Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

DANDALIN MATASA (2)


Mu'assasar Al-Balagh


5- Lafiya...Kaddara Ce Da Ba 'a Kwatanta ta Da Dukiya...

Ya zo cikin hadisi cewa wajibi ne mu ribanci abubuwa biyar kafin faruwar wasu abubuwan biyar:
Samartaka kafin tsufa, faraga kafin ayyuka su yi yawa, karfi kafin rauni, rashin lafiya kafin ciwo...
Ya rage mana mu dakata mu dan yi tunani kan wannan dukiya da Allah Ya arzurtamu da ita...yaya za mu yi idan muka rasa ta ba tare da mun shirya ba...
Da dama daga cikin marasa lafiya sukan yi burin ina ma da suna da lafiya, don su ci gaba da ayyukansu na rayuwa...
Hakika lafiya kaddara ce wacce dole ne mu kula da kuma kare ta ta hanyar ba ta abincin da ya dace, tsabta da kuma wasannin motsa jiki...sannan kuma dole ne mu ba da muhimmanci ga daya bangaren kiwon lafiyan, shi ne kuwa tsabtace kawukanmu daga munanan ayyuka, keta, hassada, kiyayya da kuma canza su da kyawawan ayyuka, kamar yadda muke kula da tsabtar jikinmu.
Bayan samuwar wadannan kaddarorin, shin a matsayina na matashi zan ji cewa ni fakiri, marar abin hannu ne, musamman ma cewa wadannan ni'imomi ba wai sun kare a kan ni'imomin da na hadu da wanina a kansu ba ne, a'a akwai wadansu ni'imomin da suka kebanta da ni kawai. Don ko wane mutum akwai ni'imomin da ya kebantu da su shi kadai...ba abin da ya rage masa face kawai ya yi amfani da kuma daukaka su kamar yadda dan kasuwa yake amfani da uwar kudinsa wajen nemo riba da hada su da uwar kudin nasa don ya ci gaba da jujjuya su...
Bayan dukkan hakan, akwai wadansu ni'imomin da muna iya sanya su cikin rayuwarmu, kuma su haifar mana da canje-canje masu girman gaske cikin rayuwarmu sannan kuma su sanya mu mu zamanto masu iya kirkiro muhimman ayyuka da za su kai mu ga manufofi da kuma hadafofinmu na rayuwa. Wadannan ni'imomi kuwa suna nan a cikin rayuwarmu, musamman ma a shekarun samartaka, da za su iya tabbatar mana da wadansu abubuwan da ba za mu taba tunanin afkuwarsu ba...daga cikinsu, akwai:

1- Kirkira: ita ce karfi, shiri da kuma iyawan da mutum yakan samu ta hanyar hankali, ilimin da kuma masaniyar da yake da shi...
Kirkira tana daga cikin sirrorin da suke haifar da daukaka a rayuwa, kuma takan sa ma'abucinta ya sami daman gano sabbin hanyoyin canza duniya da kuma tsira daga rashin ci gaba...
Idan har muna son binciko irin wadannan iyawa a cikin rayuwarmu, dole ne mu sanya wadansu alamomi a gabanmu, mu bi hanyar kirkira tare da su. Wadannan alamomi kuwa su ne:
• Karfafa riyawa da ji a jiki.
• Karkatar da ji-a-jika zuwa ga kyawawan manufofi.
• Raya tunani, wayewa da kuma masaniya.
• Saukaka rayuwa da rashin kuntata wa kai.
• Haifar da tsari ga abubuwa marasa tsarin.
• Haifar da sabbin abubuwa a ko da yaushe.
• Mu so kanmu da sauran mutane, to amma son namu ya kasance fiye ga Mahalicci.
• Mu yi abokantaka da ma'abuta kirkira.
• Mu dinga karanta littattafa, labarai da wakokin da za su sanya mana tunanin kirkiran abubuwa, ba mu kasance masu koyi ba.

2- Imani: Karfi ne mai girman gaske wanda muke samunsa ta hanyar ingantacciyar akida da yarda da Mahaliccin duniya kana kuma Mai jujjuya ta, bugu da kari kan ganin girma da kamalarSa cikin dukkan halittu, manya da kananansu da kuma jin rahamarSa wacce ta mamaye dukkan kome. Sannan kuma ta hanyar bauta maSa, wacce take kawata mutum da karfin ruhi, mutum yakan zama mai karfi da juriya yayin wahalhalu...
Imani ni'ima ce wacce matashi yakan same ta cikin sauki sama da waninsa saboda zuciyarsa a bude take wajen karbar yanayin rayuwa, shin wannan yanayi na madda (duniya) ne ko kuma na ma'anawiyya (na ruhi da lamurra lahira).

3- Madaukakiyar Himma: Wannan wata ni'ima ce da kuma karfi mai girman gaske da ke kai mutum zuwa ga manufarsa da kuma nesantar da shi daga fargaba da kuma yanke kauna.
An ruwaito wani hadisi yana cewa mutum yana tashi da himmarsa kamar yadda tsuntsu yake tashi da fuka-fukansa...don haka mutum yana bukatuwa da himma madaukakiya a hanyarsa ta isa ga sa'ada da kuma ci gaba...wannan hanya da take tabbatar masa da manufarsa ta rayuwa...
Lalle babu makawa muna iya isa ga wannan babbar ni'ima idan muka yi riko da wasu ka'idoji a rayuwarmu, su ne kuwa:
1. Mu dinga tuna cewa mu mutane ne kuma za mu iya kaiwa zuwa ga kamalar da muke so.
2. Mu daure taragonmu zuwa ga tauraro (sama), kamar yadda masu iya magana su kan ce wai: himma bata ga rago.
3. Kada mu shagaltar da kanmu da kananan al'amurra marasa muhimmanci.
4. Mu kyautata alakarmu da sauran mutane, kada mu bari maslaharmu ta kewaye mu.
5. Mu kasance masu kula da ka'ida hatta cikin zaben manufofi da hanyoyin da za mu isa gare su.
6. Mu ba da muhimmanci ga kyawun badini kamar yadda muke kula da kyawun zahiri.
7. Mu zabi abokai masu madaukakiyar himma.
Abubuwan da muka ambata a wannan fasali su ne mafi muhimmancin ni'ima da kyautar da muka mallaka mu matasa, ko kuma abubuwan da muke da damar samo su ta hanyar karfi da kuma shirin da muke da shi. Lalle ya kamata mu yi imani da cewa rayuwa da kuma Mahaliccinta Suna iya kara mana wadannan ni'imomi, matukar dai muka ci gaba da bincike da kuma bahasi, don kuwa ajiyoyin rayuwa ba sa da iyaka "...kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba...".

Ya Ya Za Mu Iya Guje Wa Sharrin Rayuwa?

Hakika dan'Adam ma'abucin manufa da sako ne, to amma abin tambaya a nan shi ne mene ne sakonsa a wannan duniya?
An halicci dan'Adam ne don neman alheri da kuma sa'ada a rayuwa, kana kuma ya guje wa sharrori da kuma abubuwan da za su kai shi zuwa ga halaka. Don haka cikin rayuwa akwai alheri da kuma sharri, dan'Adam shi ne mai zaba wa kansa abin da ya dace da shi na daga alheri da kuma nesantar abubuwan sharri wadanda ba su dace da shi ba.
Ya 'yan'uwa, idan da a ce wani mutumin da ba mu san shi ba zai ba mu abinci ko kuma halawa, shin za mu kama ci ko sha ne haka kawai daga ya ba mu, ko kuma za mu tsaya mu gani cewa wannan abinci ko kuma halawar suna da tsabta alal akalla?
Lalle mu mukan zabi tsabta cikin dukkan abin da za mu ci ko kuma za mu yi amfani da shi don kiyaye kanmu daga kwayoyin cutar da za su janyo mana cututtuka da kuma sanya lafiyarmu cikin hatsari. Don haka wajibi ne mu aikata haka ga munanan ayyukan da suke lalata mana dabi'u da kuma mutumci.
Sannan kuma a duk lokacin da mutum ya kamu da wata cuta yakan tafi wajen likita don neman maganin wannan cuta, sai dai kuma a wasu lokuta yakan kamu da cutar ruhi, to amma sai ya ki zuwa neman magani; don kuwa ba ya ganinta a fili, amma kuwa tana iya lalata masa al'amurra daga karshe.
Dukkanmu, baya ga jiki, muna da ruhi da kuma hankali, don haka mafi munin sharrin rayuwa shi ne abin da yake damun ruhinmu da kuma lalata mana tsare-tsarenmu mu na kyawawan halaye.
Wadannan tsare-tsare na kyawawan halaye su ne suke nuni da daukakar dan'Adam da kuma ruhinsa, don haka idan dan'Adam ya rasa wadannan tsare-tsare, to babu abin da ya saura masa in ban da kawai abubuwa marasa amfani a rayuwarsa kuma zai yi rayuwa ce irin ta dabbobi da tsirrai.
Siffofin daukaka da alheri sukan arzurta mutum da abubuwan da za su taimaka masa da kuma sanya shi ya zamanto mabubbugar alheri ga kansa da kuma sauran mutanen da yake tare da su.
Baya ga haka kuma, akwai wata hakikar, ita ce kuwa cewa, mutum a wannan rayuwa yana nan ne tsakanin tuddan alheri da kuma na sharri...don haka duk lokacin da ya kusanci tudun alheri, da hakan ne kuma zai nesanci tudun sharri...
Idan waninmu yana da wani aboki da yake sadaukar da kansa dominsa a duk lokacin da yake fuskantar wata matsala, to a hakikanin gaskiya babu yadda za a yi ya cuce shi ko kuma ha'ince shi...don haka sakamakon hakan shi ne son abokanmu da kuma fahimtar abubuwan da suke kewaye da mu.
Haka nan kuma idan wani daga cikinmu ya kasance mai biyayya ga mahaifansa, hakan yana nuni da cewa kenan ba za mu saba musu ba, kuma babu makawa abin da za mu samu shi ne kauna da kuma girmamawarsu gare mu, ko kuma kaunar sauran mutane da kuma girmamawarsu gare mu. Sannan kuma sama da hakan shi ne kauna da kuma yardar Ubangiji Madaukakin Sarki gare mu.
Wadansu mutane suna kokarin nuna mana cewa ma'anar alheri shi ne nisantar dadin duniya da kuma kaurace musu. To amma a gaskiya ma'anar alheri shi ne kyautata mu'amala da ni'imomi da iyawan da aka arzurtamu da su. Shi ne kuwa amfani da wadannan abubuwan jin dadi ta hanyar da ta dace.
Don kuwa Wanda Ya arzurtamu da wadannan ni'imomi da kuma iyawa ba Ya so ya haramta mana dadinsu, face dai so Yake mu yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace da za su sanya mu a kan tafarkin alheri har abada.
Saboda haka sharri shi ne mu gagara amfani da wadannan ni'imomi ta hanyar da ta dace da kuma mance manufofin da suka sa aka arzurtamu da su. To amma tambayar da take da muhimmanci a nan ita ce, mene ne yake sanya mu a wasu lokuta mukan zabi sharri duk kuwa da irin bala'in da ke tattare da shi ko kuma muke ba shi damar ya shiga cikin rayuwarmu ta samartaka mai kyawun fuska?!
Amsa wannan tambaya tana bukatuwa da gabatar da wasu tambayoyin na daban.

Shin muna daga cikin mutanen da suke kaskantar da kansu da cin mutumcin kansu ne? idan kuwa har haka ne, to sharri zai mamaye mu...
Babu wani daga cikinmu da zai yarda a ce masa wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashe ko kuma ja-gora daga cikin ja-gorori zai sunkuya kasa don daukan wani abu maras amfani.
Mai yiyuwa ne wannan abu yana da girma da muhimmanci ga wasu, to amma irin girman shugaba ko kuma ja-gora zai hana shi damuwa da wannan abu, kuma bai kamance shi yayi hakan ba. Hakan nan ma, bai dace da mu 'yan'Adam ba mu bar kawukanmu su zamanto wajajen gwajin munanan ayyuka, hassada, zalunci, karya, sata, da dai zunubai da sharrori.
Shin muna daga cikin masu wasa da abokan gaba?
To alal akalla kada mu yi haka da abokan gabanmu na daga kwayoyin cuta...shin za mu yi haka da sauran nau'in kwayoyin cuta, wato kwayoyin cutar munanan ayyuka?.
Akwai wata kissa ta sahabban Annabi (s.a.w.a.) lokacin da suke tare da shi a wani bushasshen guri kuma ga shi ana tsananin sanyi. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tambaye su ko za su iya tattaro itatuwa don su kunna wuta da kuma jin dumi?
Sai dukkan sahabban suka ce: babu tsiro ko bishiya a wannan wuri ya ya za su iya hado itatuwa?
Sai Annabi (s.a.w.a.) ya ce musu: to kowannen-ku ya tafi ya nemo abin da ya sawwaka.
Sai sahabbai suka bazama don nemo duk wani abin da suka gani na daga kayoyi da busassun tsirrai, daga nan sai suka zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da itatuwa masu yawan gaske.
Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) yace musu, da haka ne kananan zunubai suke taruwa da yawa kamar yadda kuka tattaro wadannan itatuwa. Sannan kuma ya ce musu: ina gargadinku da kananan zunubai.

Shin muna daga cikin wadanda ba sa gani face abubuwan da suke gaban kafufunsu, kuma ba sa ganin abubuwan da za su faru nan gaba sannan kuma suke jahiltar karshen al'amurra?
Da wuya ace dokin da ke daure a jikin injin tatsan rake don jujjuya shi, kamar yadda ake yi a da ko kuma a halin yanzu a wasu wurare, zai nuna bacin rai kan wannan aiki ga shi kuwa yana tafiyar dubban mila-milai ba tare da ya bar inda yake ba...
Mai yiyuwa ne hakan ya faru saboda shi abin da ke gaban kafafuwansa kawai yake gani, to amma wanda yake ganinsa daga nesa da kuma wajen injin zai tausaya masa halin da yake ciki...

Shin muna daga cikin wadanda suke ba da muhimmanci ga harkokinsu ne kawai?
Idan har al'amarin haka ne, to mun kasance kamar kwadon da ke cikin rijiya kuma ba ya so ya bar cikinta, amma yana ganin duniya kawai ita ce abin da ke kewaye da wannan rijiya, bai san abin da ke wajen wannan rijiya ba da suka hada gonaki da sauran ruwayen da suke gudu a wajen rijiyar.

Shin muna daga cikin mutanen da suke fara tafiya ba tare da sun duba kawukansu ba?
Hakan shi ne yanayin matafiyin da ya zabi batacciyar hanya ba tare da kula da alamomin da suke gefen hanyar ba, sannan kuma bai tambayi kowa ba...to matukar dai wannan matafiyi ya ci gaba a irin wannan yanayi, to babu yadda za a yi ya kai ga inda yake son zuwa ko da kuwa ya kara saurin tafiyarsa don saboda karin nisan inda zai je din.

Shin muna daga cikin mutanen da suke barin aikata ayyukan alheri har zuwa wani lokaci?
Alal misali, mu ce akwai isasshen lokaci a nan gaba da za mu aikata alheri...ko kuma mu ce mu har yanzu yara ne da ba mu da wani nauyi a kanmu, da dai makamantan irin wadannan maganganu da kuma tunani...
Hakan kuwa yana nufin kenan muna son mu bar kofofin sharri a bude ba tare da mun bude na alheri ba...bayan dan wani lokaci sai mu ga ma'ajiyar zuciyarmu ta cika da sharri; don kuwa mun riga mun rufe kofofin alheri ba tare da mun ba shi daman cika zukatanmu da kuma kawata rayuwarmu ba.

Shin muna abota da ashararai ma'abuta munanan ayyuka ne?
Shin a shirye muke mu kulla alaka da irin wadannan mutane?
Idan haka ne kuwa, to za mu karfafa hannayen sharri a tattare da mu kenan ta yadda a sannu-sannu za mu fada cikin rijiyar bala'insa; don kuwa kusanta hannun sharri da kuma misaltuwa da shi yana nesanta mu daga hannayen alheri ne.

Shin za mu yi amfani kwakwalwarmu da kuma ci gaba da shirye-shiryenmu na kyawawan dabi'u?
Idan har muka bari kwayoyin cutar sharri suka shiga cikin wadannan shirye-shirye namu, shin muna neman wata hanya mafi saurin da za mu fitar da su? Kamar yadda muke yi ga kwamfutocinmu da suke cikin gidaje, ko kuma kamar yadda muke yi a makarantu da kuma wuraren ayyukanmu...
Akwai tambayoyi da yawan gaske da muke tam-baya don sanin hanyoyin da sharri yake bi wajen shiga rayuwarmu. Misali, muna iya tambaya, shin muna daga cikin mutanen da suke damuwa da adon zahiri da kuma adon tufafi da dai sauransu? Ko kuma muna damuwa da kawan badini da kuma kyawawan dabi'u?

Kana kuma, shin muna iya bambance alheri da sharri?
Mai yiyuwa ne sharri ba zai bayyana mana a matsayi mai muni ba, face dai zai zo mana ne da yanayi mai kyau yana hade da guba da kuma zuma...
Don haka mu kula da sharri dukkan kula musam-man ma idan ya sanya tufafin alheri.
Hakika mafi kyawun tafarkin gano sharri ko kuma hakikanin ayyukan da ake kiransu da sharri da munanan ayyuka ko kuma zunubai shi ne mu yi dubi cikin karshe da kuma sakamakonsu.
To daga cikin sakamako da kuma karshen wadannan ayyuka akwai, tabewa, shaye-shaye, aikata muggan laifuffuka, shiga gidan yari da dai sauransu...
Daga karshe muna iya cewa alheri shi ne yada kyawawan siffofi cikin rayuwarmu da kuma rayuwar wadanda suke kewaye da mu...hakan kuwa yana nufin amfani da kuma jin dadin ni'imomin rayuwa da kuma kyawunta tare da kwanciyar hankali, daidaituwa da kuma sa'ada.
Sannan kuma ba makawa sharri ba zai samar mana da hakan ba, face dai zai bayyana cewa zai samar mana da hakan ne, amma karya ce kawai.
Shin rayuwar son kai ba tare da kula da sauran mutane ba yana daga cikin alheri? Shin yana daga cikin alheri mutum ya dinga wasa da abinci alhali kuwa miliyoyin yara suna mutuwa da yunwa?
Irin wadannan tambayoyi sukan samu yin tunani don zaban rayuwar da za mu yi don kada mu fada cikin sharrin da wasunmu suka fada. Sannan kuma mu yi amfani da damar rayuwa wajen tafarkin kiyaye mutum da al'ummarsa daga hatsarori da kuma matsalolin rayuwa.

Daga Karshe...

Ba abin da za mu ce a karshen wannan dan karamin littafi, "Shingen Matasa", face dai muna kira ga masu karatu, membobin "Dandalin Matasa", samari da 'yan mata da su rubuta mana ra'ayoyinsu kan wannan littafi da kuma abin da ya kumsa...
Muna maraba da duk wanda yake ko take son ya/ta aiko da ra'ayinsa/ta a wannan dandali, kana kuma muna maraba da duk wanda yake ko kuma take son taimakawa da ra'ayinsa/ta wanda zai taimaki matasa.Ra'ayinku

isah aliyu alkaleri - [2012-11-02]
A nawa ra\'ayin shine, matasa mu tashi haikan wurin neman ilmin addinin musulumci.

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
7+5 =