Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

BAYYANAR IMAM MAHADI (A.S) DA AYYUKANSAIdan ana magana game da bayyanar imam Mahadi (A.S) kai kace mutum ya zauna ne a gefen koram a wani koren wuri mai fulawowi da furanni yana kuma jin sautin bulbul yana tashi.
A wannan bangaren zamu yi magana game da abin ya shafi bayyanar imam Muhammad Mahadi (A.S) domin mu yi tsinkayo ga haskensa maras iyaka da shamaki kuma maras misali.

Zamanin Bayyanar Imam Mahadi (A.S)

Daya daga cikin abubuwan da suka shagaltar da zukatan mutane masu yawa shi ne cewa imam Mahadi (A.S) a wane zamani ne zai bayyana kuma wane lokacin aka sanya domin aukuwar hakan.
Game da wannan imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: mu a baya ba mu ayyana lokacin bayyana ba, haka nan kuma a nan gaba ma ba zamu ayyana ba. [1]
Don haka ne duk wani wanda yake ayyana lokacin bayyana to makaryaci ne kuma mayaudari, wannan kuma ruwayoyi da dama sun karfafe shi.
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa da daya daga sahabnsa da ya tambaya game da lokacin bayyana: masu ayyana lokaci karya suke fada, masu ayyana lokaci karya suke fada, masu ayyana lokaci karya suke fada. [2]
A wannan ruwayoyi zamu ga imamai (A.S) suna nuni da a karyata masu ayyana lokaci ko a zamanin da ya gabata ko mai zuwa.
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa da daya daga sahabbansa: kada ka sassauta wajen karyata duk wani maiayyana lokai, domin mu ba mu ayyana lokacin bayyana ba ga wani mutum. [3]

Boye Lokacin Bayyanarsa

Kamar yadda yagaba ta ne cewa Ubangiji mai hikima ya boye lokacin bayyanar imam Muhammad Mahadi (A.S), don haka ba makawa akwai wasu hikmomi da suke tafe da hakan da zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:

Dawwamar Fata

Boye lokacin bayyana ya sanya hasken neman bayyana da kauna da fata a cikin zukatan masu sauraro a kowane zamani, tabbas da za a cewa wani daga Shi'a cewa ai bayyana ba yanzu ba ne, to da wannan yana nufin rusa karfin sa na tsayawa kyam gaban fituntunu da suke aukuwa.

Shirya Yanayin Zuwansa

Ba makawa sauraro da yake shi ne mafi griman abin da yake raya motsawa zai iya kasancewa ne a lokacin da ya zamanto a boye, domin idan an bayyana lokacin to wadanda suka san ba zasu kai wannan lokaci ba to lallai zasu dakushe daga gina kai, da kokarin gyara a cikin al'umma.
Don haka boye wannan bayyanar ya sanya fata a cikin ukata mutane na kowane lokaci da zamani, da kuma ganin kokarin gina al'umma domin shirya fagen yanayin bayyanarsa (A.S).
Sannan kuma akwai maslahar boyewa domin idan al'amrin Allah ya samu canji da ikonsa wannan yana iya kai masu sauraro ga barin addini da kuma karyata sakon Allah (S.W.T).
Game da amsar tambayar cewa shin an ayyana lokacin bayyana, Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: wadanda suke ayyana zamanin bayyana karya suke! (ya maimaita wannan maganar) yayin da annabi Musa (A.S) ya tafi daga mutanensa da kiran da Allah ya yi masa a matsayin kwanaki talatin, kuma aka kara masa kwanaki goma, sai mutanensa suka ce: Musa (A.S) bai cika alkawarin da ya dauka ba, kuma ya yi abin da bai kamata ba, to daga nan ne suka yi ridda suka kuma bauta wa dan maraki. [4]

Lokacin Bayyyanarsa

Kowa yana son ya san mene ne zai faru a zamanin da imam Muhammad Mahadi (A.S) zai zo? kuma daga ina ne zai fara motsawa? kuma da wane mutane ne zai samu gwabzawa? kuma yaya zai yi galaba kan dukkan duniya har ya samu kama duniya gaba daya? wadannan tambayoyi ne da suka cika kwakwalen masu bege da sauraro, da masu tambayoyi masu yawa.
Amma fadin abin da zai faru nan gaba a bisa dabi'arsa wani abu ne mai wahala da ba zai yiwu ba ga kowane mutum, sai dai muna iya kawo wasu abubuwan da suka zo a dunkule a ruwayoyi.

Yaya Zai Fara Motsinsa

A zamanin da duhun zalunci ya cika duniya, azzalumai suna rashin mutunci da danniya. Su kuma sauran al'umma suna neman mai ceto wanda zai kama hannunsu; sai ga kira daga sama a cikin daren wata Ramadan yana albishir da zuwan wanda aka yi alkawarin zuwansa [5], a lokacin ne zuciya mai kaguwa zata saurari wayewar wannan gari.
A wannan zamani kuwa Sufyana ya kama yanki mai fadi a Siriya, da Jodan da Palasdin, kuma ga rundunarsa tana kan hanyar Makka domin neman imam Mahadi (A.S), da za a kisfe su a wani wuri mai suna Baida'u. [6]
Bayan shahadar Nafsu zakiyya da wani dan lokaci sai imam Mahadi (A.S) ya bayyana wani saurayi a masallacin Makka mai alfarma, a lokcin rigar manzon Allah (S.A.W) mai albarka tana jikinsa, kuma yana jingina da dakin ka'aba tsaknin rukuni da makam Ibrahim (A.S), bayan godiya ga Allah da kuma salati ga Manzon rahama (S.A.W) da alayensa sai ya ce: Ya ku mutane mu muna neman taimakon Allah ne, kuma duk wanda ya amsa kiranmu, muna neman taimakawarsa.
A lokacin sai ya sanar da kansa ga mutane kuma ya sanar da iyayensa: ku ji tsoron Allah kan hakkokinmu kada ku ki taimaka mana, ku taimaka mana Allah madaukaki zai taimake ku.
Daga nan ne fa sai mutanen sama su riga na kasa amsa masa kiransa, sannan saijama'a jama'a su gangaro domin yi msa bai'a, a lokacin da jibril ya kasance mai rakiya ga imam Mahadi (A.S), sai ga mutane 313 daga sahabbansa na musamman su ma sun zo su yi masa bai'a, bayansu kuma sai wasu mutane rundunar mayaka dubu goma su zo tantinsa domin su yi wa dan manzon Allah bai'a. [7]
Sannan sai imam Mahadi (A.S) ya daga tutar yaki, kuma ya salladu da gaggawa a kan Makka da gefenta, sannan ya kawar da miyagun bayi da masu barna daga wadannan yankuna, sannan sai ya kama hanyar Madina domin samar da adalci da tausayawa ga bayi. Daga nan ne kuma sai ya tafi Iraki birinin Kufa domin ya rike shi cibiyarsa kuma hedkwatarsa wacce daga nan ne zai tafiyar da al'amuran duniya, kuma ya kira dukkan mutanen duniya zuwa ga hukunci da Kur'ani da dokokin Allah madaukaki.
Imam Mahadi (A.S) shi ne mabudin asasi na cimma nasara, domin bayan muminai mataimaka da yake da su, sannan kuma yana da taimakon Allah na musamman, kamar dai lokacin manzon Allah (S.A.W) da aka taimaka masa da tsorata makiya kafin ya yake su, don haka Allah yana da ikon sanya firgici a zukatan makiya, ta yadda ba su da wani iko na yin taho mu gama da imam Mahadi (A.S).
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: imam Mahadi (A.S) zai samu taimako daga firgici da tsoro. [8]
Wani abu mai ban sha'awa shi ne cin nasara da kama baitul mukaddas [9], wannan al'amari mai albarka zai faru ne a lokacin da annabi Isa (A.S) zai sauko daga sama, kamar yadda muka sani shi rayayye ne kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma, kuma zai karfafi gwagwarmayar imam Mahadi (A.S), sannan kuma zai yi masa bai'a ya yi salla a bayansa, wannan kuwa tana nuni uwa ga fifkon imami na goma sha biyu (A.S) ne kan annabi Isa (A.S).
Manzon tsira da aminci yana cewa: Na rantse da wanda raina yake hannunsa, da rayuwar duniya ta kasance saura wuni daya rak, da Ubangiji ya tsawaita wannan rana har sai dana Mahadi (A.S) ya tashi, sannan sai Isa dan Maryam (A.S) ya zo ya yi salla a bayansa. [10]
Da wannan ne da yawa daga Kiristoci zasu yi bai'a ga ajiyar Allah kuma jagoran Shi'a masoya iyalan gidan annabi (S.A.W) imam Mahadi (A.S), kai kana iya cewa; annabi Isa (A.S) ya ajiye wannan rana ne domin ya nuna wa mutanen duniya gaba daya hanyar shiriyarsu.
Koda yake bayyanar mu'ujizozi a hannun imam Mahadi (A.S) yana daga cikin tsarin da ya yi domin kawo shiriya ga duniya baki dayanta.
Don haka ne ma imam (A.S) zai tono allunan Attaura da ba a canja su ba -wato littafin Yahudawa mai tsarki- wadanda aka bunne su a wani wuri a wannan duniya [11], kuma Yahudawa su ga alamomin imamancinsa a wadannnan alluna, sannan sai su yi imani da shi. Haka nan mabiyan sauran addinai zasu ga irin wannan canji mai girma, kuma da ganin wannan kira na imami mai gaskiya da kuma mu'ujizozisa, sai su zo jama'a jama'a suna masu yi masa bai'a, kuma alkawarin Allah madaukaki ya tabbata, musulunci ya daukaka a ko'ina a duniya.
Shi ne wanda ya aiko manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya yi galaba a kan addini dukkaninsa, kuma koda kuwa mushirikai sun ki. [12]
Idan an yi la'akari da abin da aka fada a nan, babu wani wanda zai rage bai mika wuya ba sai azzalumai wadanda suke shirye su tsaya gaba da gaba da gaskiya, wadannan kuwa ba su da karfin tsayawa domin yakar muminai, kuma zasu samu sakamakon aikinsu da takobin adalci ta imam Mahadi (A.S), kuma duniya da mutanenta zasu kubuta daga sharrinsu na har abada.


1. Gaiba, Dusi, fasali 7, h 412, shafi: 426.
2. Abin da ya gabata, h 411, shafi: 425.
3. Abin da ya gabata, h 414, shafi: 426.
4. Gaiba, Nu'umani, babi 16, h 13, shafi: 305.
5. Gaiba, Nu'umani, babi 14, h 17.
6. Biharul anwar, j 53, shafi: 10.
7. Gaiba, Nu'umani, babi 14, h 67.
8. Kamaluddin, j 1, babi 32, h 16, shafi: 603.
9. Ruzgare rahayi, j 1, shafi: 554.
10. Biharul anwar, j 51, shafi: 71.
11. Ruzegare rahayi, j 1, shafi: 522.
12. Tauba: 33.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
2+4 =