Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Hadisan Imam Ali Al-Hadi Annaki (A.S)1. الامام على الهادى النقى عليه السلام لبعض مواليه: عاتب فلانا، و قل له إن الله إذا أراد بعبد خيرا إذا عوقب [عوتب] قبل. (بحار الانوار:75: 65، ح 4)
1. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce da wani daga bayinsa: ka yi wa wane faxa ka gaya masa idan Allah yana son alheri ga bawan da idan an yi masa faxa sai ya karba.

2. الامام على الهادى النقى عليه السلام: إن لله بقاعا يحي أن يدعى فيها، فيستجيب لمن دعاه، و الحير منها. (المراد من الحير حرم الإمام الحسين عليه السلام) (تحف العقول: 361)
2. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Hakika Allah yana da wani wuri da yake son a kira shi a ciki, sai ya amsa wa wanda ya roke shi da addu’ar alhri da kuma haramin imam husain (A.S) yana ciki.

3. الامام على الهادى النقى عليه السلام: من اتقى الله يتقى، و من أطاع الله يطاع، و من اطاع الخالق لم يبال سخط المخلوقين، و من أسخط الخالق فلييقن ان يحل به سخط المخلوقين. (بحار الأنوار 71: 182 ح 41)
3. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wanda ya ji tsoron Allah za a ji tsoronsa, kuma wanda ya bi Allah za a bi shi, kuma wanda ya bi mahallici bay a damuwa da fushin ababan halitta, kuma wanda fushin mahalicci ya same shi to ya yi yakinin samun fushin ababan halitta.

4. الامام على الهادى النقى عليه السلام: من أمن من مكر الله و أليم أخذه، تكبر حتى يحل به قضاؤه، و نافذ امره، و من كان على بينة من ربه، هانت عليه مصائب الدينا، و لو قرض و نشر. (تحف العقول: 362)
4. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wanda ya aminta da makircin Allah da zafin rikonsa zai yi girman kai har sai hukuncinsa ya sauka a kansa, kuma ya zartar da hukuncinsa a kansa , kuma wanda yake da wata shiriya daga ubangijinsa sai musibun duniya su yi masa sauki, koda kuwa an yayyaga namansa an yanyanka shi.

5. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الشاكر أسعد بالشكر منه بالنعمة التى أوجبت الشكر، لان النعم متاع، و الشكر نعم و عقبى. (تحف العقول: 362، و بحار الأنوار 78: 365 ح 1)
5. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: mai godiya ya fi rabauta da godiya fiye da ni’imar da ta sanya shi godiya, domin ni’ima jin daxi ne , godiya kuwa ni’ima ce kuma mai zuwa.

6. الامام على الهادى النقى عليه السلام: إن الله جعل الدنيا دار بلوى و الآخرة دار عقبى، و جعل بلوى الدنيا لثواب الآخرة سببا، وثواب الآخرة من بلوى الدنيا عوضا. (تحف العقول: 362)
6. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Hakika Allah maxaukaki ya sanya wannan duniya gidan jarabawa lahira kuwa gidan wanzuwa, sai ya sanya jarabawar duniya sababin samun ladan lahira, ladan lahira kuwa musanya ne na bala’in duniya.

7. الامام على الهادى النقى عليه السلام: إن الظالم الحاكم يكاد أن يعفى على ظلمه بحلمه، و إن المحق السفيه يكاد ان يطفئ نور حقه بسفهه. (بحار الأنوار 78: 365 ح 1)
7. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: hakika azzalumi mai hakuri yana kusan ya yafe wani laifi da hakurinsa yana kuma kan zaluncinsa, amma mai cancantar (wani abu) wawa yana kusan ya yi asarar hakkinsa da wautarsa.

8. الامام على الهادى النقى عليه السلام: من جمع لك وده ورأيه، فاجمع له طاعتك. (تحف العقول: 362)
8. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wanda duk ya ba ka soyayyarsa da ra’ayinsa , to ka ba shi biyayyarka.

9. الامام على الهادى النقى عليه السلام: من هانت عليه نفسه فلا تأمن شره. (بحار الأنوار 78: 365 ح 1)
9. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wanda ransa ta wulakanta gunsa, to kada ka aminta da sharrinsa.

10. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الدنيا سوق ربح فيها قوم و خسر آخرون. (تحف العقول: 362)
10. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: duniya kasuwa ce da wasu mutane suka ci riba wasu kuma suka samu faxuwa.

11. الامام على الهادى النقى عليه السلام: من رضى عن نفسه كثر الساخطون عليه. (أعلام الدين: 311)
11. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wanda ya yarda da kansa to masu kiyayya da shi zasu yawaita.

12. الامام على الهادى النقى عليه السلام: المقادير تريك ما لم يخطر ببالك. (بحار الأنوار 78: 369)
12. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Yaudagobe zata nuna maka abin da ma ba taba zuwa a kwakwalwarka ba.

13. الامام على الهادى النقى عليه السلام: من أقبل مع أمر ولى مع انقضائه. (بحار الأنوار 78: 369)
13. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wanda ya gabato da wani lamari, to zai juya tare da karewar lamarin.

14. الامام على الهادى النقى عليه السلام: راكب الحرون أسير نفسه، والجاهل أسير لسانه. (أعلام الدين: 311)
14. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: mai hawa tsattsauran doke zai kai kansa ya baro, shi kuwa jahili harshensa ne zai kai shi ya baro.

15. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الناس فى الدنيا بالأموال، و فى الآخرة بالأعمال. (أعلام الدين: 311)
15. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Masu dukiya a duniya su ne mutane, (amma) a lahira kuwa masu ayyuka (na alheri).

16. الامام على الهادى النقى عليه السلام: المراء يفسد الصداقة القديمة، و يحلل العقدة الوثيقة، و أقل ما فيه أن تكون فيه المغالبة، و المغالبة أس أسباب القطيعة. (بحار الأنوار 78: 369، و 368،3)
16. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Jayayya yana bata tsohuwar abota, kuma yana warware alkawarin amintuwa da juna, kuma mafi karancin abin da yake cikinsa shi ne neman galaba kan juna, kuma neman galaba kan juna ita ce asalin yanke wa juna.

17. الامام على الهادى النقى عليه السلام: العتاب مفتاح المقال، و العتاب خير من الحقد. (أعلام الدين: 311)
17. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Zargi shi ne mabuxin ance-ance da kace-nace, Kuma gwara zargi da mugun kulli.

18. الامام على الهادى النقى عليه السلام: المصيبة للصابر واحدة، و للجازع اثنتان. (بحار الأنوار 78: 369، و 368 ح3)
18. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Musiba abu guda xaya ce ga mai juriya, kuma guda biyu ce ga mai raki.

19. يحيى بن عبد الحميد: سمعت الامام أبا الحسن على الهادى النقى عليه السلام يقول لرجل ذم إليه ولدا له، فقال: العقوق ثكل من لم يثكل. (بحار الأنوار 78: 369)
19. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Yahaya xan Abdulhamid y ace: Na ji Abul hasan (A.S) yana cewa da wani mutum da yake faxin mummuna kan xansa, sai y ace: saba iyaye kamar mutuwar xa ce ga wanda xansa bai mutu ba.

20. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الهزل فكاهة السفهاء، و صناعة الجهال. (أعلام الدين: 311)
20. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wasan banza rahar wawaye ne kuma aikin jahilai ne.

21. الامام على الهادى النقى عليه السلام: السهر ألذ للمنام ،و الجوع يزيد فى طيب الطعام يريد به الحث على قيام الليل و صيام النهار. (بحار الأنوار 78: 369)
21. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: a cikin wani wa’azinsa: rashin baccin dare ya fi daxin bacci, kuma yunwa tana daxa daxin abinci. (wato yana son kwaxaitar da mutane tsayuwar dare da azumin rana).

22. الامام على الهادى النقى عليه السلام: اذكر مصرعك بين يدى أهلك، ولا طبيب يمنعك، ولا حبيب ينفعك. (أعلام الدين: 311)
22. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: ka tuna magagin mutuwarka a gaban iyalinka, kuma babu wani likita da zai hana ka mutuwa kuma babu wani masoyi da zai amfane ka.

23. الامام على الهادى النقى عليه السلام: أذكر حسرات التفريط تأخذ بقديم الحزم. (بحار الأنوار 78: 369)
23. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: ka tuna hasarar sakaci, ka yi riko da zurfin tunani.

24. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الغضب على من لا تملك عجز، و على من تملك لؤم. (أعلام الدين: 311)
24. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Fushi kan abin da ba ka mallaka gajiyawa ce, kuma fushi a kana bin da kake mallaka abin kyama ne.

25. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الحكمة لا تنجع فى الطباع الفاسدة. (بحار الأنوار 78: 369)
25. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: hikima ba ta haifar da alheri a cikin mummunar xabi’a.

26. الامام على الهادى النقى عليه السلام: خير من الخير فاعله، و أجمل من الجميل قائله، و أرجح من العلم حامله، و شر من السوء جالبه، و أهول من الهول راكبه. (أعلام الدين: 311)
26. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wanda ya fi alheri (zama alheri) shi ne mai aikata alheri, kuma mafi kyawu da kyawun shi ne mai faxinsa, mafi rinjaye (wato wanda ya fi ilimi) kan ilimi shi ne mai xauke da ilimin, mafi sharrin (zama sharri) shi ne mai jawo sharrin, kuma mafi tsoro (daga tsoron kansa) shi ne mai hawa kan tsoron.

27. الامام على الهادى النقى عليه السلام: إياك و الحسد، فإنه يبين فيك، ولا يعمل فى عدوك. (بحار الأنوار 78: 369)
27. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Na hane ka hassada domin yana shi yana bayyana a gareka kuma bay a cutar da makiyinka.

28. الامام على الهادى النقى عليه السلام: لا تطلب الصفاء ممن كدرت عليه، ولا الوفاء ممن غدرت به، ولا النصح ممن صرفت سوء ظنك إليه، فإنما قلب غيرك لك كقلبك له. (أعلام الدين: 312)
28. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Kada ka nemi tsarki daga wanda ka gurbata, ko kuma cika alkawari ga wanda ka yaudara, ko nasiha ga wanda kake yi masa mummunan zato, ka sani hakika zuciyar waninka gareka kamar zuciyarka ce gareshi.

29. الامام على الهادى النقى عليه السلام: القوا النعم بحسن مجاورتها، والتمسوا الزيادة فيها بالشكر عليها، واعلموا أن النفس أقبل شىء لما أعطيت، و أمنع شىء لما منعت. (أعلام الدين: 312)
29. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: ku kasance tare da ni’ima da kyakkyawar kulawa gareta, ku nemi daxuwarta da godiya kanta, ku sani hakika rai tana karbar abin da aka ba ta ne, kuma tana kin abin da aka hana ta ne.

30. الامام على الهادى النقى عليه السلام: لو سلك الناس واديا و شعبا لسلكت وادى رجل عبد الله وحده خالصا مخلصا. (بحار الأنوار 70: 245 ح 19)
30. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Da mutane sun biy wani wuri kwararo, da na bi hanyar wani mutum day a bauta wa Allah xaya yana mai tsarkake shi da ikhlasi.

31. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الحسد ماحق الحسنات، والزهو جالب المقت، و العجب صارف عن طلب العلم، داع إلى الغمط، والجهل و البخل أذم الأخلاق، و الطمع سجية سيئة. (بحار الأنوار 72: 199)
31. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: hassada tana shafe kyawawan ayyuka, ganin fifiko kan mutane yana jawo fushin mutane, girman kai da jiji-dakai yana hana neman ilimi, yana kuma sanya wulakanta mutane, jahilci da rowa suna daga mafi munin halaye, kwaxayi kuwa xabi’a ce mummuna.

32. الامام على الهادى النقى عليه السلام: الغناء قلة تمنيك، و الرضا بما يكفيك، و الفقر شره النفس و شدة القنوط. (بحار الأنوار 75: 109 ح 12)
32. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: wadatuwa karancin burinka ce (tana karanta burinka) da yarda da abin da yake isarka, kuma ta talauci zarin kai ne da kuma tsananin yanke kauna.

33. الامام على الهادى النقى عليه السلام: العقوق يعقب القلة، و يؤدى إلى الذلة. (بحار الأنوار 74: 84 ح 95)
33. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: sabon iyaye yana jawo karanci kuma yana kai wa zuwa ga kaskanci.

34. الامام على الهادى النقى عليه السلام لرجل، و قد أكثر من إفراط الثناء عليه: أقبل على شأنك، فإن كثرة الملق يهجم على الظنة، و إذا حللت من أخيك فى محل الثقة فاعدل عن الملق إلى حسن النية. (بحار الأنوار 73: 295)
34. Abul hasan na uku (A.S) y ace da wani mutum da ya yawaita yabonsa: ka fuskanci sha’aninka, ka sani hakika yawan bambaxanci yana kawo yawan zato da kokwanto, idan ka samu yarda daga xan’uwanka to sai ka bar bambaxanci ka koma kyautata niyya.

35. أحمد بن هلال، قال: سألت أبا الحسن الأخير عليه السلام عن التوبة النصوح ما هى؟ فكتب عليه السلام: أن يكون الباطن كالظاهر، و أفضل من ذلك. (معانى الأخبار: 174 ح 1)
35. Ahmada xan hilal, y ace; na tambayi abul hasan na karshe (A.S) game da tuba bakome mene ne shi? Sai (A.S) ya rubuta: zahirin ya kasance kamar baxini ko ma ya fi hakan.

36. الامام على الهادى النقى عليه السلام: إذا كان الجور أغلب من الحق لم يحل لأحد أن يظن بأحد خيرا حتى يعرف ذلك منه. (الكافى 5: 298 ح 2)
36. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: na ji abul hasan (A.S) yana cewa: idan zalunci ya kasnce ya yi rinjaye kan gaskiya, to bai halatta bag a wani ya yi zaton alheri ga wani har sai ya san haka daga gareshi.

37. الامام على الهادى النقى عليه السلام: إن العبد ليقوم فى الليل، فيميل به النعاس يمينا و شمالا، وقد وقع ذقنه على صدره، فيأمر الله تبارك وتعالى أبواب السماء، فتفتح، ثم يقول للملائكة: انظروا إلى عبدى ما يصيبه فى التقرب إلى بما لم أفترض عليه راجيا منى لثلاث خصال: ذنبا أغفره له، أو توبة أجددها له، أو رزقا أزيده فيه، فأشهدكم ملائكتى! أنى قد جمعتهن له. (ثواب الأعمال: 42)
37. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Hakika bawa yana tsayawa da dare , sai gyangyaxi ya karkatar da shi dama da hagu , kuma habarsa ta faxan kan kirjinsa, sai Allah ya umarci a buxe kofofin sama, sai a buxe, sai y ace da mala’iku ; ku duba bawana da abin da yake samunsa a kan neman kusanci da ni da abin da ban wajbta masa ba yana mai neman abubuwa uku daga gareni; zunubi d azan gafarta masa, ko tuba d azan jaddada masa, ko arziki da zan daxa masa a cikinsa, to ina shaida muku mala’ikuna ni na haxa masa duka gareshi.

38. الامام على الهادى النقى عليه السلام: إن الحرام لا ينمى، و إن نمى لا يبارك له فيه، وما أنفقه لم يؤجر عليه، و ما خلفه كان زاده إلى النار. (الكافى 5: 125 ح 7)
38. Imam Ali al-hadi (A.S) ya ce: Haramun bat a yaxo, idan ma ta daxu ba a sanya albarka a cikinta, kuma abin day a ciyar ba a ba shi lada a kansa, kuma abin day a bari guzuri ne nasa zuwa wuta.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
4+1 =