Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

ADALCIN SAHABBAI: MANUFA DA RADDI


Sa id Yakub

Hafiz Muhammad Sa’id

Bibiyar wannan littafin bugun “sharikatu shamsul mashriq” a bairut na Lauya ahmad husain yakub, yana da muhimmanci wajen sanin alaqar rayuwar sahabbai da aqidar musulunci alaqa mai qarfi, domin an sanya aikinsu ya kasance xaya daga aqida, da zaran manzo (s.a.w) ya yarda da wannan aikin ko kuma ya yi shiru gareshi, ta yadda wannan al’amari ya shiga cikin isxilahin ma’anar sunnar annabi (s.a.w).
Wannan al’amarin fikirar cewa dukkan sahabbai adalai ne ya kai zuwa ga samara da wani savani mai muni day a kai ga rabuwar al’umma gida biyu, kuma a bisa gaskiyar lamari wannan fikira bat a kasance a lokacin annabi (s.a.w) ba domin annabi ya tona asirin wasu kuma ya kushe wasu da kakkausan suka, haxa da ayoyin kur’nai masu girma da suke Magana kan munafukai da babu wanda ya san su sai allah, tare da cewa wasu daga cikinsu ko kuma mafi yawansu allah ya sanar da manzonsa su da sunayensu kuma suna rayuwa a madina da gefenta.
Don haka sai binciken tarihi ya kasnce wani vangare na aqida ba kawai bincike na rayuwar mutane ta tarihi ba.
Sahabbai mutane ne da suke kuskure suke kuma yin daidai, babu wanda yake ma’asumi sai Annabi (s.a.w) sai kuma wanda Allah (S.W.T) ya yi shedar tsarkake shi daga dauxar savo. Kamar yadda ya zo a cikin ingatattun littattafai cewa “da sannu za a kore wasu mutane daga waxanda suka yi sahibanci na suka gan ni, sai in ce: ya ubangiji sahabbaina! sahabbaina! Sai a ce da ni: Kai ba ka sani abin da suka yi bayanka ba”.
Muna iya ganin wannan hadisi kuma da aka yi qagensa aka qirqira da yake cewa: “Sahabbaina kamar taurari ne duk wanda kuka yi koyi da shi zaku shiriya”. Don haka ne sai ya kasance wajibi ne a yi bincike game da adalcin sahabbai ta kowane janibi domin kiyaye sunnar annbi maxaukakkiya, haxa da kuma lamarin nan na kiyaye amanr tarihin al’umma, zuwa ga abin da ya haxa da bayanin ainihin abin da ya jawo savani a cikin musulunci wanda ya faru kai tsaye bayan wafatin Annabi (s.a.w). da wannan ne zamu gane muhimmancin wannan bahasi na adalcin sahabbai.
Mas’alar adalcin sahabbai yana nufin daidaiton dukkan sahabban Manzon Allah (s.a.w) a adalci, wannan kuwa yana nufin cewa dukkansu masu gaskiya ne masu jihadi tsarkaka …, sai mai vuya yana gudun qin zuwa yaqi ya zama daidai da wanda yake zuwa yaqi, wanda ya musulunta da son saa da gamusuwarsa sai ya kasance xaya yake da wanda ya musulunci ranar buxe Makka wato ranar da ya ga mutuwa bai da mafaka sai musulunci, sannan sai mai savo ya zama daidai da wanda yake bin Allah, wanda yake yaro yayin wafatin Annabi (s.a.w) sai ya kasance kamar wanda ya zauna da shi ne ya kare musulunci ya ji maganganunsa.
Don haka ne sai sayyidina Hamza ya yi daidai da Wahashi wato; da wanda aka kasha da wanda ya yi kisa sun zama a daraja xaya kenan kamar yadda duk sahabbai zasu zama xaya kenan, sai kuma wanda Annabi ya la’anta kamar Abu Sufyan, da Abul Asi da kuma Ibn Abi Sarh wanda Manzo (s.a) ya yi umarnin a kashe shi duk inda yake, duk tun da sahabbai ne sai su yi daidai da waxanda suka yi yaqi suka wahala musulunci ya tsayu a kan kafaxunsu, don haka ne ma, mawallafin sai ya ga ya dace ya kasa sahabbai gida biyu:
Na farko ya haxa da waxanda suke su ne mafi girman sahabbai waxanda musulunci ya tsayu da guminsu da taimakon Annabi (s.a.w) da kuxinsu da rayukansu har suka koma zuwa ga ubangijinsu, to babu shakka waxannan su adalai ne.
Na biyu; sauran sahabbai tare da samun bambancin da yake tsakaninsu da babu wanda ya san shi sai Allah maxaukaki.. koda kuwa wasu an san zahirinsu, sannan kuma ga munafukai da an san wasunsu. Kuma goma sha biyu daga cikinsu sun so kashe Manzon Allah (s.a.w) amma ya qi kashe su, saboda kada a ce Muhammad (s.a.w) yana kashe sahabbansa (sai wannan ya sanya qyamar musulunci gaba xaya babu wanda zai sake shigarsa).
Mas’alar fifikon tsakanin juna ba wani baqon abu ba ne tun da kur’ani mai ya zo da shi yayin da yake cewa: “Haqiqa mun fifita sashen annabawa a kan sashe” da faxinsa: “Waxanda suka ciyar kafin buxin Makka ba zasu I daidai da waxanda ba su ciyar ba, waxancan su ne suka fi daraja”.
Daga cikinsu akwai wanda ka sayar masa da haddi ko a zamanin Manzo (s.a.w) ko kuma lokacin halifofi.
Da wannan ne marubuci wato; Ustaz Yakubu ya fara wannan rubutun na batun “adalcin duka” da cewa wannan al’amari ne da siyasa (ta banuUmayya) ta qirqira, kuma aka yaxa ta ga kowa domin cimma hadafinsu , suka kai matuqar kaiwa ga cewa duk wanda ma ya kawo wani kuskure da wani sahabi ya yi to ya fita daga addini ba a ciyayya da shi ko shayayya ko kuma a yi masa salla yayin da ya mutu.
Babu makawa batun adalcin dukkan shahabbai ya sava da dalilin hankali na kur’ani mai girma da ma abin da yake faruwa a yau. Idan muka koma ayoyin kur’ani sai mug a suna Magana da suka kakkausa kan wasu mutane na Madina da sun zauna tare da Annabi (s.a.w) kuma su ma sahabbai ne, don haka muna iya ganin maganar Abdullahi xan Umar yayin da yake cewa: “mu muna tare da wanda ya yi galaba” a yaqin Harra a Madina a shekara ta 63 Hijira, ya faxe ta ne bayan yawan waxanda aka kashe na xaruruwan sahabbai ne a hannun sojojin Umayyawa qarqashin jagorancin wani sahabi ne mai suna Maslama bn Uquba wanda Yazidu xan Mu’awiya ya turo, kuma shi Ma’awiya ne wanda Ibn Hisham a cikin tarihinsa yake faxa game da shi cewa; ya yi wa xansa Yazid wasiyya da cewa idan yana son mulkinsa ya kafu to sai ya gama da mutanen Madina .. ga kuma cewa shi ma sahabi ne amma ya yi umarnin a riqa zagin imam Ali (s.a) wanda yake a matsayin sahabi mai daraja a kan mimbari, haxa da cewa shi ne farkon wanda ya yi umarnin a qirqiri hadisai na qarya a jingina wa Manzon Allah (s.a.w) domin kawai kafa qarfin mulkinsa da kuma gama wa da abokan hamayya da maqiyansa.
Haxarin wannan ra’ayin shi ne mayar da maganganun sahabbai a matsayin madogara bayan kur’ani da hadisan Annabi (s.a.w), abu hanifa yana cewa: “idan ban samu wani abu ba a littafin Allah ko sunnar Annabi (s.a.w) sai in yi riqo da faxin sahabbai idan kuwa ra’ayoyinsu suka rarrabu suka yi savani sai in xauki maganar wanda na so.
Haka nan aka mayar da waxancan maganganu suka kasance hujja kuma wani vangare na shari’a kuma suka kai zuwa ga tsarkakewa, yayin da Ahlul Baiti (s.a) suke cewa idan mun yi Magana ba ma magana sai da abin da ya yi daidai da littafin Allah, kuma dukkan hadisin da aka danganta mana bai yi daidai da littafin Allah ba to ku jefar da shi.
A fasali na uku kuma mawallafin ya kawo wasu misalai na yaqin da ya faru tsakanin rundunar imam Ali da mu’awiya, ya yi bayani sosai a nan game da adalcin sahabbai da kuma kore hakan ta hanyar qiyastawa ta mahangar adalci. Sannan ya kawo batun da ake yi domin tabbatar da adalci ga duk wani sahabi ko mai abin da ya yi, da yadda aka danganta wa zubair da xalha cewa sun tuba da abin da suka yi domin dai a tabbatar da wannan adalcin.
Sannan ya kawo cewa; bayyanar Manzon Allah (s.a.w) ba ta tsayar da yaqin da yake gudana tsakanin umayyawa da hashimawa ba, ya kara hasa wutar ne ma, don haka ne aka samu masu goyon bayan umayyawa suna neman hana hashimawa kaiwa ga jagoranci ta kowane hali ne. don haka ne ma aka yi nesa da zuriyar Annabi (s.a) aka hana su komai na jagorancin al’umma.
Amma vangaren siyasa na wannan ra’ayin ya shafi haxin kan musulmi qarqashin halifa xaya wanda yake al’amari ne da ya shafi haxin kan al’ummar musulmi, kuma hatta da halifancin usmaniyya sai ga malaman musulmi suna ganin sa halifanci koda kuwa bai yi daidai da tsarin da musulunci ya zo da shi ba. Al’amarin ya kai ga lokacin da Umar bn Abdul’aziz ya hana la’anar imam Ali (s.a) a kan mimbari sai da malaman musulunci suka nuna yardar su da ganinsu na cewa ya vata sunnar Annabi (s.a.w) ne.
Amma tsarin musulunci na siyasa da ya yi daidai da kur’ani mai girma yana faxar cewa; Annabi (s.a.w) ya bar halifansa kuma Allah ya umarce shi da ya ayyana shi ga al’umma bayan Annabi (s.a.w) wanda kuma a nassi ya zo da cewa; shi ne imam Ali (s.a) a ghadir khum wanda yake shahararre ne, kuam akwai alaqa mai qarfi a musulunci tsakanin jagora da aqidar addinin musulunci.
Kuma rashin bin wannan tafarkin na musulunci sakamakon son rai da son duniay da son jagoranci da qiyayyar da ake yi ga dangin Annabi (s.a) wacce aka gajeta tun lokacin jahiliyya ya kawo bala’I mai girma a duniyar musulmi, sannan sai ya haifar da sababbin ra’ayoyin da suka sanya canje-canje a cikin hukunce-hukuncen musulunci masu yawa kamar ra’ayin nan na qaddara da tilasci da aqidar irja’I ta mur’ji’a da batun cewa duk sahabi adali ne, sannan aka ba wa daula haqqi na shari’a ta yadda duk zaluncin jagora da kaucewar daga tafarkin Allah to shi ne kan shiriya, kuma sava masa zindiqanci ne fita ne daga addini, aka qirqiro hadisai domin kare varnar wasu kamar mu’awiya da cewa: wanda ya cuci sahabi ni ya cuta, ko kuma duk wanda ka yi riqo da shi to ka shiriya, sai abin takaici ayyukansu suka zamanto wani vangare na musulunci ko mai vacinsa kuwa.
Wani abin tanaqudi shi ne yayin da wannan ra’ayin yake ganin wanda ya zagi sahabi a matsayin zindiqi sai ga shi ya yi halin ko-inkula da la’anar da mu’awiya ya yi wa imam Ali (s.a) gomomin shekaru da umarninsa, amma ba mu ga an yi wa mu’awiya hukunci da cewa; shi ma zindiqi ba ne!?
Sai ga shi ana kaucewa ruwaya daga sayyidi Ali (s.a) kuma a lokaci guda ana karvo hadisai daga waxanda suka yi tarayya wajen kashe imam husain (s.a) jikan Annabi (s.a.w) kamar yadda muka buhari yana karvo hadisi daga Umar xan saa’ad kuma ya ambace shi da cewa amintacce ne, wanda yake yana yi wa Allah qarya!
Sannan daga qarshe sai ya yi nuni da yadda quraishawa suka yi ittifaqi a kan cewa kada a bar alayen Annabi (s.a.w) su samu mulkinsa, sannan kuma daga qarshe sai ga ra’ayin abdullahi xan Umar na qauracewar ga yaqi da faxinsa “mu muna tare da wanda ya yi galaba” ya zama doka ce da ake amfani da ita wajen biyayya ga dukkan wani wanda ya yi galaba komai kuwa fajirci da qin Allah da yake da shi. Sai ya kasance jama’ar da ta rage kan biyayya ga tafarkin Manzon Allah (s.a.w) na asali ‘yar kaxan ce. Don haka yana kan kowane musulmi ya san musulunci kamar yadda yake kuma ya bi shi haka nan, ba tare da bin son rai ba.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+7 =