Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

ZALUNCI DA AIKIN OFISHIN AZZALUMI


Muhammad Riza Muzaffar

Hafiz Muhammad Sa’id

Ketare haddin wani da zaluntar mutane suna daga cikin mafi girman abubuwn da Imamai (AS) suke girmama muninsa, wannan kuma bi ne ga abin da Kur’ani ya zo da shi na daga tsoratarwa game da zalunci da munana shi, kamar fadinsa madaukaki: “Kada ka tsammaci Allah mai sha’afa ne game da abin da azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta musu ne saboda ranar da idanuwa zasu zazzaro”. (Surar Ibrahim: 42)
Hakika abin da yake kai matukar bayyana munin zalunci da kyamarsa ya zo a maganganun Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (AS), kamar fadinsa shi mai gaskiya ne abin gaskatawa, a Nahjul balaga huduba ta 219: “Wallahi idan da za a ba ni Sammai bakwai da kuma abin da yake kasan falakinta, a kan in saba wa Allah game da tururuwa da in kwace mata Sha’irin da ta jawo, ba zan aikata ba”. Wannan shi ne matukar abin da mutum zai iya surantawa game da kame kai da tsoratarwa daga zalunci da kyamar yinsa.
Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan kwayar sha’ir koda kuwa an ba shi sammai bakwai, to yaya halin wanda yake zubar da jinin musulmi, yake handame dukiyoyin mutane, yake cin mutuncinsu? Yaya za a auna tsakaninsa da aikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayinsa da iliminsa (AS)? Wannan ita ce tarbiyyantarwar Ubangiji da addini yake bukatar ta daga kowane mutum.
Na’am, hakika zalunci yana daga mafi girman abubuwan da Allah ya haramta, saboda haka ne zarginsa ya zama abu na farko da ya zo a hadisan Ahlul Baiti da addu’o’insu, da kuma nesantar da mabiyansu daga gare shi.
Wannan ita ce siyasarsu, kuma a kanta suke mu’amala hatta da wanda yake yi musu shisshigi yake rashin kunyar hawa matsayinsu. Kissar imam Hasan (AS) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuma ya tausaya masa ya kuma tausasa masa, har sai da shi ya ji kunyar mummunan abin da ya aikata. Kuma ka riga ka karanta abin da ya gabata a addu’ar shugaban masu sujjada na daga ladubba madaukaka game da afuwa ga masu ketare iyaka, da nema musu gafara. Wannan kuma shi ne matukar daukakar ran mutum da kamalar mutumtakarsa, duk da kuwa ketare haddin azzalumi kwatankwacin yadda ya ketara ya halatta a shari’a, kamar yadda yin addu’a a kansa ya halatta, sai dai halacci wani abu ne, afuwa kuma wacce take daga kyawawan dabi’u wata aba ce daban, kai gun imamai shige gona da iri wajan yin addu’a a kan azzalumi ana kirga shi zalunci.
Imam Sadik (A.S) ya ce: “Bawa yana kasancewa abin zalunta, ba zai gushe ba yana ta yin addu’a har sai ya zamanto azzalumin”. Idan wannan shi ne halin wanda aka zalunta to yaya halin wanda ya fara zalunci da ketare iyakar tun karon farko yake kuma cin mutuncinsu, yana kwashe dukiyarsu, yana munafuncinsu gun azzalumai, ko yake yaudarar su, yana jefa su cikin halaka, ko ya cutar da su, ko ya yi leken asiri a kansu!? Irin wadannan a wajan Ahlul Baiti (AS) su ne mafi nisantar mutane a wajan Allah, mafi tasananinsu sabo da azaba, mafi muninsu ayyuka da dabi’u.

Taimakekeniya Da Azzalumai

Yana daga abin da yake nuna girman zalunci da munin karshensa cewa, Allah (S.W.T) ya hana taimakekeniya da azzalumai, da kuma karkata zuwa gare su. “Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wasu masoya koma bayan Allah, sannan ba za a taimake ku”. Hudu: 113. Wannan shi ne ladabin Kur’ani da Ahlul Baiti (AS). Hakika hadisai da dama sun zo daga garesu wadanda suka kai matuka wajan hana karkata zuwa ga azzalumai, da alaka da su, da yin aiki tare da su a cikin kowane irin aiki, da taimaka musu ko da tsagin dibino ne.
Babu shakka mafi girman abin da aka jarrabci musulmi da musulunci da shi, shi ne sassauci ga azzalumai, da kawar da kai game da miyagun ayyukansa, da mu’amala tare da su, ballantana taimaka musu a kan zaluncinsu. Ba abin da ya jawo wa al’ummar musulmi bala’o’i sai karkacewa daga tafarki madaidaci da gaskiya, har Addini ya yi rauni tare da shudewar zamani, karfinsu ya tafi, ya kai halin da yake a yau ya koma bako. Musulmi ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani mataimaki ban da Allah, kuma su ba za a taimake su ba hatta a kan mafi raunin makiyansu, da mafi kaskancin masu tsaurin ido a kansu kamar Yahudawa kaskantattu, balle kuma Kiristoci masu karfi.
Imamai (AS) sun wahala wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, suka kuma tsananta wa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abota zalunci da cudanya da su, kuma hadisansu a game da wannan babin ba zasu kirgu ba, daga ciki akwai abin da Imam Zainul Abidin (AS) ya rubuta zuwa ga Muhammad Bn Muslim Azzuhuri, bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai a kan zaluncinsu da fadinsa: “Shin a kiran su gareka yayin da suka kira ka ba su sanya ka kan dutsin nika da suke juya nikan zaluncinsu da kai ba, kuma gada da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’o’insu ba, da tsani na bi zuwa ga batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malamai, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu na musamman da mafiya karfin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen gyara barnarsu, da kaikawon kebatattun mutane da saura jama’a zuwa garesu, abin da suka ba ka ya yi matukar karanta a maimakon abin da suka karba daga gareka da ya yi matukar girmama! Abin da suka gina maka ya yi matukar kankanta a maimakon abin da suka rusa maka da ya girmama! Ka duba kanka domin ba mai duban ta sai kai, ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya” [1].
Wannan kalma ta “Ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”. ta girmama! Yayin da son rai ya yi rinjaye a kan mutum sai ya wulakanta sirrin samuwarsa da karamarsa, kuma ba zai samu wani mai daukar nauyin aikinsa ba, ya wulakanta abin da yake yi na ayyuka, ya raya cewa ba shi ne zai yi wa kansa hisabi a kan abin da yake yi ba na zunubi, wannan kuwa yana daga sirrorin ran mutum mai umarni da mummuna, sai Imam (A.S) ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirrin na rai da yake boye a cikinta, domin kada wahami ya yi galaba a kansa, sai ya yi sakaci da nauyin da yake kansa.
Mafi isa matuka daga wannan a suranta haramcin taimakekeniya da azzalumai shi ne maganar Safwan Jammal tare da Imam Musa Kazim (AS), wanda ya kasance daga cikin shi’ar Imam din, kuma daga masu rawaito hadisinsa amintattu (kamar yaddda ya zo a littafin Rijal na Alkashi game da Safwan) ya ce: “Na shiga wajansa.
Sai ya ce da ni: Ya Safwan duk wani abu daga gareka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu daya.
Na ce: A sanya ni fansa gare ka! Wane abu ne?
Ya ce: Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Harunar Rashid.
Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai ashararanci, ko dagawa, ko don farauta, ko wasa ba, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato hanyar Makka, kuma ba na aikin da kaina, sai dai ina tura shi da bayina.
Ya ce: Ya Safwan kudin hayarka yana zama bashi a kansu?
Na ce: Na’am, a sanya ni fansa gareka.
Ya ce: Shin kana so su wanzu har su biya ka kudin hayarka?
Na ce: Na’am.
Ya ce: To duk wanda ya so wanzuwarsu yana cikinsu, duk wanda ya kasance daga cikinsu shi mai shiga wuta ne.
Safwan ya ce: Sai na tafi na sayar da rakumana baki daya.
Idan son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu ya kai wannan matsayi, to ina ga wanda suke hada kai da shi a kan zalunci ko kuma yake karfafa su a zalunci, ina ga wanda ya shiga cikin jama’arsu ko yake aiki irin nasu, ko yake bin tawagarsu ko kuma yake bin umarninsu?.

Aiki A Hukuma Azzaluma

Idan har taimakar azzalumai koda da rabin dabino ne, kai hatta ma son wanzuwarsu suna daga mafi tsananin abubuwa da lmamai (AS) suka yi gargadi game da su, to menene hukuncin tarayya da su a cikin hukunci da shiga cikin ayyukansu da rikon ofisoshinsu. Menene kuma hukuncin wadanda suke daga wadanda suka assasa daularsu, ko kuma ya zama cikin rukunan shugabacinsu masu dulmuya cikin karfafa hukumarsu, (domin karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta, da raya barna dukkaninta, da bayyana zalunci da fasadi) kamar yadda ya zo a Hadisi a “Tuhaful Uku1” daga Imam Sadik (AS).
Sai dai kuma halaccin aiki a karkashin azzalumi ya zo daga gare su (AS) idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna. Ya zo a ruwaya cewa “Allah yana da wadanda ya haskaka hujjoji da su, ya ba su iko a kasashe a kofofin azzalumai, da su ne yake kare waliyyanSa, ya kuma gyara al’amuran musulmi da su, wadannan su ne muminai na hakika, su ne manarorin Allah a bayan kasa, su hasken Allah ne a cikin bayinsa”. Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Imam Musa Bin Ja’afar (AS). A wannan Babin akwai hadisai da dama da suke bayyana tafarkin da ya kamata masu rike ofis da ma’aikata su gudanar da ayyukansu a kai, kamar abin da ya zo a wasikar Imam Sadik (AS) zuwa ga Najjashi Shugaban Ahwaz [2].

Umarni Da Kyakkyawa Da Hani Ga Mummuna

Suna daga cikin farillai kuma mafiya daukakarsu, kuma da su ne ake tsayar da farillai, kuma wajabcinsu yana daga cikin larura na addini, hakika littafi mai girma da hadisai madaukaka sun kwadaitar a kansu, da mabanbantan lafuzza.
Allah (S.W.T) ya ce: "Lalle ne wata al'umma daga cikinku ta kasance mai kira zuwa ga alheri, mai yin umarni da kyakkyawa kuma mai yin hani ga mummuna, kuma wadannan su ne masu rabauta". Ali Imran: Aya 104.
Allah (S.W.T) ya ce: "Kun kasance mafificiyar al'umma da aka fitar wa mutane, kuna horo da kyakkyawa kuma kuna hani ga mummuna, kuma kuna yin imani da Allah". Ali imran: aya 110.
An karbo daga Manzo (S.A.W) cewa: "Al'ummata ba zata gushe a cikin alheri ba mutukar sun yi horo da kyakkyawa kuma sun yi hani ga mummuna, kuma sun yi taimakekeniya a kan aikin biyayya (ga Allah), idan kuwa ba su aikata haka ba, za a debe musu albarku, kuma a sallada sashinsu a kan sashi, kuma ba zasu samu mai ceto a doron kasa ba, ko a sama".
An karbo daga imam Ali (A.S) cewa ya yi huduba wata rana, sai ya yi godiya ga Allah kuma ya yabe shi, sannan ya ce: "Amma bayan haka, kadai abin da ya hallaka wadanda suka gabace ku shi ne; yayin da suka aikata sabo sai malamai masana Allah da masu bauta ba su hana su ba, hakika yayin da suka zurfafa a cikin sabo kuma malamai masana Allah da masu bauta ba su hana su ba sai ukubobi suka sauka a kansu, ku yi horo da kyakkyawa ku yi hani ga mummuna, ku sani cewa, lalle horo da kyakkyawa da hani ga mummuna ba su taba, kuma ba zasu taba kusanto da ajali ba, sannan ba su taba, kuma ba za su taba yanke arziki ba".
Umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, wajabcinsu na isarwa ne idan wasu suka tsayar da su, to ya sauka daga kan kowa.
Da aiwatar da wata farilla ko kawar da wani mummuna daga al'umma ya hau kan wasu gungun mutane, to wajabcin ba ya saraya don wasu sun yi aiki da shi, kuma ya wajaba a hadu a kan wannan gwargwadon iko.
Wajibi ne mai umarni da kyakkyawa da hani da mummuna ya kassance ya san cewa abin da baligi ya bari ko ya aikata kyakkyawa ne ko mummuna, don haka umarni da kyakkyawa da hani da mummuna bai wajaba ga wanda ya jahilce su ba.
Ya wajaba ga wanda yake son yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, ya yi tsammanin tasirin yin hakan, da zai san ko ya yi tsammanin rashin tasirinsu, bai wajaba ya yi umarni ko hani ba.
Wajibi ne yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna idan mai sabon ya ci gaba da yi, duk sadda aka san ya daina, wajabcin ya saraya.
Da zai sani ko ya yi tsammani mai karfi cewa; a cikin yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna akwai hadari ga rayuwarsa, ko mutuncinsa, ko rayukan mumunai, ko dukiyar su, ya haramta ya yi hanin, sai in ya kasance umarnin da hanin suna daga cikin lamuran da shari'a mai tsarki take ba su mihimmanci, kamar kiyaye rayukan wasu kabilu daga musulmi, da keta alfarmarsu, ko shafe alamomin musulunci, da shafe hujjarsa, ta yadda zai kai ga bacewar musulmi, ko shafe sashin alamomin musulunci, kamar dakin Allah mai girma, ta yadda za a shafe alamominsa, a nan babu makawa a lura da mafi muhimmanci.
Da wata bidi'a zata auku a musulunci kuma yin shirun malaman addini, ya kasance zai kai ga keta alfarmar musulunci, da raunana akidar musulmai, to ya wajaba garesu su musa ta, ta kowace irin hanya, shin musantawar zata yi tasiri a wajen tsige barnar ko kuwa.
Umarni da kaykykyawa da hani ga mumuna suna da matakai, wanda ya fara daga zuciya, zuwa harshe, sannan aiki, ta yadda ya wajaba a yi aiki da su bisa matakai, ta yadda idan matakin farko ya isar don yin umarni ko hani, ba zai yi amfani da martaba ta baya ba.
Musantawa ta zuci ita ce ya yi wani aiki da zai nuna damuwarsa daga cikin zuciyarsa ga mummunan aikin, kamar runtse ido, da murtukewa, da kauracewa, da kin yin mu'amala da shi, da makamancin wannan.
Haramun ne yarda da munkari da kuma barin kyakkyawa.
Da zai san cewa abin neman ba zai samu ta hanyar matakin farko ba, ya wajaba ya ciratu zuwa mataki na biyu, idan ya yi tsammanin cin nasara da dadadan kalmomi, to bai halatta ba ya kausasa magana. Idan kuwa gusar da mummuna da tsayar da kyakkyawa ya tsayu a kan kausasa magana da tsanantawa a cikin umarni da tsoratarwa a cikin hani, ya halatta a yi hakan.
Idan ya san cewa ko kuma ya nutsu da cewa ba za a cimma buri ta hanyar martabobi biyu da suka gabata ba, wajibi ne ya ciratu zuwa ta uku, shi ne: yin amfani da iko yana mai kiyaye mafi sauki sannan mafi sauki.
Bai halatta ba ga mai horo da kyakkyawa da hani ga mummuna ya aikata zunubi ko wani kuskure, kamar alfasha da karya da wulakanci.
Ya kamata mai horo da mai hani su kasance a cikin horonsu da haninsu kamar likita ne mai yi wa maras lafiya magani, kamar uba mai tausayi wanda yake kare maslahar wanda yake aikata sabo, kuma ya yi nufin yin hakan don Allah da neman yardarsa, kuma ya tsarkake aikinsa daga son rai, da kuma neman girma.
Yana daga cikin mafi daukakar nau'o'in horo da hani mutum a kankansa ya kasance wanda ya dabi'antu da kyawawan halaye madaukaka, yana mai aiki da mafifitan halaye, kuma wanda yake barin kaskantattun ayyuka, ta yadda rayuwarsa zata zama abin koyi ga wasu, kamar yadda Imam Sadik yake cewa: "Ku kasance masu kira tare da yin shiru".


1. Tuhaful Ukul: sh, 66.
2. Al- Wasa’il Kitabul Bai’i Babi na 78.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+3 =