Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

AHLULBAITI (A.S.) CIKIN SUNNAR ANNABI


Mu'assasar Al-Balagh


Dukkan wanda ya bibiyi sunnar Manzon Allah (s) da tarihinsa na aikace da kuma alakarsa da mutanen gidansa wadanda nassin Alkur'ani ya kawo, sannan shi (Manzo) kuma ayyanasu (Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu), zai san cewa mutanen wannan gida suna da wata rawar da za su taka a bangaren nauyin rike sako da kuma wayewar wannan al'umma. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mai tsare-tsare domin al'ummar tasa da kuma shirya da ita domin ta karbi wannan ni'ima ta Ahlulbaiti (a.s), da umarnin Allah (S.W.T.).
Hakika wannan yanki mai haske na tsare-tsaren Annabi (s.a.w.a), wadanda ya yi da umurnin Allah, ya soma ne da aurar da Fadima (a.s.) ga Imam Ali (a.s.), da dasa wannan itaciya mai albarka, domin rassanta su mamaye sansanin wannan al'umma, tsawon rayuwarta.
An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) yayin da ya aurar masa da Fadima (a.s.) cewa:
"Lalle Allah Madaukakin Sarki Ya umurce ni da in aurar maka da Fadima bisa sadaki gwargwadon nauyin miskalin azurfa dari hudu, shin ka yarda da hakan". Sai Aliyu (a.s.) ya ce: "Lalle na yarda da hakan, Ya Manzon Allah". Anas bin Malik ya ce: Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Allah Ya hada kanku, Ya arzurta kokarinku, Ya albakace ku, Ya kuma fitar da zuriya mai albarka". Sai Anas ya ce: "Wallahi, hakika kuwa Allah Ya fitar da zuriya mai albarka daga gare su" [1].
An ruwaito cewa yayin da Annabi (s.a.w.a) ya aurar da Fadima ga Aliyu (a.s.), sai ya shiga wajenta ya kira ta sai Ummu Aiman ta kawo kasko da ruwa a ciki, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi tofi a ciki sannan ya yayyafa a kanta da tsakanin nononta, sannan ya ce:
"Ya Allah! Ni ina nema mata tsarinKa da zuriyarta daga shaidan jefaffe". Sai kuma ya ce wa Ali (a.s.): "Miko min ruwa", sai Aliyu (a.s.) ya kawo masa, sai ya zuba a kansa da kuma tsakanin kafadunsa (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ina nema masa tsarinKa da zuriyarsa daga shaidan jefaffe".
A wata ruwayar kuma cewa aka yi, sai ya bukaci a kawo masa ruwa, bayan ya yi alwala da shi sai ya zuba a kan Aliyu da Fadima (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ka albarkace su cikin zuriyarsu [2]".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana neman uzuri ga duk wani daga cikin sahabbai da ya zo neman a ba shi Fadima (a.s.), yana mai cewa:
"Hukumci bai sauko ba tukunna [3]".
Hakika wannan kula ta Ubangiji da AnnabinSa ta aurar da Fadima (a.s.) ga Aliyu (a.s.) ta sanya aurar da ita bai faru ba face da umurni daga Allah (S.W.T.) domin wannan ya yi nuni ga matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kuma alherin al'umma da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake nufi da alakarsa da su. Wannan matsayi na su kuwa shi ne Alkur'ani mai girma ya fassara, haka nan ma sunnar Annabi (s.a.w.a) mai daraja.
Watakila hasken da muke tsinkaya daga ruwayoyi da hadisai Manzon Allah (s.a.w.a.) da Ahlulbaiti (a.s) (wadanda kuwa masu yawa ne) suna riskar da mu ne irin zurfaffar kula ta Allah da ManzonSa (s.a.w.a) wajen gina wannan gida, da yawaita soyayya da albarka da kula gare shi. Domin mutanen wannan gida su zama ja-gororin al'umma cikin rayuwarsu da kuma hanyoyin tsirarsu daga bala'u da kuma kasancewa tsari da makoma ta hadin kanta yayin da ta rarraba, kamar yadda ruwayoyi da hadisai suka yi nuni da hakan.
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana danganta zuriyar Aliyu da Fadima (a.s.) da kansa, yana cewa: "Lalle su zuriyata ne 'ya'ya ne, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana hakan da cewa:

(فَمَنْ حاجَّكَ فيهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءكَ ك مِنَ الْعِلْمِ فَقُل تَعالَوا نَدْعُ أبْنَاءَنَا وأبْنَاءَكُمْ ونِسَاءَنَا ونِسَاءَكُمْ وأَنْفُسَنَا أنْفُسَكُمْ )

"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku". (Surar Ali Imrana, 3: 61)
Abin nufi da 'ya'yansa a wannan aya su ne Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda maganganun malaman tafsiri da ma'abuta tarihi suka sanar da mu.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karfafa wannan ma'anar wa al'ummarsa sau da yawa, bari mu ambaci kadan daga cikinsu. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Allah Ya sanya zuriyar kowane Annabi daga tsatsonsa, (ni kuma) Ya sanya zuriyata cikin tsatson wannan", yana nufin Aliyu (a.s.) [4].
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana rungumar Hasan da Husaini (a.s.), yana cewa:
"Dukkan 'ya'yan wani uba dangantakarsu ta ubansu ce, ban da 'ya'yan Fadima, ni ne ubansu, da ni ake dangantasu". Imam Ahmad ya fito da wannan hadisin cikin al-Manakib [5].
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) yana karfafa matsa-yin Ahlulbaiti (a.s) a kowani muhimmin lokaci, domin al'umma ta koma gare su, ta lizimci tafarkinsu, ta kuma yi riko da soyayyarsu. A ruwayoyi da dama, muna samun cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya nuna mana su a matsayin tudun tsira ga wannan al'umma, yana gwama su da Alkur'ani, yana kuma sanya rawar da za su taka a fagen akida da rike sakon Musulunci, mai lizimtar Littafin Allah ne, ba sa rabuwa da shi. Hakan kuwa don al'umma ta fuskanto su wajen fahimtar Alkur'ani mai girma, da ciro ma'anoninsa da hukumce-hukumcensa.
Littattafan hadisi da tarihi sun taru bisa kawo hadisin Annabi (s.a.w.a) da ake kira da Hadisin Nauyaya Biyu (Hadith al-Thakalain). Musulmi sun ruwaito wannan hadisi duk da bambance-bambancen mazhabobinsu na siyasa da fikihu. Za mu ambace shi a nan tare da sashin isnadinsa (maruwaitan da suka ruwaito shi), kamar yadda masu ruwaya da malaman hadisi suka nakalto.


1. Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30.
2. Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Abdullah bn Muhammad bn Amir al-Shabrawi al-Shafi'i, shafi na 21.
3. Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30.
4. Zakha'irul Ukba na Dabari, shafi na 67.
5. Dabari ya ruwaito wannan hadisi da dan bambancin lafazi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 24, haka nan cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 220, Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 121, da Suyudi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 29, da wannan lafazi" "Dabarani ya fitar da shi daga Umar, cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Dukkan wani mutum, to danganta-karsa tana komawa ne ga mahaifinsa, in ban da 'ya'yan Fadima, don dangantakarsu tana komawa ne gare ni, ni ne mahaifinsu".Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+2 =