Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

BAYANI GAME DA ANNABCI


Muhammad Riza Muzaffar

Hafiz Muhammad Sa’id

Mun yi imani da cewa annabci aiki ne na Allah kuma jakadanci ne na ubangiji (S.W.T) da yake bayar da shi ga wanda ya so ya kuma zaba daga bayinsa na gari da masoyansa kammalallu a mutumtakarsu, sai ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abin da yake da amfani da maslaha garesu duniya da lahira, tare kuma da nufin tsaftace su da tsarkake su daga dauxar miyagun xabi’u, da munanan al’adu, da koya musu hikima, da ilimi, da bayyana musu hanyoyin rabauta da alheri, domin ‘yan’adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita, ta xaukaka zuwa ga daraja maxaukakiya a gidajen duniya da lahira.
Kuma mun yi Imani cewa ka’idar tausasawa -kamar yadda bayaninta zai zo- ta wajaba ga Allah mahalicci mai luxufi ga bayinsa, ya aiko manzanninsa ne domin su shiryar da xan Adam, da kuma isar da sakon kawo gyara, kuma su zamanto jakadun Allah kuma halifofinSa. Kamar yadda muka yi imani da cewa Allah maxaukaki bai ba wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko tsayar da shi -takara- ko zabensa. Ba su da wani zabi a kan haka, domin al’amarin dukkan wannan yana hannun Allah ne, domin “Shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSa”. Surar An’am Aya ta 124.
Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargaxi, ko kuma su yi hukunci kan abin da ya zo da shi na daga hukunce-hukunce, da sunnoni, da shari’a.

Annabci Tausasawa Ne

Mutum halitta ne mai iyakoki mai ban al’ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa, da xabi’arsa, da ruhinsa, da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kowane xaya daga cikin mutane. Xabi’ar fizguwa zuwa ga fasadi sun tattara a cikinsa, kamar yadda xabi’ar motsarwa zuwa ga aikata alheri da gyara suka tattara a cikinsa [1], ta wata fuskar kuma an halitta shi a kan xabi’u [2] daban-daban kamar son fifita wani a kansa, da sha’awa, kuma an halitta shi a kan son rinjaya da mamayar waninsa, da kwaxayin rayuwar dauniya, da adonta, da kawarta, da tarkacenta, kamar yadda Maxaukaki yake cewa:
“Hakika mutum yana cikin hasara”. Surar Asri: 2. “Hakika mutum yana xagawa. Don kawai ganin ya wadata”. Surar Kalam:6-7. “Hakika rai mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan waxannan da suke bayyanawa a sarari da nuni ga irin yadda ran mutum yake kunshe da xabi’u da kuma sha’awa.
A wani bangaren, Ubangiji maxaukaki ya halitta masa hankali mai shiryarwa da yake shiryar da shi zuwa ga gyara da ayyukan alheri, da kuma zuciya mai gargaxi da take hana shi aikata mummuna da zalunci, tare da aibata shi a kan aikata abin da yake mummuna abin zargi.
Husumar cikin zuciya da take cikin ran mutum ba ta gushewa tsakanin hanakali da xabi’u, duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan xabi’arsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a ‘yan’adamtakarsu, kuma su ne kammalallu a ruhinsu. Amma wandanda kuwa xabi’arsu ta rinjaye su, to lalle suna daga cikin masu hasarar matsayi, masu ci baya a ‘yan’adamtaka, masu gangarawa zuwa ga matsayin dabbobi.
Mafi tsananin abokan gabar rai su ne zuciya da rundunarta, saboda haka ne muke samun mafi yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha’awace-sha’awace da amsa kiran zuciya: “Kuma mafi yawan mutane ba zasu zama muminai ba koda kuwa ka yi kwaxayin haka”. Surar Yusuf: 103. Saboda gazawar mutum da rashin tsinkayonsa game da abubuwan da suke kewaye da shi, da asiran abubuwan da suke kewaye da shi, da ma waxanda suke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukkan abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, kuma ba zai iya sanin abin da zai kai shi ga samun sa’ada ko tsiyacewa ba, shin a kan abin da ya kebantu da shi ne shi kaxai, ko kuwa wanda ya shafi ‘yan Adam baki xaya da kuma al’ummar da take kewaye da shi. Shi bai gushe ba yana jahiltar kansa kuma yana kara jahilci ko kuma kara gane jahilcinsa duk yayin da iliminsa game da halittu na xabi’a da sauran samammu na binciken ilimi ya karu ba.
Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kai wa ga darajar sa’ada yana bukatar wanda zai xora shi a kan hanya mikakkiya bayyananniya zuwa ga shiriya, domin rundunar hankali ta karfafa da hakan, kuma ya iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da na zuciya. Saudayawa bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara tana kara tsananta ne yayin da zuciya take yaudarar sa ta hanyar nuna masa kyawun fanxarewarsa, sai ta nuna masa abin da yake mummuna cewa kyakkyawa ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne, ta kuma rikita wa hankali tafarkinsa zuwa ga gyara, da sa’ada, da ni’ima, a lokacin da shi ba shi ¬da masaniyar da zai bambance dukkan abin da yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna mai cutarwa. Koma kowane mutum ya sani cewa yana cikin waxannan gwagwarmayar xauki-ba-daxi ko ya sani ko bai sani ba sai dai wanda Allah ya kare shi.
Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukkan tafarkunan alheri da amfani, da kuma sanin dukkan abin da zai amfane shi ko ya cutar da shi a Duniya da Lahira, ballantana kuma jahili. Al’amarin ya kebance shi ne ko kuma ya shafi al’umma da yake zaune a cikinta ne, kuma ba ya iya kai wa ga wannan masaniyar koda kuwa ya haxa kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi, kuma koda kuwa sun haxu sun yi bincike ko sun yi tarurruka da zama daban-daban da kuma shawarwari.
Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. “Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima”. Surar Juma’a: 2. Domin su yi wa mutane gargaxi game da abin da yake da cutarwa gare su, da yi musu albishir da abin da yake da alheri, da gyara, da sa’ada, a gare su.
Tausasawar Allah ga bayinSa wajibi ce domin tana daga cikin tsantsar kamalarSa, shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar ya kwarara kyautarSa da tausasawa, to babu makawa ya kwararo tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu tawaya a kyautarSa da karimcinSa.
Ma’anar wajibi a nan ba yana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba, sai ya wajabta a kan Allah maxaukaki ya bi shi, Allah ya xaukaka ga haka xaukaka mai girma! Ma’anar wajibci a nan tana daidai da ma’anar faxinka da kake yi cewa shi wajibin samuwa ne wato ba zai taba yiwuwa a kore masa samuwa ko a raba shi da ita ba.

Mu’ujizar Annabawa

Mun yi imani da cewa yayin da Ubangiji (S.W.T) yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa ko manzo, to babu makawa ya sanar da shi gare su ya kuma nuna musu shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasawarsa da kuma kammala rahamarsa. Kuma wannan dalilin dole ya kasance ya zo daga mahaliccin halittu mai juya al’amuran samammu [3], wato ya zama abin da ya gagari kudurar xan Adam, sai ya sanya shi a hannun shi Manzon mai shiryarwa domin a san shi da shi, kuma mai shiryarwa zuwa gare shi, wannan dalili shi ake kira mu’ujiza saboda kasancewarsa ya gagari xan Adam ya gudanar da irinsa, ko kuma ya zo da misalinsa.
Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu’ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja, haka nan babu makawa wannan mu’ujizar ya bayyanar da ita ta yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa ballantana sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu’ujizar da da’awar Annabci daga shi mai mu’ujizar saboda ta kasance dalili a kan da’awarsa.
Idan irin waxancan kwararru suka gaza zuwa da irinta sai a sani cewa ta fi karfin ikon xan Adam, kuma ta keta al’ada, daga nan sai a san cewa ma’abocinta yana sama da kudurar xan Adam, kuma yana da alaka da mai juya al’amuran samammu. Idan wannan ya tabbata ga mutum -bayyanar mu’ujiza wadda ta saba wa al’ada- ya kuma yi da’awar Annabci da sako, to sai ya zamanto abin gaskatawar mutane ga kiran da yake yi tare da yin imani da sakon nasa da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi ya yi imani da manzancinsa da kaskan da kai ga umarninsa, wanda zai yi imani da shi ya yi, wanda kuma zai kafirce masa ya kafirce.
Wannan shi ne abin da ya sa muka ga cewa mu’ujizar kowane Annabi ta dace da abin da ya shahara a zamaninsa na ilimi da fasaha, mu’ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda take hadiye sihiri da abin da suke yin baduhunsa saboda kacancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri, yayin da sandan ya zo sai dukan abin da suke aikatawa ya baci, suka san cewa wannan abu ya fi karfinsu, kuma yana saman fannin fasaharsu, kuma xan Adam ya gajiya ya kawo shi, kuma kwarewa da ilimi sun gajiya a gabansa [4].
Haka nan mu’ujizar Annabi Isa (A.S) ita ce warkar da makafi da masu baras, da rayar da matattu, saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci ne yake ya yaxu a tsakanin mutane, kuma akwai malamai likitoci da suke da kwarewa mai girma, sai iliminsu ya kasa gogayya da abin da Isa (A.S) ya zo da shi [5].
Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Kur’ani mai girma mai gajiyarwa -ga waninsa na daga fasahohi- da balagarsa da fasaharsa a lokacin da balagar magana ta kasance ita ce fanni sananne, ma’abota ilimin balaga da azancin magana su ne kan gaba a tsakanin mutane da kyawun bayaninsu da xaukakar fasaharsu, sai Kur’ani ya zo musu kamar tsawa, ya ximautar da su, ya fahimtar da su cewa su ba zasu iya fito na fito da shi ba. Don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza gasa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya bar su [6].
Ya kuma kalubalance su da su kawo sura goma suka kasa, yayin da muka ga sun gajiya sai muka ga sun koma faxa da shi da takobi maimakon harshe, sai muka san cewa lallai Kur’ani wani abu ne na mu’jiza da ya zo daga Muhammad xan Abdullahi haxe da da’awar manzanci, sai muka san cewa ya zo ne da gaskiya kuma ya gasgata shi.

Ismar [7] Annabawa

Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma’asumai ne dukkaninsu, haka nan Imamai (A.S), sai dai mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma ga Annabawa ballantana ga Imamai (A.S).
Isma: lta ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu da kuma kubuta da tsarkaka daga mantuwa koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba, kuma wajibi ne ya tsarkaka hatta daga dukkan abin da yake zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane, ko kuma kyalkyala dariya da sauti mai girma, da dukkan aikin da ake munana yin sa a tsakanin mutane.
Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi shi ne: Da ya halatta ga Annabi ya aikata sabo, ko kuma ya yi kuskure, ko ya yi mantuwa, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare shi, da sai ya zamanto imma dai ya wajaba a yi masa biyayya a aikin da ya yi na sabo ko kuskure, ko kuwa bai wajaba ba, idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, kai mun wajabta ne ma, wannan kuwa abu ne batacce na larurin Addini da na hankali, idan kuwa biyayya gare shi ba ta wajaba ba a kan haka, to kuwa wannan ya kore Annabcin da babu makawa tana tare da wajabcin biyayya har abada.
Ta kowane hali dai aiki ko zance ya zo daga gareshi da ya zama muna tunanin sabo ne ko kuskure, sai ya zama ba wajibi ba ne a bi shi a cikin kowane abu, sai fa’idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan, sai Annabin ya zama kamar sauran mutane da maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da’iman, kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba, babu kuma nutsuwar zuciya da maganganunsa da ayyukansa baki xaya.
Wannan kuwa dalili ne a kan cewa Isma tana tare da Imami, domin kaddarawar cewa shi zababbe ne daga Allah (S.W.T) don shiryar da bayi a matsayin halifan Annabi, kamar yadda zamu yi karin bayani a fasalin Imamanci.

Siffofin Annabi

Mun yi imani da cewa, kamar yadda ya wa.jaba Annabi ya zamanto ma`asumi, haka nan ya wajaba ya zamanto mai siffantuwa da mafi kamalar siffofin xabi’a da hankali waxanda mafifitan su, su ne jarumtaka, da iya tafiyar da al’amuran mutane, da shugabanci, da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba, da bai inganta ba ya zamanto yana da shugabanci a kan dukkan halittu baki xaya ba, ko ya zamanto yana da karfin tafiyar da al’amuran duniya dukkaninta ba.
Haka nan wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa xan halas, amintacce, mai gaskiya, wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun xabi’u kafin aiko shi saboda zukata su nutsu da shi, rayuka kuma su karkata zuwa gareshi, kuma domin ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.

Annabawa Da Littattafansu

Mun yi imani a dunkule da cewa dukkan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da ismarsu da tsarkinsu, musanta Annabcinsu kuwa da zaginsu da isgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda ya ba da labari game da su da kuma gaskiyarsu.
Waxanda aka san sunayensu da shari’o’insu kamar Annabi Adam (A.S) da Annabi Nuhu (A.S) da Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Dawud (A.S) da Annabi Sulaiman (A.S) da Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) da sauran Annabawan da Kur’ani ya ambace su a sarari, ya wajaba a yi imani da su a ayyane, duk kuwa wanda ya karyata xaya daga cikinsu to ya karyata su baki xaya, kuma ya karyata Annabcin annabinmu a kebance.
Haka nan ya wajaba a yi imani da littattafansu da abin da aka saukar musu. Amma Attaura da Injila da suke hannayen waxanda aka canza su daga yadda suka sauka saboda abin da ya auku gare su na daga canje-canje da sauye-sauye, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S), saboda wasan da ma’abuta son rai da kwaxayi suka yi da su, waxanda ake da su yanzu mafi yawancinsu ko ma dukkansu kagaggu ne da aka farar a zamanin mabiyansu bayan wucewarsu (A.S).

Addinin Musulunci

Mun yi imani cewa Addini a wajan Allah kawai shi ne musulunci, kuma shi ne Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari’ar karshe, kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga sa’adar xan Adam, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al’amuran duniya da lahirarsu, kuma mai dacewa ga wanzuwa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa kuma mai kunshe da dukkan abin da xan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar xaixaiku da zamantakewar jama’a da na siyasa. Da yake Shari’ar musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari’a da za tazo ta yi gyara ga xan Adam da ya rigaya ya dulmuya cikin zalunci da fasadi, to babu makawa wata rana ta zo da Addinin musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.
Da an xabbaka Shari’ar musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da aminci ya game ‘yan Adam kuma da rabauta ta game su, kuma da sun kai kololuwar abin da xan Adam yake mafarkinsa na daga walwala, da izza, da yalwa, da annashuwa, da kyawawan xabi’u, kuma da zalunci ya kau daga duniya, soyayya da ‘yan’uwantaka sun yaxu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba xaya.
Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu waxanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa suke tun daga karni na farko, kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummunan hali zuwa mafi muni har zuwa yau xin nan da muke ciki. Ba riko da musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa musulmi wannan mummunan cibaya ba, sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar musulunci, da tozarta dokokinsa, da yaxuwar zalunci, da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki xayansu. Wannan kuwa shi ne abin da ya lahanta yunkurin cigabansu, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala’i da halaka har Allah (S.W.T) ya halakar da su saboda zunubansu. Allah maxaukaki yana cewa:
“Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni’ima da ya ni’imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da yake ga kawukansu”. Surar Anfal 53.
Da faxinsa “Kuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta”. Surar Yunus: 17.
Da faxinsa maxaukaki: “Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Huxu: 117.
Da faxinsa: “Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai raxaxi ne mai tsanani”. Surar Huxu: 102.
Ta yaya ake sauraron Addinin musulunci ya tayar da al’umma daga dogon baccinta, alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Hakika imani, da amana, da gaskiya, da tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, da sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa xan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, da makamantansu, tun farkon assasa Addinin musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama’a-jama’a da kungiya-kungiya, suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya, suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al’amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin Addini da maslaharsu da maslahar al’ummarsu, da faxawa cikin jayayya game da halittar Kur’ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja’a, da kuma cewa aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halicce su ne nan gaba.
Makamantan waxannan gardandamin waxanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasu, babu abin da suke nunawa sai kaucewar musulmi daga madaidaicin tafarki zuwa ga halaka da karewa. Fandarewa ta karu tare da shuxewar zamani, har Jahilci da bata suka mamaye su, suka shagaltu da abu maras kima, da camfe-camfe, da surkulle, da wahamce-wahamce, da kuma yake-yake, da jayayya, da alfahari, sai suka faxa a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau yammacin Turai wayayye, faxakakke, babban sanannen makiyin mlusulunci, ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi, su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kaxai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah maxaukaki yana cewa: “Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Huxu: 117.
A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa, ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu. Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma, kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi [8].
Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam, ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi gama-gari, da zalunci mai xorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da kyawawan xabi’u da ruhin ‘yan’adamtaka, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.

Mai Shara’anta Musulunci

Mun yi imani da cewa ma’abocin sakon Addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu xan Abdullahi, kuma shi ne cikamakon Annabawa, shugaban Manzanni, kuma mafificinsu baki xaya, kamar yadda shi ne shugaban ‘yan Adam baki xaya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci, babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali, babu wani kamarsa a kyawawan xabi’u: “Lalle kai kana kan manyan xabi’u masu girma”. Surar Kalam: 4. Wannan kuwa tun farkon samuwar xan Adam har zuwa ranar tashin kiyama [9].

Kur’ani Mai Girma

Mun yi imani cewa Kur’ani wahayin Ubangiji ne, kuma abin saukarwa daga Allah maxaukaki a harshen AnnabinSa mai daraja, a cikinsa akwai bayanin komai, shi ne mu’ujiza madawwamiya wacce ta gagari xan Adam ya zo da kamarta a balaga, da fasaha, da azanci, tare da abin da ya kunsa na daga hakika da ilimomi maxaukaka, jirkita, ko canji, ko karkacewa, ba sa bujuro masa [10], Kur’anin da yake hannunmu wanda ake karantawa shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W), duk kuma wanda ya yi da’awar sabanin wannan to shi mai kage ne, mai kawo ruxu, kuma mai rikitarwa, kuma ba a kan shiriya yake ba, domin shi Kur’an zancen Allah ne “Wanda karya ba ta zo masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa”. Surar Fusilat: 42.
Daga cikin dalilan da suke tabbatar da mu’ujizarsa akwai cewa, duk sadda zamani ya cigaba, ilimomi da fannoni suka daxa cigaba, Kur’ani yana nan daram a kan xanyantakarsa da zakinsa, da xaukakar manufofinsa, da abin da ya kunsa na tunani, babu wani kuskure da yake bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi, kamar yadda ba ya taba kunsar wani warwara game da hakika da yakini na falsafa, sabanin littattafan da malamai da manyan masanan falsafa komai matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani suka rubuta, sai ka samu wani abu na kuskure a cikinsu da tuntube. Kuma Kur’ani yana nan daram duk sadda aka samu cigaba a sababbin bincike na ilimi da sababbin ra’ayoyi. Kurakurai suna bayyana hatta a rubuce-rubucen manyan masana falsafar Yunan kamar su Sakrato, da¬ Aplato, da Arasto, da duk waxanda suka zo daga bayansu suka yi musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma fifiku na tunani da amfani da kwakwalwa.
Kuma mun yi imani da wajabcin girmama Kur’ani mai girma da xaukaka shi a cikin magana ko a aiki, bai halatta ba a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda ake xauka cewa ita yanki ce daga cikinsa, da kuma nufin cewa daga cikinsa take, kamar yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ba ya taba kalmominsa ko harrufansa: “Babu mai shafarsa sai waxanda suke tsarkakakku”. Surar Waki’a: 79. Shin sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba, ko haila, ko jinin biki, da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne, sai dai idan sun yi wanka ko alwala kamar yadda bayani ya zo dalla-dalla a cikin littattafan fikihu.
Haka nan bai halatta ba a kona shi ko wulakanta shi ta kowace fuska da abin da yake wulakanci ne a ganin mutane, kamar jefar da shi, ko sanya masa kazanta, ko shurinsa da kafa, ko sanya shi a wuri wulakantacce, Idan da wani zai wulakanta shi da gangan, ko tozarta shi, da aikata xaya daga cikin waxannan abubuwan da muka ambata da makamantansu, to shi yana daga cikin masu karyata Addinin musulunci da alamominsa masu tsarki, kuma shi abin hukuntawa ne da fita daga Addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.

Gaskiyar Addinin Musulunci

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin Addinin musulunci zamu iya kayar da shi ta hanyar tabbatar masa da mu’ujizarsa dauwamammiya wato Kur’ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagara badau. Haka nan Kur’ani shi ne hanyar gamsar da kawukanmu yayin da kokwanto ya fara zo mana, saboda irin waxannan tambayoyi da kokwanto ba makawa su taso ga mutum mai ‘yanci a tunani yayin karfafa akidarsa ko tabbatar da ita.
Amma shari’o’in da suka gabata kamar Yahudanci da Kiristanci, ba mu da wata hujja ko hanyar da zamu gamsar da kanmu, ko kuma mu gamsar da mai tambaya game da ingancinsu, domin su waxannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza da ta rage garesu, abin da mabiyan waxannan addinan suke nakaltowa na daga abubuwan mamaki da mu’ujizozi da suke danganta su ga annabawan da suka gabata, su ababan tuhuma ne a kan haka. Kuma babu wani abu da yake cikin littattafan addinan da suka gabata da yake hannunmu a wannan zamani waxanda ake danganta su ga annabawan, kamar Attaura da Injila, da ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya da zai iya zama hujja yankakkiya, kuma dalili mai gamsarwa idan ba musulunci ne ya gasgata da ita ba.
Sai dai mu musulmi ya inganta ne a garemu mu gaskata annabacin ma’abota shari’un da suka gabata, domin bayan gaskatawarmu da Addinin Musulunci, to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abin da ya zo da shi. Kuma a cikin abin da ya zo da shi akwai gaskata annabcin wasu daga annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a baya.
Don haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari’un da suka gabata, domin gaskatawa da shi gasgatawa ne garesu, kuma imani da shi imani ne da manzannin da suka rigaya da annabawa magabata, don haka bai wajaba ba a kan musulmi ya yi wani bincike game da gaskiyar mu’ujizar annabawa ma’abota waxancan shari’o’i, domin abin kaddarawa shi ne ya riga ya yi imani da ita ta hanyar imani da musulunci kuma wannan ya isar.
Na’am, idan da mutum zai yi bincike game da Addinin musulunci ingancinsa bai tabbata gareshi ba, to dole ne a kansa kamar yadda hankali ya wajabta neman sani da ilimi ya yi bincike game da Addinin Kiristanci domin shi ne Addinin karshe kafin Musulunci, idan ya bincika Addinin Kiristanci bai gamsu ba, to sai kuma ya dukufa a kan Addinin da ya gabace shi wato Yahudanci. Haka nan dai zai yi ta binciken addinan da suka gabata har sai ya kai ga yakini da ingancin addinan da suka gabata, ko kuma rashin ingancinsu sai ya yi watsi da su baki xaya.
Sabanin wanda ya tashi a Addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da Addininsa ba zai wadatar da shi ga barin binciken Addinin Kiristanci da Addinin Musulunci ba, dole ne a kansa ya yi bincike a bisa wajabcin hankali ga neman sani. Haka nan kirista ba zai isu da imani da Almasihu (A.S) ba, wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa, ba zai samu uzuri ba da gamsuwa da addininsa ba, ba tare da bincike ba. Domin Yahudanci da Kiristanci ba su kore shari’ar da zata zo bayansu mai shafe su ba. Annabi Musa (A.S) bai ce babu Annabi bayansa ba, haka ma Annabi Isa (A.S) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa [11].
Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da Addininsu kafin su yi bincike game da ingancin shari’ar da ta biyo bayansu, kamar Kiristanci dangane da Yahudanci, ko musulunci dangane da Kiristanci da Yahudanci. Wajibi ne a bisa hukuncin hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga bayansu, idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta su bar Addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su wanzu a kan Addininsu na da, su kuma karkata zuwa gareshi
Amma musulmi kamar yadda muka riga muka faxa idan har ya yi imani da Musulunci, to ba ya bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci Addininsa da kuma waxanda ake da’awa bayansa. Waxanda suka gabata dai domin shi ya yi imani da su, to don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da su, sai dai kawai ya yi hukunci da cewa ita shafaffiya ce da Shari’ar Musulunci, don haka bai wajaba ya yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littattafansu ba. Amma waxanda ake da’awarsu daga baya kuwa dalili shi ne, saboda Annabin Musulunci Muhammad (S.A.W) ya ce: “Babu wani Annabi bayana”. Kuma shi Mai gaskiya ne kuma Amintacce. “Kuma shi ba ya magana a kan son rai, ba wani abu ba ne face wahayi da aka yi masa”. Surar Najmi: 3-4. Don haka saboda menene zai bukaci dalili a kan ingancin da’awar Annabcin da aka yi da’awarsa daga baya idan har mai da’awar ya yi da’awa.
Na’am yana wajaba a kan musulmi -ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da ma’abocin sako (S.A.W), da sabanin mazhabobi da ra’ayoyi, da kuma samuwar kungiyoyi- ya yi bincike, ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a, domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a kamar yadda suka zo. Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari’ar da aka saukar kamar yadda take, alhali musulmi sun sassaba jama’a-jama’a, sun rarraba, babu salla guda xaya, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai iri xaya ba a cikin dukkan mu’amala. Don haka yaya zai yi? Ta wace irin hanya zai yi salla? Da wane ra’ayi zai yi aikin ibada da mu’amalarsa, kamar aure, da saki, da gado, da saye da sayarwa, da tsayar da haddi, da diyya da sauransu?
Kuma bai halatta gare shi ba ya bi ra’ayin iyaye ko ya koma ga abin da zuriyarsa da mutanensa suke a kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah (S.W.T), domin a nan babu wani boye-boye da nuku-nuku, ko sassauci, ko bangaranci. Na’am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da yake kansa tsakaninsa da Allah, ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai zarge shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai”. Surar Alkiyama: 36.
“Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne”. Surar Alkiyama: 14. “Lalle wannan faxakarwa ce, don haka ga wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa”. Surar Muzzammil 19.
Farkon abin da mutum zai tambaya shi ne; Shin ya kama tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Baiti (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya Isna Ashariyya masu bin Imamai sha biyu shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin waxansu daga bangarori daban-daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi, daga cikin mazhabobi hudun ne ko kuma daga wasu mazhabobin daban da suka rushe? Haka nan tambayar zata yi ta zo wa wanda yake da ‘yanci a tunani da zabi har sai ya kai ga wata gaskiya a bar dogaro.


1. “Da rai da abin da ya daidaita ta kuma ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta”. Surar Shamsi: 7-8.
2. Xabi’a al’amura ne kamar ki, so, fushi, yarda, da sauran halayen rai da zuciya.
3. “Manzanni masu bushara kuma masu gargaxi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a kan Allah bayan manzanni kuma Allah mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Nisa’i: 165.
4. “Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandarka sai ga shi tana haxixxiye abubuwan da suke kirkira. Kuma gaskiya ta tabbata abin da suke aikatawa kuma ya baci, Sai aka rinjaye su a nan sa’annan suka juya suna kaskantattu, Kuma aka kifar da masu sihirin suna masu sujada”. Surar A’araf; 117-120.
5. “Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra’ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abin da yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa sai ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai cutar albaras kuma ina rayar da matattu da izinin Allah, kuma ina ba ku labarin abin da kuke ci da wanda kuke taskacewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai”. Surar AI- Imran: 49.
6. Duba faxin Allah maxaukaki: “Kuma idan da mutane da aljannu zasu taru a kan su zo da kwatankwacin wannan kur’anin to da ba zasu zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe”. Surar Isra’i: 88.
“Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda zaku iya wanda ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Hud: 13
kalubalantar su kan su kawo sura guda kamarsa: “Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abin da muka saukar to ku zo da sura xaya kamarsa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Bakara: 23.
Allah Ta’ala Yana cewa: “Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya koma bayan Allah in kun kasance masu gaskiya”. Surar Yunus: 38.
7. Isma shi ne rashin aikata sabo a kowane hali da zamani a rayuwar mai ita, shin a lokacin yarinta ne ko girma ko tsufa, kafin aike da xaukar nauyi ko a lokacin hakan.
8. Faxinsa maxakaki: “Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa duniya bayina salihai ne zasu gaje ta, lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada”. Surar Anbiya’i: 105-106. Hadisai kuwa sun zo da silsila daban-daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.) da kuma Imamai (A.S) cewa: Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Faxima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
9. Amirul muminin Aliyyu Xan Abi Xalib (A.S) ya siffanta shi a xaya daga cikin huxubobinsa yana cewa: “Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mai tsororuwar xaukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai kuma shi ne mabubbugar hikima”. Daga cikin wannan huxubar har ila yau Amirul Muminin (A.S) yana cewa: “Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren ruxewa. Ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo a duwatsu masu tsauri.” (Nahajul Balagha Huduba: 108).
10. Ubangiji maxaukai yana cewa: “Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma lallai Mu masu karewa ne gare shi”. Surar Hijri: 9.
11. Duba faxinsa maxaukaki: “Kuma yayin da Isa xan Maryam ya ce: Ya Bani Isra’la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abin da yake gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da zai zo bayana sunansa Ahmad. Sai dai a yayin da ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne”. Surar Saff: 6.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
8+4 =