Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

HIJABI LULLUBIN MUSULUNCI (3)


Mu'assasar Al-Balagh


5- Shubhohi Kan Hijabi

Tambaya a nan ita ce dai: shin masu inkarin ci gaba (kasashen Turai) za su iya yarda da hijabi tattare da irin fahimtar da suka yi masa na cewa shi wani kokari ne na mayar da mace baya da kuma raunanar da ita daga tawaye ga zaluncin da ake mata, wanda hakan raunana rabin al'umma ne?
Hakika, wannan mummunar fahimta ta faro ne daga irin yadda wasu masana da 'yan siyasar kasashen musulmai suke nuna hijabi wanda ya saba wa 'yancin mace da kuma kange ta daga cim ma burinta na yin kafada-kafada da mazaje cikin ayyukan gina kasa.
Wannan al'amari yana bukatar da a fahimci tushen matsalar, ita ce kuwa: shin su wadannan masu ikirarin ci gaba da gaske suke yi yayin da suke yada wannan jita-jita? Shin me suke nufi da " 'yancin" mata?
Idan har abin da ake nufi shi ne 'yancin fadin albarkacin baki; mutum ya fadi ra'ayinsa, 'yancin mallaka; 'yancin zaben mijin aure da kuma 'yanci cikin ayyukan yau da kullum da dai saurans; to ai a Musulunci babu wani abu da ya hana ta wannan 'yancin da kuma makamantansu!
Shin hijabi ya hana mata musharaka cikin bangaro-rin rayuwar yau da kullum da kuma neman ilimi ne?
Shin hijabi ya hana mata fadin albarkacin bakinsu ne?
Shin hijabi ya shiga tsakanin mace da kuma hakkinta na mallakan dukiya ne?
Yana da kyau a tambaya cewa, shin tun asali hijabi yana da wata alaka da wadannan tambayoyi ko kuma shi wani al'amari ne wanda yake da alaka da irin sa tufafin mace, mutunci da kuma irin kyakkyawan alakarta da wadanda suke tare da ita.
Sannan kuma wannan al'amari na hijabi ya shafi al'amurran tattalin arziki da kuma samar da abubu-wan bukatuwa ne. Domin irin hasarar da ake yi a fili take. A bisa misali mu dauka cewa akwai asasai guda biyu na samar da abubuwa:
Na farko yana da alaka da ma'aikata mata, wadanda suke sanya hijabin Musulunci kana kuma suna mu'amala da mazajen da ba muharramansu, ba mu'amala irin wadda Musulunci ya yarda da ita.
Na biyun kuma yana da alaka da ma'aikata mata wadanda suke sanya tufafi masu janyo hankali, kana suke bin irin tafarkin Turai wajen mu'amala da mazaje.
To hakika, za mu ga cewa asasin da ke kulawa da hijabi sai ya fi kokari da kuma samar da abubuwa da ake bukata, saboda irin alakar da ke tsakanin maza da mata.
Kana, a daya bangaren kuwa, za mu ga cewa a daya asasin (asasi na biyu), wanda lalata da munanan ayyuka suke kan gaba, ana bata lokaci mai yawan gaske wajen mu'amaloli na neman biyan bukatun sha'awa (jima'i).
Kana mu dauka cewa akwai dakunan karatu guda biyu:
A na farkon ana kula da mu'amalolin samari da 'yan mata kamar yadda Musulunci ya tsara.
Kana ana biyun kuma ba a kula da mu'amaloli tsakanin samari da 'yan mata kamar yadda Musulunci ya tanada. Shin me ku ke tsammanin zai faru dangane da gudanar da aiki a kowane daya daga cikin wadannan misalai?
Shin za a iya bayyana daki na biyu a matsayin wurin da ya dace da karatu?
A takaice dai, ashe bai fito fili cewa hijabin Musulunci, duk da irin yanayinsa, bai kasance abin barazana ga 'yancin mace ko aiki ko kuma sauran mu'amaloli na rayuwa ba.
Lalle gaskiya ne (hijabi mummunan abu ne) idan mutum ya yi la'akari da irin hijabin (kulle) da ake yi a kasar Indiya, Iran, Masar da sauransu a lokacin jahiliyya, inda suke kulle mata a cikin gida. Hakika dole ne mace ta ji cewa an take mata hakkinta da kuma katsalandan cikin ayyukanta, wanda abin da hakan zai haifar shi ne ruguje rabin al'umma ko ma fiye. Lalle wannan al'amari ne da ya kamata mu yi dubi cikinsa dangane da irin mummunan yanayin da irin wannan hijabin da ke kange mata daga duk wani irin aiki na ci gaban al'umma yake haifarwa. Musulunci ya yi Allah wadai da irin wannan hijabi na jahiliyya, inda ya sauya shi da wani lullubin wanda ke cike da tsarkake mu'amala karkashin sunan hijabi. Kamar yadda muka bayyana, akwai bambance-bambance masu girman gaske tsakanin wadannan nau'o'i guda biyu na hijabi.
Hakika yadda masu ikirarin ci gaba suke daukan hijabi ya saba wa asalin al'amarin. Al'ummar da lalata ta yi kanta a cikinta, hakan shi ne babban dalilin rashin ci gabanta, saboda abubuwa da kuma karfin da take da su suna tafiya ne wajen al'amurran zinace-zinace, neman mata da almubazzaranci, sabanin al'ummar da tsarkakakkiyar mu'amala take gudana tsakanin mata da maza.
Kana dangane da tunaninsu kan danne wa mata 'yancinsu karkashin inuwar sanya tufafi da kuma tsarkaka wanda hijabin Musulunci ya zo da shi, lalle abin da suke nufi da 'yanci a nan shi ne 'yancin zinace-zinace da duk wasu bangarorinsa wanda ake yadawa a kowane lungu da kuma yanayi. To amma dangane da sauran 'yancocin kuwa ko ma tunaninsu ma ba sa yi.
A takaice dai, hijabi, a mahangar Musulunci, ba shi da wani mummunan tunani dangane da 'yancin mace ko kuma duk wani aiki nata da kuma musharakanta cikin al'amurran yau da kullum. Face ma dai hijabin Musulunci ya tabbatar da 'yancin mata ne da kuma mutuncinsu, bugu da kari kan irin babbar gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da 'yancin mata da kuma musharakansu cikin ayyukan ci gaban al'umma.
Sama da haka ma, hijabin Musulunci a ainihinsa, yana ba wa mace mutuncinta ne da kuma daukaka matsayinta a cikin al'umma. Don kuwa mutane sukan yi mu'amala da duk macen da take sa tufafi irin na Musulunci (hijabi) ta bangaren cewa ita cikakkiyar 'yar'Adam ce. Kana ita kuwa macen da ba ta kula da hijabi, ita ma jama'a suna mu'amala da ita ne a matsayin 'yar'Adam, amma saboda abin da take da shi a matsayinta ta mace da kuma jikinta da take barinsa a waje don dadinsu. Don haka, hijabin Musulunci zai ci gaba da zama wani makami na yakan bakin ciki, damuwa da wulakanci.
Yana da kyau a nan a gane cewa duk da irin muhimmancin da Musulunci ya bayar wajen mace ta rufe jikinta gaba ga mazajen da ba muharramanta; yana kuma kiranta da ta kula da kanta da jikinta (wajen yin ado) a cikin gidanta, don kawata matsayin da take da shi na mace wanda Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta ta da shi, kuma don biyan bukatunta wadanda shari'ar Musulunci ta halalta mata.
Duk da cewa an hana mace nuna jiki da adonta ga sauran mutane, to amma an kwadaita mata cewa ta gyara jikinta da kuma yin ado wa mijinta. Hakika ma ana yabonta a duk lokacin da ta kawata kanta domin mijinta da kuma jin dadi tare da shi.
Wani abin da ya kamata a ambata a nan shi ne cewa macen da take kula da shiga irin ta Musulunci (hijabi) baya ga irin girmamawa da mutuntawar da take samu daga wajen jama'a da kuma iyalanta, tana kuma dadadawa Ubangiji Mahaliccinta rai ne kana tana samun lada daga wajenSa saboda biyayyar da ta yi wa umurninSa.
Hakika wannan babban nasara ce gare ta, don kuwa tana biyayya ne ga Alkur'ani mai girma da kuma hadisan AnnabinSa (s.a.w.a); kana tana kare al'umma ne daga munanan ayyuka da lalata. Tana mai kawar da munanan tunanunnuka da ayyuka; tana mai daga yanayin aiki da samar da abubuwan bukata da kuma kawo tsarki da daukaka ga al'umma. Duk ta sami damar gudanar da hakan ne kuwa ta hanyar amfani da hijabin Musulunci. Lalle irin albarkatun da za ta samu kan wannan babban aiki, ba zai iya lissaftuwa ba.
Shakka babu, a duk lokacin da mace ta kiyaye zakin muryarta, yanayin motsin jikinta, yanayin dabi'unta da kuma sirrin kanta daga wadanda ba su da 'yancin amfanuwa da su a shar'ance, to hakan taimakon al'umma ne.
Wannan babban aiki da ta dauka yana haifar da kwanciyar hankali da sauki ga sauran halittu 'yan-'uwanta, don ta haka ne za mu iya fahimtar dalilin da ya sa Musulunci ya sanya irin wannan muhimmanci a gare ta cikin sauki. Don ita ce kashin bayan al'umma kuma asasin ci gaban mutum a matsayinsa na dan-'Adam. A saboda haka ne a duk lokacin da ta lalace, to za ta lalata dukkan al'umma ne. Kana kuma a lokacin da ta tsarkaka kuma ta samu kiyayewa irin ta hijabi, to al'umma ma za ta tsarkaka.
Hakika za a iya magance da yawa daga cikin bala'o'i da cututtukan da suka addabi kasashen Yammaci, shaye-shayen giya da kwayoyi, zinace-zinace da sauran matsaloli, idan har aka bar mata suka fahimci akidar hijabi. A wadancan al'ummai, ana kula da kwakwalen mutane da kuma zaluntar samuwarsu da kuma hana su isa zuwa ga kamala, kamar yadda aka halicce su. Wadannan lalatattun al'umma da kuma shuwagabanninsu sun gano hanyar cimma wannan buri na su, don haka sai suka lalata mata, kuma ta haka ne sai suka sami damar lalata al'umma.

6- Gudummawar Mace A Wayewar Musulunci


Hikayoyi Da Misalai
A shafuffukan da suka gabata mun ga matsayin Musulunci dangane da mace da kuma hijabi. Hakika tabbataccen ra'ayi ne. To amma hakan ya tabbata? Ya ya mace, a tarihin Musulunci, ta gudanar da ayyukan-ta, kana kuma wace gudummawa ta bayar wanda ke nuna irin babban matsayin da Musulunci ya bata yayin da ta fita daga zaluncin lokacin jahiliyya, kana ta rungumi hijabin Musulunci? A shafuffuka masu zuwa, za mu yi dubi ne a aikace na wasu mataye wadanda suka tsinka sasarin bauta ga mazaje, kana suka dauki bautar Ubangiji, Allah Madaukakin Sarki.
Hakika Musulunci da kansa, ya tabbatar da irin hikimar da ke cikin dokokinsa, kuma suka ci gaba da zama wasu matakala na shiriya zuwa ga madaukakiyar rayuwa wacce take cike da kyautatawa da samar da sakamako mai kyau, samun kyawawan dabi'u, tsira da kuma tsarkaka.
Tun da hasken Musulunci ya bayyana ne a Jazirar Larabawa, mace musulma ta sami damar kade kurar wulakanci da bauta kana kuma ta yi ban kwana da ranakun zalunci da kuma bisine 'ya'ya mata da rai. Inda ta fara rayuwa irin wadda wahayi da kuma dokokin Allah Madaukakin Sarki suka tsara. Kana ta fara taka rawa cikin aikin gina madaukakiyar al'umma wacce Manzon Allah (s.a.w.a.) yake kula da ita.
Don haka, 'yan'Adam suka gano irin wannan sabon yanayi wanda ya haskaku da hasken annabci. Wannan hanya wadda wata mace wato Khadija bint Khuwailid, shugaban iyayen muminai, ta fara zabenta. Inda ta ba da dukkan dukiyarta don gudanar da dukkan ayyukan wannan da'awa, yayin da Annabi (s.a.w.a.) yake gwagwarmaya da masu bautan gumaka na lokacin Jahiliyya. Hakika ma dai, irin wannan taimakon kudi na wannan mace madaukakiya a wancan lokaci ya kasance mafi girman makami na fada tsakanin shiriya da kuma bata (gaskiya da kuma karya).
Hakika wannan madaukakiyar mace ta fuskanci da yawa daga cikin wahalhalun rashin abin duniya ne saboda irin ci gaba da tayi na taimakon da'awa zuwa ga gaskiya da kuma da'awar wannan mai ceto, Annabi (s.a.w.a.); da kuma irin tsayuwar dakan da ta yi a kan imani da kuma kare wannan sako da kuma wanda ya zo da shi. Tun daga farkon da'awar, ta kasance a gefen Manzon Allah (s.a.w.a.), tana mai bashi taimakon dukiya, kana da taimako mafi muhimmanci na karfafa shi, soyayya da kuma tausayi ga wannan "Rahama ga Talikai". Ita ce ta farko da ta yi imani da shi, kare shi da dukiya da matsayinta, kuma ita ce ta karfafa shi da kuma kwantar masa da hankali a lokuta mafi wahala na rayuwarsa.
Amirul Muminina, Imam Ali (a.s.) a daya daga cikin huduboninsa a littafin Nahjul Balaga yana fadi dangane da matsayinta cewa:
"...a kowace shekara ya (Annabi) kasance yakan zauna a kogon hira na wani lokaci, babu wani wanda yake tare da shi sai ni. Babu wani wanda zai ganshi ko ya ji shi ko kuma ya kusace shi sai ni. A wancan lokaci babu wani musulmi daga Annabi (s.a.w.a.) sai matarsa Khadija, sai kuma ni na ukunsu. A duk duniyan nan babu wani wanda ya karbi Musulunci. A wasu lokuta a wancan lokacin nakan ga hasken wahayi kana na kan ji kamshi mai dadi irin na annabci" [1].
Sauran matayen Annabi (s.a.w.a.), bayan rasuwar Khadija (a.s.), su ma sun sami wani babban matsayi cikin tarihi. Ba za mu taba mancewa da irin gudummawar Ummu Salama wacce ta haddace da yawa daga cikin hadisan Manzon Allah (s.a.w.a.) ba. Hakika irin kauna da biyayyarta ga gaskiya da kuma hanya madaidaiciya, shahararren abu ne a cikin tarihin Musulunci inda har wasu daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s.) sukan bata amanar abubuwan da suka gada na annabci yayin da suke cikin mawuyacin yanayi.
Lalle irin gudummawar mata a tarihin zamantakewa da siyasar Musulunci yana da muhimmanci gaske. Daga cikin shahidan farko na Musulunci akwai wata mace mai suna Sumayya, matar Yasir, wacce aka gana mata tsananin azaba inda daga karshe ta kasance wacce ta fara yin shahada a Musulunci. Hakika za a iya ganin gudummawa da zaluntakan mata musulmai a shafuffukan tarihi. Wadannan mataye irin su Sumayya suna da madauka-kiyar daraja. Irin gudummawar da suka bayar ga al'amurran addini da siyasa sun zama darussa ga mataye a duk duniya wajen dawo da mutuncinsu da suka rasa.
Daga cikin irin misalin karfin da Musulunci ya ba wa mataye a farko-farkon tarihi, ita ce wata mace da ake kira Nusaiba wacce take zaune a birnin Madina. Ta kasance Ba'ansariya (mutanen Madina wadanda suka taimaki musulman da suka yi hijira daga garin Makka) ce ana kiranta da Nusaibatu Jarrah. Ta yi aure, sannan tana da 'ya'yaye guda biyu, masu suna Amarah da Abdullah. Sunanta ya fara fitowa ne a cikin tarihi yayin wata bai'a da wadansu Ansarawa, mazaje guda sittin da mataye guda biyu, suka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a.) bayan da suka karbi Musulunci. Wannan bai'a ana kiranta da Bai'atul Akbah.
Manzon Allah (s.a.w.a.) wanda yake tsananin girmama mata, yayin wannan bai'a sai ya sanya hannunsa cikin kwano cike da ruwa kana ya mika wa wadannan mata, inda su ma suka yi hakan. Wadannan mutane sun taimaki gwamnatin Manzon Allah (s.a.w.a.) matukar taimako. Domin mijin wannan mata Sumayya ya yi shahada a yakin Badar, kana daya daga cikin 'ya'yayenta ma ya yi shahada a wannan lokacin.
Hakika tarihi ya nuna mana irin yadda wannan mace Nusaiba ta kasance a wurin yaki tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) a matsayin likita. Ta yi musharaka cikin yakukuwa da daman gaske, tana dauke da jakar ruwa, inda take yin magani ga marasa lafiya da wadanda aka ji musu rauni a filin daga.
Kana kuma Nusaiba tare da danta da ya saura, Amarah, sun halarci yakin Uhudu. Yayin wannan yakin, lokacin da musulmai suka tarwatse, sai ta dauki jakan ruwanta tana bi tana shayar da masu jin kishirwa da kuma taimakon wadanda aka raunana ta hanyar magunguna da take da su.
An ruwaito ta tana cewa: "Lokacin ana tsakiyar yakin, sai na ga dana yana gudu, sai na tsai da shi na ce masa: Ya dana! Ina za ka? Shin daga wa kake gudu? Daga Allah ko daga ManzonSa?".
Nan take ta komar da shi, kana ta tsaya tana kallo daga nesa. Daga nan ne ta ga makiya sun kewaye Manzon Allah (s.a.w.a.), nan da nan ita da wannan da nata suka nufi inda Annabi (s.a.w.a.) yake don kai masa agaji. A nan ne daya daga cikin kafirai ya kashe wannan da nata, ita kuma Nusaiba sai ta dauki takobin dan nata, da taimakon Allah ta kashe wanda ya kashe mata da. Ko da ganin haka, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata: "An gaishe ki, Ya Nusaiba, Allah Ya yi miki albarka".
A wannan yaki ne wannan jarumar mace ta sami raununnuka har guda goma sha uku, daya daga cikinsu saran takobi ne a wuyanta, sannan kuma ta rasa hannunta guda a yakin Yamama. An ruwaito cewa wannan mace mai tsananin sadaukarwa za ta dawo lokacin Imami na karshe, Imam Mahdi (a.s.) a matsayin likita (wacce za ta taimaka masa).
Sayyida Zainab (a.s.), wannan jarumar 'ya ta Imam Ali (a.s.), ita ma ta kaddamar da muhimmiyar gudummawa lokacin da ta dauki nauyin isar da sakon dan'uwanta Imam Husaini (a.s.) bayan shahadarsa a Karbala a hannun azzaluman sarakunan Umayyawa, karkashin ja-gorancin Yazid bin Mu'awiyya.
Ta dauki nauyin yin bayani da kuma isar da dalili da manufar wannan babban yunkuri na Imam Husaini (a.s.) a duk guri ko kuma taron da ta halarta. Kana ta tona asiran azzalumai a garuruwan Kufa, Damaskas da Madina. Sannan kuma ta dauki nauyin kare fursu-nonin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.), wadanta suka hada da mata da kananan yara, tare da yankakken kan Imam Husaini (a.s.) daga sahara mai zafin gasken nan ta Karbala zuwa birinin Damaskas.
Hakika tarihi ya rusunar da kai cikin kunya gaba ga wannan madaukakiyar mace wacce Musulunci da raunana ke gode mata, saboda irin sadaukarwar da ta yi, da kuma irin juriya, hakuri da kuma gudumma-warta ga tafarkin gaskiya.
Cikin jarunta ta fuskanci azzalumai kana ta tona munanan ayyuka da tsarur-rukansu. Ta bayyanar da sakon gwagwarmaya, daukaka, mutunci da gaskiya a dukkan garuruwa.
Jawabanta a fadojin wadanda suka kamo ta, suna cike da hikima da motsa rai. Lalle ta shahara ta wajen fuskantar Yazid da ta yi a fadarsa da ke Damaskas. Ta fuskance su gaba dayansu kana ta zarge su kan abubuwan da suka aikata ba tare da tsoron mutuwa ko gallazawa, wanda ya zamanto ruwan dare ga makiyan wancan hukuma.
Haka ta ci gaba har karshen rayuwarta wajen tona asirin zalunci da azzalumai da kuma isar da sakon dan'uwanta (a.s.). Ta kasance mai fada da zalunci, kana ta mallaki tsarkakakkiyar dabi'a da jaruntaka a duk tsawon rayuwarta. Tana daga cikin madaukakan mutane a duk inda ta kasance. Ta ci gaba da gwa-gwarmayar Imam Husaini (a.s.) da kuma taimakon al'umma wajen fahimtar abin da ya hau kansu na yakan zalunci da babakere.
Idan har muna son mu yi bincike cikin shafuffukan tarihin Musulunci, babu yadda za a yi mu mance da ayyukan Hamida, matar Imam Ja'afar Sadik (a.s.) kuma mahaifiyar Imam Musa Kazim (a.s.). Ta kasance tana kula da mabukata da marasa galihu na birnin Madina, a bisa umurnin Imam Sadik (a.s.). Inda take rarraba kudi ga fakirai da kuma ziyarar marasa galihu, don taimaka musu da abubuwan da suke bukata.
Misalin wata matar kuma mai tsoron Allah wacce ta ba da muhimmiyar gudummawa a tarihin Musulunci, ita ce Salil, mahaifiyar Imam Hasan bin Ali al-Askari (a.s.).
Ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen kare gaskiya da kuma kulawa da shiriyar Ubangiji. Wannan mace mai daukaka ta kasance a matsayin mai sadarwa tsakanin Imaman nan guda biyu, wato: Imam Aliyu al-Hadi da Hasan Askari (a.s.), da sansanin muminai mabiyansu lokacin da wadannan Imamai suka shiga halin tsanantawa daga wajen azzaluman zamaninsu. Ita take isar da sako da umur-nonin wadannan Imamai ga muminai mabiyansu, kana ta isar da tambayoyi da sakonninsu da kuma halin da suke ciki ga wadannan Imamai (a.s.).
Yana da muhimmanci mu fahimci cewa kasancewar mata a cikin al'amurran siyasa yana da matukar muhimmanci. Domin kuwa, a wasu lokuta, mataye sukan dauki rabin adadin al'ummar kowace kasa, kuma su kan iya canza alkiblar al'umma zuwa ga alheri ko sharri gwargwadon irin wayewarsu ta siyasa da kuma musharakarsu. Hakika hijabi ba ya hana irin wannan gudummawa kamar yadda bai hana kowacce daga cikin wadannan mataye da muka ambata a baya ba.
A wannan zamani namu za mu ga misalin irin wannan wayewa da kasancewa a lokacin gwagwar-mayar Musulunci a kasar Iran. Inda mata duk da cewa ga jarirai a hannayensu kana ga kananan yara a gefensu, amma haka suke fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu ga gwamnatin zalunci ta Sarki Shah, sanna kuma ga 'yan sanda suna karkashe su. A sakamakon haka da dama daga cikin wadannan iyaye mata da 'ya'yayensu suka yi shahada yayin zanga-zangogin da suka dinga yi.
A lokacin da sakon gaskiya ya bayyana kana aka sake rayar da sautin gwagwarmaya a karni na ashirin, za mu ga yadda matan Palasdinawa, suke nuna hannu wa sojojin Yahudawa 'yan-share-guri zauna, kana a daya hannun kuma suna dauke da duwatsu suna jiran samun dama don su jefi abokan gaba. A halin yanzu, wadannan mataye da sauran mataye irinsu a duk fadin duniya, ana daukarsu a matsayin kashin bayan wannan gwagwarmaya. Hakika hijabi shi ne tutarsu kuma suna alfahari da matsayinsu na masu yaki da babban makiyin gaskiya.
Kana za mu ga irin tasirin da Musulunci yake da shi a kan jama'a kana shi kuma hijabi a kan mata, idan muka yi la'akari da abubuwan da suka faru a kasashen Azarbaijan da kuma Bosniya Hazgovina.
Musulunci ya bayyanar da kansa a cikin su kana kuma ya ba su jaruntaka da karfin jure wa zaluncin da ya mamaye su. Tun shekaru da dama tsarin kwaminisanci da Gurguzu ya cire musu tsarin Musulunci daga al'adunsu. Suna kiran kansu musulmai to amma sun jahilci dokoki da tsare-tsaren Musulunci. Lokacin da suka sami 'yancin kansu daga wannan tsari da babu Allah a ciki, sai suka juya zuwa ga hasken gaskiya, kana suka karbo abin da da suka rasa. Babu shakka, daya daga cikin alamun hakan shi ne yin hijabi ga mata.
Wadannan misalai suna ba da tunanin irin abin da matayen musulmi masu bin dokoki da ka'idojin Musulunci za su iya cimmawa. Suna nuni da irin babbar gudummawar da ta bayar ga rayuwar al'um-ma, wanda ya saba wa irin wadancan munanan tuna-nunnuka da kuma ra'ayoyi na wadanda suka jahilci Musulunci da kuma irin tabbatacciyar karfinsa na ruguza kangin da yake hana mata musulmai gudanar da ayyukansu karkashin inuwar ci gaban Musulunci.

7- Abubuwan da Kur'ani Da Hadisai Suka Fadi Kan Mace Da Rayuwa


Neman Izini
" Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku shiga gidaje wadanda ba gidajenku ba, sai kun sami izini, kuma kun yi sallama a kan ma'abutansu. Wannan ne mafi alheri a gare ku, tsammaninku, za ku tuna". (Surar Nur, 24: 27)

Yin Kama
Imam Ali (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Allah Ya la'anci mazaje masu mai da kansu kamar mata, ko kuma matan da suke mai da kansu kamar maza" [2].

Shafa Turare Yayin Fita Waje
Imam Husaini (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Duk macen da ta shafa turare sannan ta fita wajen gidanta, Mala'iku suna la'antanta kana ana debe mata albarkar Ubangiji har sai ta dawo gida" [3].

Mummunan Kallo
Imam Husaini (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Mummunan kallo daya ne daga cikin kibiyoyi masu guba na Shaidan, kana mummunan kallo yana haifar da mummunar nadama" [4].
Nesantar Abubuwan Haramun:
Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"A ranar kiyama, dukkan idanuwa za su yi kuka, in banda guda uku: idon da yaki barci don gadin musulmai (dukiyoyinsu, kasarsu da dai sauransu), saboda Allah; kana da idon da ya yi kuka don tsoron Allah; da kuma idon da aka rufe shi daga kallon abubuwan da Allah Ya haramta" [5].

Kallon Mata
An tambayi Imam Sadik (a.s.) kan ko ya halalta ga namiji ya kalli fuskan macen da yake son ya aura, kuma ya kalle ta ta baya. Sai ya ce:
"Na'am babu laifi ga namiji ya kalli fuskar macen da yake son ya aura da kuma kallon ta ta baya" [6].

Gaishe Da Mata
Imam Husaini (a.s.) yana cewa:
"Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yakan gaishe da mata, kana su ma sukan mayar masa da sallamar tasa. Kana Amirul Muminina, Imam Ali (a.s.) shi ma ya kasance yakan yi sallama ga mataye, to amma ba ya son ya gai da budurwaye daga cikin matayen, inda yake cewa: "Ina tsoron kada muryarta ta yi min tasiri, har ya kai ni ga aikata zunubi maimakon samun lada".

Azabar kallon Mata
Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Wata rana wani saurayi Ba'ansare ya gamu da wata mace a garin Makka. A wancan lokacin, mata sukan sanya lullubi, sai ya fara kallonta tun tana zuwa. Lokacin da ta wuce sai ya ci gaba da kallonta, har sai da ta shiga wani lungu. Kana ya ci gaba da kallonta yayin da yake wucewa ta lungun, har lokacin da wani kashin da ke jikin garu ya kwarzane shi a fuska, inda daga nan macen ta bace masa. Kwatsam sai ya ga jini yana zuba masa. Daga nan sai ya ce: Dole ne in je in sanar da Manzon Allah (s.a.w.a.) wannan abu da ya faru. Lokacin da Annabi (s.a.w.a.) ya gan shi cikin wannan hali sai ya tambaye shi me ya faru ne. Sai ya gaya wa Annabi (s.a.w.a.) duk abin da ya faru. Nan take sai Mala'ika Jibril (a.s.) ya sauko da wannan aya:
"Ka ce wa muminai maza su runtse idanuwar-su, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa" [7].

Zaman Gefen Titi
Abu Sa'id al-Khudri yana cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ku guji zama a gefen titi",sai wasu sahabbai su ka tambaye shi cewa: "Ya Manzon Allah! Ba za mu iya barin zama a gefen titi inda muke tattauna abubuwan daban-daban ba". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu: "Idan ba za ku iya barin hakan ba, to ku ba wa titin hakkokinsa". Sai suka ce: "Menene hakkokin titin". Sai yace: "Su ne ku rufe idanuwanku; ku nisanci cutar da sauran jama'a; ku amsa sallama; kuma ku yi umurni da alheri, kana ku yi hani da sharri" [8].

Kwadayin Daukakan Muminai:
Amirul Muminina (a.s.) yana cewa:
"Lalle Allah Yana fushi da daukakar masu imani maza da masu imani mata. Saboda haka tilas mai imani ya yi fushi (da daukakar da yake samu), saboda wanda bai yi fushi da daukakar da ya samu ba, shi ne mai juyayyiyar zuciya" [9].

Falalar Kawar Da Idanuwa:
Abu Imamah yana cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Musulmi shi ne wanda yayin da ya kalli mace kyakkyawa sai ya kawar da idanuwansa, Allah Zai ba shi ladar ibadar da dadinta a zuciyarsa take" [10].

Kiyaye Kai
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ku kiyaye kanku daga abubuwa guda shida, ni kuwa zan lamunce muku aljanna; idan za ku yi magana, ku fadi gaskiya; in kuka dauki alkawari, to ku cika; ku rike amana; ku kare farjojinku (sai ga matayenku); ku kawar da idanuwanku (daga kallon haram); kana ku kame hannayenku daga aikata zalunci da kuma abubuwan haramun" [11].

Girmama Mace
Yayin da yake jawabi wa musulmai lokacin aikin hajjin ban-kwana, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya gargade su dangane da abubuwan da yake tsoron za su bar su bayan rasuwarsa, inda ya ambaci mace a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwa. Ya na cewa:
"Ku ji tsoron Allah dangane da mata, kana ku kula da su da kyau" [12].

Aure Mai Albarka
Anas ya ruwaito cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Duk wanda ya auri mace don daukaka da kyawunta, to Allah ba zai kara masa nasa ba, face ma ya kawo masa wulakantuwa; duk wanda ya aure ta don dukiyarta, Allah ba Zai kara masa nasa ba, sai dai ma Ya sanya masa talauci; duk wanda ya aure ta don dangantakanta, to Allah ba Zai kara masa nasa ba, sai dai ya mai she shi ba kome ba; duk wanda ya auri mace ba don kome ba face sai don ya kalle ta (ya ji dadi), kuma ya kare farjinsa (daga aikata haramun) da kuma kulla zumunta, Allah Zai albarkace shi ta hanyarta, haka ita ma" [13].
Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Kuma daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku nitsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani".(Surar Rum, 30:21)
A wata ayar kuma, ana magana kan mace mai biyayya:
"…..to, salihan mata masu da'a ne, masu tsarewa (yayin da mazansu ba sa nan) kan abin da Allah ya tsare....".(Surar Nisa'i, 4: 34)

Kwadaitarwa Da Kuma Kulawa Da Hijabi:
Musulunci, duk da irin tausayin mata da yake yi, yana kwadaita musu kulawa da hijabi a wannan aya ta Alkur'ani mai girma:
"Ya kai Annabi! Ka ce wa matanka da 'ya'yanka da matayen muminai su kusantar da kasa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauki ga a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin kai". (Surar Ahzabi, 33:59)

Daidaitawa
A ayoyi da dama, Alkur'ani mai girma yana magana kan daidaitawa tsakanin jinsosin nan biyu. A daya daga cikinsu yana cewa: "....kuma su matan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani...". (Surar Bakara, 2: 228)
A wani gurin kuma, Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Ya ku mutane! Lalle ne mu, mun halitta ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da kabiloli, domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (Shi ne) wanda yake mafificinku a takawa. Lalle ne, Allah Masani ne, Mai kididdigewa".(Surar Hujurati, 49:13)
Dangane da aiki da kuma aikata kyawawan dabi'u, kuma Alkur'ani mai girma ya bayyana daukakan Musulunci da kuma daidaitawarsa ga ma'aikata. Hakika hakan wani abu ne da kasashen Turai suka gagara tabbatar da shi. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan kwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhali kuwa yana mumini, to wadannan suna shiga aljanna kuma ba za a zalunce su da gwargwadon hancin dabino ba". (Surar Nisa'i, 4: 124)
(Wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko kuwa mace, alhali yana mumini, to hakika, Muna rayar da shi, rayuwa mai dadi. Kuma hakika, Muna saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa). (Surar Nahali, 16: 97)
A wata ayar kuma, Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawarin cewa:
"...lalle ne Ni, ba zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sashenku daga sashe....". (Surar Ali Imrana, 3:195)


1. Nahjul Balagah, huduba ta 192.
2. Bihar al-Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 79, shafi na 64, Ibn Dawud, Tirmizi, Nisa'i, Bukhari da Ibn Majah duk sun ruwaito shi.
3. Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 74.
4. Kamar na sama, shafi na 82.
5. 1- Mishkat al-Anwar, shafi na 155.
6. 2- Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 63. 3- Kamar na sama, juzu'i na 1, shafi na 163.
7. Wasa'il al-Shi'ah, juzu'i na 9, shafi na 63. Ayar kuma ta na cikin Surar Nur ne aya ta 30.
8. Sahih Bukhari, juzu'i na 7-9, shafi na 63.
9. Mishkat al-Anwar, shafi na 236.
10. Al-Targib wa al-Tarhib min Hadith al-Sharif, juzu'i na 3.
11. 2- Kamar na sama, shafi na 35.
12. Tuhaf al-Ukul an Aali al-Rasul na al-Harrani, shafi na 23.
13. Al-Targib wa al-Tarhib, juzu'i na 3, shafi na 46.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+2 =