace da namiji.
Wannan shi ne babban jigon wannan al'amari, wanda kuma duk wani bayani daga jikin shi aka ciro. Duk wata dabi'ar mutum dangane da mace an ciro ta ne daga wannan mahanga ta farko, wadda ke da alaka da sha'awarsa ta jima'i da mace a wuraren bukukuwa, tarurruka da wasu mataye da ba matayensa ba da kuma cakuda tsakanin jinsosi, da kuma sanya mace ta zamanto wata abin kawa da burge mazaje da dai sauran abubuwa makamantan haka.
Dangane da mahangar Musulunci kuwa, al'amarin ya kasu kashi-kashi:
Lalle umurnin mace da ta rufe dukkan jikinta, in banda fuskoki da tafukanta, daga idanuwan mazaje, face mijinta da danginta, kana kada ta bata lokacinta wajen zance maras amfani da kuma tafiya da mazaje da makamancin haka, sannan kuma haramta ta keban-tu da wani namiji in dai ba danginta ba, da kuma sauran mu'amaloli da fikihun Musulunci ya yi bayani, da kuma mahangar Musulunci dangane da alakar namiji da mace, duk kariya ce da kuma kiyayewa daga lalacewa da rashin kunya.
Hakika idan muka yi la'akari da irin yanayin wadannan ra'ayoyi guda biyu da kuma abubuwan da suka haifar, to lalle za mu kai ga natijar cewa Musu-lunci yana tsananin kishi dangane mutuncin mace da kuma daukakarta, tsarki da girmanta, ta yadda ba za ta zama wata haja abin sayarwa ga mazaje ba.
Don haka, Musulunci yake ba da muhimmanci wajen daidaitawa da tsara alaka irin ta jima'i, kana kuma ya yi kokari wajen toshe duk wata hanyar da wadannan mugayen mutane suke amfani da ita wajen tozarta mace don biyan bukatunsu na sha'awa (da ita) yadda suke so.
Sannan kuma abin da ita wannan mahanga ta jahiliyya, tsohuwar ce ko sabuwar, take son ta cim ma shi ne yin rikon sakainar kashi ga wannan ka'ida don saboda amfanin maza. Babbar matsalar wannan mahanga ita ce cewa ta ginu ne kan amfanin namiji da biyan bukatansa ko da kuwa macen tana iya samun wani amfani!!
Kana idan muka sake yin la'akari da irin girman amfani da ribar da mazaje sukan samu ta bangaren jima'i da tattalin arziki a karkashin wannan mahanga, za mu ga wannan al'amari na haramci da kuma dabi'ar tozarta mace da aka gudanar a zamanin jahiliyya, daidai yake da irin abin da ake gudanarwa a yau da sunan wayewa, wadda hakan cutarwa ce ga ita mace. Lalle irin iyakance mace da aka yi a sabuwar jahiliyya (ta wannan zamani) kawai ya banbanta da tsohuwar (jahiliyya) ce kawai ta bangaren zahiri da abin da ya fito fili. Amma yana nan dai a matsayinsa na sarka da ta dabaibaye mace, ta hana ta 'yancinta, kuma ta kwace mata ikonta. Don haka namiji ya mai da mace kamar wata kamammiya ko kuma baiwa ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban na kasuwanci, gidajen karuwai, gidajen sinimomi, gidajen radiyoyi da talabijin, jaridu da wuraren nuna kawa don biyan bukatunsa.
Koda yake, a lokacin da wadansu matayen suka fara nuna damuwarsu da irin wahalhalun da suke fuskanta a karkashin irin wannan al'ada ta Turai, to an samu wasu mazaje 'yan kadan wadanda suka mike tsaye don kalubalantar irin wannan bala'i da mata suke fuskanta a Turai, saboda dabi'un wasu mazajen.
Ga wadansu misalai nan da suke nuna irin wuce gona da irin da mazaje suke yi wa mataye da kuma mummunan sakamakonsa:
A kasar Biritaniya, 'yan mata 9 daga cikin 12 - 'yan kasa da shekaru 20 - suna fuskantar fyade da sacewa. To amma jami'an tsaro sun sami daman kama kashi 13 cikin dari ne kawai na daga cikin masu laifin. Kana kuma a 'yan shekaru da suka gabata yanayin aikata laifuffuka ya karu da kashi 84 cikin dari; kana kuma laifuffukan kananan yara ya karu da ninki biyar a watannin farko na shekarar 1975 [1].
Wata jaridar kasar Italiya mai suna "Omiga" ta fitar da wasu labarurruka kan irin laifuffukan da aka aikata a wannan kasa inda take cewa:
" Hakika mace Ba'italiya tana tsoron fita daga gidanta, don kare mutuncinta daga lalatattun samari wadanda suke yawo a kan tituna da kuma wadanda ba su da wani aiki face kai hari ga mataye da budurwaye da kuma sace su da nufin yin fashi ko kuma aikata fyade… hakika mace takan ki yarda da duk wani aiki kome daukakarsa, idan dai har aikin zai kai ta ga dawowa gida cikin dare ne, don kada ta sanya mutunci da lafiyarta cikin hatsari" [2].
A wani rahoto da kungiyar Kulawa da Iyali ta kasar Amirka ta buga ta bayyana cewa:
" Lalacewar iyali (aure) wanda ya zamanto ruwan dare, ita ce babbar matsalar da take damun al'umma. Domin a kowace shekara a kan raba auren ma'aurata sama da miliyan daya, wanda haka ya nunka na karnin da ya gabata har sau bakwai."
" Kana yawan shegun 'ya'ya ya karu sau uku in aka yi la'akari da na shekarar 1938, sannan a duk shekara a kasar Amirka a kan haifi shegun 'ya'ya sama da miliyan hudu. Sannan dangane da matsalar lalacewar matasa kuwa wanda hakan yana da alaka da irin rabe-raben aure da ke faruwa, kididdigar ta nuna cewa al'amarin ya nunka na shekarar 1940 har sau uku".
Wani rahoton kuma cewa yake:
"A wani rahoton da Hukumar Binciken Laifuffuka ta Kasar Amirka (F.B.I) ta fitar, ya nuna cewa a cikin irin shari'o'in kisan kai da ke faruwa a tsakanin iyalai, sau da dama mazajen ne ke kashe matayen nasu; kana kuma kashi 15 cikin dari na laifuffukan da suka shafi iyali cutarwar da ke cikinsa tana dawowa ne ga yara kanana ne".
Sannan wata kididdiga da تungiyar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta nuna cewa "kashi 60 cikin dari na matan aure a Amirka da Turai sun sami kansu cikin kunci, damuwa da halin kaka-ni-ka-yi" [3].
A lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Dr. Homer wata baturiyar kasar Sweden kan ta yi bincike kan matsayin mata a kasashen Larabawa a shekarar 1975, inda ta sanar cewa:
" Hakika macen kasar Sweden ce, take da bukatuwa da ta nemi 'yancinta, domin kuwa su matan kasa-shen larabawa sun riga sun sami nasu 'yancin tuntuni karkashin addinin Musulunci". Ta ci gaba da cewa: " a wannan lokaci macen kasar Sweden ta yi ta kokarin ganin an bayyanar da wannan shekarar a matsayin "Shekarar Mata ta Duniya" kana kuma a sake bayyanar da wata shekarar a matsayin ta mazaje, don ya samu daman kwato hakkokinsa daga wajen mataye."
Dr. Homer ta ci gaba da cewa: " Kashi 25 cikin dari na matayen kasar Sweden suna fama da ciwon ruhi da na jiki, sannan ana kashe kashi 40 cikin dari na kudin shigar kasar Sweden ne a wajen magance wadannan cututtuka da wannan 'yanci na jeka-na-yika da matayen kasar Sweden suke gudanarwa ya haifar. Hakika, babbar matsalar macen kasar Sweden ita ce irin wannan yanke kauna wanda ya tura ta zuwa ga gabar wani abu mai hatsarin gaske da ke fuskantar rugujewa [4]".
Hakika wannan bakar cuta ta haifar da rugujewar zaman lafiyar iyali a kasar Biritaniya, wanda hakan ya haifar da karuwar adadin zaurawa ko kuma maza da matan da suke zaman daduro. A bisa kididdigar da gwamnatin Birtaniya ta buga a ran 14 ga watan Janairun shekarar 1988, ta nuna cewa yawan haihu-war shegun 'ya'ya ya tashi daga kashi 4 cikin dari a shekara ta 1950 zuwa kashi 21 cikin dari na dukkan haihuwar da aka yi a shekara ta 1986, kana in banda kasar Denmark da take da kashi 43 cikin dari, kasar Birtaniya ce take da adadi mafi yawa a duk kasashen Turai.
Kididdigar da aka yi ta nuna cewa kasar Biritaniya ce take da adadin shika mafi yawa a kasashen Turai, kusan ninki biyu na kasashen Faransa da Jamus.
An gano cewa tsakanin shekarar 1979 da kuma shekarar 1985, adadin maza da matan da suke zama da junansu ba tare da aure ba, ya kusan ninkuwa. Kana a shekarar 1985, kashi 15 cikin dari na dukkan matayen da ba su da aure, har ma da wadanda aka sake su, suna aikata daduro.
Hakika za a iya fahimtar yanayin yadda ake tafiyar da mace a kasashen Turai, wadanda suke ikirarin cewa su ne ma'abuta 'yanci da adalci, daga Taron Duniya Kan Mata da Kafafen Watsa Labarai da aka gudanar a birnin Athens na kasar Girka ran 20 ga watan Nuwamban shekaran 1985.
A wannan taro, daya daga cikin mahalalta taron mai suna, Petra Kelly 'yar majalisar kasar Jamus, ta yi kukan cewa: " A kasar Jamus, suna tafiyar da mu (matayen Jamus) kamar 'yan tsiraru, wadanda ba su da amfani, musakan cikin al'umma kamar yara. Suna amfani da mu wajen tallen kayayyakinsu kuma suka dauka cewa zaluntarmu ba laifi ba ne. A duk cikin mintuna 15 sai an yi fyade wa wata mace."
Daga baya wannan taro, ya yi kira ga majalisar kasar Girka da ta kafa dokar da ta haramta amfani da mata a talibijin don biyan wata bukata. Ko da yake an tabbatar da ana wulakanta mata a wadannan kasashe, to amma su ma matayen wadannan kasashe da suke ikirarin ci gaba su ne abin zargi. Don kuwa idan mata ba su yarda ba, to da ba a yi amfani da su wajen buga littattafa da finafinan jima'i da kuma tallace – tallace da su tsirara ba.
Wannan kididdiga mai zuwa za ta nuna mana irin yadda wannan al'amari na rugujewar iyali ya zamanto a al'ummomin da ba na Musulunci ba:

A Kasar Faransa

Daya daga cikin aurarraki hudu yana karewa ne ta hanyar shika; a birane ma adadin ya fi haka yana kai wa kashi 50 cikin dari. A kowace shekara kimanin masoya 600,000 ne suke yin aure, 100,000 kuma suke zaban su zauna tare ba tare da aure ba, kana a kan sami rabuwar aure guda 100,000.

A Kasar Kanada

Kusan kashi 40 cikin dari na aurarrakin fari, sukan kare ne ta hanyar shika. Sannan a tsakanin shekarun 1972 zuwa 1982, an sami ninkuwan wannan adadi har sau biyu.

A Tsohuwar Tarayyar Sobiyet

Kimanin kashi 70 cikin dari na aurarraki sukan lalace ne cikin shekaru goma, dalilan da ke jawo hakan kuwa sun hada da shaye-shaye, rashin kudi da kuma rashin wadatuwa da juna da sirri.

A Kasashen Amirka ta Tsakiya da ta Kudu:

Wata jaridar kungiyar UNESCO ta Majalisar Din-kin Duniya tana cewa sau da dama ana samun 'ya'yaye masu iyaye guda (wadanda suka tashi karka-shin kulawan uwa kawai ko kuma uba kawai) ne ta hanyar irin hijirar da mataye suke yi zuwa birane da kuma samar da 'ya'yaye a aurarrakin da ba jimawa suke yi ba. A dalilan shaye-shaye da kuma gazawar miji wajen samun takamammen aiki, yakan haifar da watsewar iyali da kuma barin uwaye da 'ya'yayensu cikin tsananin talauci da wahalhalu. A duk duniya kasashen da suka fi adadin shegun 'ya'ya su ne kasashen Karebiya, Tsakiya da kuma Kudancin Amirka.

Kasar Sin (China):

Ko da yake adadin shika a kasar Sin yana da karanci a kan da dama daga kasashen Turai, to amma a cikin shekaru biyar, an sami hauhawansa da kashi 70 cikin dari. Mujallar Peiking Review ta kawo rahoton cewa ana samun hauhawar adadin shika a kasar.

Kasar Amirka:

Kimanin rabin adadin aurarrakin da aka yi suna karewa ne ta hanyar shika. Don haka ne ma kashi 60 cikin dari na yaran da aka haifa suna tafiyar da bangaren yarintarsu ne a wajen uwa ko ubansu.

Kasar Japan:

A shekaru ashirin da suka gabata, adadin shika ya ninku kashi biyu. Kafin shekarar 1947, mazaje suna da daman shikan matayensu ko da a kan titi ne. to amma yanzu, kashi 70 cikin dari na shikan, matayen ne suke jawo shi.

Kasar Afirka Ta Kudu:

Kungiyar kwato hakkin matayen Afirka ta Kudu tana cewa a rayuwar daya daga cikin biyun matayen Afirka ta Kudu ana musu fyade. Hakan kuwa ya hada har da kananan yara da tsofi.

Kasar Biritaniya:

Adadin shika a kasar Biritaniya ya dara na kowace kasa a kasashen Yammacin Turai. Kusan mace guda cikin mataye marasa maza guda bakwai masu shekaru 18 zuwa 49, suna zama da wani namiji ba tare da aure ba.
Wata mujallar birnin London mai suna "The Hospital Today", a bugunta na watan Afrilun shekarar1975, ta buga rahoton shekara-shekara na Ma'aikatar Lafiya da Jin Dadin Al'umma ta kasar Biritaniya, inda take cewa:
"…..duk da yawan abubuwan hana daukan ciki da kuma halaccin zubar da ciki, to amma duk da haka an gano cewa kashi 86 cikin dari na yara, mata da ba su da maza ne suke haihuwarsu! A nan gaba akwai babban matsala. A shekarar 1973 an sami wadannan rahotanni kamar haka: an sami rahoto guda na wata yarinya 'yar shekara 11 da ciki; rahotanni guda shida na yara 'yan shekaru 12 masu ciki; rahotanni guda 38 na yara 'yan shekaru13 masu ciki; rahotanni 255 na yara 'yan shekaru 14 masu ciki. Kana kuma a dai-dai wannan shekarar an sami rahoton zubar da ciki har guda 166,000, kashi 50 cikin dari na wannan adadi ya faru ne daga mata marasa aure [5].
Idan muka koma ga gabashin (duniya) kuwa, za mu ga lalacewar al'umma a duniyar kwaminisanci ba boyayyen al'amari ba ne a kan na duniyar 'yan jari hujja. Mujallar "Interphase" a bugunta na watan Afrilun shekarar 1977 ta ba da rahoton cewa:
"Babbar matsalar 'yan Gurguzun kasar Sobiyet ita ce cewa, a yammacin kasar Rasha daya daga cikin aurarraki biyu da suke daurawa yana karewa ne ta hanyar shika. Misali, a birnin Mosko, kusan kashi 49 cikin dari na aurarraki, sukan kare ne ta hanyar shika bayan da aka haifi dan farko. A yankin Mavadanski kawai adadin shika ya kai yawan kashi 72.9 cikin dari. A saboda haka ne ma wani taron kara wa juna ilimi na likitoci da aka yi a Jami'ar Mosko a shekarar 1975, taron ya yi kira da a nemo wata mafita ga wannan matsala ta yawan hauhawar adadin shika da karancin adadin haihuwa [6]".
Ko da yake ya kamata a gane cewa wadannan matsaloli na iyali sun ta'allaka ne kawai ga garuruwan da ba na musulmai ba ne na Tarayyar
Sobiyet. Duk da irin hana gudanar da koyarwa irin ta Musulunci a garuruwan musulmai da suke karkashin kasar Sobiyet daga bangaren 'yan Gurguzu, to amma sai da Musulunci ya ci gaba da tasirinsa a rayuwa da dabi'un musulman wadancan garuruwa, yana mai rage matsalolin iyali da kuma wulakanta mata.
Wadannan bala'o'i da makamantansu, su ne abubuwan da wannan mahanga ta Turai kan mu'amaloli tsakanin maza da mata ta haifar.
A dalilin haka ne, Musulunci ya dauki matakan ruguza tushen lalacewar al'umma da kuma kokarin tsayar da wulakanci da ake wa mata da kwace musu hakkokinsu kana da kuma tabbatar da mutunci da girmamawa a cikin rayuwar 'yan 'Adam.
Don haka, hijabi yana daga cikin mashahuran abubuwan da Ubangiji Ya yi amfani da su wajen kare mutuncin mace da kuma gina tsarkakakkiyar al'umma.
Za mu iya ganin irin halin da ke wanzuwa a da dama daga cikin kasashen musulmai wadanda suka maye gurbin koyarwar Musulunci da na kasashen Turai. Al'ummar wadannan kasashe sun kaurace wa ka'idojin Musulunci, wadanda suka hada har da hijabi, inda suka dauki halayen kasashen Turai a matsayin abin koyi. Don haka ne shika, karuwanci, shaye-shayen giya da muggan kwayoyi, kana da kuma bullar cututtuka irin su ciwon kanjamau (AIDS) da dai sauransu, suka buwayi wadannan al'ummomi da suka zabi su bijire wa ka'idojin addininsu. Kana kuma suka halalta haramtacciyar mu'amaloli tsakanin samari da 'yan mata, maza da mata kuma alal akalla ana iya cewa suka yi musu rikon sakainar kashi.
To amma a kasashen musulmai wadanda al'umma da gwamnatocinsu suka kasance suna bin ka'idojin Musulunci, akwai karancin afkuwar keta alfarmar mata, rashin kunya, shika da sauran muggan ayyuka. Ginshikin iyali yana da karfin gaske, mataye ba sa da sauran tsoro kana kuma suna cikin aminci wajen yawo a kan tituna da kasuwanni.
To a nan wani tsari ne ya fi? Shin za mu zabi takaitaccen 'yanci ne, wanda daga karshe yake haifar da rugujewa da rashin samun nasara, ko kuma tsarin da ke kai wa ga kiyaye al'umma, sannan wanda yake kare namiji da mace ba tare da nuna wani bambanci ba?
Masana kimiyya ta hanyar binciken rayuwar dan'Adam sun gano cewa, an halicci mutum da wasu sha'awoyi guda biyu:
(A)- Su ne sha'awoyin da suke bijirowa da kansu ba tare da tasirin wasu abubuwa daga waje ba, kamar sha'awar abinci, sha'awar nuna kansa ga sauran mutane da kuma sha'awar mallaka da dai sauransu.
(B)- Su ne sha'awoyin da duk da suna nan tare da mutum, to amma ba sa bijirowa sai wasu abubuwa daga waje sun motsar da su.
Daga cikin muhimman irin wadannan sha'awoyi, akwai: Sha'awar jima'i, wanda wakoki da littattafan batsa da tsiraici da dai sauransu suke haifar da ita.
Musulunci, wannan addini na Ubangijin talikai, Mahalicci, Masanin kome, yana da cikakkiyar masaniya kan mafi karancin al'amurran da suke tankwara dan'Adam da kuma hatsarin da ke tattare da rayuwar mutum a duk lokacin da ya ketare haddin da aka sanya masa. Wanda idan da zai bi shi, da zai samu daman daidaita wadannan sha'awoyi a duk bangarorin rayuwarsa.
Saboda masaniyar Musulunci kan wadannan al'amurra ne, ya sa ya haramta motsa wadannan bakaken abubuwa da suke motsa sha'awa.
Don kiyaye wannan bukata, Musulunci ya sanya wadansu tsarurruka na zamantakewa, tattalin arziki da siyasa. Wadannan tsarurruka sun haifar da kyakkyawan yanayi na yarda tsakanin wadannan bukatu na cikin dan'Adam da kuma bukatun sauran jama'a da kuma al'ummar da yake raye a ciki.
Wannan tsari na Musulunci kan hijabi da kuma kyautata alakar da ke tsakanin namiji da mace, an gina shi ne a bangare guda don kiyaye daidaituwan da ke tsakanin bukatuwan mutum da kuma babban burinsa na tsarkake da kuma kiyaye alakar da ke tsakanin wadannan jinsuna guda biyu a daya banga-ren. Don haka, hijabi ya kasance wani asasi ne da ke da alaka da yanayin rayuwar dan'Adam, bugu da kari kan kiyaye kyawawan dabi'u kana kuma tsarkaka da kuma tsara rayuwar al'umma dai-dai da koyarwar Musulunci.
Musulunci, ta hanyar tsara hijabi ga mata, ya takaita yanayin alakoki tsakanin wadannan jinsuna biyu ta mafi kyan tafarki. Kana ya tafiyar da namiji da mace gaba dayansu, yana mai takaita ayyuka ga kowane daya daga cikinsu don gudanar da su yadda ya dace. A al'amarin hijabi ne kawai aka bambance mace da namiji, to amma a sauran ayyuka, daya suke.
Hakan kuwa ba wai yana nuna cewa gudummawar maza da na mata a al'ummar musulmai dai-dai yake ba, lalle ba dai-dai suke ba. Shi namiji shi yake daukan nauyin kula da gida ta hanyar amfani da dukiyarsa wajen samar da abinci, matsuguni, sitira, kula da lafiya da dai sauran abubuwan jin dadin iyali. Mace kuwa tana da 'yancin neman kudi da kuma sarrafar da shi yadda take so, to amma ba hakkinta ba ne ta ciyar da gida.
Hakkin mace musulma ne kulawa da kuma tarbiyyantar da 'ya'yayenta da kuma samar da kyak-kyawan yanayi na ci gaba da daukakar iyali.
Hakika hijabi yana da amfani ta bangaren iyali da kuma ga al'umma. Domin a gidan da ake girmama hijabi da kuma sanya shi, za mu ga iyalan gidan suna nuna tausayawa, taimakawa da kuma neman zaman lafiya tsakaninsu. Kana a dalilin rarraba wadannan jinsuna biyu, za a iya magance aikata laifuffukan zinace-zinace wanda ya zama ruwan dare a al'ummar kasashen Turai, inda zina tsakanin 'yan gida guda (misali wa da kanwa ko kuma kani da yarsa) ya zama jiki.
Hijabin Musulunci ba wai kawai ya takaita da rufe jiki ba ne. A'a shi wani lullubi ne da yake aiki a matsayin abin da ke nisantar wa daga aikata duk wani laifi da sabo wanda ke lalata mutum da kuma al'umma.

4- Abin Da Ya Hau Namiji da Mace Kan Hijabi

Bari mu yi dubi cikin muhimman al'amurran da suka shafi dukkan jinsunan biyu, don bambance abubuwan da suka hau kansu dangane da wannan muhimmin al'amari na hijabi.
Namiji da mace suna da abubuwan da suka hau kansu, kamar yadda wannan aya ta Alku'ani ta bayyana:
"Ka ce wa muminai maza da su kawar da idanuwansu kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce wa muminai mata su kawar da idanuwansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana kawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu…". (Surar Nur 24: 30-31)
Manyan malumman fikihu sun yi bayanin wannan hukumci kamar haka:
(A)- Dole ne mace ta rufe dukkan jikinta daga idon wanda ba muharraminta ba.
(B)- Haramun ne ga mutum ya dubi jiki da gashin macen da ba muharramansa ba, amma ban da fuska da tafukan hannayenta. Kana kuma haramun ne ga mace ta kalli maza in dai ba mahaifanta ko danta ko kaninta ko kakanta ko dan'uwanta da kuma sauran wadanda suke da dangantaka da ita ba.
(C)- Haramun ne ga mutum ya kalli fuska ko hannayen macen da ba muharramansa ba da nufin jin dadi, haka ita ma macen.
(D)- Ya halalta ga mutum ya kalli jikin macen da yake son ya aura don ya ga irin yanayin jikinta, haka ita ma macen.
(E)- Yana halalta namiji ko mace su kalli jikin muharramansu (amma ban da al'auranta) matukar dai ba da niyyar jin dadi ba ne, amma kallo irin na sha'awa yana haramta ga muharramai da ma wadanda ba muharramai ba.
(F)- Wajibi ne ga mace da ta rufe jikinta da kuma gashinta daga idon mazajen da ba muharramanta ba.
(G)- Haramun ne ga namiji da ya kadaita da matar da ba muharramansa ba a wajen da babu mai shigansa, idan har suna jin tsoron faruwar aikata haramun; to amma babu laifi ga mutum ya kadaita da macen da ba muharramansa ba a wajen da mutane suke da 'yancin shiga.
(H)- Haramun ne ga mutum ya taba jikin macen da ba muharramansa ba, haka ita macen, ya haramta ta taba jikin namijin da ba muharraminta ba, kamar gaisuwa ta hannu da dai sauransu.
(I)- A yayin lalura, kamar wajen yin magani ko kuma kubutar da mutumin da ruwa yake kokarin cinyewa, yana halalta ga namiji da ya taba jikin mace ko kuma ita macen ta taba namiji, matukar dai babu macen da za ta iya wannan aiki ga 'yan'uwanta mata ko kuma namiji ga 'yan'uwansa maza.
(J)- Yana halalta ga mazaje su saurari muryar macen da ba muharramansu ba ce, matukar dai ba da niyyar jin dadin ko kuma wani abin da zai kai mutum ga aikata haramun ba. Haka kuma yana halalta ga mace da ta jiyar da muryarta ta hanyar tattaunawa da kuma yin jawabi ga mazajen da ba muharramanta ba. To amma da sharadin muryar na ta ba zai janyo fitina ga masu sauraronta ba, domin haramun ne ga mace ta yi magana da mazaje cikin rangwadi da karya murya.
(K)- Mustahabi ne ga mace da ta kiyaye kyau da adonta ga mijinta kawai, don kuwa jan hankali da kuma kyau suna da muhimmiyar rawa da suke takawa a rayuwar mace, kuma muhimmin al'amari ne cikin abubuwan da suke kawo jin dadin rayuwar iyali.
(L)- Haramun ne ga mace da ta kwaikwayi maza (wajen sa tufafi, aiki da dabi'a), haka shi ma namijin.
(M)- Haramun ne ga mace ta bude kanta da shafa turare yayin da za ta fita waje, wato haramun ne ta sanya turare ta yadda mazajen da ba muharramanta ba za su iya jin kamshin nasa lokacin da take wucewa cikinsu ko kuma yin mu'amala da ita.
Idan muka dubi wadannan shar'antattun ayyuka wadanda suke karkashin hijabin Musulunci da kyau, za mu ga cewa dukkan mazaje da mataye suna da nasu kaso cikin wannan doka, tare da jaddadawa ga mata wajen rufe dukkan jikinsu. Hakika hakan a fili yana nuna mana cewa Musulunci yana so ne ya assasa tsarkakakkiyar alaka tsakanin wadannan jinsu-na biyu; yada tsarki da mutunci tsakanin al'umma; kana da kuma kare al'umma ta hanyar kyawawan mu'amaloli. Kana kuma ba burinsa (Musulunci) ba ne ya wulakanta matsayin mace ko kuma ya kange ta daga ba da tata gudummawa ga rayuwa ba, kamar yadda wadannan dokoki da suka gabata suka nuna a fili.
Hakika idan har muna so mu yi hukumci kan al'amarin rufe dukkan jiki ga mata, kana ga shi kuwa mun ce maza da mata daya suke a mahanga ta gaba daya dangane da hijabin Musulunci, to tambaya a nan ita ce: Me ya sa mace kawai ne aka kallafa mata rufe dukkan jikinta ba namiji ba?
Amsa a nan, wanda babu wani cikakken mutum da zai musanta, ita ce cewa dalilin kallafa wa mace rufe jiki ita kadai yana da alaka da irin dabi'u da kuma zahirinta. Domin kuwa bangaren janyo hankalin abu da mace take da shi ya fi na namiji; tana da cikakkun abubuwan motsa rai. Don haka, ado da kyau suna daga cikin abubuwan da ake fara siffanta ta da su. Hakika idan har ba a takaita su ba, to tana iya sanya kamilin mutum, da saninsa ko kuma ba da saninsa ba, ya aikata haramun.
Wannan irin siffa da mace take da shi, wanda ke ba ta daman janyo hankalin maza gare ta, shi ne babban ummul aba'isin da ya sanya Musulunci ya wajabta wa mace rufe jikinta don magance faruwar barna. Don haka bai dace a umurci namiji da ya rufe dukkan jikinsa kamar mace ba; domin kuwa namiji bai mallaki wadannan siffofi ba, kuma shi ba a halicce shi da dabi'ar yin ado da kawata kansa, don ya jawo hankalin mata ba. To amma duk da haka fa, Musulunci bai son mutum ya yi mummunan shigar da ba ta dace ba, don kada ya nuna wasu wuraren da ba su dace ba na daga jikinsa.
Dangane da janyo hankali, akwai wasu abubuwa guda biyu da suke wanzuwa, daya ga mace dayan kuwa ga namiji. Wanda yake tare da mace kuwa shi ne sha'awar nuna ado da kyanta, hakan yana daga cikin dabi'unta. Na namiji kuwa shi ne sha'awar kallon mace ba wai kallo kawai ba, a'a har ma da samun jin dadi daga hakan. Duk wadannan abubuwa suna nan tare da su. Wani masani mai suna, Will Durant yana cewa, a wannan duniya babu wani abu da ya fi tabbatuwa kuma ake so a tabbatar da shi kamar sha'awar da mutum yake da ita na kallon mace.
Kana kuma a fili yake cewa sha'awoyin maza da mata na jima'i suna iya tashi ne ta hanyoyi daban-daban. Mace, a matsayinta na halitta mai taushin zuciya, tana bukatuwa da shafa jikinta wajen tayar mata da hankali. A daya bangaren kuma shi namiji halitta ne mai kaurin jiki da karfin sha'awa, hanka-linsa na iya tashi ta hanyar kallo kawai. Don haka mace take rufe jikinta don kada ta nuna jikinta kana shi kuma namiji ba zai ga wani abu da zai tayar masa da hankali ba. Madalla da Musulunci da ya zaba wa al'umma hijabi! Hakika ya yi dai-dai da irin yanayin mace!.
A saboda la'akari da wannan al'amari na jan han-kali, za mu ga kuma Musulunci ya haramta abubuwa kamar su luwadi ga mazaje da kuma madigo tsakanini mataye, domin kowane guda daga cikin wadannan dokoki guda biyu yana da abubuwa da yake haifarwa da kuma dalilansa, kamar yadda sauran dokoki na shari'a suke da nasu dalilan da suka dogara da su.
Wadannan su ne manyan abubuwan da aka lura da su wajen kafa wannan doka; wato ta hijabin Musulunci


1. Jaridar kasar Kuwait ta "al-?abas" ta ranar 6/2/1976, ita ma ta ciro ne daga wata mujallar kasar Italiyya mai suna Timbo.
2. kamar na sama ta ranar 6/10/1976.
3. Littafin "Man and Religion", na turanci, bugun farko, shafi na 81, wadda Mu'assasar Al-Balagh ta buga , tana ciro shi ne daga wata makala ta Jami'ar Iskandariyya.
4. Kamar na sama shafi na 82.
5. Kamar na sama shafi na 84.
6. Kama na sama.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
7+4 =