Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

BAHASI KAN MUSULUNCI


Muhammad Riza Muzaffar

Hafiz Muhammad Sa’id

Mun yi imani cewa Addini a wajan Allah kawai shi ne musulunci, kuma shi ne Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari’ar karshe, kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga sa’adar dan Adam, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al’amuran duniya da lahirarsu, kuma mai dacewa ga wanzuwa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa kuma mai kunshe da dukkan abin da dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar daidaiku da zamantakewar jama’a da na siyasa. Da yake Shari’ar musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari’a da za tazo ta yi gyara ga dan Adam da ya rigaya ya dulmuya cikin zalunci da fasadi, to babu makawa wata rana ta zo da Addinin musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.
Da an dabbaka Shari’ar musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da aminci ya game ‘yan Adam kuma da rabauta ta game su, kuma da sun kai kololuwar abin da dan Adam yake mafarkinsa na daga walwala, da izza, da yalwa, da annashuwa, da kyawawan dabi’u, kuma da zalunci ya kau daga duniya, soyayya da ‘yan’uwantaka sun yadu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba daya.
Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu wadanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa suke tun daga karni na farko, kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummunan hali zuwa mafi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Ba riko da musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa musulmi wannan mummunan cibaya ba, sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar musulunci, da tozarta dokokinsa, da yaduwar zalunci, da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu. Wannan kuwa shi ne abin da ya lahanta yunkurin cigabansu, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala’i da halaka har Allah (S.W.T) ya halakar da su saboda zunubansu. Allah madaukaki yana cewa:
“Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni’ima da ya ni’imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da yake ga kawukansu”. Surar Anfal 53.
Da fadinsa “Kuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta”. Surar Yunus: 17.
Da fadinsa madaukaki: “Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.
Da fadinsa: “Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai radadi ne mai tsanani”. Surar Hudu: 102.
Ta yaya ake sauraron Addinin musulunci ya tayar da al’umma daga dogon baccinta, alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Hakika imani, da amana, da gaskiya, da tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, da sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, da makamantansu, tun farkon assasa Addinin musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama’a-jama’a da kungiya-kungiya, suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya, suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al’amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin Addini da maslaharsu da maslahar al’ummarsu, da fadawa cikin jayayya game da halittar Kur’ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja’a, da kuma cewa aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halicce su ne nan gaba.
Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasu, babu abin da suke nunawa sai kaucewar musulmi daga madaidaicin tafarki zuwa ga halaka da karewa. Fandarewa ta karu tare da shudewar zamani, har Jahilci da bata suka mamaye su, suka shagaltu da abu maras kima, da camfe-camfe, da surkulle, da wahamce-wahamce, da kuma yake-yake, da jayayya, da alfahari, sai suka fada a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau yammacin Turai wayayye, fadakakke, babban sanannen makiyin mlusulunci, ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi, su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kadai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah madaukaki yana cewa: “Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.
A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa, ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu. Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma, kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi [1].
Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam, ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi gama-gari, da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da kyawawan dabi’u da ruhin ‘yan’adamtaka, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.

Hanyar Tabbatar Da Gaskiyar Addinin Musulunci

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin Addinin musulunci zamu iya kayar da shi ta hanyar tabbatar masa da mu’ujizarsa dauwamammiya wato Kur’ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagara badau. Haka nan Kur’ani shi ne hanyar gamsar da kawukanmu yayin da kokwanto ya fara zo mana, saboda irin wadannan tambayoyi da kokwanto ba makawa su taso ga mutum mai ‘yanci a tunani yayin karfafa akidarsa ko tabbatar da ita.
Amma shari’o’in da suka gabata kamar Yahudanci da Kiristanci, ba mu da wata hujja ko hanyar da zamu gamsar da kanmu, ko kuma mu gamsar da mai tambaya game da ingancinsu, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza da ta rage garesu, abin da mabiyan wadannan addinan suke nakaltowa na daga abubuwan mamaki da mu’ujizozi da suke danganta su ga annabawan da suka gabata, su ababan tuhuma ne a kan haka. Kuma babu wani abu da yake cikin littattafan addinan da suka gabata da yake hannunmu a wannan zamani wadanda ake danganta su ga annabawan, kamar Attaura da Injila, da ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya da zai iya zama hujja yankakkiya, kuma dalili mai gamsarwa idan ba musulunci ne ya gasgata da ita ba.
Sai dai mu musulmi ya inganta ne a garemu mu gaskata annabacin ma’abota shari’un da suka gabata, domin bayan gaskatawarmu da Addinin Musulunci, to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abin da ya zo da shi. Kuma a cikin abin da ya zo da shi akwai gaskata annabcin wasu daga annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a baya.
Don haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari’un da suka gabata, domin gaskatawa da shi gasgatawa ne garesu, kuma imani da shi imani ne da manzannin da suka rigaya da annabawa magabata, don haka bai wajaba ba a kan musulmi ya yi wani bincike game da gaskiyar mu’ujizar annabawa ma’abota wadancan shari’o’i, domin abin kaddarawa shi ne ya riga ya yi imani da ita ta hanyar imani da musulunci kuma wannan ya isar.
Na’am, idan da mutum zai yi bincike game da Addinin musulunci ingancinsa bai tabbata gareshi ba, to dole ne a kansa kamar yadda hankali ya wajabta neman sani da ilimi ya yi bincike game da Addinin Kiristanci domin shi ne Addinin karshe kafin Musulunci, idan ya bincika Addinin Kiristanci bai gamsu ba, to sai kuma ya dukufa a kan Addinin da ya gabace shi wato Yahudanci. Haka nan dai zai yi ta binciken addinan da suka gabata har sai ya kai ga yakini da ingancin addinan da suka gabata, ko kuma rashin ingancinsu sai ya yi watsi da su baki daya.
Sabanin wanda ya tashi a Addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da Addininsa ba zai wadatar da shi ga barin binciken Addinin Kiristanci da Addinin Musulunci ba, dole ne a kansa ya yi bincike a bisa wajabcin hankali ga neman sani. Haka nan kirista ba zai isu da imani da Almasihu (A.S) ba, wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa, ba zai samu uzuri ba da gamsuwa da addininsa ba, ba tare da bincike ba. Domin Yahudanci da Kiristanci ba su kore shari’ar da zata zo bayansu mai shafe su ba. Annabi Musa (A.S) bai ce babu Annabi bayansa ba, haka ma Annabi Isa (A.S) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa [2].
Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da Addininsu kafin su yi bincike game da ingancin shari’ar da ta biyo bayansu, kamar Kiristanci dangane da Yahudanci, ko musulunci dangane da Kiristanci da Yahudanci. Wajibi ne a bisa hukuncin hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga bayansu, idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta su bar Addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su wanzu a kan Addininsu na da, su kuma karkata zuwa gareshi
Amma musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci, to ba ya bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci Addininsa da kuma wadanda ake da’awa bayansa. Wadanda suka gabata dai domin shi ya yi imani da su, to don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da su, sai dai kawai ya yi hukunci da cewa ita shafaffiya ce da Shari’ar Musulunci, don haka bai wajaba ya yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littattafansu ba. Amma wadanda ake da’awarsu daga baya kuwa dalili shi ne, saboda Annabin Musulunci Muhammad (S.A.W) ya ce: “Babu wani Annabi bayana”. Kuma shi Mai gaskiya ne kuma Amintacce. “Kuma shi ba ya magana a kan son rai, ba wani abu ba ne face wahayi da aka yi masa”. Surar Najmi: 3-4. Don haka saboda menene zai bukaci dalili a kan ingancin da’awar Annabcin da aka yi da’awarsa daga baya idan har mai da’awar ya yi da’awa.
Na’am yana wajaba a kan musulmi -ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da ma’abocin sako (S.A.W), da sabanin mazhabobi da ra’ayoyi, da kuma samuwar kungiyoyi- ya yi bincike, ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a, domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a kamar yadda suka zo. Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari’ar da aka saukar kamar yadda take, alhali musulmi sun sassaba jama’a-jama’a, sun rarraba, babu salla guda daya, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai iri daya ba a cikin dukkan mu’amala. Don haka yaya zai yi? Ta wace irin hanya zai yi salla? Da wane ra’ayi zai yi aikin ibada da mu’amalarsa, kamar aure, da saki, da gado, da saye da sayarwa, da tsayar da haddi, da diyya da sauransu?
Kuma bai halatta gare shi ba ya bi ra’ayin iyaye ko ya koma ga abin da zuriyarsa da mutanensa suke a kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah (S.W.T), domin a nan babu wani boye-boye da nuku-nuku, ko sassauci, ko bangaranci. Na’am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da yake kansa tsakaninsa da Allah, ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai zarge shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai”. Surar Alkiyama: 36.
“Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne”. Surar Alkiyama: 14. “Lalle wannan fadakarwa ce, don haka ga wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa”. Surar Muzzammil 19.
Farkon abin da mutum zai tambaya shi ne; Shin ya kama tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Baiti (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya Isna Ashariyya masu bin Imamai sha biyu shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori daban-daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi, daga cikin mazhabobi hudun ne ko kuma daga wasu mazhabobin daban da suka rushe? Haka nan tambayar zata yi ta zo wa wanda yake da ‘yanci a tunani da zabi har sai ya kai ga wata gaskiya a bar dogaro.
Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bincike a kan abin da yake biye da ita a akidar Imamiyya Isna Ashariyya.

Mai Shara’anta Musulunci

Mun yi imani da cewa ma’abocin sakon Addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi, kuma shi ne cikamakon Annabawa, shugaban Manzanni, kuma mafificinsu baki daya, kamar yadda shi ne shugaban ‘yan Adam baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci, babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali, babu wani kamarsa a kyawawan dabi’u: “Lalle kai kana kan manyan dabi’u masu girma”. Surar Kalam: 4. Wannan kuwa tun farkon samuwar dan Adam har zuwa ranar tashin kiyama [3].

Ma’anar Shi’anci Wurin Ahlul Baiti

Ahlul Baiti (AS) ba su da wata himma bayan sun debe tsammanin al’amarin al’umma ya dawo hannunsu sai gyara halin musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari kamar yadda Allah (S.W.T) yake so daga garesu. Don haka suka kasance tare da duk wanda yake bin su, kuma suka aminta da shi a kan sirrinsu, suna bayar da kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari’a, da cusa masa ilimin addini, da sanar da shi abin da yake nasa, da kuma wanda yake kansa.
Ba sa daukar mutum cewa mabiyinsu ne kuma shi’arsu sai idan ya kasance mai bin umarnin Allah, mai nisantar son zuciyarsa, mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu. Kuma ba sa ganin son su ya wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu suke raya wa kansu daga cikin masu holewa da bin sha’awece-sha’awece da son ransu wadanda ke neman hanyar fandare wa bin Allah. Imamai ba sa daukar sonsu da biyayya garesu mai tseratarwa ne sai dai idan ta hadu da kyawawan ayyuka, kuma mabiyansu sun siffantu da gaskiya da rikon amana, da tsentseni da tsoron Allah.
“Ya Khaisama! ka isar daga garemu cewa ba zamu wadatar da su daga komai ba sai da aiki, kuma ba zasu samu soyayyarmu ba sai da tsentseni, kuma mafi tsananin hasarar mutane ranar alkiyama shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa ga waninsa” [4].
Su suna son mabiyansu su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya ne, masu shiryarwa zuwa ga alheri da shiriya, kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga gare ku” [5].
A yanzu zamu kawo maka wasu muhawarori da suka gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san matukar tsanantawarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi’un mutane:
1- Muhawarar Abu Ja’afar Bakir (AS) shi da Jabir Ju’ufi [6]: “Ya Jabir! Ashe ya isa ga wanda ya siffantu da cewa shi shi’a ne ya yi da’awar yana son mu? Wallahi! Ba kowa ne shi’armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shi”.
“Su ba a gane su sai da kaskan da kai, da tsoron Allah, da rikon amana, da yawan zikiri, da azumi, da salla, da bin iyaye, da taimakon makwabta na daga fakirai, da mabarata, da masu bashi, da marayu, da gaskiyar magana, da karatun Kur’ani, da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma su ne aminan jama’arsu a kan al’amura. Ku ji tsoron Allah ku yi aiki saboda abin da Allah ya tanada, kuma babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, kuma mafi soyuwar bayi a wajan Allah wanda suka fi jin tsoronsa suka fi biyayya gareshi. Ya Jabir! Wallahi ba mu kusanta zuwa ga Allah sai dai da da’a, kuma babu kubuta daga wuta a gare mu, kuma babu wani mai hujja a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gunmu, kuma ba a samun soyayyarmu sai da aiki da tsentseni.
2- Tattaunawar Abu Ja’afar (AS) da Sa’id Bn Hasan [7]:
Abu Ja’afar (AS) “ Shin dayanku zai zo ga dan’uwansa ya sanya hannunsa a jakarsa ya dauki abin da yake so bai cire shi ba?
Sa’id: Ban san da haka ba a cikinmu.
Abu Ja’afar (AS): To Babu komai kenan.
Sa’id: To halaka ke nan.
Abu Ja’afar (AS): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna.
3- Muhawar Imam Sadik (A.S) da Abu Sabah Alkinani [8].
Alkinani: Muna shan wahalar mutane game da ku.
Abu Abdullah: Menene abin da kuke gamuwa da shi daga mutane?.
Alkinani: Magana ba ta gushewa tsakaninmu da mutun, sai ya ce: Wannan Dan Ja’afariyya ne mugu.
Abu Abdullahi: Mutane suna aibata ku da ni?
Alkinani: E mana.
Abu Abdullah: Wallahi karancin mai bin Ja’afar a cikinku ya yawaita! Kadai sahabbaina shi ne wanda tsantseninsa ya tsananta, ya yi aiki don mahaliccinsa ya kaunaci ladansa, wadannan su ne sahabbaina!
4- Abu Abdullahi (AS) yana da wasu maganganu game da wannan al’amari da zamu kawo wasu kamar haka:
A- “Baya daga cikinmu sam, wanda ya kasance a wani gari da a cikinsa akwai mutane dubu dari ko fiye da haka, ya zama a cikin garin akwai wanda ya fi shi tsantseni”.
B- “Mu ba ma kirga mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukan umarninmu yana mai nufi, ku sani daga cikin bin umarninmu da nufinsa akwai tsentseni, don haka ku yi ado da shi Allah ya yi muku rahama”.
C- “Wanda mata masu tsari ba sa magana game da tsantsaninsa ba ya daga cikin shi’armu, haka nan wanda ya kasance a cikin wata alkarya mai mutane dubu goma, a cikinsu akwai wata halitta ta Allah da ta fi shi tsentseni, shi ba ya daga cikin masoyanmu”.
D- “Kadai shi’ar -Ja’afar- shi ne wanda ya kame cikinsa da farjinsa, kokarinsa ya tsananta, kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa, ya kaunaci ladansa, ya ji tsoron azabarsa, to idan ka ga wadannan to wadannan su ne shi’ar Ja’afar.

Hukunce-hukuncen Addinin Musulunci

Mun yi imani cewa Ubangiji ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ayyukansu, abin da maslaharsa ta zama tilas sai ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da take tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa a garemu ta zama mai rinjaye ya soyar da shi - mustahabbi- a garemu.
Wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa, kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hukuncin Allah a kansa koda kuwa hanyar saninsa ta toshe garemu. Kuma hakika yana daga mummuna ya zama ya yi umarni da abin da yake akwai barna a cikinsa, ko kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Sai dai wasu daga daga cikin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne abin da Ubangiji ya hana kawai, kyakkyawa kuwa shi ne abin da ya yi umarni da shi, babu wata maslaha ko cutuwa a cikin ayyukan su a kan-kansu, wannan magana kuwa ta saba wa hukuncin hankali.
Kamar yadda suka halatta wa Allah ya aikata mummuna ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Hakika ya gabata cewa wannan magana akwai ketare iyaka mai girma a cikinta, ba domin komai ba sai domin lizimta danganta jahilci da gazawa ga Allah (T.A.U.K).
A takaice dai abin da yake ingantacce a yi imani da shi, shi ne : Ubangiji madaukaki ba shi da wata maslaha ko amfani a cikin kallafa mana wajibai da hana mu aikata haram, maslahar wannan duk tana komawa zuwa garemu ne, babu wata ma’ana wajen kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni da su ko hani ga barin su, domin Allah ba ya hani kara zube don wasa, kuma shi mawadaci ne ga barin bayinsa.

Hawan Hukunci A Kan Baligi

Mun yi imani cewa Allah (S.W.T) ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani.
Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
Kuma mun yi imani cewa: Babu makawa Allah madaukaki ya kallafa wa bayinsa ayyuka ya kuma sanya musu shari’o’in abin da yake na maslaharsu da alherinsu da rabautarsu ta har abada, ya kuma gargade su ga barin abin da yake akwai barna da cutuwa a kansu da mummunan karshe gare su, koda kuwa ya san cewa su ba zasu bi Shi ba, domin wannan tausasawa ce da kuma rahama ga bayinSa domin su suna jahiltar mafi yawancin maslaharsu da hanyoyin samunta a nan duniya da kuma lahira. Suna kuma jahiltar da yawan abubuwan da zasu jawo musu cutarwa da tabewa, Shi kuwa Ubangiji Shi ne Mai Rahama mai Jin kai, kuma Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa da yake mustahili ne ya rabu da shi har abada.
Ba ya janye wannan tausasawa da wannan rahama domin kasancewar bayinsa sun bujire wa bin sa, sun ki bin abubuwan da ya yi umarni da abubuwan da ya hana.

Annabawa Da Littattafansu

Mun yi imani a dunkule da cewa dukkan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da ismarsu da tsarkinsu, musanta Annabcinsu kuwa da zaginsu da isgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda ya ba da labari game da su da kuma gaskiyarsu.
Wadanda aka san sunayensu da shari’o’insu kamar Annabi Adam (A.S) da Annabi Nuhu (A.S) da Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Dawud (A.S) da Annabi Sulaiman (A.S) da Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) da sauran Annabawan da Kur’ani ya ambace su a sarari, ya wajaba a yi imani da su a ayyane, duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya, kuma ya karyata Annabcin annabinmu a kebance.
Haka nan ya wajaba a yi imani da littattafansu da abin da aka saukar musu. Amma Attaura da Injila da suke hannayen wadanda aka canza su daga yadda suka sauka saboda abin da ya auku gare su na daga canje-canje da sauye-sauye, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S), saboda wasan da ma’abuta son rai da kwadayi suka yi da su, wadanda ake da su yanzu mafi yawancinsu ko ma dukkansu kagaggu ne da aka farar a zamanin mabiyansu bayan wucewarsu (A.S).


1. Fadinsa madakaki: “Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa duniya bayina salihai ne zasu gaje ta, lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada”. Surar Anbiya’i: 105-106. Hadisai kuwa sun zo da silsila daban-daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.) da kuma Imamai (A.S) cewa: Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
2. Duba fadinsa madaukaki: “Kuma yayin da Isa dan Maryam ya ce: Ya Bani Isra’la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abin da yake gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da zai zo bayana sunansa Ahmad. Sai dai a yayin da ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne”. Surar Saff: 6.
3. Amirul muminin Aliyyu Dan Abi Dalib (A.S) ya siffanta shi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa: “Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mai tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai kuma shi ne mabubbugar hikima”. Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminin (A.S) yana cewa: “Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa. Ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo a duwatsu masu tsauri.” (Nahajul Balagha Huduba: 108).
4. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu ziyaratul ikhwan.
5. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.
6. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babut ta’a wat takawa.
7. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu Hakkil mu’umini ala akhih.
8. Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.



Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
2+1 =