Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

BAYANIN AURE


Hafiz Muhammad Sa’id


Aure alaka ce kebantacciya ta shari’a ko al’ada wacce ake kulla ta tsakanin mace da namiji, da lafazi na musamman, wacce take halatta wa kowanne daga bangarori biyu junansu ta fuskacin mu'amalar kebewa, da haifar da 'ya'ya, da sauransu. Shari’ar musulunci ta nisantar da mutane daga zaman gwagwarci, ta kwadaitar da su yin aure domin samun al’umma ta gari mai kame kai, da renon manyan gobe wadanda zasu ci gaba da shiryar da na baya zuwa ga tafarkin tsira.
Aure yana bayar da damar kusanci tsakanin namiji da mace; sai dai ba shi kadai ne yake bayar da halaccin kusancin ba [1], shari’a ta bayar da damar kusantar abin da namiji ya mallaka na bayi mata da ta kira su “mulku yamin”.
Aure ya kasu gida biyu ne a shari’ar musulunci, ya hada da Aure maras iyaka [2] da aka fi sani da “Da’imi” da kuma aure mai iyaka da aka fi sani da “Mutu’a”, dukkan wadannan biyun shari’a tana da hikima, kuma an sanya musu sharudda, sannan aka kwadaitar da yin su. Yawancin aure maras iyaka yakan kasance don hada gida da tara iyali, da renonsu, da samar da al’umma ta gari wacce zata gaji na baya.
Amma aure mai iyaka yakan kasance ne domin kariya daga zina, da fadawa cikin haramun; wannan yana da amfani matuka ga mutane mabambanta; muna iya kawo misalin matafiyi, da wanda ya kasa aure, ga shi kuma yana jin tsoron fadawa cikin zina, da maras ikon sama da mata hudu; ga shi kuwa yana iya fadawa fasadi, da sauran misalai masu yawa. Don haka ne Imam Ali (a.s) ya ce: “Ba don Umar ya haramta auren mutu’a ba, da babu mai yin zina sai fasiki” [3].
Wannan lamarin kamar yadda yake ga maza, haka nan yake ga mata; sau da yawa macen da ba ta samun aure, sannan tana son kiyaye kanta daga zina da fada wa cikin sabon Allah madaukaki sakamakon ba zata iya kame kanta ba, ko kuma tana cikin yanayin rayuwa a al’ummar da ko dai ta fada wa fasadi, ko kuma ta zabi kiyaye dokar Allah.
Sai dai wannan bayani ne kawai na wasu daga cikin hikimomin aure mai iyaka, amma ba su ne kawai dalilan sanya shi a shari’a ba, domin akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu. Allah yana da hikimomin da yakan sanya shi zartar da hukunce-hukuncensa, muna iya fahimtar wasu sashe, wasu kuwa ba ma iyawa.

Ma'aurata a Kur'ani

Ayoyin masu yawa ne suka zo a cikin littafi mai girma na Kur'ani suna nuni zuwa ga dokokin zamantakewar aure da zamu kawo su a dunkule kamar haka:
1- Namiji shi ne shugaba a cikin iyali: Nisa’I:34.
2- Mace nutsuwar mijinta ce: Rum: 21.
3- Miji da mata tufafin juna ne: Bakara: 187.
4- Kyautata zaman tare da mata: Nisa’I: 19.
5- Kiyaye adalci tsakanin mata: Nisa’I: 3.
6- Namiji da mace daidai suke a kamalarsu ta ‘yan adamtaka: Nahal: 97.
7- Kiyaye hakkokin mata: Nisa’I: 7.
8- Abin da namiji zai yi wa mace mai kin shimfidarsa; Na farko: Wa’azi. Sannan sai: kauracewa shimfidarta. Sannan sai: sanya karfi da duka da takurawa daidai yadda shari’a ta gindaya. Nisa’I: 34.
9- Kyautata wa mace yayin da ake ci gaba da zaman tare ko yayin da za a rabu: Bakara: 231.
10- Bayar da kyauta mai dacewa ga mace yayin da za a rabu: Ahzab: 49.
11- Bayar da kyauta ga mace daidai ikonsa idan za a rabu kuma ba a san juna ba a shimfida, kuma ba a ayyana sadaki ba: Bakara: 236.
12- Bayar da rabin sadaki ga mace yayin rabuwa kuma an ayyana sadaki amma har suka rabu din ba su san juna ba a shimfida: Bakara: 237.
13- Kada a takura wa mace domin ta halatta masa sadakinta: Nisa’I: 19.
14- Dokokin hakkokin mace bayan rabuwa, kamar wajan zamanta, da rashin kuntata mata, da ciyar da ita: Dalak: 6.
15- Rashin halaccin cin sadakin mace ga miji yayin rabuwa: Bakara: 229.
16- Sulhu tsakanin miji da mata: Nisa’I: 35 [4].


1. Ahkamusshari’a: shafi:444 – 467
2. Ahkamusshari’a; shafi: 467 - 471
3. Almusannaf: Abdurrazak; 7/500. Tafsiru Dabari: 5/17. Durrul Mansur: 2/40. Tafsirur Razi: 3/200. Aljami'u Li Ahkamil Kuru'an: 5/130.
4. Yeksado fanjo mauzu az kur’ani karim, Akbar Dehkan: shafi: 191 – 193.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+1 =