Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

FAI'DOJIN BOYUWAR IMAM MAHADI (A.S)


Muhammad Mahadi Ha’iri Fuur

Hafiz Muhammad Sa’id

Daruruwan shekaru kenan dan Adam ya rasa alherin bayyanar imam Mahadi (A.S) kuma al'ummar musulmi ta ci gaba sa asarar rashin amfanuwa daga jagoran da Allah ya ayyana wa duniya kuma jagoran ma'asumi. Hakika samuwarsa da fakuwarsa da rayuwarsa ta boye da kuma nisantarsa daga duniya dole ne ya zama abin tambaya cewa wane amfani yake da shi ga mutanen duniya. Shin a nan kusa ba za a samu bayyanarsa ba, a kawar da wannan wahala ta shi'arsa da ta kasance sakamakon boyuwarsa?
Wannan tambaya da makamantanta duk suna tasowa ne sakamakon rashin sanin imami ma'asumi da matsayinsa wanda yake hujjar Allah a duniya.
Hakika matsayin imami a duniyar samammu yaya zai kasance, shin almomin samuwarsa sun takaita da bayyanarsa ko kuma shi domin jagorancin mutane ne kawai yake, shin samuwarsa tana da albarka da tasiri ga dukkan samammu ne ko kuwa?

Imam Shi Ne Ginshikin Samuwa

A mahangar Shi'a da kuma koyarwar addini imami shi tsakatsaki domin falalar Allah ga dukkan samammu d ahalittu, shi ne wanda yake ginshiki na tsarin samuwar kuma madogara, idan babu shi to dukkan duniya da 'yan Adam da aljanu da mala'iku da dabbobi da sandararru ba zasu rage ba.
An tambayi imam Ja'afar Sadik (A.S) cewa, shin duniya zata kasance ba tare da imami ba? Sai ya ce: idan duniya ta kasance babu imami to kowane mai samuwa a doronta zai kawu.
Kuma shi a matsayinsa na tsakiya kuma wasila ta isar da sakon Allah da shiryar da mutane zuwa ga kamalar dan Adam kuma dukkan wata falala da albarka ta Ubangiji ta hanyarsa ne take isa zuwa ga kowa.
Wannan kuwa wani abu ne bayyananne domin Allah ya sanya annabawansa hanyar shiryay ga mutane da kuma masu mayewa bayansa, Kuma mun samu daga maganganun ma'asumai cewa samuwar imamai a fadin duniya yana kasancewa ne domin isar da ni'imar Allah da falalarsa zuwa ga dukkan manya da kananan halittunsa, wato dukkan abin da yake isa zuwa ga halittu na falalar Allah (S.W.T) suna samunsa ne ta hannun imamai (A.S). Don haka samuwarsu ta hanyar imamai ne, haka ma ni'imar Allah garesu a tsawon rayuwarsu ta hannunsu ne.
Ya zo a cikin ziyarar jami'a babba game da sanin imami (A.S) cewa: Da ku ne Allah ya bude da ku ne kuma zai cika, da ku ne yake saukar da ruwa da kuma yake rike da sama don kada ta fado kan ma'abotanta.
Don haka albarka da ni'imar samuwar imami ba sai yana bayyane ba, samuwarsa tana da albarkarta koda kuwa yana boye ne, kuma shi ne ruwan rayuwar halittu gaba daya, kuma Allah ne ya so hakan ta kasance da ikonsa da nufinsa, ya sanya mafifitan halittunsa su kasance tsaka-tsaki wajen kwararar ni'imarsa ga sauran bayinsa, kuma a wannan fage babu bambanci tsakanin bayyanarsa da boyuwarsa. Don haka dukkan halittu ba su da wani matsala da zasu samu domin boyuwarsa. Wani abin kayatarwa shi ne an tambayi imam Mahadi (A.S) game da boyuwarsa d akuma amfana daga gareta sai ya ce: Amma yadda za a amfana daga gareni a boyuwata kamar yadda rana take amfanar mutane ne koda kuwa ta shamakance da gajemare.
An kamanta samuwar imam Mahadi (A.S) da rana da take buya a bayan gajimare kuma an kamanta boyuwarsa da kisfewarta, a nan akwai muhimman bayanai masu yawa wadanda zamu yi nuni da wasu a nan.
Rana a tsarin taurari da duniyoyi ita ce a tsakiya, kuma dukkansu suna kewaya ta, haka ma samuwar imami (A.S) kamar cibiyar duniyoyi ce da sauran duniyoyi da taurari suke kewayarta. "Da wanzuwarsa ne duniya ta wanzu kuma da albarkarsa ne aka arzuta halittu, da samuwarsa ne kasa da sama suka tabbata suka tsaya.
Wani lokaci rana ba ta barin haskakawa a kowane lokaci, kuma kowa yana da rana daidai alakarsa da ita, kuma yana amfana daga haskenta, haka nan samuwar waliyyi shuganba wannan zamani yake samar da dukkan ni'ima ta duniya da ta lahira, wacce take daga ubangijin halitta gaba daya, amma kuma kowa yana samu ne daidai gwargwadon kamalarsa yake amfana daga shi.
Idan rana ba ta kasance a bayan gajimare ba, to tsananin sanyi da duhu za su kawu, haka nan ne ma duniya idan ba ta da imami (A.S) a cikinta, to bala'i da wahalhalu da musibu marasa dadi zasu sanya cigaban rayuwa ya kasance wani abu ne da ba zai yiwu ba.
Imam (A.S) a cikin wasikarsa zuwa ga sheikh Mufid (K.S) yana cewa: Mu ba masu barin kiyaye wa gareku ba ne, kuma ba masu mantawa da ambatonku ba ne, ba domin haka ba da bala'o'i sun sauka a kanku, kuma da makiya suna kawar da ku daga doron kasa.
Sabo haka ranar samuwar imami (A.S) tana haskaka wannan duniya, kuma tana kwararai falalar allah ga kowane samamme, kuma a cikin al'ummu musamman musulmi al'ummarsa shi'arsa suka yi imani da shi to sun fi kowa amfana daga albarkarsa kuma zamu kawo wasu misalai game da hakan.

Karfafa Buri

Buri yana da ga cikin jarin tafiyar rayuwa, burinmu shi ne jarinmu na rayuwa kuma nishadinmu mai cigaba ba yankewa, kuma shi ne yake sanya mu motsi da aiwatarwa. Samuwar imami a duniya yana sanya mana burin samun nan gaba mai haske, kuma yana sanya shauki. Shi'a a tsawon tarihinsu sama da shekaru dubu daya da dari hudu, sun fuskanci bala'o'i daban daban, amma burin samun cewa akwai nan gaba mai haske ga muminai ya hana su samun rauni da gajiyawa da tsayawa kyam da kokari da rashin mika wuya. Addini imani ne kuma samun nan gaba ba tatsuniya b ace, nan gaba mai zuwa wacce take mai kusanci da take kusa, domin shugaban wannan zamani mai zuwa a raye yake, kuma a kowane sakand zai iya bayyana, don haka a kodayaushe da ni da kai dole mu kasance a shirye.

Tabbatar Mazhaba

Duk al'umma wata al'umma tana da bukatar samun jagora masani domin kiyaye samuwarta domin takai zuwa ga hadafinta datake buri, domin al'aummar ta kasance mai motsawa karkashin jagorancinsa. Samun jagora wani wani kariya ce mai karfi domin mutane su samu tsari mai karfi wanda yake bayar da kariya ga al'amarinta da ya gabata, kuma karfafa al'amarin da zai zo nan gaba.
Shugaba rayayye kuma mai aiki koda kuwa baya cikinjama'arsa amma ba zai ta ba takatitawa ba wajen nuna mata hanyar da zata bi, kuma zai tsawata mata ta hanyoyi da dama daga kauce wa hanya.
Imam Mahadi (A.S) duk da ya kasance a boyuwa amma samuwarsa wani babban lamari ne wajen kare mazhabin Shi'a. kuma shi yana maganin mummunan makarkashiyar makiya ta hanyoyi da dama, kuma yana kare tunanin shi'arsa daga karkacewa kuma yayin da makiya suke yaudarar ma'abota addinai da akidu ta hanya daban-daban to shi yana kangiya daga kaidinsa ta hannun malmai masu shiryarwa da gyara da yake zaba.
Domin misali bari mu kawo kulawar imam Mahadi (A.S) ga shi'arsa na Bahrain, daga bakin Allama Majalisi:
Wata rana wani komanda makiyin Ahlul Baiti (A.S) yana jagorancin hukuma, wanda yake wazirinsa a gaba da Ahlul Baiti (A.S) kamar ba shi da na biyu, wata rana ya shiga wajen komanda ya taho da wani ruman a jikinsa an rubuta "La'ilaha illal-Lah, muhammadur rasulul-Lah, Abubakar da Umar da Usman da Ali halifofin Manzon Allah". Sai ya nuna wa komanda, shi kuma da ya ga haka sai ya yi murna, ya ce da waziri: Wannan ya nuna lalacewar shi'anci da karyarsa; Yaya kake ganin waziri game da Shi'a'wan Baharain?
Waziri ya ce: Dole ne mu kawo su mu nuna musu wannan, idan sun karba sun fita daga mazhabarsu to shi kenan, amma idan ba haka ba, to sai mu ba su zabi uku, ko su kawo dalili, ko kuma su biya jiziya, ko mu yake su, matansu su koma ribatattu, dukiyoyinsu su koma ganima.
Komanda ya karbi wannan ra'ayi kuma ya kirawo Shi'a, sannan ya nuna musu Ruman ya ce: idan ba ku da wani dalili to zan ribace matanku da dukiyoyinku, ko kuma ku biya jiziya.
Malaman Shi'a suka rasa yadda zasu yi, amma bayan tattauanawa sai suka zabi mutanensu na gari 10 daga cikinsu suka zabi 3, a dare na farko suka aika mutum na farko domin ya je sahara bakin ruwa ya yi tawassuli da imam Mahadi (A.S) amma bai samu wata amsa ba, a rana ta biyu suka aika mutum na biyu shi ma ya dawo babu amsa, amma a rana ta uku da dare suka tura wani mutum mai suna Muhammad dan Isa ya tafi sahara ya yi kuka ya yi addu'a ya nemi taimako daga imam Mahadi (A.S) sai ya ji kira da sauti mai cewa: ya kai Muhammad dan Isa yaya na gan ka a wannan halin? Yaya ka fito a sahara?.
Sai Muhammad dan Isa ya nemi ya nuna masa shi waye.
Sai ya ce: Ni ne ma'abocin wannan zamani, ka fadi bukatarka!
Sai Muhammad dan Isa ya ce: Idan kai ne imam Mahadi (A.S) ka san halina kuma ba ka bukatar wani labari daga gareni!
Sai ya ce: ka yi gaskiya, yanzu saboda wannan musibar ne ka zo nan?
Ya ce: na'am, ka san abin da ya same mu, kuma kai ne imaminmu mafakarmu.
Sai imam (A.S) ya ce: ya Muhammad dan Isa! A gidan wannan wazirin akwai bishiyar ruman. Yayinda ruman ya fara sabonsa, sai ya kwaba tabo da wannan shakalin ya raba shi biyu, kuma a tsakiyarsa sai ya rubuta wadannan kalmomin, ya kuma sanya wannan shakalin a cikin ruman da yake dan karami sabon farawa sannan ya rufe, tun da ruman ya girma ne a cikin wannan shakalin sai wannan zanen ya fito masa! Gobe ka je wajen wannan komanda ka gaya masa ni zan ba ka amsa ta a gidan waziri ne. Idan ka shiga gidan waziri sai ka shiga daki kaza akwai wani buhu fari da wannan shakalin na tabo yake cikinsa, kuma ka nuna wa komanda wannan.
Alama ta biyu wacce take ita ma karamarmu ce, ka gaya wa komanda ya raba wannan ruman din biyu, zai ga ba komai a ciki sai tsutsa da toka!
Muhammad dan Isa ya yi farin ciki da wannan magana, ya koma ya gaya wa Shi'a. A rana mai zuwa suka zo wajen komanda kuma dukkan abin da imam (A.S) ya gaya masa sai da ya tabbatar da su. Da komanda ya ga wannan karamomi sai ya zama Shi'a kuma ya bayar da umarni aka sare kan wannan waziri mai yaudara. [1]

Gina Kai

Kur'ani mai girma yana cewa: "ku yi aiki, da sannu Allah da manzonsa da muminai zasu ga ayyukanku". [2]
Ya zo a ruwayoyi masu yawa cewa: Abin da ake nufi da muminai a nan su ne imamai ma'asumai.
Don haka ne ayyukan mutane suke a gaban imam zaman (imam Mahadi). kuma shi yana ganin wadannan ayyuka, wannan kuwa wani nau'i na tarbiyya ne da yake iya ba wa Shi'a damar gyara ayyukansu gaban Allah da kuma imaminsu, domin su gyara ayyukansu kuma su kawar da dukkan wani sabo. Don haka ne ma duk sadda mutum ya fuskanci makomarsa to ya fi tsarkaka kuma zuciyarsa ta fi tsakarka da samun haske, wannan kuwa abu ne wanda yake afili kuma bayyananne.

Madogarar Ilimi Da Tunani

Imamai ma'asumai su ne masu ilmantarwa da bayar da tabbiyaya ga al'umma kuka mutane suna sha daga dadadan ruwansu a lokacin boyuwar imam Mahadi (A.S) duk da cewa ba ma iya samun sa kai tsaye mu amfana daga garesu amma dai shi ne ma'adinin ilimin Allah wanda dukkan matsalolin ilmin da tunani na Shi'a shi ne yake bude su ya warware. Kuma a lokacin boyuwarsa karama an samu tambayoyi masu yawa daga malamai da mutane da ya amsa su ta hanyar tambyoyi da sa hannunsa da suka shahara.
A amsar wasikar Ishak dan Ya'akub imam Mahadi (A.S) yana cewa: Ubangiji ya shiryar da kai kuma ya tabbatare dakai, amma masu musunmu da ka tambaya daga 'ya'yan amminmu ka sani cewa Allah ba shi da alakar jini da wani, duk wanda ya yi musuna, ba ni, ba shi, kuma karshensa kamar na dan annabi Nuhu (A.S) ne… amma dukiyarka matukar ba ka tsarkake ta ba, to ba zamu karba ba… Amma dukiyar da ka aiko mana daga irin wannan mai tsarki ce kuma zamu karba…
Duk kuma wanda ya ci dukiyarmu ya dauke ta a matsayin halal to ya ci wuta ne… amma yadda za a amfana daga gareni kamar yadda ake amfana daga ranane da take boye bayan gajimare, kuma ni aminci ne ga mutanen duniya kamar yadda taurari suke aminci ga mutanen sama. Kuma duk abin da ba shi da amfani gareku kada ku tambaya game da shi, kuma kada ku wahalar da kanku wajen sanin abin da ba a nema daga gareku ba, kuma ku yi addu'a matuka domin neman bayyanata, wannan shi ne farin cikinku, aminci tabbata gareka ya Ishak dan Ya'akub, kuma aminci ya tabbata ga dukkan wanda ya bi shiriya.
Bayan boyuwa karama saudayawa malaman Shi'a sun yi tambaya game da matsalaoli masu yawa kuma sun samu amsa daga imam (A.S).
Mir Allama daya daga daliban Mukaddis Ardabili yana cewa: Wata rana rabin da re a Najaf a haramin imam Ali (A.S) na ga wani mutum yana tafiya zuwa harami sai na tafi wajensa, koda na yi kusa da shi sai na ga wani tsoho ne da wani malami mai suna Ahmad Mukaddis Ardabili, sai na boye kaina.
Ya tafi kusa da haram sai kofa da take kulle, nan take ta bude masa sai ya shiga, sai bayan wani lokaci ya fita ya tafi Kufa.
Sai na bi shi a baya ta yadda ba zai ganni ba, kuma ya shiga masallacin Kufa kuma sai ya kusanci wurin da a nan ne aka sari imam Ali (A.S) sai bayan wani lokaci ya fita daga wurin sannan sai ya tafi Najaf kuma ni duk a hakan ina ta binsa, har ya kai masallacin Hanane, sai tari ya kama ni, da ya ji tarina sai ya juyo ya kalle ni ya ce: Ko mir Allama ne? sai na ce: na'am. Sai ya ce; me kake yi a nan? Sai na ce: ai tun lokacin da ka shiga haramin imam Ali (A.S) ina bin ka a baya, don Allah ina hada ka da girman wannan kabari sai ka gaya mini me ya faru tun da farko na daga sirrin wannan al'amari da ya faru!
Sai ya ce: da sharadin matukar ina raye ba zaka fada wa kowa ba! Sai na dauki alkawari, sai ya ce: wani lokacin mas'aloli sukan rikice mana ta yadda ba yadda zamu samu warwara sai ta hannun tawassuli da imam Ali (A.S), a yau ma wata mas'ala ce nake tunanin warware ta don haka sai na ga bari in tafi wajansa in yi tambaya.
Amma da na kusanci harami sai na ga kofa ta bude kamar yadda ka gani, sai na shiga na yi kuka domin in samu amsa, sai na ji sauti daga kabarin ya ce: ka tafi masallacin Kufa domin imam Mahadi (A.S) yana can, kuma shi ne imamin zamaninka, don haka ka tambaye shi.
Sai na tafi masallacin Kufa na tambaye shi kuma na samu amsa, yanzu haka zan tafi gidana ne.

Shiryarwa Ta Badini Da Kuma Zurfafa Cikin Ruhi

Imami shi ne hujjar Allah kuma aikinsa shi ne shiryar da mutane, kuma kokarin sa shi ne ya shiryar da mutane domin su samu wannan shiriya din, kuma wani lokaci yana alaka da mutane a fili domin isar da al'amarin Allah kuma yana nuna musu hanyar rabauta ta duniya da lahira, wani lokaci kuma yana amfani da karfinsa domin ya sanya wa mutane tasiri ta hanyar badini kuma yana karkatar da su zuwa ga alheri ta irin wannan hanya wacce take ita ce hanyar kamala da shiriya. A wannan bangare babu wata bukata ga shiriya ta zahiri abin da ake so shi ne shiriya ta badini. Imam Ali ya yi bayanin wannan da cewa:
Ubangiji ba don akwai hujjarka a duniya ba wanda zai kama hannun halittu zuwa ga shiriya… idan da koda ba mu ga wannan samuwa ta imami a zahiri ba amma babu kokwanto muna ganin koyarwa da tarbiyyarsa a zukatan muminai kuma su suna aiki ne bisa wannan asasin.
Imami boyayye yana aiki domin shiryar da mutane domin motsawa da kuma samar da sauki karkashin tarbiyyantarwarsa ta musamman domin su shirya wa zama cikin tawagar wannan imami, kuma wannan duk yana faruwa ne don albarkar samuwar imami boyayye.

Kariya Daga Bala'o'i

Babu wani kokwanto cewa asalin asasin rayuwa shi ne kariya da aminci kuma faruwan bala'o'i suna sanya rayuwa ta fada cikin hadarin karewa kuma sarrafa wadanan musibu da kawar da su duk da abubuwan na zahiri suna iya tasir wajen ahaka mama abubuwan badini su suka fi taka rawa a ciki, kuma akwai ruwayoyi na magabata masu yawa da suka zo game da samuwar imami wanda yake shi ne aminci ga mutanen duniya gaba daya.
Imam Mahadi (A.S) yana cewa: ni ne aminci ga mutanen kasa…
Samuwar imami yana hana saukar musifu da jawo azabar Allah da fushinsa da sukan iya sauka sakamakon ayyuka da fasadi da barna da mutane suke yi.
Kur'ani mai girma yana fada cewa: Allah ba zai azabtar da su alhalin kana cikinsu…
Imam Mahadi (A.S) shi ne asasin bayyanar rahamar Allah kuma da shi ne ake kare al'umma daga bala'o'i manya musamman ga al'ummar da take shi'arsa, duk da cewa su kansu Shi'a ba kasafai sukan kula da wannan karamomi nasu ba, ko su fahimci cewa wani hannun boye ne ya taimaka musu.
Imam Mahadi (A.S) yana cewa: Ni ne cikamakon wasiyyai, kuma da ni ne Allah yake kare bala'i daga ma'abotana da Shi'ata.
Zamu iya gani a kwanakin juyin musulunci da kuma yakin daular musulunci ta Iran sauadyawa mabiya imam Mahadi suka tsallake wani babban tarkon da makiya suke danawa kuma suka karya hukuncin nan na dokar hana yawon dare a 21 ga watan Bahaman 1357, da umarnin imam Khomaini, kuma duba fadowar helikwaftan Amurka a saharar Dabs a 1359 H.Sh. da kuma gano juyin nan na 21 ga watan Tir 1361, da kuma kasawar makiya a yakin shekaru takwas na yaki.

Imam Mahadi (A.S) Ruwan Raham

Abin yin alkawari ga duniya kuma alkibalar burin dukkan muslmi kuma abin so gun Shi'a wato; imam Mahadi (A.S) kodayaushe yana kula da halayen mutane ne, kuma boyuwar wannan ranar rahama da tausayi ba ya hana ta bayar da rayuwa da karfafa ga masoyanta ta bayan gajimare, kuma ba ya hana ta yi walimar garar baki ga masoyanta. Wannan wata ne shi mai soyayya da kauna mai dauke bakin cikin masu neman taimamkonsa dagamasoyansa, kuma shi ne mai warkar da ciwon masu miki da suka kwanta a gadajen asibiti da suka rasa magani, kuma wani lokaci yakan nuna wa wadanda suka bace hanya a daji. Shi ne mai lallashin zukatan masu sauraronsa, kuma mai ruwan rahamar Allah ga masoyansa. Duba ka ga abin da yake roka wa masoyansa wajen Allah madaukaki da fadinsa: ya kai wanda yake shi ne hasken haske, ya mai juya al'amura ya mai tayar da kaburbura, ka yi tsira da aminci ga Muhammad da alayen Muhammad ka sanya mini ni da shi'ata mafita daga wannan kunci, kuma da farin ciki daga bakin ciki, ka yalwata mana tafarki, ka kuma saukar mana abin da zai faranta mana, ka kuma yi mana abin da kake ahlinsa ne kai, ya mai baiwa.
Wadannan abubuwa da aka kawo suna nuna samuwar imami a fakuwa da buya, kuma wadanda suke samun haduwa da shi su ne wadanda suke da cancanta da samun dacewa ga hakan.

Daga LIttafin: Imam Mahadi Adon Halitta / Mawallafa: Muhammad Mahadi Ha’iri Fuur-Mahadi Yusufiyan-Muhammad Amin Bolo Dastyan. Mafassari: Hafiz Muhammad Sa'id

1. Biharul anwar: j52, shafi 178.
2. Tauba: 105.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
6+4 =