Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

DALILIN WALI GA BUDURWA


Hafiz Muhammad Sa’id


Mace da yake tana amfani da dabi’ar zuciya ne [1] wajan so ko kin abu, sannan kuma idan ta kasance da yarinta ba kasafai takan iya tantance abin da zai amfanar da ita ko cutar da ita ba, wannan lamarin ne ya sanya musulunci bai ba wa budurwa ikon yin aure ba sai da hannun waliyyanta in suna raye, domin mace musamman budurwa sau da yawa idan abu ya kayatar da ita ba tare da ta kalli karshensa ba tana iya gaggautawa zuwa gareshi.
An sanya wa budurwa wajabcin yardar waliyyinta ba don namiji ya fi ta hankali ba kamar yadda wasu suka dauka, sai dai don mafi yawan maza sun fi yin amafani da shi in an kwatanta da mafi yawan mata. Amma wani yakan iya cewa: Ai a kwai Hadisi da ya nuna namiji ya fi mace hankali. Sai na ce: Hadisin ya fassara abin da yake nufi da karancin hankali, wato sau da yawa sukan fi namiji mantuwa.
Mai tsira da aminci yana cewa: Ashe (ba a sanya) shedar mace rabin shedar namiji ba? Suka ce: Haka ne. Sai ya ce: Ai wannan shi ne daga tawayar hankalinta. Ashe idan ta yi haila ba ta salla, ba ta azzumi ba? Suka ce: haka ne. Sai ya ce: Ai wannan shi ne daga tawayar addininta [2]. Sai ya nuna yawan mantuwa da sukan samu kansu a kai a wasu lokuta da karancin hankali, kamar yadda ya kira daina salla da suke yi yayin da suke jinin haila da tawayar addini.
Sannan kuma akwai Hankali na dabi’ar mutum da al’umma take gani da tunani ta hanyarsa, da su matan a kan kansu aka sanya musu cewa haka suke, wato tunanin al’umma haka yake ganin su har wannan ya zama jiki gun maza da mata domin su ma wani bangare ne na al’ummar, kamar yadda irin wannan tunanin da yake tafiyar da al’amarin al’umma ya sanya mata suke ganin maza suna da matsala.
Amma sanannen abu shi ne Allah ya halicci maza da mata da dabi’a iri daya ta hankali, sai dai a kan sami wani ya fi wani amfani da shi da kuma hangen nesa, namiji da mace a nan babu bambanci. Tarihi ya kawo labarin mata da babu kamarsu a zamaninsu, duba Bilkisu [3] da mutanenta da kaifin basirarta, duba sayyida Maryam, da sayyida Hadiza, da sayyida Fadima (a.s) a cikin al’ummarsu.

Zabar Abokin Zama

Samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama ba ya yiwuwa sai ta hanyar auratayya, domin idan ta fuskar fasikanci ne ake zaune da juna wannan nutsuwar ruhi har abada ba ta samuwa, wannan kuwa abu ne sananne da dabi’ar halittar mutum, da ilimi, suka gaskata da shi.
Saboda haka duk wanda zai yi aure ya tuna ko ta tuna cewa za ta yi aure ne da wanda zasu zauna domin gina rayuwa maras iyaka da gina gida salihi. Amma tambaya a nan ita ce: Wane mutum ne zamu zaba domin wannan rayuwa da kuma samun nutsuwa, da soyayya, da tausasawa, da tausayawa juna?.
Lokacin da aka tashi neman abokin zaman tare yaya ya kamata a zabi juna? Mene ne ma’auni wajan zabar wanda za a aura? Wace fuska zamu futowa wanda zamu zaba? Shin yana daga cikin sharadi sai mai kudi ko mai shedar takardar digiri ko wani gwarzo?
Yayin zabar abokin rayuwar aure kada a yaudari juna kamar yadda samari suke yi, sai ya ari agogo, da takalmi, da mota, da karyar aiki, da karatau a jami’a, da tafiye tafiye, wannan bai halatta ba, domin kamar yadda aka hana mace canja kama da zata sanya ta yaudari masoyi haka ma namiji bai halatta ba ya yaudare ta, haramcin yaudara ya shafi duk bangare biyun, don haka mai son yin aure sai ya duba siffofi da shari’a ta kwadaitar da su kamar imani, da takawa, da kula da addini.
Mu sani zabar abokin zama ba kamar zabar riga ko mota ba ne da za ta tsufa a yar, a sake wata, abin ba haka ba ne, don haka iyaye su san wa yake zuwa wajan ‘yarsu? Kuma wa za ta aura? Matukar mumini ne to su ba shi, sannan kada su dage a kan wanda ba ta so, ko sai mai kudi da makamantansu.
Zabar abokin zaman aure yana da muhimmanci matuka, kuma idan ba a yi dace ba to yakan kasancewa wanda yake cutuwa kamar kurkuku ne. Idan abokin zaman aure ba shi da siffofi na kamala yakan canza gida ya zama azaba maimakon rahama da tausasawa, muhimmancin wannan lamarin ne ya sanya muka ga mai daraja da daukaka annabin rahama yana addu'a yana mai cewa: “Ya Allah! Ina neman tsarinka daga matar da zata sa ni yin furfura tun kafin lokacin tsufana” [4].

Babu Tilasci A Aure

Musulunci ya hana auren dole [5], ya sanya shi kamar ba aure ba ne [6], don haka Uba ko Kaka na wajan uba duk da yana da hakkin yardarsa da izininsa a aurar da budurwa, amma idan zai yi mata auren dole da wani wanda ba ta kauna, a nan yarinya tana da iko ta yi aure da wanda take so matukar mumini ne kuma ba wani abu na tawayar Addini gareshi.
Wannan wani abu ne da musulunci ya tabbatar da shi, domin Allah ne ya ba shi hakkin walitakar, idan kuwa ya saba masa sai ya kwace izininsa. Sannan a fili yake bisa koyarwar mazhabar alayen Annabi (s.a.w) da aka fi sani da mazhabar Ahlul-baiti (a.s) cewa auren dole ba a lissafi da shi [7]. A wannan koyarwar bazawara, ko matar da ta cika hankali tana mai dogaro da kanta a rayuwa, ko kuma mai zaman kanta musamman wacce ta rasa waliyyanta na shari'a, idan zasu yi aure, su ne suke da ikon aurar da kansu, babu wani mai iko a kansu sai wanda suka wakilta, kamar dai namiji baligi da yake mallakar ikonsa da nufinsa.
Al’amarin aure ba a sanya shi hannun waliyyai ba gaba daya kamar yadda ba a sanya shi a hannun ‘yan mata ba gaba daya, shari’a ta sanya shi shawara ne tsakanin waliyyai da ‘ya’yansu mata [8], amma maza samari baligai su ne waliyyan kansu, sai dai idan sun wakilta wani.
Da wannan ne na kai ga sakamakon cewa, da al’ummarmu tana rayuwa ne bisa mahangar Ahlul-baiti (a.s), da ba a samu matan banza da karuwai da yawa haka ba, wadannan mata da suka fada wadannan halaye sun cancanta da a tausaya musu domin kaucewa kyakkyawar koyarwa ya jefa su cikin wannan halin, kuma ya kamata ne a kama hannunsu zuwa tudun tsira ba a rika nuna musu kyama ba.
A bisa bincike akwai shaidar cewa, mata masu zaman kansu da yawa sun tabbatar da cewa, auren dole ne ya sanya su guduwa [9] daga zaman aure da jefa su cikin wannan hanya ta fasikanci.
Ina ganin da wannan al’umma ta fahimci tafarkin kofar birnin Ilimin Annabi Sayyidi Ali (a.s), da ba mu samu kanmu cikin wannan yanayi mai muni haka ba, da Addini ya yi sauki ga mutane, domin da yawa abubuwa sun kuntata ne sakamakon tazara da aka samu da wancan tafarkin.
Don haka zabi ga ‘ya mace abu ne muhimmi, in ba haka ba sai fasadi ya yadu a ko’ina, mace tana yawan yin amfani da abubuwan da suke sosa rai ne wurin hukunci, bisa misali mace ta fi namiji tausayi, amma in ta bushe, takan fi shi kekashewa.
Babban misalin hakan shi ne na samun wasu mata -galibi matan banza- da suka gudu suka kama hanyar banza, kuma wannan hanyar tana jawo musu wulakanci da cin mutunci, amma suka kekashe a kanta. Sannan kuma akwai misalin da zamu gani na wasu mata -galibi matan banza- da sukan iya hana dan da suka haifa nono, ko ma suka kashe shi, ko suka wurgar da shi suka gudu. Akwai kuma misalai na matan da suka sanya wa angwaye da abokanansu maganin bera a abinci saboda kawai ba sa kaunarsu.

Jahiliyyar Da Aka Raya

A yankunan Hausa an kirkiro mummunar al'ada ta cewa ba a ba wa mai fawa aure dogaro da tatsuniyoyin da aka kirkiro na wai ya sayar wa Annabi (s.a.w) da naman kare maimakon akuya! Kuma ga dukkan alamu wannan tunanin ya samo asali ne daga masu kin mahota kamar makiyayan filani.
Mafi munin wannan shi ne kirkiro shigen irinsa da sunan addini kamar yadda aka gurbata mana koyarwar musulunci aka ce: Ba a ba wa masaki aure, ko wanzami. Haka nan aka canja koyarwar addini aka kirkiro cewa wanda ba bakuraishe ba ne ba tsaran bakuraishiya ba ne, larabawa kuma suna sama da waninsu, wannan duk Jahiliyyar da aka raya ce bayan Annabi (s.a.w).
Wannan ne dalilin da ya sa Imam Muhammad Bakir (a.s) yayin da yake amsa wa Allaisi wanda ba ya daga cikin masu biyayya ga tafarkinsu da yake nuna ba zai aura wa masaki ‘yarsa ba, sai ya gaya masa cewa: Me ya sa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa amma dai masaki ba tsarana ba ne. Sai Imam Bakir (a.s) ya ce masa: Amma Allah ya yarda da aikinsa, ya kuma kaunace shi, ya kuma aura masa huurul’in, a yanzu kana kin wanda Allah yake kauna? Kana nisantar wanda yake tsaran ‘yan matan hurul’in don girman kai da shisshigi?. Don haka Musulunci ya sanya imani da musulunci su ne ma’auni da tamka ko tsara a aure babu wani abu bayan wannan.
Ga cikakkiyar ruwayar game da wannan al’amari tare da wasu karin bayanai:
Al’abi ya ce: A cikin littafin Nasruddurar: An rawaito daga Abdullahi dan Mu’ammar Allaisi ya ce da Abi Ja’afar (a.s): Labari ya zo mini cewa kai kana bayar da fatawa da yin auren mutu’a? ya ce: Allah ya halatta ta a littafinsa kuma Manzo (s.a.w) ya sunnanta, sannan sahabbansa sun yi aiki da ita, sai Abdullah ya ce: Ai Umar ya hana yin ta. Sai Imam Muhammad Bakir ya ce: Kai kana kan maganar sahibinka, ni kuma ina kan maganar Manzon Allah (s.a.w). Sai Abdullah ya ce: Shin zai faranta maka rai (‘ya’yan) matanka su aikata haka? Sai Abu Ja’afar (Imam Muhammad Bakir) (a.s) ya ce: Kai wawa? Wannan da ya halatta a littafinsa kuma ya halatta ga bayinsa ya fi ka kishi da kai da wanda ya hana, yana mai dora wa kansa nauyi, a yanzu zai faranta maka rai cewa ‘yarka tana karkashin auren wani masaki daga masakan garin Yasrib (Madina)? Sai ya ce: A’a. Sai Imam (a.s) ya ce: Me ya sa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa, amma dai masaki ba tsarana ba ne. Sai ya ce: Ai hakika Allah ya yarda da aikinsa ya so shi, ya aura masa Hurul-i’n, a yanzu kana kin wanda Allah yake son sa? kana kin wanda yake tsara na Hurul-i’n din aljanna saboda shisshigi da girman kai? Sai Abdullah ya yi dariya ya ce: Wallahi ba na ganin kirazanku (zukatanku) sai mabubbugar ilimi, sai ‘ya’yan itacensa suka zama a hannunku, ganye kuwa ya rage a hannun mutane [10].
A littafin Khilaf na Sheikh Dusi ya zo cewa; Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Muminai sashensu tsararrakin juna ne, jini yana daidaito, mafi karantarsu yana kulla alkawarinsu [11].
Haka nan zamu ga wannan a cikin Littafin Fikihu kamar yadda ya zo a risalar sayyid Sistani, cikin: Mas’ala 28: Ya halatta ga ajami ya yi aure da balarabiya, da bakuraishiya, da bahashima idan yana cikin ma’abota addini, kuma yana da yalwa.


1. Kamar ki, da so, da sauran dabi’un mutum na zuciya.
2. Nailil Audar, Asshaukani, j 1, shafi 353, Daga Abi Sa'id.
3. Manakibu Ali Abi dalib, Shah’ra shub, j 3, shafi 102: Daga Alkali Abu bakar Muhammadul karkhi, a littafinsa daga Imam Sadik (a.s) daga Fadima (a.s) a tafsrinta game da ayar: Kada ku sanya kiran Manzo kamar kiran sashenku ga sashe.
4. Alkafi, Juzu’i 5, Babin Shirarunnisa’i, Sh 326: Daga Ali dan Ibrahim daga babansa, daga Nufali, da Sakuni, daga abu Abdullah (a.s).
5. Kanzul ummal, j 16, shafi: 532. Da kuma littafin Tahrirul wasila, Kitabun nikahi, mas’ala: 25, shafi: 253.
6. Almashakilul jinsiyya lisshabab, Ayatul-Lahi Makarim Shirazi, bugu na biyu, tarjamar Abdurrahim al’humrani, shafi 13.
7. Sahihul Buhari, j 6, shafi 135.
Daga Isma'il ya ce: Malik ya ba ni labari daga Abdurrahaman dan kasim daga babansa, daga Abddurrahman da Majma’a ‘ya’yan Yazid dan Jariya, daga Khansa’u ‘yar Khazami Al’ansariyya cewa: Tana bazawara babanta ya aurar da ita tana kin hakan, sai ta zo wajen Manzon Allah (s.a.w) sai ya yi raddin auren.
8. Almashakilul jinsiyya lisshabab, Ayatul-Lahi Makarim Shirazi, bugu na biyu, tarjamar Abdurrahim al’humrani, shafi 61.
9. Almashakilul jinsiyya lisshabab, Ayatul-Lahi Makarim Shirazi, bugu na biyu, tarjamar Abdurrahim al’humrani 13.
10. Biharul anwar: Allama majlisi, j 64, shafi 356.
11. Alkhilaf, Shaikh Dusi, j 4, shafi 272.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
6+5 =