Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

HADIN KAI A MUSULUNCI


Muhammad Riza Muzaffar

Hafiz Muhammad Sa’id

An san Ahlul Baiti (AS) da kwadayinsu a kan wanzuwar addinin musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hada kan mabiyansa, da kiyaye ‘yan’uwantaka a tsakaninsu, da cire mugun kuduri daga zukatansu, da kullace-kullace daga rayukansu, ba za a mance da matakin Amirul Muminin Aliyyu dan Abi Dalib (AS) game da halifofin da suka gabace shi ba, duk da fushin da ya yi da su da kuma yakininsa da kwacewarsu ga hakkinsa, amma sai ya tafi tare da su, ya zauna lafiya da su, kai an boye ra’ayinsa na cewa shi ne wanda aka yi wasiyya da halifancinsa, har ya zama bai bayyana nassin ba a bainar jama’a har sai da al’amarin ya koma hannunsa, sannan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al’amarin nassin Al-Ghadir a ranar Rahba da ta shahara. Ya kasance ba ya boye shawara garesu game da abin da ya shafi musulmi ko musulunci na amfani da maslaha, saudayawa yana fada game da wannan al’amari: “Sai na ji tsoron idan ban taimaki musulunci da ma’abotansa ba zan ga gibi a cikinsa ko rushewa”.
Kamar yadda babu wani abu da ya taba zowa daga gareshi wanda zai yi tasiri a karfafa mulkinsu, ko raunana jagorancnsu, ko rage kwarjininsu, sai ya kuntata wa kansa, ya zauna a gida duk da abin da yake gani daga gare su. Dukkan wannan saboda kiyaye maslahar musulunci ta gaba daya, da kiyaye kada a ga wani gibi a musulunci ko rushewa, har aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar dan Haddabi ya kasance yana fada yana kuma maimaitawa: “Kada na kasance cikin wani al’amari mai wuyar sha’ani da Abul Hasan ba ya ciki.” Ko fadinsa: “Ba don Ali (A.S) ba da Umar ya halaka”.
Haka nan ba za a mance da matakin Imam Hasan dan Ali (AS) ba dangane da yin Sulhu da Mu’awiya, bayan ya ga cewa dagewa a kan yaki zai shafe ya kuma kawar da Alkawari mafi girma –Kur’ani- da adalci har ma da musulunci daga samuwa har zuwa karshen zamani, a kuma shafe shari’ar Ubangiji, a kuma gama da wadanda suka yi saura daga Zuriyar Manzo daga Ahlul Baiti, sai ya fifita kiyaye zahirin musulunci da sunan Addini, duk da ya yi sulhu da Mu’awiya babban makiyin Addini da ma’abotansa, mai husuma mai mugun kuduri ga imam Hasan (A.S) da shi’arsa, tare da abin da ake tsammani na faruwar zalunci da kaskanci gareshi shi da mabiyansa, ga kuma takubban Banu Hashim da na shi’arsa a zazzare ba sa son komawa ba tare da sun yi aikinsu na kariya da gwabzawa ba, sai dai maslahar musulunci madaukakiya ita ce ta fi dukkan wadannan al’amuran.
Amma Shahidi Imam Husain (AS) idan ya motsa to domin ya ga cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki, Banu Umayya ba su sami wanda zai tona asirinsu ba, to da sannu zasu shafe sunan Musulunci, su kawar da darajarsa, sai ya so ya tabbatar wa tarihi ketare iyakarsu, ya fallasa abin da suke kulla wa Shari’ar Manzon Allah (S.A.W). Ba don yunkurinsa mai albarka ba, da Musulunci ya zama wani labari ne da tarihi zai rika ambatonsa tamkar wani addinin barna. Kwadayin Shi’a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban- daban ya zamanto saboda kammala sakon da yunkurinsa na dauki-ba-dadi da zalunci ne, kuma domin raya al’amarinsa na cika umarni da biyayya ga Imamai (A.S) [1].
A nan kwadayin Ahlul Baiti (A.S) na wanzuwar izzar musulunci zata bayyana garemu koda kuwa mai mulki ya kasance mafi tsananin makiyansu ne a matakin Imam Zainul Abidin (A.S) da sarakunan Banu umayya alhalin sun maraita shi, an keta alfarmarsa a lokacinsu, kuma yana mai yawan bakin cikin a kan abin da suka yi wa babansa da Ahlin gidansa a waki’ar karbala, amma duk da haka yana yi wa rundunar musulmi addu’a da nasara, musulunci kuma da izza, musulmi kuma da yalwa da aminci, kuma ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi Shi ne addu’a, ya koya wa Shi’a yadda zasu yi addu’a ga sojojin Musulunci da musulmi, kamar addu’arsa da aka sani da “Addu’ar masu dakon iyaka” wacce yake cewa a cikinta: Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad, ka yawaitasu, ka kaifafa makamansu, ka kare matattararsu, ka kange iyakarsu, ka hada taronsu, ka shirya al’amarinsu, ka kadaita da wadatar da bukatunsu, ka karfafa su da cin nasara, ka taimake su da hakuri”. Zuwa inda yake cewa: “Ya Allah ka karfafa guraren Musulunci da haka, ka kiyaye gidajensu da shi, ka yawaita dukiyarsu da shi, ka shagaltar da su gabarin yakarsu don su dukufa ga ibadarka, da hana kai musu farmaki don su kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a bayan kasa sai kai, kuma ba a sanya wa goshi kasa saboda wani sai kai.” Haka nan ya ci gaba da addu’arsa mai fasaha, -kuma tana daga mafi tsawon addu’o’insa- wajen fuskantar da sojojin musulmi zuwa ga abin da ya kamace su na daga kyawawan dabi’u, da kuma shirya kansu, da tanadi a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki na jihadin Musulunci da bayanin manufarsa da fa’idarsa, kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin gargadi da takatsantsan dangane da makiyansu, da abin da ya wajaba su yi riko da shi a mu’amalarsu da kariyar kansu, da kuma abin da ya wajaba a kansu game da yankewa daga komai zuwa ga Allah baki daya, da nisantar abubuwan da ya haramta, da yin abu saboda girman zatinsa.
Haka nan sauran imamai (A.S) a matakansu da suka dauka game da sarakunan lokutansu, duk da sun sami takurawa daga garesu iri-iri, da kuma azabtar da su da dukkan nau’i na kekasar zuciya da tsanantawa, domin su yayin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo hannunsu ba, sai suka juya zuwa ga koya wa mutane al’amuran Addininsu, suna fuskantar da mabiyansu fuskantarwa ta addini madaukaki. Dukkan wani yunkuri da ya faru a zamaninsu daga bangaren Alawiyyawa da wasunsu, bai kasance da ishararsu da son su ba, ya ma saba wa umarninsu da karfafawarsu ne a fili, duk da cewa sun fi kowa kwadayin kafa hukumar musulunci hatta sun fi Abbasawa son haka su kansu.
Ya isa garemu mu karanta wasiyyar Imam Musa Alkazim (AS) ga shi’arsa: “Kada ku kaskantar da kawukanku da barin biyyyar shugabanku, idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah wanzuwarsa, idan kuwa ya kasance azzalumi to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma shugaba adali yana matsayin uba mai rahama ne, ku so masa abin da kuke so wa kanku, kuma ku ki masa abin da kuke ki wa kanku”[2].
Wannan ita ce matukar abin da ake siffantawa na kiyayewar al’umma ga amincin shugaba da su so masa abin da suke so wa kansu, su ki masa abin da suke ki wa kansu.
Bayan duk wannan muna cewa: Alhakin shi’a da wasu marubuta na wannan zamani suke dauka ya girmama! Yayin da suke siffanta shi’a da cewa ita kungiya ce ta asiri mai barna, ko kuma wata jama’a ce ta ‘yan juyin juya hali. Haka nan cewa wajibi ne a kan mabiyin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ya ki zalunci, da azzalumai, da fasikai, ya yi duba zuwa ga mataimakansu duba na kyama, da rashin yarda, da wulakanci, wannan dabi’a ba ta gushe ba suna gadonta jikoki da ‘ya’ya, amma sam ba ya daga dabi’arsu su yi yaudara ko cin amana, kuma ba tafarkinsu ba ne yin juyin juya hali, ko su yi tawaye a kan jagorancin da yake an kafa shi da sunan musulunci, ko a boye ko a sarari.
Kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko afka wa musulmi ko wace irin Mazhaba ko Darika yake bi, wannan kuwa domin rikonsu ne da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), kuma duk musulmin da ya yi kalmar shahada biyu a wajansu, dukiyarsa da jininsa kubutattu ne, kuma cin mutuncinsa haramun ne; “Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai da son ransa”. Musulmi dan’uwan musulmi ne, kuma yana da hakkoki a kansa kamar yadda bahasi mai zuwa zai yi bayani”.

Hakkin Musulmi A Kan Musulmi

Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne ‘Yan’uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci.
Domin mafi karancin koyarwar wannan ‘yanuwatakar ita ce “Ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S).
Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi’a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S), zaka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi’a ta so wa dayansu dan’uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai.
Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma’anar hakkin ‘yan’uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga ‘yan Adam sun zama ‘yan’uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa’adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko ‘yan sanda, ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi, kuma da ba su rusuna wa ‘yan mulkin mallaka ba, kuma da dagutai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni’ima kuma gidan sa’ada.
Bugu da karin cewa, da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar ‘yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar ‘yan’uwantaka, to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma’anar cewa, ba zamu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri, da aminci, da sa’ada, da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya, kamar da, da dan’uwa, sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba.
Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa da kuma abin da ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa, sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa, ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so, ya yi fansa da shi saboda son wani.
Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su, su ne, ya kasance yana jin hakkin ‘yan’uwantaka ga sauran mutane, idan kuwa ya kasa wannan, to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci, da kyautata biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T), kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisin imam (A.S) mai zuwa. Saudayawa sha’awar mutum takan yi galaba a kansa, sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne, ransa ta yarda da akidar adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha’awarsa.
Saboda haka ne ma kiyaye hakkin ‘yan’uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan babu imani na gaskiya game da ‘yan’uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yi wa sahabinsa “Almu’ula Bn Khunais” bayanin dalla-dallan tambayarsa game da hakkin ‘yan’uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa, domin tsoron kada ya koyi abin da ba zai iya aiki da shi ba.
Sai Mu’ula ya ce [3]: Menene hakkin musulmi a kan musulmi?
Sai Abu Abdullahi ya ce: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.
Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?
Sai ya ce: Ya Mu’ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba zaka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba zaka aikata ba.
Na ce: Babu karfi sai da Allah.
Yayin nan sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: “Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan’uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka”.
SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a gare mu yau mu musulmi? Kaicon fuskokin da suke da’awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.
Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:
l- Ka so wa dan’uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.
2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, ka kuma bi umarninsa.
3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.
4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.
5- Kada ka koshi, shi kuma yana cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.
6- In kana da mai hidima shi kuma dan’uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.
7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana’izarsa. Idan kuma ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ka, sai dai ka gaggauta masa.
Sannan ya rufe maganarsa da cewa: “Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa, kuma soyayyarsa da soyayyarka”.
Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma’anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S), wasunsu daga littafin Wasa’il a babobi daban-daban.
Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da ‘yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu’awiya Dan Wahab ya ce [4]:
Na ce masa [5]: Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu, da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al’amarinmu”.
Sai Ya ce: “Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu, suna halartar jana’izarsu, suna ba da shaida garesu da kuma a kansu, kuma suna bayar da amana garesu”.
Amma ‘yan’uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci, kuma kai ka riga ka ji wasu hadisai a fasalin bayanin sanin shi’a da ya gabata. Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin [6] da Abana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullahi (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.
Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?
Na ce: Na’am.
Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai?
Na ce: Na’am.
Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.
Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi?
Ya ce: Na’am.
Abana ya ce: Sai na tafi, bayan nan -wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kalle ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?
Na ce: Haka ne!
Ya ce: “Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
Na ce [7]: Hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen. Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin, sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.

Ma’anar Shi’anci Wurin Ahlul Baiti

Ahlul Baiti (AS) ba su da wata himma bayan sun debe tsammanin al’amarin al’umma ya dawo hannunsu sai gyara halin musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari kamar yadda Allah (S.W.T) yake so daga garesu. Don haka suka kasance tare da duk wanda yake bin su, kuma suka aminta da shi a kan sirrinsu, suna bayar da kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari’a, da cusa masa ilimin addini, da sanar da shi abin da yake nasa, da kuma wanda yake kansa.
Ba sa daukar mutum cewa mabiyinsu ne kuma shi’arsu sai idan ya kasance mai bin umarnin Allah, mai nisantar son zuciyarsa, mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu. Kuma ba sa ganin son su ya wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu suke raya wa kansu daga cikin masu holewa da bin sha’awece-sha’awece da son ransu wadanda ke neman hanyar fandare wa bin Allah. Imamai ba sa daukar sonsu da biyayya garesu mai tseratarwa ne sai dai idan ta hadu da kyawawan ayyuka, kuma mabiyansu sun siffantu da gaskiya da rikon amana, da tsentseni da tsoron Allah.
“Ya Khaisama! ka isar daga garemu cewa ba zamu wadatar da su daga komai ba sai da aiki, kuma ba zasu samu soyayyarmu ba sai da tsentseni, kuma mafi tsananin hasarar mutane ranar alkiyama shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa ga waninsa” [8].
Su suna son mabiyansu su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya ne, masu shiryarwa zuwa ga alheri da shiriya, kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga gare ku” [9].
A yanzu zamu kawo maka wasu muhawarori da suka gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san matukar tsanantawarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi’un mutane:
1- Muhawarar Abu Ja’afar Bakir (AS) shi da Jabir Ju’ufi [10]: “Ya Jabir! Ashe ya isa ga wanda ya siffantu da cewa shi shi’a ne ya yi da’awar yana son mu? Wallahi! Ba kowa ne shi’armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shi”.
“Su ba a gane su sai da kaskan da kai, da tsoron Allah, da rikon amana, da yawan zikiri, da azumi, da salla, da bin iyaye, da taimakon makwabta na daga fakirai, da mabarata, da masu bashi, da marayu, da gaskiyar magana, da karatun Kur’ani, da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma su ne aminan jama’arsu a kan al’amura. Ku ji tsoron Allah ku yi aiki saboda abin da Allah ya tanada, kuma babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, kuma mafi soyuwar bayi a wajan Allah wanda suka fi jin tsoronsa suka fi biyayya gareshi. Ya Jabir! Wallahi ba mu kusanta zuwa ga Allah sai dai da da’a, kuma babu kubuta daga wuta a gare mu, kuma babu wani mai hujja a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gunmu, kuma ba a samun soyayyarmu sai da aiki da tsentseni.
2- Tattaunawar Abu Ja’afar (AS) da Sa’id Bn Hasan [11]:
Abu Ja’afar (AS) “ Shin dayanku zai zo ga dan’uwansa ya sanya hannunsa a jakarsa ya dauki abin da yake so bai cire shi ba?
Sa’id: Ban san da haka ba a cikinmu.
Abu Ja’afar (AS): To Babu komai kenan.
Sa’id: To halaka ke nan.
Abu Ja’afar (AS): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna.
3- Muhawar Imam Sadik (A.S) da Abu Sabah Alkinani [12].
Alkinani: Muna shan wahalar mutane game da ku.
Abu Abdullah: Menene abin da kuke gamuwa da shi daga mutane?.
Alkinani: Magana ba ta gushewa tsakaninmu da mutun, sai ya ce: Wannan Dan Ja’afariyya ne mugu.
Abu Abdullahi: Mutane suna aibata ku da ni?
Alkinani: E mana.
Abu Abdullah: Wallahi karancin mai bin Ja’afar a cikinku ya yawaita! Kadai sahabbaina shi ne wanda tsantseninsa ya tsananta, ya yi aiki don mahaliccinsa ya kaunaci ladansa, wadannan su ne sahabbaina!
4- Abu Abdullahi (AS) yana da wasu maganganu game da wannan al’amari da zamu kawo wasu kamar haka:
A- “Baya daga cikinmu sam, wanda ya kasance a wani gari da a cikinsa akwai mutane dubu dari ko fiye da haka, ya zama a cikin garin akwai wanda ya fi shi tsantseni”.
B- “Mu ba ma kirga mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukan umarninmu yana mai nufi, ku sani daga cikin bin umarninmu da nufinsa akwai tsentseni, don haka ku yi ado da shi Allah ya yi muku rahama”.
C- “Wanda mata masu tsari ba sa magana game da tsantsaninsa ba ya daga cikin shi’armu, haka nan wanda ya kasance a cikin wata alkarya mai mutane dubu goma, a cikinsu akwai wata halitta ta Allah da ta fi shi tsentseni, shi ba ya daga cikin masoyanmu”.
D- “Kadai shi’ar -Ja’afar- shi ne wanda ya kame cikinsa da farjinsa, kokarinsa ya tsananta, kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa, ya kaunaci ladansa, ya ji tsoron azabarsa, to idan ka ga wadannan to wadannan su ne shi’ar Ja’afar.

Hukuncin Zalunci

Ketare haddin wani da zaluntar mutane suna daga cikin mafi girman abubuwn da Imamai (AS) suke girmama muninsa, wannan kuma bi ne ga abin da Kur’ani ya zo da shi na daga tsoratarwa game da zalunci da munana shi, kamar fadinsa madaukaki: “Kada ka tsammaci Allah mai sha’afa ne game da abin da azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta musu ne saboda ranar da idanuwa zasu zazzaro”. (Surar Ibrahim: 42)
Hakika abin da yake kai matukar bayyana munin zalunci da kyamarsa ya zo a maganganun Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (AS), kamar fadinsa shi mai gaskiya ne abin gaskatawa, a Nahjul balaga huduba ta 219: “Wallahi idan da za a ba ni Sammai bakwai da kuma abin da yake kasan falakinta, a kan in saba wa Allah game da tururuwa da in kwace mata Sha’irin da ta jawo, ba zan aikata ba”. Wannan shi ne matukar abin da mutum zai iya surantawa game da kame kai da tsoratarwa daga zalunci da kyamar yinsa.
Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan kwayar sha’ir koda kuwa an ba shi sammai bakwai, to yaya halin wanda yake zubar da jinin musulmi, yake handame dukiyoyin mutane, yake cin mutuncinsu? Yaya za a auna tsakaninsa da aikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayinsa da iliminsa (AS)? Wannan ita ce tarbiyyantarwar Ubangiji da addini yake bukatar ta daga kowane mutum.
Na’am, hakika zalunci yana daga mafi girman abubuwan da Allah ya haramta, saboda haka ne zarginsa ya zama abu na farko da ya zo a hadisan Ahlul Baiti da addu’o’insu, da kuma nesantar da mabiyansu daga gare shi.
Wannan ita ce siyasarsu, kuma a kanta suke mu’amala hatta da wanda yake yi musu shisshigi yake rashin kunyar hawa matsayinsu. Kissar imam Hasan (AS) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuma ya tausaya masa ya kuma tausasa masa, har sai da shi ya ji kunyar mummunan abin da ya aikata. Kuma ka riga ka karanta abin da ya gabata a addu’ar shugaban masu sujjada na daga ladubba madaukaka game da afuwa ga masu ketare iyaka, da nema musu gafara. Wannan kuma shi ne matukar daukakar ran mutum da kamalar mutumtakarsa, duk da kuwa ketare haddin azzalumi kwatankwacin yadda ya ketara ya halatta a shari’a, kamar yadda yin addu’a a kansa ya halatta, sai dai halacci wani abu ne, afuwa kuma wacce take daga kyawawan dabi’u wata aba ce daban, kai gun imamai shige gona da iri wajan yin addu’a a kan azzalumi ana kirga shi zalunci.
Imam Sadik (A.S) ya ce: “Bawa yana kasancewa abin zalunta, ba zai gushe ba yana ta yin addu’a har sai ya zamanto azzalumin”. Idan wannan shi ne halin wanda aka zalunta to yaya halin wanda ya fara zalunci da ketare iyakar tun karon farko yake kuma cin mutuncinsu, yana kwashe dukiyarsu, yana munafuncinsu gun azzalumai, ko yake yaudarar su, yana jefa su cikin halaka, ko ya cutar da su, ko ya yi leken asiri a kansu!? Irin wadannan a wajan Ahlul Baiti (AS) su ne mafi nisantar mutane a wajan Allah, mafi tasananinsu sabo da azaba, mafi muninsu ayyuka da dabi’u.

Taimakekeniya Da Azzalumai

Yana daga abin da yake nuna girman zalunci da munin karshensa cewa, Allah (S.W.T) ya hana taimakekeniya da azzalumai, da kuma karkata zuwa gare su. “Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wasu masoya koma bayan Allah, sannan ba za a taimake ku”. Hudu: 113. Wannan shi ne ladabin Kur’ani da Ahlul Baiti (AS). Hakika hadisai da dama sun zo daga garesu wadanda suka kai matuka wajan hana karkata zuwa ga azzalumai, da alaka da su, da yin aiki tare da su a cikin kowane irin aiki, da taimaka musu ko da tsagin dibino ne.
Babu shakka mafi girman abin da aka jarrabci musulmi da musulunci da shi, shi ne sassauci ga azzalumai, da kawar da kai game da miyagun ayyukansa, da mu’amala tare da su, ballantana taimaka musu a kan zaluncinsu. Ba abin da ya jawo wa al’ummar musulmi bala’o’i sai karkacewa daga tafarki madaidaci da gaskiya, har Addini ya yi rauni tare da shudewar zamani, karfinsu ya tafi, ya kai halin da yake a yau ya koma bako. Musulmi ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani mataimaki ban da Allah, kuma su ba za a taimake su ba hatta a kan mafi raunin makiyansu, da mafi kaskancin masu tsaurin ido a kansu kamar Yahudawa kaskantattu, balle kuma Kiristoci masu karfi.
Imamai (AS) sun wahala wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, suka kuma tsananta wa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abota zalunci da cudanya da su, kuma hadisansu a game da wannan babin ba zasu kirgu ba, daga ciki akwai abin da Imam Zainul Abidin (AS) ya rubuta zuwa ga Muhammad Bn Muslim Azzuhuri, bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai a kan zaluncinsu da fadinsa: “Shin a kiran su gareka yayin da suka kira ka ba su sanya ka kan dutsin nika da suke juya nikan zaluncinsu da kai ba, kuma gada da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’o’insu ba, da tsani na bi zuwa ga batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malamai, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu na musamman da mafiya karfin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen gyara barnarsu, da kaikawon kebatattun mutane da saura jama’a zuwa garesu, abin da suka ba ka ya yi matukar karanta a maimakon abin da suka karba daga gareka da ya yi matukar girmama! Abin da suka gina maka ya yi matukar kankanta a maimakon abin da suka rusa maka da ya girmama! Ka duba kanka domin ba mai duban ta sai kai, ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya” [13].
Wannan kalma ta “Ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”. ta girmama! Yayin da son rai ya yi rinjaye a kan mutum sai ya wulakanta sirrin samuwarsa da karamarsa, kuma ba zai samu wani mai daukar nauyin aikinsa ba, ya wulakanta abin da yake yi na ayyuka, ya raya cewa ba shi ne zai yi wa kansa hisabi a kan abin da yake yi ba na zunubi, wannan kuwa yana daga sirrorin ran mutum mai umarni da mummuna, sai Imam (A.S) ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirrin na rai da yake boye a cikinta, domin kada wahami ya yi galaba a kansa, sai ya yi sakaci da nauyin da yake kansa.
Mafi isa matuka daga wannan a suranta haramcin taimakekeniya da azzalumai shi ne maganar Safwan Jammal tare da Imam Musa Kazim (AS), wanda ya kasance daga cikin shi’ar Imam din, kuma daga masu rawaito hadisinsa amintattu (kamar yaddda ya zo a littafin Rijal na Alkashi game da Safwan) ya ce: “Na shiga wajansa.
Sai ya ce da ni: Ya Safwan duk wani abu daga gareka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu daya.
Na ce: A sanya ni fansa gare ka! Wane abu ne?
Ya ce: Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Harunar Rashid.
Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai ashararanci, ko dagawa, ko don farauta, ko wasa ba, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato hanyar Makka, kuma ba na aikin da kaina, sai dai ina tura shi da bayina.
Ya ce: Ya Safwan kudin hayarka yana zama bashi a kansu?
Na ce: Na’am, a sanya ni fansa gareka.
Ya ce: Shin kana so su wanzu har su biya ka kudin hayarka?
Na ce: Na’am.
Ya ce: To duk wanda ya so wanzuwarsu yana cikinsu, duk wanda ya kasance daga cikinsu shi mai shiga wuta ne.
Safwan ya ce: Sai na tafi na sayar da rakumana baki daya.
Idan son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu ya kai wannan matsayi, to ina ga wanda suke hada kai da shi a kan zalunci ko kuma yake karfafa su a zalunci, ina ga wanda ya shiga cikin jama’arsu ko yake aiki irin nasu, ko yake bin tawagarsu ko kuma yake bin umarninsu?.

Aiki A Hukuma Azzaluma

Idan har taimakar azzalumai koda da rabin dabino ne, kai hatta ma son wanzuwarsu suna daga mafi tsananin abubuwa da lmamai (AS) suka yi gargadi game da su, to menene hukuncin tarayya da su a cikin hukunci da shiga cikin ayyukansu da rikon ofisoshinsu. Menene kuma hukuncin wadanda suke daga wadanda suka assasa daularsu, ko kuma ya zama cikin rukunan shugabacinsu masu dulmuya cikin karfafa hukumarsu, (domin karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta, da raya barna dukkaninta, da bayyana zalunci da fasadi) kamar yadda ya zo a Hadisi a “Tuhaful Uku1” daga Imam Sadik (AS).
Sai dai kuma halaccin aiki a karkashin azzalumi ya zo daga gare su (AS) idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna. Ya zo a ruwaya cewa “Allah yana da wadanda ya haskaka hujjoji da su, ya ba su iko a kasashe a kofofin azzalumai, da su ne yake kare waliyyanSa, ya kuma gyara al’amuran musulmi da su, wadannan su ne muminai na hakika, su ne manarorin Allah a bayan kasa, su hasken Allah ne a cikin bayinsa”. Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Imam Musa Bin Ja’afar (AS). A wannan Babin akwai hadisai da dama da suke bayyana tafarkin da ya kamata masu rike ofis da ma’aikata su gudanar da ayyukansu a kai, kamar abin da ya zo a wasikar Imam Sadik (AS) zuwa ga Najjashi Shugaban Ahwaz [14].


1. Sun kasance suna cewa Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al’amarinmu.
2. Alwasa’il, Kitabul amri bil ma’arufi wan nahayi anil munkari: Babi 17.
3. Alwasa’il, Kitabul hajji, Abwabu ahkamul ushura, Babi 122, hadisi 7.
4. Usulul Kafi, Kitabul ushura, Babi na farko.
5. Wato yana nufin Imam Assadik (A.S).
6. Alwasa’il kitabul hajji, Abwabul ushura: babi 122, hadisi 16.
7. In ji fawallafin littafin.
8. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu ziyaratul ikhwan.
9. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.
10. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babut ta’a wat taqawa.
11. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu Hakkil mu’umini ala akhih.
12. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.
13. Tuhaful Ukul: sh, 66.
14. Al- Wasa’il Kitabul Bai’i Babi na 78.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+4 =