Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

DUKA DA CUTAR DA YARO


Hafiz Muhammad Sa’id


Wannan marhalar ta tsawatawa ce, don haka ne idan yaro ya kai shekaru bakwai sai ka ga iyaye sun fara dukansa. Duka yana daga cikin makami da manya kan yi amfani da shi a kan yara, amma ya kamata su sani cewa don ka haifi yaro ba yana nufin kana da ikon cutar da shi ba [1], domin yaro amana ce da Allah ya ba ka. A bisa koyarwar musulunci babu mai ikon dukan yaro sai mahaifinsa kawai, don haka Uwa, ko malami, ko makoci, ba su da ikon dukan yaro sai da izinin shugaban daular Musulunci idan akwaita, ko kuma izinin babansa. [2]

Sayyid Sistani yana cewa: Ya halatta dukan ‘yan makaranta idan suka cutar da wasu, ko suka aikata haram, amma da izinin waliyyansu (Uba), kuma dole ne dukan ya kasance ba mai sanya fata ta yi ja ba (ta tashi), idan kuwa ya kai ga hakan sai an biya diyya. [3]

Shi ma Uba, ba a yarda ya doki yaro ba, sai idan akwai maslaha da tsammani mai karfi na cimma wannan maslahar, kuma ya zama dukan ba ya tayar da fata, ko ya sanya wata alama a kanta, balle kuma ya kai ga fitar da jini, duka ne wanda ba ya lahanta naman jikinsa, ko kashinsa, ko canja masa launin fata.

Sannan bai kamata ba a ajiye wani abin duka domin yaro ya rika gani yana tsorata, wannan ba ya kara masa komai sai kashe masa kuzari, da azama, da kai shi ga sukewa daga rayuwar cikin gida. Don haka bai kamata ba a ajiye bulala domin duka sai dai don tsoratarwa ga laifin da aka san haka zai yi tasiri wajan tarbiyyarsa.

Sau da yawa wasu mutane sukan ajiye abin duka kusa da yaro a kan laifin da bai kai ga haka ba, ko kuma ya kasance ba shi ne mafita ba, kamar wasu da sukan ajiye bulala don yaro ya ci abinci, yaron da ba ya cin abinci yana bukatar likita ne ba duka ko ajiye bulala ba, domin ta yiwu da bitamin “C” cokali uku a rana matsalarsa ta warware.

Amma wasu iyayen sun dauka komai duka ne maganinsa, sai su yi ta dukan yaro ko daka masa tsawa, alhalin da yawa wasu abubuwan malami, ko likita, ko makoci, ko abokai, zasu iya warware su ga yaro ba iyaye ba. Wani abin ma laifin iyaye ne amma sai su doki yaro: kamar yaro ya ga suna wani abu shi ma sai ya yi, kamar wani da yake shan taba amma da ya ga yaronsa yana sha a boye sai ya zane shi.

Kausasawa da tsanantawa a kodayaushe ba sa magani ga yaro, sabanin tausasawa da nuna kauna da mayar da shi abokin hira, da cin abinci, da zama tare, da tafiya yawo ko unguwa tare da shi. Bisa tarbiyyar da muka samu wajan iyayenmu, da abin da muka samu na tajribar da wasu suka bayar da labari game da rayuwarsu, wannan ya fi tasiri.

Yawancin wadanda aka horar ta hanyar kausasawa da takurawa ana bata su ne su taso mutane masu kekashewar zuciya, da bushewar zuciya, da rashin tausayi, da rashin kunya, har ma sukan iya jin ba a kaunarsu ne don haka sai su kama hanyar lalacewa, ko su yi tunanin daukar fansa kan wanda ya azabtar da su.

Ka taba jin labarin wani dalibi da a furamare da malaminsu ya gallaza masu, bayan ya gama jami’a sai ya zama shi ne mai kula da fayel din Furamare Board a jahar tasu, wata rana yana binciken fayaloli sai ya ga malaman makarantarsu ta furamare, da ya duba sai ya ga sunan malamin wanda a wannan lokaci har ya manta da malamin amma ganin fayel din sai ya tuna masa shi. Saboda haka sai ya batar da fayel din, a lokacin da aka zo Pepa red sai ya zama shi malamin ba a ga na shi fayel ba, a sakamakon haka ya rasa nasa albashi da aiki, ya zama sai dai ya je wajan abokansa in an dauki albashi don su taimaka masa da wani abu na cefane.

Wasu malamai masu tsangwamar yara sukan samu kyama daga dalibai musamman wanda ya zama mai bulala, an ce lokacin da turawan yamma suka zo kasashenmu a makaranta sai a ba wa malamin ilimin Addini ya zama shi ne mai duka sai duk dalibai ka ga suna kin malamin da ma darasin nasa, shi kuma yana daure fuska da barazana ga dalibai wai shi ne mai bulala. Wasu sun so in kasance daga cikin masu irin wannan hali a makaranta, amma sai na zabi in kasance mai bayar da tarihi da kissoshin salihan bayi ga yara, don haka sai na fi kowane malami farin jini.

Wannan mummunar hanyar tarbiyya har yanzu tana nan a cikin makarantun addini musamman na karatun Kur’ani da aka fi saninsu da makarantun allo. Kamar yadda har yanzu akwai wata mummunar al’ada ta bakin zalunci a makarantun boko da aka fi sani da “Siniyorati”, ta yadda daliban manyan azuzuwa sukan azabtar da na kananan azuzwa.

Dukan yaro ba shi da kyau in ba wajan tilas ba, da kuma cewa zai yi amfani, haka ma daka wa yaro tsawa ba shi da kyau, domin yana iya haifar masa da ciwon tsoro ko ya firgita shi, abin da kan iya haifar masa da ciwo a jikinsa ko raunin zuciya.

A wannan marhalar ce iyaye ko mutanen waje, ko abokai, ko kuma makota sukan iya sanya wa yaro karan tsana, wasu mutanen wawaye ne ta yadda idan suna gaba da iyayen yaro suna iya hucewa a kansa. Wannan marhala tana da hadari matuka sosai, domin idan aka bari tarbiyyar yaro ba ta daidaitu ba tun farko sakamakon sakacin iyaye, to dawo da shi kan hanya yana da wuya.

Mu sani kyamar yaro, da kushe shi, ko muzguna masa, da sukansa, da cin fuskarsa, suna daga cikin abubuwan da kan iya rusa himmar yaro, da azamarsa, da kuzarinsa, da tunaninsa, ta yadda za a sanya masa tunani da yakan kai shi ga rushe masa kwazonsa, da jin cewa; ba shi da hakkin bayyanar da ra’ayi.

Takura yaro da bakanta masa rai, da dukansa ba ji ba gani, abubuwa ne da sukan sanya shi jin cewa yana bukatar ya girma domin ya zama mutum ya shiga sahun manya don ya huta da wannan nau’o'in azaba da gallazawa, ko ya sanya shi fadawa hanyar banza, ko daukar fansa da kece reni.
A nan ne idan ya fusata kuma ya samu masu karbarsa kowane irin mutane ne, sai ya mayar da su abokansa ya kuma tasirantu da su. Irin wanann nau’i na tarbiyya ba komai a cikinta sai danne hakkin dan Adam, da rusa manyan gobe.

Wasu mutane ko wasa suka ga yara suna yi sai su daka musu tsawa da zagi [4], kamar dai ba su taba jin fadin Allah a Surar Yusuf ba: “Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dadi, kuma ya yi wasa, kuma lalle mu masu tsaro ne gareshi”. [5] Sau da yawa yara sukan ga irin wadannan mutane masu takura musu a matsayin mugwayen makiyansu.

Su mutane ne masu bacin rai da bakin ciki da halayen yara kodayaushe, yara ba su isa su ga dariyarsu ba sai dai bakin cikinsu. Annabin rahama bai yardar wa muminai da wannan halin ba: Ya zo a wata ruwaya cewa; "Mumini shi ne wanda yake farin cikinsa yana fuskarsa, bakin cikinsa yana zuciyarsa.[6]
Wasu ruwayoyi sun yi nuni da tausaya wa yara da nuna jin kai garesu; Manzon rahama (s.a.w) mai tsira yana cewa: “Duk wanda ya sumbanci dansa to Allah zai rubuta masa kyakkyawa (lada)”. [7] Sai dai wannan kuma ba yana nufin nuna makauniyar so ga 'ya'ya ba, ta yadda wasu iyayen sukan kai 'ya'yansu su baro cikin halaka sakamakon nuna musu kauna maras kan gado. Imam Bakir (a.s) yana cewa: “Mafi sharrin iyaye shi ne wanda kyautatawa (soyayya) ta kai shi ga shisshigi (wuce gona da iri)”. [8]

Wannan marhala ta shekaru bakwai zuwa sha hudu saboda ta kasance marhala ce da take bayan wacce aka saba shagwaba yaro, don haka ne ko yaya yaro ya kasance yana saba wa sai iyaye su yi fushi da shi, maimakon su gane cewa yaro ya samu canji ne, kuma yana bukatar sauyi a hankali sai su shiga fusata da fada, da duka, har ma wani lokaci da zagi, ko mummunan abu tsinuwa.

Wasu iyaye sukan yawaita tsine wa yaransu da mummunan zagi da kan iya kara wa yaro lalacewa, a tarbiyyar musulunci hatta dukiya, da tumaki, da kaya, da gida, da tufafi, da abin hawa, da matar mutum, an hana la’antar su don su zama masu amfani da alheri ga al’umma.

Maimakon su yi wa yaronsu addu’a da za ta gyara shi kamar yadda Littafin Allah madaukaki ya shiryar da mu da yi wa ‘ya’ya addu’a ta gari: Ibrahim: 35, sai su yi ta yi masa mugun baki da mummunan fata, su sani duk wata tabewa da wahalar da hakan zai haifar ga yaro tasirinsa zai dawo ga iyaye a karshe, domin idan wannan tsinuwa ta bi shi ya lalace ba abin da zai same shi a duniya sai talauci da rashin albarka a kan duk abin da ya sa a gaba.

Bincika rayuwar irin wadannan yara da kullum iyaye kan tsine musu, zai wahala ka ga dayansu wanda ya girma ba ya fama da talauci ko tabarbarewa kan duk abin da ya sa gaba, saboda haka ya kamata iyaye su sani cewa lalacewar 'ya'yansu, su ne farkon wanda abin zai fara shafa.

Wani mutum da ya kai kukan ‘ya’yansa masu tsananin saba masa wajen manzon rahama (s.a.w), sai Annabi (s.a.w) ya tambaye shi cewa; Shin ka kyamace su ne (da mugun baki)? sai ya ce: Haka ne. sai Annabi (s.a.w) ya ce: Kai ne ka jawo tabewarsu. A wata ruwayar manzon rahama (s.a.w) yana cewa: “Ku kiyayi mummunar addu’ar iyaye, domin tafi takobi kaifi”. [9]

Sakamakon tsine wa yara yakan kai ga girbar mummunan sakamako yayin da suka kai shekaru sha hudu zuwa ishirin da daya ko sama da haka, a daidai lokacin da zasu yi wa iyayensu hidima saboda karfinsu ya fara kawowa, sai su kasance masu tsananin rashin tausayi kan iyaye.

Don haka yi wa ‘yayanka addu’a kullum da alherin Duniya da na Lahira, wannan ya zama abin da ba zaka taba mantawa da shi ba, koda kuwa ka manta da yi wa kanka addu’o'i to kuskure ne babba ka manta da yi wa yaranka.

Wasu jama'ar kuwa sun dauki zagi a matsayin al'ada, sai suka kasance hatta da fada ga yaro suna yin sa ta hanyar zagi ne. Irin wadannan mutane ya kamata su sani cewa; zagi koda sau daya faufau ba ya iya zama warwarar matsalar yaro ko hanyar tarbiyyarsa, yana zama sabanin yadda ake zato ne, domin zai kasance hanyar koya masa zagi ne.

Yana da kyau idan ka ga yaronka yana yin abin da kasan ba mai kyau ba ne ka nuna masa fushinka da rashin jin dadinka, ya san cewa wannan abin na iya bata maka rai da ba zai iya ganin murmushinka ba, amma a sani yana bambanta daga laifi babba da karami, sannan kuma da kula da bambancin da yake tsakanin yara gwargwadon shekarunsu, sannan kuma matakin farko ba shi ne ka fara dukan yaro ba domin ta yiwu shi a wajansa bai san wannan laifi ba ne.

Idan laifin dan karami ne ko ba shi da tasiri wajan bata tarbiyya a nan ya isa ka yi masa nuni da shi cikin labaru, ko hani. Wato abin da yake bukatar tsanani a tsananta, wanda yake bukatar sauki a saukaka, ba komai tsanani, ko komai sassauci ba.

Haka ma wannan yana da bambanci tsakanin shekarun yara da suka bambanta, amma ma’aunai suna iya zama a gane su da hankali, kamar yaro dan shekara daya da rabi ya rika kiran sunan abokanka da sunansu domin ya ji kana kiran su da wannan sunan, a nan ba bukatar ka tsawata ka ce bai da ladabi domin bai ma san me kake nufi ba a nan, amma dan shekara bakwai yana iya gane wannan, akwai misalai masu yawa a kan haka.

Saboda haka a tsawata wa yara kada duka ya zama mataki na farko, wannan yana iya saba masa da dukan har ya zama ba ya magani, haka nan ma yana iya kasancewa shi a lokacin bai san wannan abin laifi ba ne. Sannan kada ka ga kai ka haife shi, idan ya zama akwai zaluntarsa, ko cutar da shi da daukar matakai sabanin shari’a da hankali, Allah (s.w.t) zai yi maka hisabin rashin kiyaye amanar da ya ba ka.


1. Manla yah’dhuruhul fakih: j2, 45/3.
2. Al’baharur ra’ik, Ibn Najim almisri, shafi: 584. Da kuma, Takmilatu hashiyatu raddil mukhtar, Ibn Abidin (Ala’uddin) j 1, shafi: 134 – 135.
3. Fatawal muyassara, sayyid sistani: Al’hawaiyyatul amma assaniya.
4. Mukhtasaru basa’iruddarajat, Na Hasan dan Sulaiman alhilli, shafi 68. Idan ka duba zaka ga dogon labari game da nishadin imam Hasan da Husain (a.s) tun suna yara.
5. Surar Yusuf: 12.
6. Nahajul Balaga, j 4, Hikam da Mawa'iz, shafi: 333.
7. Almuhazzabul bari'u, j 3, Ibn Fahad Hilli, shafi: 155.
8. Almuhazzabul bari'u, j 3, Ibn Fahad Hilli, shafi: 155. Aljauhara fi nasabi Imam Ali, Albari, shafi: 52.
9. Mustadarakul wasa'il, Mirza Nuri, j 5, shafi: 256.



Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
2+4 =