Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

HADA ALLAH DA WASU BAYINSA NA KWARAI DON NEMAN BIYAN BUKATA


Ja’afar Subhani

Yunus Muhammad Sani

Kur’ani yana ambatar wasu gungu Masu hakuri, masu gaskiya, masu wadatar zuci, masu ciyarwa, masu neman gafara da asubahi, ga abin da kur’anin yake cewa: “Kuma masu Hakuri da masu gaskiya da masu bautar Allah da masu bayar da imfaki da masu neman gafarar Ubangiji da asubahi”[1]
Duk wanda ya tashi da tsakiyar dare ya yi sallar nafila ya yi kuka zuwa ga Allah yana mai cewa: “Ya Allah ina rokonka don darajar masu neman gafararka da asubahi, ka gafarta mini zunubbaina”
Hada Allah madaukaki da matsayin wasu daga cikin bayinsa masu kadaita shi, kuma suka nutse a wajen kadaita shi, ta yaya zai zama shirka da Allah a cikin bauta? A bahsimmu na baya mun bayyanar da ma’anar bauta da shirka, muka ce bauta ita ce mutum ya kaskantar da kansa a gaban wani wanda ya dauke shi a matsayin Allah ko kuma ya dauka shi ne yake tafiyar da wasu abubuwa a cikin duniya’ (rububiyya) alhalin wanda yake hada Allah da matsayin annabawa da manyan bayin Allah sam ba shi da wannan akida, domin kuwa ya dauke su a matsayin manyan bayin Allah masu biyayya gare shi, ba alloli ba.
Tare da bayyana hakikanin bangare na farko wato hada Allah madaukaki da wasu daga cikin bayinsa masu biyayya gare shi ba yana nufin bauta ba ne, don haka dole ne mu ba da muhimmanci a cikin bangare na biyu wato yin hakan ya halatta a shari’a ko kuwa? Domin kuwa zai iya yiwuwa wani abu ba bauta ba ne ga wanin Allah amma bai halatta ba a shari’a.
Amsar wannan tambaya kuwa dole ne mu koma zuwa ga ruwayoyi da tarihin rayuwar rayuwar Manzo da ta iyalansa (a.s) a nan zamu bayar da dalilai da suke tabbatar da halascin wannan al’amari na hada Allah da bayinsa na kwarai.

1-A cikin addu’ar da Manzo ya koyar da wani makaho, wacce a baya muka yi magana a kanta, a cikin wannan addu’a munga yadda aka hada Allah da manzonsa, domin kuwa ga abin da Manzo ya ce masa: ka yi alwala sannan ka yi salla raka’a biyu sai ka karanta wannan addu’ar kamar haka: “Allahumma inni as’aluka wa atawajjahu ilaika bi nabiyyika Muhammadin nabiyyir rahama”. Wato “Ya Allah ina rokonka kuma ina fuskantarka da manzonka Muhammad annabin rahama”. A cikin wannan hadisi zamu ga yadda Manzo ya koyar da wannan makaho wannan addu’a yadda a fili yake hada Allah da manzonsa kan ya biya masa bukatarsa. Idan har hada Allah da bayinsa na kwarai ya haramta, shin Manzo zai koyar da wannan makaho addu’a kamar haka?

2-Abu Sa’id khudri ya ruwaito daga Manzo (s.a.w) yana cewa: Duk wanda ya fita daga gidansa zuwa masallaci domin ya yi salla sai ya karanta wannan addu’a Allah zai yi masa kulawa ta musamman sannn mala’iku dubu saba’in zasu ci gaba da nema masa gafara a wajen Allah, wannan addu’a kuwa ita ce kamar haka: “Allhumma inni as’aluka bi hakkis sa’ilina alaika, wa as’aluka bi hakki mash’yaya haza.. “ [2]
Ma’anar wannan addu’a kuwa shi ne kamar haka; “Ya Allah ina rokonka albkarcin wadanda suke rokonka, kuma ina rokonka da albarkacin wannan tafiya tawa…”
Mai yiwuwa wasu su ce ai wannan hadisi mai rauni ne, wato su ce a cikin danganen hadisi a kwai Atiyya Aufi, alhalin laifinsa kawai shi ne ya kasance masoyin iyalan gidan Manzo ne, Sannan kuma Ibn khazima ya ruwaito wannan hadisi a cikin sahihi dinsa ta ingantacciyar hanya a wajen AhlusSunna. [3]

3-Umar Bn khattab yana ruwaitowa daga Manzo (s.a.w) inda yake cewa: Lokacin da annabi Adam ya yi kuskure (bai aikata abin da ya kamata ya yi ba) sai ya fuskanci Ubangiji yana cewa: Ya ubangijina, ina rokonka albarkacin manzoka muhammad da ka gafarta mini”Sai Allah madaukaki ya ce masa Ya Adam ta yaya ka san Muhamma duk da cewa ban halicce shi ba, sai Adam ya ce masa: Ya Allah lokacin da halitta ni ka hura mini rai sai na daga kaina a sama, sai na ga an rubuta “La’ilaha illallahu’muhammad rasulullah” a kan kafar al’arshi, sai na san cewa lallai ba zaka hada sunanka da na wani ba sai wanda ya fi soyuwa gareka a cikin halittu…[4]
Babu wata matsala dangane da danganen wannan hadisi ko kadan, domin kuwa mustadrikul Hakim wanda aka ruwaito wannan ruwaya daga gareshi matsayinsa kamar matsayin sahihi Bukhari da Muslim yake.
Wadannan su ne ruwayoyin da suka bayyanar da tarihin tsayuwar Manzo (s.a.w) Sannan idan muka koma zuwa ga addu’o’in da suka zo mana daga A’immatu Ahlul baiti (a.s) zamu tabbatar da wannan a fili, domin kuwa sun kasance suna rokon Allah da albarcin waliyyansa a kodayaushe. Idan muka koma zuwa ga Sahifa sajjadiyya zamu samu wannan a fili.

4-Imam zainul Abideen (a.s) ga abin da yake cewa yayin da yake munajati da Ubangiji: “Ya Allah albarkacin wanda ka zaba daga cikin bayinka, albarkacin wanda ka zaba don kanka, Ya Allah don albarkacin wadanda ka zaba daga cikin bayinka, Albarcin wadanda ka zaba domin a san matsayinka da su, ya Allah albarkacin wadanda ka hada biyayyarka da tasu, albarkacin wadanda ka sanya adawa da su adawane da kai”. [5]

5- Imama Sadik (a.s) ya je ziyar kakansa Imam Ali (a.s) a Najaf, bayan ya yi gaisuwa ga Imam sai ya fuskanci Allah ya roki Allah shi wasu abubuwa wadanda sun zo a cikin wannan ziyara, a karshen addu’ars ga abin da yake cewa: “Ya Allah ka karbi addu’ata ka kuma karbi yabona. ya Allah ka hada ni tare da waliyaina, albarkacin Muhammad, Ali, Fadima, da Hasan, Da Husaini (a.s)”. [6]
Irin wannan addu’a ta hanya neman albarkacin manyan bayin Allah da yawa sun zo ta hanyar Imam Ali (a.s) da ‘ya’yansa tsarkaka, don haka babu bukatar kawo misalai masu yawa a kan haka.
A nan mun ga dalilai da dama wadanda suke nuni da halascin irin wannan addu’a ta hanyar hada Allah da wasu daga cikin waliyyansa. Yanzu zamu yi Bahasi don bincike a kan dalilan da wasu masu haramta irin wannan hada Allah da bayinsa na kwarai, kamar haka:

Babu Wani A Cikin Bayi Wanda Yake Da Hakki A Wajen Allah

Suna cewa: Rokon Alla ta hanyar wani matsayi da wani yake da shi a wajen Allah sam ba ya halatta, domin kuwa babu wani daga cikin bayi wanda yake da hakki a kan Allah. [7]
Amsa: Ana iya bayar da amsar wannan magana ta hanyoyi guda biyu kamar haka; Hanya ta farko kuwa ita ce, akwai ruwayoyi da dama wadanda suke nuni da cewa bayin Allah suna da hakki a kan Allah madaukaki, a nan zamu yi nuni ne da wasu daga cikin kamar haka:
“Taimakon Muminai wani hakki ne a kanmu”. [8]
“Alkawarin hakki a kan Allah yana cikin Attaura da Injila”. [9]
“Tseratar da muminai hakki ne a kanmu”. [10]
“Lallai hakkin karbar tuba ya wajaba a kan Allah ga wadanda suka kasance suna aikata mummuna a cikin jahilci”. [11] Shin wannan ya inganta kawai saboda mutum yana da wannan tunanin ya zamana mun yi tawilin wadannan ayoyi?

Misalai Daga Hadisai

1- Hakki ne a kan Allah ya taimaki wanda ya yi aure saboda ya kiyaye kansa daga haram. [12]
Manzo (s.a.w) yana cewa: “Hakki ne a kan Allah ya taimaki wasu mutane guda uku: Mai yaki a tafarkin Allah, bawan da suka yi yarjejeniya da ubangijinsa zai ba shi wasu kudi ya ‘yanta shi, da wanda ya yi aure domin ya kiyaye kansa daga haram”. [13]

2- Shin ka san hakkin bayi a kan Allah”. [14]
Hanya ta biyu: Gaskiya ne babu wani daga cikin bayi wanda yake da hakki a kan Allah domin kuwa bayi ba wasu da wani abu ballantana su kasance suna da hakki a kan Allah, Amma Allah wanda yake mai girma ta hanyar tausayi da rahamarsa ya sanya wannan hakkin a kan bayinsa, sannan ya bayyanar da kansa a matsayin wanda bayinsa suke binsa bashin wannan hakkin. Wannan tausayi da rahama ta Ubangiji kuwa ba ta takaita da wannan ba kawai, duk da cewa shi ne mamallakin kowa da komai amma yana daukar bashi da rance daga bayinsa, kamar inda yake cewa: “Wa zai bai wa Allah kyakkyawan rance sai ya nunka masa nunki-nunki banunki mai yawa”. [15] Fahimtar gaskiyar koyarwar muslunci tana tare da bin diddigi da kulawa ta musamman.

Wahabiyanci / Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani - Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

1. Aali Imaran
2. Sunan ibn majah:1/256hadisi na 778 musnad Ahamad:3/21
3.Ta’aliki a kan suna ibn majah na Muhammad Fu’ad Abdul baki.
4. Mustadrikul Hakim:2/615 Durrul mansur:1/59 Ruhil ma’ani:1/217.
5. Sahifa sajjadiyya:addu’a ta 47.
6. Misbahul Mujtahid:682 ta sheikh Tusi
7. Kashful irtiyab:331.
8. Rom:47
9. Tauba:111
10. Yunus:103
11. Nisa:17
12. Jami’us Sagir Suyudi:2/33
13. Sunan Ibn majah:2/841
14. Nuhaya Ibn Asir:kalmar Hakk
15. Bakara:245Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+2 =