Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

ALAMOMIN BAYYANAR IMAM MAHADI (A.S)Juyin juya halin duniya na imam Mahadi (A.S) yana da alamomi, kuma sanin wadannan alamomi yana da muhimmanci matuka, kasancewarsu alamomi ya sanya su alama ta farin ciki da bayyanarsa, kuma faruwar kowanne daga cikinsu alama ce ta haske da yake kusantowa da kuma farin ciki a zukatan masu sauraro. Sannan kuma su tunatarwa ce ga masu shisshigi da karkatattun akidu. Kuma wannan yana iya bayar da damar sanin matsayin da za a dauka ga dukkan wasu fitintinu da suke wakana, a lokaci guda kuwa suna nuna mana karya masu da'awar mahadiyyanci na karya, domin duk wanda ya yi da'awar mahadiyyanci to idan babu wadannan alamomi tare da shi wannan yana nuna karyarsa da tonon asirinsa a fili ne.
Alamomi masu yawa na bayyanar imam Mahadi (A.S) ne suka zo a ruwayoyi masu yawa, amma mu zamu takaita da wasu daga cikinsu ne a takaice.
Imam Ja'afar Assadik (A.S) a wata ruwaya yana cewa: bayyanar imam Mahadi (A.S) tana da alamomi guda biyar: bayyanar Sufyani, da yamani, da kira daga sama, da kashe Nafsuz zakiyya, da kuma kisfe wasu mutane a Baida'u. [1]
Bisa dogaro da wannan ruwaya ne zamu kawo wasu bayanai, duk da cewa ba zamu iya shiga cikin bayanansu dalla-dalla ba.

A- Bayyanar Sufyani

Zuwan Sufyani yana daga abubuwa da suka zo a ruwayoyi masu yawa, shi mutum ne daga salsalar nasabar jikokin Abu Sufyan, wanda zai zo kafin bayyanar imam Mahadi (A.S) a Sham (Siriya, Labanon, Palasdinu a yau) zai kashe mutane babu wani tausayi, kuma duk wani mai gaba da shi zai yi masa kisa na gilla ta mummunar hanya.
Imam Ja'afar Sadik yana cewa: idan ka ga Sufyani, to ka ga mafi munin mutanen duniya. [2]
Zai fara yaki a watan Rajab ne, bayan ya kama Sham sai kuma ya mamaye gefen Iraki, a nan ne zai kashe mutane masu yawan gaske.
Wasu ruwayoyi sun yi nuni da cewa tun daga futowar Sufyani zuwa lokacin kashe shi zai dauki tsawon watanni goma sha biyar ne. [3]

B- Kisfewa A Baida'u (Wuri Ne)

Kisfewa wato a nutsar da mutum kasa ta hanyar halakarwa, amma Baida'u wani wuri ne tsakanin Makka da Madina.
Abin da ake nufi da kisfewa shi ne, Sufyani zai tara runduna mai yawa domin yakar imam Mahadi (A.S), kuma zai nufi hanyar Makka domin ya kashe imam (A.S), Yayin da rundunarsa ta kusa zuwa yankin Baida'u sai ya yi kasa (kasa ta hadiye shi da shi da jama'arsa) ta hanyar mu'ujiza.
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: labari zai zo wa kwamandan sojojin Sufyani cewa imam Mahadi (A.S) ya tafi Makka, sai rundunarsa ta bi shi amma ba ta samun sa, to yayin da ita wannan runduna zata kai Baida'u, sai wani kira ya sauko daga sama: "Kai wannan wuri na Baida'u ka halakar da wadannan mutane!" Sai wannan kasa ta Baida'u ta rufta kasa da su gaba daya. [4]

C- Bayyanar Yamani

Bayyanar wani mutum a yaman tana daga cikin almamomin bayyanar imam Mahadi (A.S), shi wani mutum ne salihi mai yaki domin kawar da munana da karkacewa daga addini.
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: "..Daga cikin tutocin da za a daga kafin bayyanar imam Mahadi (A.S), babu wata tuta da ta fi tutar Yamani shiryarwa, wannan tuta ce ta shiriya tun da tana kira ne zuwa ga ma'abocinku (imam Mahadi) (A.S). [5]

D-Tsawar Shela Da Sanarwa Daga Sama

Wata daga cikin alamomi kafin bayyanar imam Mahadi (A.S) ita ce tsawa daga sama. Wannan kira ne dagasama da ya zo a wasu ruwayoyi da ake cewa da shi; kira ne na Jibril (A.S) da za a ji shi a watan Ramadan [6]. Tun da kowa yana jiran wannan mai gyara na duniya ne, da juyi na duniya kuma kowa yana sauraron faruwar hakan, to daya daga hanyoyin sanin hakan shi ne a sanar da mutane ta hanyar wannan kiran daga sama.
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: imam Mahadi (A.S) ba zai bayyana ba, har sai mai shela ya yi shela daga sama da mutanen gabas da yamma zasu ji shi. [7]
Wannan shela kuwa ita ce asasin farin cikin muminai kuma mai tsoratarwa ga masu munanan ayyuka domin ya zama dole su janye hannayensu daga ayyukan sabo, kuma su isar da kansu cikin rundunar mai kawo gyara na duniya.
Game da abin da wannan kira ya kunsa kuwa akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo, kamar abin da ya zo daga imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: mai shela daga sama zai yi shela da sunan imam Mahadi (A.S) da kuma sunan babansa (A.S). [8]

E- Kashe Nafsuz Zakiyya

Nafsuz zakiyya mutum ne da kai matukar kamala, ko kuma mu cemutum ne mai tsarki da kuma rashin sabo wanda bai taba kashe wani ba, abin da ake nufi da kashe Nafsuz zakiyya shi ne; kafin bayyanar imam Mahadi (A.S) da wani dan lokaci kankane wani mutum mai daraja kuma mai kima maras laifi kuma kubutacce za a kashe shi a hannun masu saba wa imam Mahadi (A.S).
Lokacin faruwan wannan al'amari kuwa a waru ruwaya ya zo cewa; kafin bayyanar imam Mahadi (A.S) da kawanaki 15 ne. imam Ja'afar Sadik (A.S) game da wannan yana cewa: tsakanin bayyanar imam Mahadi (A.S) da kashe Nafsuz zakiyya kwana 15 ne kawai. [9]
Akwai wasu alamomi masu yawa da suka zo a cikin ruwayoyi da wasu suka hada da: bayyanar Dujal (wani mugu ne mayaudari mai batar da mutane) da kuma kisfewar rana da wata a watan Ramadan, bayyanar fitintinu, da kuma tawayen wani mutum daga khurasan.
A wasu littattafai an yi bayanin wannan dalla-dalla. [10]


1. Gaiba, nu'umani, babi 14, h 9, shafi: 261.
2. Kamaluddin, j 2, babi 57, h 10, shafi: 557.
3. Gaiba, nu'umani, babi 18, h 1, shafi: 310.
4. Abin da ya gabata, babi 14, h 67, shafi:289.
5. Abin da ya gabata, h 13, shafi:264.
6. Abin da ya gabata, shafi: 262.
7. Abin da ya gabata, h 14, shafi: 265.
8. Abin da ya gabata, babi 10, h 29, shafi: 187.
9. Kamaluddin, j 2, babi 57, h 2, shafi: 554.
10. Biharul anwar, j 52, shafi: 181 – 278.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
4+6 =