Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

BAHASIN TAKIYYA


Muhammad Riza Muzaffar

Hafiz Muhammad Sa’id

Mun yi imanin cewa saboda baiwar da Allah ya yi mana ta karfin tunani da kuma kyautar hankali, to ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukaki yana cewa: “Zamu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya ne”. Surar Fussilat: 53. Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai ba”. (Surar Bakara: 170). Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zato”. Surar An’am: 116
A hakika mu abin da muke yin imani da shi shi ne cewa; Hankulanmu su ne suke wajabta mana yin tuntuntuni kan halittu da sanin mahallicin duniya, kamar yadda suke wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da’awar annabta da kuma mu’uijzarsa, kuma bai inganta ba -a hankalce- a yi koyi da wani a cikin wadannan al’amuran komai matsayinsa da darajarsa.
Abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali da ra’ayoyin ma’abota hankali suka ginu akansu, ya kuma zo ne don fadakar da mutane abin da aka halitta su a kansa na sani da hankaltuwa da tunani da kuma fadada tunani da fuskantarwa zuwa ga abin da hankula suke hukunci da shi.
Ba daidai ba ne -a irin wannan hali- mutum ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane masu tarbiyyantarwa kan wata akida ko wasu mutanen daban. Ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa [1] wadanda ake kira shika-shikan Addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne:

1. Kadaita Allah
2. Annabci
3. Adalci
4. Imamanci
5.Tashin kiyama

Duk wanda ya yi koyi da iyayensa ko kuma wasunsu a imani da wadannan shika-shikan to lalle ya ketare iyaka ya fandare daga hanya madaidaiciya, kuma ba zai taba zama abin yi wa uzuri ba har abada.

A takaice dai mu muna da’awar abubuwa biyu ne:
Na Farko: Wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida, bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba.
Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne na hankali kafin ya zamanto na shari’a, wato saninsa bai samo asali daga nassosin addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi. Kuma ba komai ake nufi da ma’anar wajabcin hankali ba sai riskar hankali ga larurar sani da kuma lizimtar yin tunani da kokarin bincike a cikin shika-shikan Addini.

Koyi Da Wani A Hukunce-hukuncen Addini

Amma rassan al’amuran Addini su ne hukunce-hukuncen shari’a wadanda suka shafi ayyuka, su bai wajaba ba a yi nazari da ijtihadi a kansu ba, wajibi ne a cikin rassan hukunce-hukucen addini idan ba laruran Addini ne ba ne kamar wajabcin salla, da zakka, da azumi, da hajji, mukallafi ya yi dayan al’amura uku a cikinsu:-
Ko ya yi ijtihadi [2] ya yi bincike a kan dalilan hukunce-hukunce idan yana cikin masu iya yin hakan, ko kuma ya zama mai ihtiyadi idan zai iya yin ihtiyadi [3], Ko kuma ya yi koyi da mujtahidin da ya cika sharudda. Ya kasance wanda zai yi koyi da shi mai hankali ne, Adali, mai kare kansa, mai kiyaye Addininsa, mai saba wa son ransa, mai bin umarnin Ubangijinsa.
Duk wanda ba mujtahidi ba ne, kuma ba mai yin ihtiyadi ba, kuma bai yi koyi da mujtahidin da ya cika sharudda ba, to dukkan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, koda kuwa ya yi salla, ya yi azumi, ya yi ibada duk tsawon rayuwarsa, sai dai idan aikinsa ya dace da ra’ayin wanda yake yi wa koyi kuma ya yi sa’ar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah (S.W.T).

Ijtihadi

Mun yi Imanin cewa: ljtihadi a rassan hukunce-hukuncen shari’a wajibi ne kifa’i [4] da ya doru a kan dukkan musulmi a zamanin boyuwar Imam, wato ya wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Sai dai idan wadanda suka wadatar sun dauki nauyin yi, to ya saraya daga kan sauran musulmai, sai su wadatu da wanda ya dauki nauyin yin hakan kuma ya kai ga matsayin ijtihadi kuma ya cika sharuddan, sai su yi koyi da biyayya gareshi, su koma masa a cikin al’amuran hukunce-hukuncen Addininsu.
A kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami wanda ya sadaukar da kansa a tsakaninsu ya kai ga matsayin Ijtihadi wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo, kuma ya kasance ya cika sharuddan da ya cancanci a yi koyi da shi a dogaro da fatawarsa, sai su wadatu da shi su yi koyin da shi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen Addininsu. Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to ya wajaba a kan kowane daya daga cikinsu ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya wanda zai dukufa domin kai wa ga wannan matsayi a tsakaninsu, tunda ba zai yiwu ba dukkansu su dukufa domin neman wannan al’amari ko kuma zai yi wahala, Kuma bai halatta ba su yi koyi da wanda ya mutu na daga cikin mujtahidai.
Ijtihadi: Shi ne nazarin dalilan shari’a domin samun sanin hukunce-hukuncen shari’ar da shugaban manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta sakewa ko canzawa da canzawar zamani da kuma halaye.
“Halal din Muhammad (S.A.W) halal ne har zuwa ranar Tashin kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa ranar Tashin kiyama.
Dalilan shari’a su ne: Kur’ani mai girma, da Sunna, da Ijma’i, da Hankali kamar yadda yake dalla-dalla a littattafan “Usulul fikihu”.
Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar sani mai yawa da ilimi wandanda ba sa samuwa sai ga wanda ya dage ya yi kokari ya cire nauye-nauyen da suke a kansa ya bayar da kokarinsa domin samunsa.

Mujtahidi

Abin da muka yi imani da shi game da mujtahidi wanda ya cika sharudda cewa shi wakilin Imami (A.S) ne a halin boyuwarsa, kuma mai hukunci, shugaba cikakke, abin da yake ga Imami (A.S) na koma wa zuwa gareshi a al’amura da hukunci a tsakanin mutane yana gare shi kuma duk wanda ya ya yi raddi gareshi tamkar mai raddi ne ga Imam (A.S) wanda kuma ya yi wa imami raddi to ya yi wa Allah, wannan kuwa yana matsayin shirka da Allah ne kamar yadda ya zo a hadisi daga Imam Sadik (A.S).
Shi Mujtahidin da ya cika sharudda ba wai makoma ba ne na mutane a fatawa kawai ba, shi yana da jagoranci na gaba daya, sai a koma zuwa gare shi a hukunci da raba gardama da shari’a, wannan duk yana daga cikin abubuwan da suka kebance shi, bai halatta ba ga wani ya dauki nauyinsu sai da izininsa, kamar yadda bai halatta ba a yi haddi ko ladadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa.
Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebance shi. Wannan matsayin ko shugabanci na gaba daya imami ne ya bayar da shi ga mujtahidin da ya cika sharudda domin ya zama wakilinsa mai maye gurbinsa a lokacin fakuwarsa, shi ya sa ma ake cewa da shi “Na’ibin Imam”.


1. Wato abubuwan da suke wajibi ne kowane mutum ya san su.
2. Shi ne nazarin dalilan shari'a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari'ar da shugaban Manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta canzawa ko sakewa da sakewa zamani da kuma halaye.
3. Ihtiyadi shi ne bin fatawar malamai da aiki da mafi nutsuwar zance daga cikin fatawowinsu.
4. Wato idan wasu suka yi sun dauke wa sauran mutane.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
8+9 =