Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

GAME DA SAURARON IMAMI BOYAYYE


Muhammad Mahadi Ha’iri Fuur

Hafiz Muhammad Sa’id

Bangare Na Farko: Boyuwarsa (A.S)

Kafin mu san wani abu game da imam Mahadi (A.S) wanda yake shi ne mai tseratar da dan Adam kuma karshen ajiyar Allah a bayan kasa, da farko zamu fara yin bayani game da buyansa (A.S) wanda yake yanki ne mai girma na tarihin rayuwarsa (A.S).

Abin da Ake Nufi Da Boyuwa

Buya yana nufin bacewa gabarin gani, ba yana nufin rashin halarta ba, don haka ne a wannan bangaren zamu yi magana game da buyan imam Mahadi (A.S) ga barin ganin mutane alhalin yana cikinsu, yana kuma rayuwa tare da su, wannan al’amari ne da ya zo a ruwayoyin imamai (A.S) imam Ali (A.S) yana cewa: Na rantse da ubangijin Ali, yana tsakanin mutane, yana zuwa gidajensu, yana kaikawo a gabashi da yammacin duniya, yana jin maganar mutane, yana yi musu sallama, yana ganinsu ba sa ganinsa har sai alkawarin Allah ya zo [1].
Na’ibinsa na biyu yana cewa: imam Mahadi (A.S) yana halartar aikin hajji, yana ganin mutane, yana kuma saninsu, amma su suna ganinsa amma ba sa saninsa [2].
Wannan ya nuna yana da buya kala biyu kenan, wani lokaci ba a ganisa, wani lokaci kuwa ana ganinsa amma ba a gane shi.

Gabatar (Gabanin) Boyuwa

Imam Mahadi (A.S) ba shi ne farkon wanda ya boyu ba a cikin bayin Allah (S.W.T), da yawa daga annabawan Allah sun boyu, wannan kuwa ba domin komai ba sai maslaha ta Ubangiji da take cikin hakan, ba maslaha ce ta su ba ko ta iyalansu, saboda haka ne buya ta zama daya daga sunnonin Allah da ta faru a lokacin annabawa kama Idris, Salih, Ibrahim, Ysufu, Musa, Shu’aibu, Iliyas, Sulaiman, Daniyal, da Isa (A.S), kowanne daga cikinsu a bisa sharudda na musamman ya boyu wasu shekaru [3].
Don haka ne ruwayoyi da suke nuna buyan imam Mahadi (A.S) suna nuna shi ne a matsayin daya da sunnonin Allah madaukaki.
Iama Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: “Hakika imam Mahadi (A.S) yana da buya da zai tsawaita, sai mai ruwaya ya ce: menen dalilin wannan buyan ya dan Manzon Allah (S.A.W) ? sai ya ce: Ubangiji yana son ya dora shi bisa sunnar annabawa a boyansu” [4].
Manzon rahama yana cewa: Mahadi yana daga ‘ya’yana ne… yana da buya da (kuma bayyanar) dimuwa (da zata mamaye mutane) har sai mutane sun kauce daga addininsu, sai ya zo a wannan zamanin kamar shihabun sakib “Tauraro mai walkiyar haske” sai ya cika duniya da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya [5].

Hikimar Boyuwar Imam Mahadi (A.S)

Saboda me imami kuma hujjar Allah (S.W.T) a kan talikai ya buya daga mutane? Mene ne ya sanya mutane suka haramtu daga albarkarsa?
Game da wannan al'amari an yi maganganu masu yawa kuma ruwayoyi masu yawa sun zo game da hakan, amma kafin mu bayar da amsar wannan tambaya ta sama dole ne mu yi nuni da wasu bayanai muhimmai:
Mu mun yi imani cewa Ubangiji masani ne wanda ba ya wani aiki babba ne ko karami sai bisa hikima da maslaha, ko mun san wannan maslahar ko ba mu sani ba.
Kuma dukkan al'amuran duniya ana tafiyar da su ne ta hannun Ubangiji madaukaki, kuma daya daga mafi muhimmancinsu shi ne al'amarin fakuwar da buyan imam Mahadi (A.S). Don haka buyansa ma ya kasance ne bisa hikima da maslaha koda kuwa mu ba mu fahimci hikimar hakan ba.
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa:
Ba makawa imam Mahadi (A.S) yana da boyuwa guda biyu wacce dukkan ma'abota bata zasu fada cikin yin kokwantonsa.
Sai mai ruwaya ya tambayi dalilin boyuwar, sai imam (A.S) ya ce:
Boyuwar ta kasance ne saboda wani al'amari da ba mu da izinin gaya muku shi… ita sirri ce daga asiran Allah (S.W.T) tunda mun san cewa Allah mai hikima ne mun yarda cewa dukkan ayyukansa suna kan hikima ne, koda kuwa hikimar hakan ta boyu garemu [6].
Kodayake duk da cewa ayyukan Allah bisa hikima suke kuma wani lokaci wannan hikima tana boyuwa garemu, amma muna neman sirrin hakan ne domin mu san hikimar wasu al'amuran domin ya ba mu nutsuwar zuciya sosai. Don haka ne zamu yi bincike game da wasu hikimomi da alamomi na boyuwar imam Mahadi (A.S) da kuma nuni da ruwayoyi da suke magana game da hakan:

Ladabtar Da Mutane

Idan wata al'umma ta kasance ba ta san matsayi da kima na wani annabi ko imami ba, kuma ba su yi abin da ya kamata ba game da shi, suka ma ki biyayya ga umarninsa, to ya kamata a raba su da shi domin masu zuwa nan gaba su amfana daga samuwarsa.
Gani albarkar samuwarsa zai sanya maslahar boyuwarsa ga al'umma duk da cewa ko su ba su gane hakan ba, ko kuma ba su san hakan ba.
An rawaito daga imam Muhammad Bakir (A.S) yace:
Idan Allah ba shi da wani mai gadonmu ko halifanmu a cikin al'umma sai ya dauke mu daga cikinta [7].

Samun 'Yanci Da Kuma Kubuta Daga Yin Bai'a Ga Wasu

Duk wadanda suke son su kawo wani sauyi a duniya yana kasance musu tilas su bi wasu sharudda da kulla wasu alkawura a farkon fara gwagwarmayarsu, amma imam Mahadi (A.S) game da kafa hukumar adalci ta duniya mai karfi da girma ba zai kai ga kulla wata yarjejeniya da wani karfi na zalunci ba. Kamar yadda ya zo a ruwayoyi shi za a umarce ne da fito-na-fito ne a fili da dukkan azzalumai ne. Don haka ne dole sharuddan bayyanarsa su kammala kafin ya bayyana domin kada a tilasta shi kulla sharudda da wani azzalumi.
Wata ruwaya daga imam Rida (A.S) tana cewa:
Domin a wannan lokacin da zai motsa da takobinsa, ya kasance babu wani da ya yi wa bai'a [8].

Jarraba Mutane

Jarraba mutane yana daga cikin sunnar Allah (S.W.T) yana jarraba bayinsa ta hanyoyi daban-daban domin su kai ga tafarki madaidaici. Kodayake sakamakon jarrabawa a wajen Allah sananne ne, amma bayi ne nasa yake jarrabawa domin su kai ga kamalar samuwarsu.
Imam Musa Kazim (A.S) yana cewa: yayin da dana na biyar zai boyu ku kula sosai game da addininku kada wani ya zo ya fitar da ku daga cikinsa… wannan boyuwar tasa jarrabawa ce da Allah yake jarraba bayinsa da ita [9].

Kare Ran Imami (A.S)

Daya daga cikin dalilan boyuwar annabawa daga cikin mutanensu shi ne domin kare rayuwarsu da rayukansu, domin su samu damar isar da sakon Allah a lokutan da dama ta samu su kan boyu da izinin Allah a wasu lokuta, kamar yadda Manzo (S.A.W) ya buya a kogon kuma wannan duk da umarnin Allah ne.
Game da imam Mahadi ma haka nan al'amarin yake, kuma ruwayoyi masu yawa sun zo suna bayanin haka:
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa:
Kafin imam Mahadi (A.S) ya tashi da motsinsa zai faku daga ganin idanuwa wani lokaci mai tsayi. Sai aka tambaye shi dalilin haka. Sai ya ce: Yana tsoron ransa ne [10].
Duk da cewa shahada wani buri ne na bayin Allah a wajen isar da sakon Allah da kawo gyara ga al'umma da kuma addinin Allah. Amma idan kashewar ta kasance tana nufin rashin kaiwa ga hadafin da ake son kaiwa gareshi ne to tsoron kisa al'amari ne da ake hankaltar sa.
Kashe imami (A.S) na goma sha biyu wanda yake shi ne karshen ajiyar Allah a bayan kasa gaba daya, kamar rushe ka'aba ne gaba daya, da rashin kaiwa ga samuwar cikar burin dukkan annabawa da waliyyan Allah (A.S), da kuma rashin tabbatar alkawarin Allah (S.W.T) na kafa hukumar adalcin Allah a karshen duniya ne.
A cikin wasu ruwayoyin an ambaci wasu dalilai din boyuwarsa wadanda ba zamu iya kawo su ba saboda karancin lokaci, amma dai abin sani shi ne, boyuwar tana daga cikin sirrorin Ubangiji madaukaki, kuma hikimar haka zata bayyana ne bayan bayyanarsa (A.S) kuma wadannan abubuwan da aka fada abubuwa ne da suka sabbaba boyuwar tasa (A.S).

Bangare Na Biyu

Nau'o'in Boyuwa
Idan mun yi la'akari da abin da aka fada a baya zamu ga cewa boyuwar imam Mahadi (A.S) wani abu ne wanda yake tilas, amma idan mu ka duba dukkan na'uin wata gwagwarmaya da wani motsi da wadanda suka gabace mu suka yi zamu ga cewa an yi ta ne domin karfafa imani da akidar mutane ne. kuma akwai abin da ake jin torso na cewa kada buyan nasa ya haifar da wani miki da ba mai warkuwa ba ne a cikin addinin musulunci, amma al'amarin boyuwa zamu ga cewa al'amari ne da aka shirya shi ya farar da tsari da lura mai zurfi kuma a kan haka ne ya ci gaba.
Shekaru masu yawa kafin haihuwar imami na goma sha biyu, maganganu da yawa game da shi sun zo daga harsunan manyan waliyyai kuma imamai (A.S) da sahabbansu. Haka nan nau'in alakar imam Askari da imam Hadi (A.S) da sahabbansu ya kasance ne bisa wani yanayi na musamman kuma sabo wanda ba a saba da shi ba kuma iyakantacce sosai, ta yadda shi'a suka saba da wani mai shiga tsakaninsu da imamai (A.S) wajen sanin addininsu ba tare da sun ga imam (A.S) kai tsaye ba.
Haka nan bayan mutuwar imam Hasan Askari (A.S) alakar Shi'a da imaminsu imam Mahadi ba ta katse gaba daya ba, sai dai mutane suna samun alaka da shi ne ta hannun wakilansa.
Ta haka ne Shi'a suka saba da cewa ba dole ne sai sun yi alaka da imami (A.S) kai tsaye wajen sanin addininsu da aikace-aikacensu ba, kuma hakan ba sharadi ba ne garesu. A bisa wannan yanayi ne ya zama ya yi daidai imam Mahadi (A.S) ya shiga boyuwa mai tsayi, kuma a yanke alakarsa da mabiyansa sabanin yadda aka saba a farko.
Kuma zamu kawo wasu bayanai game da boyuwarsa mai tsawo da dogon zango.

Boyuwarsa Mai Gajeren Zango

Da yin shahadar imam Hasan Askari (A.S) a shekarar hijira 260, a lokacin imami na goma sha daya, daga wannan lokaci ne karamar boyuwa ta fara har zuwa shekara ta 329 kusa shekaru 70 kenan.
Mafi muhimmancin al'amarin wannan lokaci shi ne alakar mutane da imam Mahadi (A.S) tana kasancewa ne ta hanyar wakilai kuma ta hanyarsu ne ake aika masa da tambaya ana kuma karbar amsa. Kuma wani lokaci har da sa hannunsa ake samu ta hanyar su [11].
Wadannan wakilai na musamman dukkaninsu suna daga cikin malaman Shi'a wadanda imam Mahadi (A.S) ya zaba daga cikin malamai domin su kasance 'yan sakonsa wadanda su hudu ne kamar haka:

1- Usman dan Sa'id Umari; wakilin imam Mahadi daga farkon boyuwa kuma ya mutu a shekarar 265, kuma shi ne wakilin imam Hadi da imam Askari (A.S).

2- Muhammad dan Usman Umari; dan wakili na farko wanda ya samu matsayin wakilcin imam Mahadi (A.S) bayan mutuwar dansa, shi kuma ya mutu a shekarar 305 hijira.

3- Husaini dan Ruhu Nobkhati ya mutu a shekarar 326, bayan ya yi shekara 21 yana wakilcin imam Mahadi (A.S).

4- Ali dan Muhammad Samuri; ya mutu a shekarar 329, kuma da mutuwarsa ne karamar boyuwa lokacinta ya kare gaba daya, kuma aka shiga dogowar boyuwa.
Wadannan wakilai na imam Hasan Askari da imam Mahadi (A.S) su ne suke zabarsu da hannunsu, aka kuma sanar da su ga mutane.
Sheikh Dusi yana rawaitowa a littafinsa na "Al'gaiba" cewa: wata rana mutane arba'in daga shi'a sun kasance tare da Usman dan Sa'id amari wakilin imam Mahadi na farko a wajen imam Askari (A.S) sai imam (A.S) ya nuna musu dansa da yake gabansa ya ce:
Bayana wannan yaron shi ne imaminku. Ku yi biyayya gareshi… ku sani cewa daga yau ba zaku sake ganinsa ba har sai shekarunsa sun cika. A boyuwarsa duk abin da Usman ya gaya muku ku yarda da shi ku karbi umarni daga gareshi, domin shi ne wakilin imaminku, kuma dukkan ayyuka suna hannunsa [12].
A wata ruwayar ya zo cewa; imam Hasan Askari da imam Mahadi (A.S) sun yi magana suna masu fada karara game da wakilcin Muhammad dan Usman wakili na biyu na imam Mahadi (A.S).

Sheikh Dusi yana cewa

Usman dan Sa'id yana tattara dukiyoyin shi'ar Yaman da umarnin imam Hasan Askari (A.S) yana kawowa, wasu mutanen sun san abin da yake gudana sai suka zo suka gaya wa imam (A.S), sai ya ce: Na rantse da Allah! Usman yana daga mafifitan Shi'a'rmu, kuma da wannan aikin da yake yi yana dada bayyana garemu a fili (cewa shi mutumin kirki ne).
Imam Hasan Askari (A.S) yana cewa: Haka ne; ku shaida Usman dan Sa'id wakilina ne, kuma dansa Muhammad wakilin dana ne [13].
Wannan ya kasance a lokacin kafin buyan imam Mahadi (A.S) ne, kuma a tsawon wannan boyuwar tasa karama kowane daga wakilansa kafin mutuwarsa aka umarce shi da ayyana wani wakilin da umarnin imam Mahadi (A.S).
Wadannan mutanen sun cancanci wakilci ne saboda siffofi na gare da suke da su, sun ada amana da tsarkaka da adalci a magana da aiki, da rike sirri, da boye sirrin Ahlul Baiti (A.S). Kuma su mutane ne da ake dogara da su da kuma yada mazhabar Ahlul Baiti (A.S).
Wasu nsu tun suna da shekaru 11 suke tare da tarbiyyantarwar imamai (A.S), kuma iliminsu yana tare da imani mai karfi a tare da su. Sunansu na gari ya yadu a harsunan mutane, tare da hakuri da juriya da dauke duk wata matsala da nauyi da wahalhalu da ya cakuda da samuwarsu, ga kuma cikakkiyar biyayyarsu ga imaminsu (A.S). Hada da dukkan wadannan siffofi na gari kyawawa kuma suna da karfin tafiyar da al'amuran Shi'a da cikakkiyar fahimta da kamala da sanin zamaninsu da amfana daga al'amura, da kuma shiryar da al'ummar Shi'a zuwa ga tafarki na Ubangiji na shiriya kuma suka wuce karamar boyuwa da aminci.
Binciken karamar boyuwa da kuma rawar da wakilai hudu suka taka mai muhaimmanci wajan samar da alaka tsakanin imam (A.S) da al'umma wannan yana nuna wani bangare mai muhimmanci na rayuwar imam Mahadi (A.S).
Kuma samuwar wannan alaka da kuma samun damar ganin imam (A.S) ga wasu jama'a na Shi'arsa a tsawon wannan boyuwa yana da tasiri mai yawa wajen tabbatar da tabbacin haihuwa da samuwar imam Mahadi (A.S) imam na goma sha biyu kuma karshen hujjar Allah a duniya. Wannan ci gaba mai girma da aka samu ya faru ne a daidai lokacin da makiya suke kokarin ganin sanya shakku game da samuwar haihuwar dan imam Hasan Askari (A.S), hada da cewa lokacin ya yi daidai da faruwar babbar boyuwa wanda a cikinta mutane ba su da wata alaka ta saduwa da haduwa da imaminsu ta hannun wasu mutane ayyanannu, amma da samuwar wannan nutsuwa ta zuciya a wannan lokuta da kuma amfanuwa daga albarkar samuwarsa sun share fagen boyuwarsa babba.
Boyuwarsa Mai Tsawo
A karshen ranakun rayuwar wakilinsa na hudu imam Mahadi (A.S) ya yi magana da wakilinsa kamar haka:
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, kai Ali dan Muhammad Samuri, ina yi maka jajen rasuwarka, da kuma ga 'yan'uwanka na addini, Allah ya ba ka ladan musibar rashinka, domin kai mai mutuwa ne nan da kwana shida, don haka kai mai tafiya ne zuwa ga marigayanka. Ka shirya sauran al'amuranka, kuma kada ka yi wa wani wasiyya da mamaye gurbin ka! Domin cikakken buya mai tsayi lokacinsa ya yi, kuma daga nan babu wani bayyana tare da ni, sai dai da umarnin Allah madaukaki, wannan kuwa bayan tsawon wata mudda mai tsaywo da zukata zasu sami mamayewar tsanani da kekashewa, kuma danniya da zalunci zai cika duniya [14].
Don haka ne bayan wafatin wakilin imam na karshe a shekarar 329 H, sai boyuwa mai tsayi da aka fi sani da boyuwa babba ta fara, kuma wanda zai ci gaba har zuwa ranan da Allah ya so, sai a samu bayyanar rana da boyuwar gajimare, kuma duniya ta samu hasken rana kai tsaye.
Haka nan ne kamar yadda ya gabata a lokacin boyuwa karama, Shi'a suna da alaka da imam ta hanyyar wakilansa ne, kuma ta haka ne suke sanin ayyukan Allah da suka hau kansu, amma a yanzu irin wannan alaka ta yanke, don haka muminai suna koma wa malaman addini ne domin sanin abin da ya hau kansu a yau, kuma wannan al'amari ne imam Mahadi (A.S) ne da kansa ya bayar da umarninsa ta hanyar wata wasika da ya yi wa manyan Shi'a'wansa yana mai cewa a cikin wannan wasika da aka samu ta hannun wakilinsa na biyu:
Amma al'amuran da suke faruwa, ku koma wa masu rawaito hadisanmu a cikinta, domin su hujjata ce a kanku, ni kuma hujjar Allah ne a kansu… [15]
Wannan al'amari hanya ce sabuwa domin amsa wa tambayoyin addini kuma mafi muhimmanci domin sani ayyukan da suka hau kan Shi'a a daidaiku da kuma a gaba daya, a cikin wannan boyuwa cikakkiya ta imam Mahadi (A.S), wannan kuwa al'amari ne da ya ke tsari ne na shugabanci a cikin shi'anci da babu wan tsari da ya kai shi, kuma al'amari ne rayayye a kodayaushe, kuma na shiriya da jagoranci mai karfi, wanda ya zamanto Shi'a sun kasance ba a bar su ba tare da mai shiryarwa ba, kuma sun wadatu da malamansu masu takawa da amanar addini da ta duniya ta mutane, wajen sanin addini a kowane fage na daidaiku da na jama'a gaba daya, kuma wannan al'amari shi ya kiyaye wannan jirgin tsira na musulunci daga ambaliyar nan ta kogunan bata da yake neman kifar da shi, kuma ya kiyaye iyakokin akidojin Shi'a gaba daya.
Game da gudummuwar da malamai suke bayarwa a lokacin boyuwar imam Mahadi, imam Hadi (A.S) Yana cewa:
Ba domin malamai ba da suke shiryar da mutane zuwa ga hujjar Allah bayan fakuwarsa, kuma suke nuna musu imamansu, kuma suke kare su da dalilai masu karfi na Ubangiji (S.W.T), kuma ba domin malamai masu tunani ba, masu tseratar da bayin Allah daga tarkon shedan da masu siffar shedan da gaba da Ahlul baiti (A.S). Da babu wani mutum face sai ya fita daga addinin Allah madaukaki, sai dai kasancewar wadannan mutane masu dauke da akidu na Shi'a masu karfi da suke kama da masu tukin jirgin ruwa, da suke kiyaye masu hawan jirgin, wadannan su ne malamai da suke mafifitan bayi kusanci da Allah madaukaki [16].
Babban abin da dubawa a nan shi ne sharuddan da siffofi da ya kamata shugaban mutane ya kasance yana da su, domin bayar da irin wannan matsayi na al'marin mutane a addini da duniya dole ya kasance tare da kula sosai da lura da zurfafawa. Don haka ne ma masu maye gurbin imam (A.S) aka san su da siffofi na wadanda suke makoma na addini kuma masu mukami mai girma da jagoranci da aka fi sani da "waliyyul fakih".
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: daga cikin malamai akwai wadanda suke sun kiyaye kawukansu daga sabo babba da karami, kuma sun tsare addini, kuma sun sabawa son ransu, kuma suna masu biyayya ga umarnin imamin zamaninsu, kuma suna umartar mutane da biyayya gareshi, wasu daga malaman Shi'a ne suke haka ba dukkansu ba [17].

Bangare Na Uku

Fai'dojin Boyuwar Imam Mahadi (A.S)
Daruruwan shekaru kenan dan Adam ya rasa alherin bayyanar imam Mahadi (A.S) kuma al'ummar musulmi ta ci gaba sa asarar rashin amfanuwa daga jagoran da Allah ya ayyana wa duniya kuma jagoran ma'asumi. Hakika samuwarsa da fakuwarsa da rayuwarsa ta boye da kuma nisantarsa daga duniya dole ne ya zama abin tambaya cewa wane amfani yake da shi ga mutanen duniya. Shin a nan kusa ba za a samu bayyanarsa ba, a kawar da wannan wahala ta shi'arsa da ta kasance sakamakon boyuwarsa?
Wannan tambaya da makamantanta duk suna tasowa ne sakamakon rashin sanin imami ma'asumi da matsayinsa wanda yake hujjar Allah a duniya.
Hakika matsayin imami a duniyar samammu yaya zai kasance, shin almomin samuwarsa sun takaita da bayyanarsa ko kuma shi domin jagorancin mutane ne kawai yake, shin samuwarsa tana da albarka da tasiri ga dukkan samammu ne ko kuwa?

Imam Shi Ne Ginshikin Samuwa

A mahangar Shi'a da kuma koyarwar addini imami shi tsakatsaki domin falalar Allah ga dukkan samammu d ahalittu, shi ne wanda yake ginshiki na tsarin samuwar kuma madogara, idan babu shi to dukkan duniya da 'yan Adam da aljanu da mala'iku da dabbobi da sandararru ba zasu rage ba.
An tambayi imam Ja'afar Sadik (A.S) cewa, shin duniya zata kasance ba tare da imami ba? Sai ya ce: idan duniya ta kasance babu imami to kowane mai samuwa a doronta zai kawu.
Kuma shi a matsayinsa na tsakiya kuma wasila ta isar da sakon Allah da shiryar da mutane zuwa ga kamalar dan Adam kuma dukkan wata falala da albarka ta Ubangiji ta hanyarsa ne take isa zuwa ga kowa.
Wannan kuwa wani abu ne bayyananne domin Allah ya sanya annabawansa hanyar shiryay ga mutane da kuma masu mayewa bayansa, Kuma mun samu daga maganganun ma'asumai cewa samuwar imamai a fadin duniya yana kasancewa ne domin isar da ni'imar Allah da falalarsa zuwa ga dukkan manya da kananan halittunsa, wato dukkan abin da yake isa zuwa ga halittu na falalar Allah (S.W.T) suna samunsa ne ta hannun imamai (A.S). Don haka samuwarsu ta hanyar imamai ne, haka ma ni'imar Allah garesu a tsawon rayuwarsu ta hannunsu ne.
Ya zo a cikin ziyarar jami'a babba game da sanin imami (A.S) cewa: Da ku ne Allah ya bude da ku ne kuma zai cika, da ku ne yake saukar da ruwa da kuma yake rike da sama don kada ta fado kan ma'abotanta.
Don haka albarka da ni'imar samuwar imami ba sai yana bayyane ba, samuwarsa tana da albarkarta koda kuwa yana boye ne, kuma shi ne ruwan rayuwar halittu gaba daya, kuma Allah ne ya so hakan ta kasance da ikonsa da nufinsa, ya sanya mafifitan halittunsa su kasance tsaka-tsaki wajen kwararar ni'imarsa ga sauran bayinsa, kuma a wannan fage babu bambanci tsakanin bayyanarsa da boyuwarsa. Don haka dukkan halittu ba su da wani matsala da zasu samu domin boyuwarsa. Wani abin kayatarwa shi ne an tambayi imam Mahadi (A.S) game da boyuwarsa d akuma amfana daga gareta sai ya ce: Amma yadda za a amfana daga gareni a boyuwata kamar yadda rana take amfanar mutane ne koda kuwa ta shamakance da gajemare.
An kamanta samuwar imam Mahadi (A.S) da rana da take buya a bayan gajimare kuma an kamanta boyuwarsa da kisfewarta, a nan akwai muhimman bayanai masu yawa wadanda zamu yi nuni da wasu a nan.
Rana a tsarin taurari da duniyoyi ita ce a tsakiya, kuma dukkansu suna kewaya ta, haka ma samuwar imami (A.S) kamar cibiyar duniyoyi ce da sauran duniyoyi da taurari suke kewayarta. "Da wanzuwarsa ne duniya ta wanzu kuma da albarkarsa ne aka arzuta halittu, da samuwarsa ne kasa da sama suka tabbata suka tsaya.
Wani lokaci rana ba ta barin haskakawa a kowane lokaci, kuma kowa yana da rana daidai alakarsa da ita, kuma yana amfana daga haskenta, haka nan samuwar waliyyi shuganba wannan zamani yake samar da dukkan ni'ima ta duniya da ta lahira, wacce take daga ubangijin halitta gaba daya, amma kuma kowa yana samu ne daidai gwargwadon kamalarsa yake amfana daga shi.
Idan rana ba ta kasance a bayan gajimare ba, to tsananin sanyi da duhu za su kawu, haka nan ne ma duniya idan ba ta da imami (A.S) a cikinta, to bala'i da wahalhalu da musibu marasa dadi zasu sanya cigaban rayuwa ya kasance wani abu ne da ba zai yiwu ba.
Imam (A.S) a cikin wasikarsa zuwa ga sheikh Mufid (K.S) yana cewa: Mu ba masu barin kiyaye wa gareku ba ne, kuma ba masu mantawa da ambatonku ba ne, ba domin haka ba da bala'o'i sun sauka a kanku, kuma da makiya suna kawar da ku daga doron kasa.
Sabo haka ranar samuwar imami (A.S) tana haskaka wannan duniya, kuma tana kwararai falalar allah ga kowane samamme, kuma a cikin al'ummu musamman musulmi al'ummarsa shi'arsa suka yi imani da shi to sun fi kowa amfana daga albarkarsa kuma zamu kawo wasu misalai game da hakan.

Karfafa Buri

Buri yana da ga cikin jarin tafiyar rayuwa, burinmu shi ne jarinmu na rayuwa kuma nishadinmu mai cigaba ba yankewa, kuma shi ne yake sanya mu motsi da aiwatarwa. Samuwar imami a duniya yana sanya mana burin samun nan gaba mai haske, kuma yana sanya shauki. Shi'a a tsawon tarihinsu sama da shekaru dubu daya da dari hudu, sun fuskanci bala'o'i daban daban, amma burin samun cewa akwai nan gaba mai haske ga muminai ya hana su samun rauni da gajiyawa da tsayawa kyam da kokari da rashin mika wuya. Addini imani ne kuma samun nan gaba ba tatsuniya b ace, nan gaba mai zuwa wacce take mai kusanci da take kusa, domin shugaban wannan zamani mai zuwa a raye yake, kuma a kowane sakand zai iya bayyana, don haka a kodayaushe da ni da kai dole mu kasance a shirye.

Tabbatar Mazhaba

Duk al'umma wata al'umma tana da bukatar samun jagora masani domin kiyaye samuwarta domin takai zuwa ga hadafinta datake buri, domin al'aummar ta kasance mai motsawa karkashin jagorancinsa. Samun jagora wani wani kariya ce mai karfi domin mutane su samu tsari mai karfi wanda yake bayar da kariya ga al'amarinta da ya gabata, kuma karfafa al'amarin da zai zo nan gaba.
Shugaba rayayye kuma mai aiki koda kuwa baya cikinjama'arsa amma ba zai ta ba takatitawa ba wajen nuna mata hanyar da zata bi, kuma zai tsawata mata ta hanyoyi da dama daga kauce wa hanya.
Imam Mahadi (A.S) duk da ya kasance a boyuwa amma samuwarsa wani babban lamari ne wajen kare mazhabin Shi'a. kuma shi yana maganin mummunan makarkashiyar makiya ta hanyoyi da dama, kuma yana kare tunanin shi'arsa daga karkacewa kuma yayin da makiya suke yaudarar ma'abota addinai da akidu ta hanya daban-daban to shi yana kangiya daga kaidinsa ta hannun malmai masu shiryarwa da gyara da yake zaba.
Domin misali bari mu kawo kulawar imam Mahadi (A.S) ga shi'arsa na Bahrain, daga bakin Allama Majalisi:
Wata rana wani komanda makiyin Ahlul Baiti (A.S) yana jagorancin hukuma, wanda yake wazirinsa a gaba da Ahlul Baiti (A.S) kamar ba shi da na biyu, wata rana ya shiga wajen komanda ya taho da wani ruman a jikinsa an rubuta "La'ilaha illal-Lah, muhammadur rasulul-Lah, Abubakar da Umar da Usman da Ali halifofin Manzon Allah". Sai ya nuna wa komanda, shi kuma da ya ga haka sai ya yi murna, ya ce da waziri: Wannan ya nuna lalacewar shi'anci da karyarsa; Yaya kake ganin waziri game da Shi'a'wan Baharain?
Waziri ya ce: Dole ne mu kawo su mu nuna musu wannan, idan sun karba sun fita daga mazhabarsu to shi kenan, amma idan ba haka ba, to sai mu ba su zabi uku, ko su kawo dalili, ko kuma su biya jiziya, ko mu yake su, matansu su koma ribatattu, dukiyoyinsu su koma ganima.
Komanda ya karbi wannan ra'ayi kuma ya kirawo Shi'a, sannan ya nuna musu Ruman ya ce: idan ba ku da wani dalili to zan ribace matanku da dukiyoyinku, ko kuma ku biya jiziya.
Malaman Shi'a suka rasa yadda zasu yi, amma bayan tattauanawa sai suka zabi mutanensu na gari 10 daga cikinsu suka zabi 3, a dare na farko suka aika mutum na farko domin ya je sahara bakin ruwa ya yi tawassuli da imam Mahadi (A.S) amma bai samu wata amsa ba, a rana ta biyu suka aika mutum na biyu shi ma ya dawo babu amsa, amma a rana ta uku da dare suka tura wani mutum mai suna Muhammad dan Isa ya tafi sahara ya yi kuka ya yi addu'a ya nemi taimako daga imam Mahadi (A.S) sai ya ji kira da sauti mai cewa: ya kai Muhammad dan Isa yaya na gan ka a wannan halin? Yaya ka fito a sahara?.
Sai Muhammad dan Isa ya nemi ya nuna masa shi waye.
Sai ya ce: Ni ne ma'abocin wannan zamani, ka fadi bukatarka!
Sai Muhammad dan Isa ya ce: Idan kai ne imam Mahadi (A.S) ka san halina kuma ba ka bukatar wani labari daga gareni!
Sai ya ce: ka yi gaskiya, yanzu saboda wannan musibar ne ka zo nan?
Ya ce: na'am, ka san abin da ya same mu, kuma kai ne imaminmu mafakarmu.
Sai imam (A.S) ya ce: ya Muhammad dan Isa! A gidan wannan wazirin akwai bishiyar ruman. Yayinda ruman ya fara sabonsa, sai ya kwaba tabo da wannan shakalin ya raba shi biyu, kuma a tsakiyarsa sai ya rubuta wadannan kalmomin, ya kuma sanya wannan shakalin a cikin ruman da yake dan karami sabon farawa sannan ya rufe, tun da ruman ya girma ne a cikin wannan shakalin sai wannan zanen ya fito masa! Gobe ka je wajen wannan komanda ka gaya masa ni zan ba ka amsa ta a gidan waziri ne. Idan ka shiga gidan waziri sai ka shiga daki kaza akwai wani buhu fari da wannan shakalin na tabo yake cikinsa, kuma ka nuna wa komanda wannan.
Alama ta biyu wacce take ita ma karamarmu ce, ka gaya wa komanda ya raba wannan ruman din biyu, zai ga ba komai a ciki sai tsutsa da toka!
Muhammad dan Isa ya yi farin ciki da wannan magana, ya koma ya gaya wa Shi'a. A rana mai zuwa suka zo wajen komanda kuma dukkan abin da imam (A.S) ya gaya masa sai da ya tabbatar da su. Da komanda ya ga wannan karamomi sai ya zama Shi'a kuma ya bayar da umarni aka sare kan wannan waziri mai yaudara [18].

Gina Kai

Kur'ani mai girma yana cewa: "ku yi aiki, da sannu Allah da manzonsa da muminai zasu ga ayyukanku" [19].
Ya zo a ruwayoyi masu yawa cewa: Abin da ake nufi da muminai a nan su ne imamai ma'asumai.
Don haka ne ayyukan mutane suke a gaban imam zaman (imam Mahadi). kuma shi yana ganin wadannan ayyuka, wannan kuwa wani nau'i na tarbiyya ne da yake iya ba wa Shi'a damar gyara ayyukansu gaban Allah da kuma imaminsu, domin su gyara ayyukansu kuma su kawar da dukkan wani sabo. Don haka ne ma duk sadda mutum ya fuskanci makomarsa to ya fi tsarkaka kuma zuciyarsa ta fi tsakarka da samun haske, wannan kuwa abu ne wanda yake afili kuma bayyananne.

Madogarar Ilimi Da Tunani

Imamai ma'asumai su ne masu ilmantarwa da bayar da tabbiyaya ga al'umma kuka mutane suna sha daga dadadan ruwansu a lokacin boyuwar imam Mahadi (A.S) duk da cewa ba ma iya samun sa kai tsaye mu amfana daga garesu amma dai shi ne ma'adinin ilimin Allah wanda dukkan matsalolin ilmin da tunani na Shi'a shi ne yake bude su ya warware. Kuma a lokacin boyuwarsa karama an samu tambayoyi masu yawa daga malamai da mutane da ya amsa su ta hanyar tambyoyi da sa hannunsa da suka shahara.
A amsar wasikar Ishak dan Ya'akub imam Mahadi (A.S) yana cewa: Ubangiji ya shiryar da kai kuma ya tabbatare dakai, amma masu musunmu da ka tambaya daga 'ya'yan amminmu ka sani cewa Allah ba shi da alakar jini da wani, duk wanda ya yi musuna, ba ni, ba shi, kuma karshensa kamar na dan annabi Nuhu (A.S) ne… amma dukiyarka matukar ba ka tsarkake ta ba, to ba zamu karba ba… Amma dukiyar da ka aiko mana daga irin wannan mai tsarki ce kuma zamu karba…
Duk kuma wanda ya ci dukiyarmu ya dauke ta a matsayin halal to ya ci wuta ne… amma yadda za a amfana daga gareni kamar yadda ake amfana daga ranane da take boye bayan gajimare, kuma ni aminci ne ga mutanen duniya kamar yadda taurari suke aminci ga mutanen sama. Kuma duk abin da ba shi da amfani gareku kada ku tambaya game da shi, kuma kada ku wahalar da kanku wajen sanin abin da ba a nema daga gareku ba, kuma ku yi addu'a matuka domin neman bayyanata, wannan shi ne farin cikinku, aminci tabbata gareka ya Ishak dan Ya'akub, kuma aminci ya tabbata ga dukkan wanda ya bi shiriya.
Bayan boyuwa karama saudayawa malaman Shi'a sun yi tambaya game da matsalaoli masu yawa kuma sun samu amsa daga imam (A.S).
Mir Allama daya daga daliban Mukaddis Ardabili yana cewa: Wata rana rabin da re a Najaf a haramin imam Ali (A.S) na ga wani mutum yana tafiya zuwa harami sai na tafi wajensa, koda na yi kusa da shi sai na ga wani tsoho ne da wani malami mai suna Ahmad Mukaddis Ardabili, sai na boye kaina.
Ya tafi kusa da haram sai kofa da take kulle, nan take ta bude masa sai ya shiga, sai bayan wani lokaci ya fita ya tafi Kufa.
Sai na bi shi a baya ta yadda ba zai ganni ba, kuma ya shiga masallacin Kufa kuma sai ya kusanci wurin da a nan ne aka sari imam Ali (A.S) sai bayan wani lokaci ya fita daga wurin sannan sai ya tafi Najaf kuma ni duk a hakan ina ta binsa, har ya kai masallacin Hanane, sai tari ya kama ni, da ya ji tarina sai ya juyo ya kalle ni ya ce: Ko mir Allama ne? sai na ce: na'am. Sai ya ce; me kake yi a nan? Sai na ce: ai tun lokacin da ka shiga haramin imam Ali (A.S) ina bin ka a baya, don Allah ina hada ka da girman wannan kabari sai ka gaya mini me ya faru tun da farko na daga sirrin wannan al'amari da ya faru!
Sai ya ce: da sharadin matukar ina raye ba zaka fada wa kowa ba! Sai na dauki alkawari, sai ya ce: wani lokacin mas'aloli sukan rikice mana ta yadda ba yadda zamu samu warwara sai ta hannun tawassuli da imam Ali (A.S), a yau ma wata mas'ala ce nake tunanin warware ta don haka sai na ga bari in tafi wajansa in yi tambaya.
Amma da na kusanci harami sai na ga kofa ta bude kamar yadda ka gani, sai na shiga na yi kuka domin in samu amsa, sai na ji sauti daga kabarin ya ce: ka tafi masallacin Kufa domin imam Mahadi (A.S) yana can, kuma shi ne imamin zamaninka, don haka ka tambaye shi.
Sai na tafi masallacin Kufa na tambaye shi kuma na samu amsa, yanzu haka zan tafi gidana ne.

Shiryarwa Ta Badini Da Kuma Zurfafa Cikin Ruhi

Imami shi ne hujjar Allah kuma aikinsa shi ne shiryar da mutane, kuma kokarin sa shi ne ya shiryar da mutane domin su samu wannan shiriya din, kuma wani lokaci yana alaka da mutane a fili domin isar da al'amarin Allah kuma yana nuna musu hanyar rabauta ta duniya da lahira, wani lokaci kuma yana amfani da karfinsa domin ya sanya wa mutane tasiri ta hanyar badini kuma yana karkatar da su zuwa ga alheri ta irin wannan hanya wacce take ita ce hanyar kamala da shiriya. A wannan bangare babu wata bukata ga shiriya ta zahiri abin da ake so shi ne shiriya ta badini. Imam Ali ya yi bayanin wannan da cewa:
Ubangiji ba don akwai hujjarka a duniya ba wanda zai kama hannun halittu zuwa ga shiriya… idan da koda ba mu ga wannan samuwa ta imami a zahiri ba amma babu kokwanto muna ganin koyarwa da tarbiyyarsa a zukatan muminai kuma su suna aiki ne bisa wannan asasin.
Imami boyayye yana aiki domin shiryar da mutane domin motsawa da kuma samar da sauki karkashin tarbiyyantarwarsa ta musamman domin su shirya wa zama cikin tawagar wannan imami, kuma wannan duk yana faruwa ne don albarkar samuwar imami boyayye.

Kariya Daga Bala'o'i

Babu wani kokwanto cewa asalin asasin rayuwa shi ne kariya da aminci kuma faruwan bala'o'i suna sanya rayuwa ta fada cikin hadarin karewa kuma sarrafa wadanan musibu da kawar da su duk da abubuwan na zahiri suna iya tasir wajen ahaka mama abubuwan badini su suka fi taka rawa a ciki, kuma akwai ruwayoyi na magabata masu yawa da suka zo game da samuwar imami wanda yake shi ne aminci ga mutanen duniya gaba daya.
Imam Mahadi (A.S) yana cewa: ni ne aminci ga mutanen kasa…
Samuwar imami yana hana saukar musifu da jawo azabar Allah da fushinsa da sukan iya sauka sakamakon ayyuka da fasadi da barna da mutane suke yi.
Kur'ani mai girma yana fada cewa: Allah ba zai azabtar da su alhalin kana cikinsu…
Imam Mahadi (A.S) shi ne asasin bayyanar rahamar Allah kuma da shi ne ake kare al'umma daga bala'o'i manya musamman ga al'ummar da take shi'arsa, duk da cewa su kansu Shi'a ba kasafai sukan kula da wannan karamomi nasu ba, ko su fahimci cewa wani hannun boye ne ya taimaka musu.
Imam Mahadi (A.S) yana cewa: Ni ne cikamakon wasiyyai, kuma da ni ne Allah yake kare bala'i daga ma'abotana da Shi'ata.
Zamu iya gani a kwanakin juyin musulunci da kuma yakin daular musulunci ta Iran sauadyawa mabiya imam Mahadi suka tsallake wani babban tarkon da makiya suke danawa kuma suka karya hukuncin nan na dokar hana yawon dare a 20 ga watan Bahaman 1357, da umarnin imam Khomaini, kuma duba fadowar helikwaftan Amurka a saharar Dabs a 1359 H.Sh. da kuma gano juyin nan na 21 ga watan Tir 1361, da kuma kasawar makiya a yakin shekaru takwas na yaki.

Imam Mahadi (A.S) Ruwan Raham

Abin yin alkawari ga duniya kuma alkibalar burin dukkan muslmi kuma abin so gun Shi'a wato; imam Mahadi (A.S) kodayaushe yana kula da halayen mutane ne, kuma boyuwar wannan ranar rahama da tausayi ba ya hana ta bayar da rayuwa da karfafa ga masoyanta ta bayan gajimare, kuma ba ya hana ta yi walimar garar baki ga masoyanta. Wannan wata ne shi mai soyayya da kauna mai dauke bakin cikin masu neman taimamkonsa dagamasoyansa, kuma shi ne mai warkar da ciwon masu miki da suka kwanta a gadajen asibiti da suka rasa magani, kuma wani lokaci yakan nuna wa wadanda suka bace hanya a daji. Shi ne mai lallashin zukatan masu sauraronsa, kuma mai ruwan rahamar Allah ga masoyansa. Duba ka ga abin da yake roka wa masoyansa wajen Allah madaukaki da fadinsa: ya kai wanda yake shi ne hasken haske, ya mai juya al'amura ya mai tayar da kaburbura, ka yi tsira da aminci ga Muhammad da alayen Muhammad ka sanya mini ni da shi'ata mafita daga wannan kunci, kuma da farin ciki daga bakin ciki, ka yalwata mana tafarki, ka kuma saukar mana abin da zai faranta mana, ka kuma yi mana abin da kake ahlinsa ne kai, ya mai baiwa.
Wadannan abubuwa da aka kawo suna nuna samuwar imami a fakuwa da buya, kuma wadanda suke samun haduwa da shi su ne wadanda suke da cancanta da samun dacewa ga hakan.

Bangare Na Hudu


Haduwa Da Masoyi

Shi'a sun fuskanci wahalhalu a rayuwa sakamakon nisanta da jagoransu imam Mahadi (A.S) kuma wannan al'amari ya sanya su cikin yanayi mai bakin ciki, koda yake a lokacin boyuwar imam Mahadi karama Shi'a sun kasance suna masu saduwa da shi ne ta hannun wakilansa na musamman, amma a boyuwarsa babba (mai tsayi) wannan alaka ta katse gaba daya.
Amma dai kodayake akwai malamai da dama da suka yi imani da haduwa da shi kuma wannan ya faru ga manyan malamai kamar Allama baharul ulum, Mukaddis Ardabili, Sayyid dan Dawus, da sauransu da suka shahara, da akwai kuma littattafai masu yawa da suka nakalto labarai game da haduwa da shi (A.S) [20].
Amma sai dai muna iya duba wasu muhimman bayanai game da haduwa da imam Mahadi (A.S) da suka hada da:
Na farko: Haduwa da imam Mahadi (A.S) wani lokaci yakan kasance a lokacin matsuwa da takan samu mutum ne, wani lokaci kuma a lokaci ne na al'ada ba tare da wani larura ba.
Akwai labaru masu yawa game da al'amarin da ya shafi damuwar masu mutane da suka bace hanya, kamar mutanen da zasu Makka ziyarar dakin Allah sai suka bace hanyarsu kuma imam (A.S) ko wani daga yaransa mabiyansa shi ne ya shiryar da su hanya ya fitar da su daga dimuwa, kuma yawancin haduwa da imam (A.S) ta irin wannan ne.
Amma game da haduwa da cewa a lokacin da ba na larura ba to wannan yana kasancewa ne yayin da shi mai haduwa da shi ya kasance mutum ne ma'abocin dukakaka da matsayi wajen Allah (S.W.T).
Bisa la'akari da abubuwan da muka kawo sama muna iya cewa:
Na daya: Duk wani wanda zai yi da'awar haduwa da imam (A.S) ba a yarda da maganarsa.
Na biyu: A wannan zamani namu an samu wasu mutane da suka yi da'awar haduwa da imam Mahadi (A.S) kuma suka kira mutane kan hakan wanda a sakamakon hakan sun batar da mutane masu yawa da kuma karkatar da akidun mutane da batar da su, kuma daga karshe za a samu cewa irin wadannan mutane sukan zo da wasu wurudodi su ba wa mutane wadanda ba su da wani armashi na gaskiya kuma sun saba wa abin da imamai (A.S) suka zo da shi.
Sannan kuma akan samu wasu suna ganin haduwa da imam Mahadi (A.S) abu ne mai sauki, alhalin wani abu ne wanda ko kokwanto babu a kan cewa; Ubangiji madaukaki ya sanya shi a cikin boyuwa cikakkiya gaba daya kuma idan ka cire mutane kalilan wadanda suka samu ludufin Allah babu wani wanda ya samu nasarar haduwa da shi kai tsaye.
Na uku: Haduwa da shi tana yiwuwa ne yayin da imam (A.S) ya ga akwai maslahar hakan, don haka ne duk sadda wani mai bege da kauna ya ga ya kasa samun haduwa da shi duk da kuwa ya yi kokari to kada ya yanke kauna daga samun ludufin Allah, kuma ya sani cewa wannan ba yana nufin cewa; shi ba ya cikin ludufin Allah ba ne, kuma ya sani haduwa da imam (A.S) ba ya nuna alamar kai wa matukar takawa da fifiko da kamala ba ne.
Duk da cewa ganin imami da magana da shi da kuma haduwa da shi sa'ace mai girma da rabauta mai daukaka, amma mu sani imamai musamman imam Mahadi (A.S) bai kwadaitar da mu ba wajen kokarin ganinsa kuma bai sanya mana ganin lallai sai mun kai ga ganinsa ba, sai dai akwai maganganu masu yawa daga imamai (A.S) da suka yi umarni da cewa a kodayaushe mu kasance cikin tunawa da shi kuma mu yi addu'a domin bayyanarsa, kuma mu yi aiki domin cimma hadafi mafi girma da dan Adam ya ke sauraro na bayyanarsa domin ya bayyana da gaggawa wannan duniya, kuma al'ummarta ta amfana daga gareshi kai tsaye.
Imam Mahadi (A.S) da kansa yana cewa: "Ku yawaita addu'ar bayyanata, ku sani wannan ne farin cikinku" [21].
A nan muna ganin ya dace mu kawo abin da ya faru na haduwarsa mai dadi tare da Alhaji Ali bagdadi wanda yake daga mutane na gari, domin takaitawa zamu takaita da wadannan bayanai masu muhimmanci:
Shi mutum ne mai takawa wanda kodayaushe yana zuwa bagadaza yana ziyartar kabairn Imam Musa Kazim da imam Jawad (A.S), yana cewa: akwia wasu kudin humusi a kain saboda haka sai na tafi Najaf da su, kuma na bayar da toman ishirin ga sheikh Ansari, ishirin ga sheikh Muhammad kazimi, ishiri kuma a Ayatullahi sheikh Muhammad Hasan sharuki, sai kuma na yi niyya cewa toman ishirin kuma idan na koma bagadaza zan ba wa Ayaltullahi aAali yasin.
Ranar alhamis sai na koma bagadaza da farko sai na je kazimain kuma na ziyarci imamai biyun, sannan sai na nufi gidan Ayatullahi aAali yasin na ba shi bangaren (wani kaso na) kudin da ya rage da suke a kaina, kuma na nemi izinin a wajensa cewa zan bayar da sauran a hankali, sai ya yarda, kuma ya dage in zauna wajensa, amma sai na bayar da uzuri na yi bankwana da shi na koma bagadaza.
Na cimma daya cikin uku na tafiyata sai na ga wani Sayyid (sharifi) da koren rawani, kuma a goshisa akwai wani bakin tabo bayyananne, kuma zai tafi kazimaini don ziyara. Sai ya yi kusa da ni ya yi mini sallama kuma ya rungume nei ya rabani da kirjinsa kuma ya yi maraba ya ce: ya yi kyau ina zaka tafi?
Sai na ce: na yi ziyara ne kuma yanzu zan tafi bagadaza ne. sai ya ce; daren juma'a ne ka koma kazimain ka tsaya a can! Sai na ce, ba zan iya ba. Sai ya ce: zaka iya koma domin in bayar da sheda cewa; kana daga masoya kakana imam Ali kuma kana daga masoyanmu, kuma shi ma sheikh ya bayar da sheda akan hakan. Ubangiji yana cewa: "ku sanya shedu biyu" [22].
Haji Ali ya ce: Ni da ma can na nema daga Ayatullahi Aali yasin ya rubuta mini sheda cewa ni ina daga cikin Shi'a kuma masoya Ahlul Baiti (A.S) domin in sanya ta a cikin likkafanina. Sai na tambayi wannan Sayyid din: yaya ka san ni? Sai ya ce: yaya kuwa wanda yake bayar da hakkinmu cikakke ba zamu san shi ba? Sai na ce: wane hakkin? Sai ya ce: hakkokin da ka ba wa wakilaina. Sai na ce: wane ne wailinka? Sai ya ce: sheikh Muhammad Hasan! Na ce: shin shi wakilinka ne? sai ya ce: na'am.
Daga manganar da ya yi sai na yi makaki mai tsanani, sannan sai na ga kamar dai akwai sanayya sabuwa da ni da shi ne wacce na manta, saoba da farko ya kira ni da sunana, sai na yi zaton akwai wani hakki na zuriyar manzon Allah ne da yake son in ba shi saboda yana cikinsu ne. sai na ce: haka ne akwai hakkokinku 'ya'yan manzon Allah amma na karbi damar sarrafa shi. Sai ya yi murmushi ya ce; haka ne akwai wani hakkinmu da ka ba wa wakilanmu a Najaf. Sai na tambaya shin aikina kuwa yardajje ne a wurin Allah? Sai ya ce: haka ne.
A zuciyata na ce: yaya wannan Sayyid yake cewa game da malaman zamanin nan a matsayin wakilansa? Amma dai sai na gafala, na manta da wannan al'amarin.
Sai na ce: shugabana shin da gaske ne da ake cewa kowane dare na juma'a idan muutm ya ziyarci imam husai (A.S) zai dawwama cikin aminci. sai ya ce: haka ne! sai a lokacin na ga hawaye sun cika masa idanuwa, babu wata jimawa sai na ganmu a haramin kazimain (A.S) ba tare da wuce hanyoyi ba, sai ga mu a harami.
Sai muka tsaya a gefen hanyar shiga. Sai ya ce: karanta ziyara! Sai na ce: shugabana ban iya ba. Sai ya ce: idan na karanta kai ma zaka karanta? Sai na ce: na'am!
Sai ya fara kuma ya yi sallama ga manzon Allah da imamai daya bayan daya, sannan bayan ambaton sunan imam Askari (A.S) sai ya fuskanto ni ya ce: ka san imaminka? Sai na ce: yaya kuwa ba zan san shi ba? Sai ya ce: to ka isar masa da sallamarka. Sai na ce: Assalamu alaika ya hujjatul lahi! ya sahibaz zaman! yab nal Hasan! Sai ya yi murmushi ya ce: Alaikas salam warahmatullahi wa barakatuhu.
Sai na shiga harami na sumbanci kabari, sai ya ce: Karanta ziyara. Sai na ce: ba zan iya ba shugabana. Sai ya ce; in karanta maka? sai na ce: na'am! Sai ya karanta ziyarar nan mash'huriya ta "Aminullah" sannan sai ya ce: shin zaka ziyarci kakana imam Husain (A.S)? sai na ce: haka ne, yau daren juma'a ne kuma daren ziyarar imam Husain ne. sai ya karanta ziyarar nan mash'huriya ta imam Husain (A.S). yayin sallar magariba sai ya ce: ka yi sallar jam'i. Bayan salla sai ya bace min daga ganina, kuma duk yadda na yi bincike ban iya gano shi ba.
Sai a lokacin na fahimci cewa na tuna wannan sayyid da ya kira sunana, kuma ya nemi in koma kazimain duk da ba na son komawa. Kuma ya ce damanyan malaman zamaninsa wakilansa ne, daga karshe kuma ya bace bagatatan, sai tunani ya zo mini cewa wannan shi ne imam Mahadi (A.S). Kaicona da sai tun daga baya na gane shi ne [23]!

Bangare Na Biyar

Tsawon Rayuwa
Daga cikin bahasosin da ake yi da suka shafi rayuwar imam Mahadi (A.S) akwai tsawon rayuwarsa, saboda haka ne ma wasu suke tambayar cewa yaya za a yi mutum ya yi wannan rayuwa mai tsawo [24]?!
Wannan tambaya ta taso ne sakamakon a yau ana ganin rayuwar mutane tana da iyaka daga 80 zuwa 100 ne [25], wasu suna ganin da wannan yanayi ba mai yiwuwa ba ne mutum ya rayu rayuwa mi tsawo hakan, ko kuma abu ne mai wahala.
Amma a hankalce da kuma ilimin dan Adam sun nuna cewa zai yiwu mutum ya rayu rayuwa mai tsayi kuma ba tare da koda tsufa ba.
Barnard show yana cewa: yana daga asasin ilimi gun malaman bayaloji cewa; ba yadda za a iya sanya iyaka ga rayuwar dan Adam, kuma hatta da mas'alar jinkirin rayuwa (dadewa a duniya) abu ne wanda ba shi da iyaka" [26].
Profesa Atingar yana rubutawa yana cewa: "a ganina ci gaban takanoloji da kuma ayyukan da muka fara a yau mutumin karni na ishirin da daya zai iya rayuwa tsawon dubunnan shekaru [27].
Saboda haka ne, sai masu ilimi suka yi kokairn gano hanyoyin da za a iya maganin tsufa da kuma kai wa gashekaru masu yawa, wannan kuwayana nuna yiwuwar wannan al'amari da kuma yin wani taki domin cimma wannan al'amari. Kuma har yanzu a duniya akwai mutane masu yawa da sakamkon wani yanayi na musamman da nau'in abinci da kuma ayyuka da suka dace da jiki da tunani da wasu ayyukan daban dasakamakon hakan sukan yi shekaru samada dari da hamsin kosama da hakan, mafi hummimmanci ma shi ne an jarraba wannan a tsawon tarihin dan Adam kuma akwai wannan a littattafai saukakku, cewa wasu mutanen sun yi shekaru masu yawa da tsawo fiye da rayuwar mutane a yau.
A kan haka ne ma akwai makaloli masu yawa da aka rubuta da zamu yi bayanin wasu daga ciki a matsayin misali:

1-Akwai aya a Kur'ani mai girma da ba kawai tana maganar tsawon rayuwa ba ne, har ma tana bayar da labarin yiwuwar mutum ya dawwama ne, wannan aya game da Yunus (A.S) tana cewa: "ba don ya yi tasbihi a cikin kifi ba, to da ya zauna a cikinsa har ranar da za a tashi kiyama" [28].
Don haka wannan aya ta Kur'ani mai girma tana nauna yiwuwar rayuwa tun daga lokacin annabi Yunus (A.S) har zuwa ranar kiyama wanda a ilimin rayuwa ake kira rayuwa madawwamiya [29].

2-Kur'ani game da annabi Nuhu (A.S) yana cewa: mu mun aika Nuhu (A.S) zuwa ga mutanesa sai ya zauna a cikinsu shekaru dubu ba hamsin [30].
Abin da muka iya gani a wannan aya shi ne tsawon shekarun annabta na annabi Nuhu (A.S) wanda wasu ruwayoyi sun kawo tsawon rayuwar sa gaba daya da cewa ta kai 2450 [31].
Abin kayatarwa an karbo daga ruwayar imam Sajjad yana cewa: imam Mahadi (A.S) yana da sunnar annabi Nuhu (A.S) ta tsawon shekaru [32].

3-Haka nan game da annabi Isa (A.S) yana cewa: Sam ba su kashe shi kuma ba su tsire shi ba, sai dai an rikitar musu ne a al'amuransu… ba su kashe shi ba bisa yakini, sai dai Allah ya daga shi zuwa gareshi ne…" [33].
Kuma bisa dogaro da wannan ne dukkan musulmi suka yi imani da cewa annabi Isa (A.S) a raye yake a sama, kuma a lokacin bayyanar imam Mahadi (A.S) zai zo domin taimaka masa.
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: "Imam Mahadi (A.S) yana da sunnoni biyar daga sunnonin annabawa (A.S)… da sunna daga Isa (A.S), wannan kuwa fadinsu cewa ya mutu, alhalin yana raye [34].
Bayan Kur'ani zamu ga Attaura da Injila su ma sun yi bayani game da mutane masu tsawon rayuwa.
Ya zo a cikin Attaura: "…ranakon da "Adam" (A.S) ya yi ya mutu su ne dari tara da talatin da uku… kuma dukkan rayuwar "kainan" shekaru dari tara da goma ne yayin da ya mutu… haka ma "Mutushalih" ya rayu dari tara da sittin da tara ne sannan sai ya mutu [35].
Saboda haka Attaura a fili tana bayanin samuwar wasu mutane masu shekaru sama da dari tara.
A cikin Injila ma akwai maganganu da suka zo da suke nuna isa ya rayu bayan kashe shi da tsire shi, kuma ya tashi sama [36]. Idan muka duba tun ranar da ya tashi sama harzuwa yau rayuwarsa tawuce shekaru dubu biyu.
Da wannan bayanin zamu gani a fili yake cewa masu bin addinin yahudanci da kiristanci bisa dogaro da littafi mai tsarki to dole ne su yarda kuma su yi imani da tsawaitar rayuwa.
Bayan haka, ta magangar ilimi da hankali wani abu ne karbabe kuma ya wuce a tarihi kuma ya wakana. Wannan kuwa idan muka duba ikon Allah da karfinsa maras iyaka to duk yana iya tabbatuwa.
Haka nan akidar ma'abota addinai saukakku dukkan kwayoyin zarra na duniya suna karkashin ikon Allah ne, kuma tasirinsu da su da sabubansu duk suna da alaka da shi ne kuma duk daga gareshi ne, shi ne ya samar da komai da sabubansu, Shi Ubangiji ne mai ikon fitar da rakumi daga cikin dutse kuma ya sanya wuta ta zamanto mai sanyi ga Ibrahim (A.S) kuma ya busar da kogi ga Musa (A.S) da mabiyansa, kuma ya sanya su tsallake tsakanin katangu biyu koraye [37]. Shin duk wanda ya yi wannan ga annabawa da waliyyansa sai ya kasance ya kasa tsawaita rayuwar karshen ajiyar Allah a bayan kasa wanda dukkan burace-buracen 'yan Adam ya dogara kan samuwarsa da zuwansa?!
Imam Hasan (A.S) yana cewa: Ubangiji zai tsawaita boyuwar imam Mahadi babba, sannan sai da ikonsa ya bayyanar da shi a cikin surar saurayi dan kasa da shekaru arba'in, domin mutane su sani cewa Allah mai iko ne a kan komai [38].
Saboda haka maganar tsawaituwar rayuwar imami na goma sha biyu (A.S) al'amari ne mai yiwuwa ta fuskancin hankali da ilimi da tarihi, kuma abu ne karbabbe, kuma fiye da haka ma akwai nuna nufin Allah da girmansa a ciki.

Hakikanin Ma'anar Sauraro

An fadi ma'anoni masu yawa game da sauraro, amma mu zamu yi bayani game da ma'anar da ta dace da wannan kalmar. Sauraro ba wani abu ne da ya takaita da badini ba kawai, abu ne wanda ya hada zahiri da badini duka, kuma ya sanya motsawa domin taka wani mataki.
A sakamamkon haka ne muka samu a ruwayoyi an fassara sauraro da cewa shi wani aiki ne, kai shi ne ma mafificin ayyuka. Kuma yana bayar da wata ma'ana ta musamman domin samar da wasu ayyuka, kuma yana bude hanyar da zata kai ga tabbatar zuwa ga wanda ake sauraro.
Saboda haka, sauraro ba ya nufin zama domin jira da kuma kame hannaye, don haka a cikin sauraro akwai motsi da kuma kai wag a wasu matakai a dunkule.
Mai sauraron bakonsa ya zo ba yana zama ba ne ba tare da ya aiwatar da komai ba, maimakon haka yana kokarin gyara wuri ne da kuma gyara kansa da kuma kawar da duk wani abu da zai hana bakonsa zuwa.
Magana game da sauraro tana da al'amura kuncshi da ita na kyawu da kamala wadanda ba su da iyaka. Wannan sauraron an ambace shi da zuwan farin ciki a ruwayoyi masu yawa kuma an siffanta shi da mafificin ayyuka da ibadoji, kuma shi ne asasin karbar dukkan ayyuka ma.
Manzon rahama (S.A.W) yancewa: "mafifinci ayyukan al'ummata, shi ne sauraron farin ciki (bayyanar imam Mahadi) [39].
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa da sahabbansa: shin ba na gaya muku abin da Ubangiji ba ya karbar wani aiki sai da shi ba? Suka ce: gaya mana. Sai ya ce: shaidawa da Ubangiji daya da annabtar annabi (S.A.W) da kuma furci da wilayarmu da kuma nisantar makiyanmu, da mika wuya garesu, dakuam nisantar abin hani da kokari da kame kai, da kuma sauraron bayyanar imam Mahadi (A.S) [40].
Don haka sauraro yana da siffofi na musamman da suka kibanta da shi wadanda wajibi ne a san su, domin a san sirrin hakan.

Abubuwa Kibantattu Ga Sauraron Imam Mahadi (A.S)

Mun san cewa sauraro wani abu ne na fidirar halittar mutum kuma kowane mutum ko addini suna da abin da suke sauraro a rayuwarsu ta daidaiku ko kuma ta al'umma. kuma idan mun kwatanta su da irin sauraron wanda aka yi alkawarin zuwansa, to zamu samu cewa su wadannan irin sauraro ba kaomai ba ne, domin sauraronsa yana da siffofi da suka kebance shi na musamman:
Sauraron imam Mahadi (A.S) ya fara tun daga farkon samuwar duniya ne kuma da yawa daga annabawan Allah da waliyansa sun yi fatan bayyanarsa, a mafi kusancin zamuna muna iya ganin hakan daga imamai (A.S) da suka yi fatan zuwan daularsa.
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: "Da zan riske shi da na yi masa hidima gaba dayan shekaruna" [41].
Sauraron Mahadi (A.S) sauraro ne na mai gyaran duniya gaba daya kuma sauraron hukumar adalci ta duniya ne kuma sauraron tabbatar dukkan kyawawa da alherai. Al'umma zata fuskanci hanyar gaskiya domin tabbatar abin da Allah ya halicci fidira mai tsarki a kansa ta dan Adam da kuma samuwar abin da yake buri ne cikakke da har yanzu duniya ta kasa samun irinsa.
Mahadi (A.S) yana nufin adalci da sanin da kyawawa, da 'yan'uwantaka da daidaito, da raya kasa da aminci da zaman lafiya da sulhu, kuma lokacin cikar hankula da ilimin dan Adam ga dan Adam, da kuma kawar da duk wani mulkin danniya da bautar da dan Adam da kore duk wani zalunci da azzalumi da kuma 'yancin al'umma da kubutarsu daga dukkan fandarewar dabi'u da kuma kawo hukumarsa.
Sauraron imam Mahadi (A.S) sauraro ne da zai kasance bayan an tanadi zamanin cigaba, kuma wannan zamani ne da dukkan mutane suke neman mai ceto wanda zai kawo gyara ga duniya, shi zai zo domin ya motsa da taimakon mabiyansa domin ya samar da mu'ujizar duniya.
Sauranron imam Mahadi (A.S) yana tare da bege da hadin gwiwa, kuma yana ba wa mutum rayuwa, kuma ya tseratar da shi daga rashin hadafi.
Wannan abubuwan da muka kawo wani bangare ne na sauraro wanda yake da fadi a cikin tarihin dan Adam kuma yake da asalin samuwa ga dukkanin mutane, kuma babu wani sauraro da yake iya kamo kafarsa, don haka ya kamata mu san ayyukan masu sauraron bayyanarsa kuma mu san ladansu maras misali.

Abubuwan Da Suke Damfare Da Sauraro

Mutum yana da bangarori mabambanta: ta wani bangare yana da bangaren nazari da kuma na aiki, ta wani bangaren kuma yana da abin da ya shafi daidaiku da kuma al'umma, ta wani bangare kuma yana da abin da ya shafi jiki da Ruhi.
Ba kokwanto kowane janibi yana bukatar bude masa hanya sahihiya da ta kamata ya bi, kuma a toshe masahanyar karkacewa, wannan hanyar da ya bukatakuwa ita ce ta sauraro.
Sauraron mai gyara yana yin tasiri a cikin dukkan bangarorin rayuwa, kuma a bangaren tunani da nazari yana karkashin aiki da dabi'ar mutum ne, kuma a cikin wannan ne za a iya kiyaye akidar mutum. Kuma ya karfafa imaninsa da tunaninsa domin kada ya fada hanyoyin bata sakamakon tsawaitar boyuwar imamin wannan zamani imam Mahadi (A.S).
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: "akwai ranar da zata zo ga mutane da imaminsu zai boyu, farin ciki ya tabbata ga masu tabbata a kan al'amarin wilayarmu a wannan zamani [42].
Wato boyuwrsa zata yi tsayi kuma za a cika ta da nau'o'in shubuhohi masu yawa domin su kawar da akidu sahihai na Shi'ar imam Mahadi na sauraronsa (A.S).
Ta fuskancin ayyuka kuwa dole ne dukkan ayyukan masu sauraro da halayen mutane bisa kokarin a ganin samuwar daular gaskiya, don haka ne masu saurare dole ne su gina kansu a wannan janibai.
Kuma su yi kokari ta fuskancin daidaiku su gina kansu da ruhinsu bisa kyawawan halaye da gaskiya, kuma su karfafi jikinsu ta hanyar samar da lafiya domin karfin da suke da shi a yi amfani da shi ta hanyar haske.
Imaa Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: "…duk wanda yake son ya kasance cikin masu taimakon imam Mahadi (A.S) to ya saurare shi, kuma ya kasance mai takawa cikin lokacin saurare kuma ya yi ado da kyawawan halaye [43].
Sauraro ba kawai yana gina mutum ba ne a matsayinsa na mutum daya, yana gina al'umma ne gaba daya kai tsaye, domin sauraron imam Mahadi (A.S) na al'umma ne gaba daya kuma bayyanar daularsa yana bukatar shiri ne na al'umma mai hadin kai. kuma kowane mutum dole ne ya yi aiki iya kokarinsa odmin gyara al'umma da shiga tsakanin al'umma da mugwayen al'adu da fasadi, domin mai sauraron mai gyara yana bin hanar gyara ne.
Sauraro abu ne mai albarka da yake gudana a dukkan bangarorin rayuwa, kuma yana ba ta siffa na gari a dukkan rayuwar mutane.
Kur'ani mai girma yana cewa: "… Rinin Allah, wane ne ya fi Allah kyautata rini…" [44].
Idan muka duba abubwan da suka gabata zamu ga cewa sauraron mai gyara ba wani abu ba ne sai siffantuwa da rinin Allah da kuma mamayewar albarka a cikin rayuwar daidaikun mutane da kuma na al'umma gaba daya. Don haka ne ayyukan mu masu sauraro ba zasu bayar da wata ma'anta ta ayyukan wahala ba, sai dai zata ma samar da wata ma'ana ne da take nufin ayyukanmu ado ne mai kayatarwa.

Ayyukan Masu Sauraro

Ya zo a ruwayoyi masu yawa da aka yi bayani game da ayyukan masu sauraron bayyanar farin ciki, wanda mu a nan zamu kawo mafi muhimmancinsu.

Sanin Imam Mahadi (A.S)

Bin hanyar sauraro ba tare da sanin imanin da ake sauraro ba abu ne wanda ba zai yiwu ba, kuma tabbata a kan sauraron yana da alaka da sani ko fahimta ta gari game da wannan shugaba da aka yi alkawarin zuwansa, don haka muna ganin bayan sanin imami da sunansa, da nasabarsa haka nan kuma a san matsayinsa da darajarsa.
Abu nasar wanda yake daga masu hidima ga imam Hasan Askari (A.S) yana daga masu halarta wurin imam Mahadi (A.S) kafin boyuwarsa. Sai imam Mahadi (A.S) ya tambaye shi shin kasan imaminka kuwa?
Sai ya bayar da amsa; na'am, kai shugabana ne kuma dan shugabana! Sai imam Mahadi (A.S) ya ce: ba irin wannan sanin nake nufi ba, sai Abu nasar ya ce: ina ganin sai ka fada min nufinka. Sai imam Mahadi (A.S) ya ce: Ni ne karshen halifan manzon Allah (S.A.W) kuma da albarkacina ne Ubangiji yake kawar da bala'i daga iyalai da kuma shi'ata [45].
Idan sanin imami ya samu ga masu sauraro, to a wannan yanayi ne mai sauraro zai iya ganin kansa cikin masu tsayuwa tare da imam (A.S) a hemarsa. Don haka sai ya shirya kansa domin tsayawa tare da imam (A.S) a fage daya.
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: … wanda ya mutu yana sanin imaminsa ba abin da zai cutar da shi, wannan al'amarin (bayyanar ta imam) ya dade ko ya yi saurin zuwa, wanda ya mutu yana sane da imaminsa ya kasance kamar wanda yake tare da imam (A.S) ne a dardumarsa [46].
Muna iya cewa wannan sanin wani abu ne wanda yake muhimmi da ya zo a maganganun ma'asumai (A.S) kuma wani abu ne dole da ake nemansa ga mataimakan imam (A.S).
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: ….A zamanin boyuwa mai tsawo ta imam Mahadi (A.S) masu baran zasu kasance cikin kokwanto. Sai Zurara ya ce: Idan na ga wannan zamanin mene ne zan yi?
Sai ya ce: ka karanta wannan addu'ar: ya Ubangiji ka sanar da ni kanka domin idan ba ka sanar da ni kanka ba to ba zan san annabinka ba, ya Ubangiji ka sanar da ni manzonka domin idan ba ka sanar da ni manzonka ka ba to ba zan san hujjarka ba, ya Ubangiji ka sanar da hujjarka (imami) idan ba ka sanar da ni hujjarka ba to zan bace daga addinina [47].
Abin da har yanzu ba a kawo ba shi ne matsayin imam a tsarin halittar talikai [48]. Shi hujjar Allah ne kuma mai tsayawa matsayin annabi kuma mai jagorantar dukkan mutane wanda biyayya gareshi wajibi ce, domin biyayyarsa ita ce biyayya ga Allah madaukaki.
Daya daga cikin abubuwan da suka shafi sanin imami shi ne sanin halayensa da siffofinsa [49] kuma wannan yana da tasiri wajen ayyukanmu da halayenmu da dabi'unmu, kuma a fili yake cewa daidai sanin mutum ga rayuwar imami wanda yake hujjar Allah a bayan kasa, to daidai irin tasirin da zata yi a rayuwarsa sosai.

Karbar Abin Koyi

A lokacin da sanin imami (A.S) ya samu to a wannan lokacin za a yi bayanin abin koyi wanda yake shi ne mahallin bayyanar kamalar Ubangiji madaukaki.
Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: farin ciki ya tababata ga wanda ya riski imam Mahadi (A.S) kuma ya yi imani da imamai da suka gabace shi kuma ya yi koyi da su kuma ya ki makiyansu, wadannan su ne mafi soyuwar mutane mafi daraja a wajena [50].
Da gaske ne cewa dukkan wanda ya yi takawa daibada da rayuwa mai sauki da baiwa da hakuri da kuma dukkkan halaye na kaywwan dabi'u, ya bi hanyar imam (A.S) to lallai ne zai samu daukaka wajen Allah.
Mu sani cewa ayyukan munanan su ne suke nisantar da mu daga sauraron farin ciki (bayyanar imam Mahadi) kuma suke jinkirta karbarmu wajen imami (A.S) da kuma bayyanarsa, a cikin wannan akwai gargadi daga imam Mahadi (A.S) da yake cewa: ba abin da yake tsare mu daga garesu sai abin da yake zo mana na munanan ayyukansu, ayyukan da ba sa faranta mana rai, kuma ba su dace da shi'armu ba [51].
Babbn burin masu sauraron daular imam Mahadi a sshi ne su kai ga kasancewa tare da hujjar Allah amma su sani wannan al'amari ba ya samuwa sai da gina kai da gaskiya da kaywwan halaye.
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa; "wanda yake son ya kasance daga sahabban imam Mahadi (A.S) to ya saurare shi, kuma ya yi aiki da tsentseni da kyawawan halaye yana kuma mai sauraron [52].
A fili yake cewa a hanyar saurare babu wani abin koyi da ya kai imami (A.S).

Tunawa Da Imam (A.S)

Abin da yake kan masu sauraro bayan sanin imami da kuma biyayya gareshi da kuma tabbata kan sauraro, shi ne kodayaushe su kasance cikin masu alaka da imami (A.S).
Bisa hakika imam (A.S) a kodayaushe yana tunawa da mabiyansa kuma bai taba manta da su ba koda kuwa kiftawr ido, kuma soyayyarsa garemu ta sanya shi da kansa yana addu'a kuma ya yi umarni da yin addu'a da cewa: "ku yi addu'a sosai domin gaggauta bayyanar farin ciki" [53]. kuma saudaywa gaba daya mukan yi addu'a: ya Ubangiji ka kasance ga masoyinka hujja dan Hasan, tsira da amincinka su tabbata gareshi da iyayensa a wannan lokaci da kuma kowane lokaci, mai jibantar lamarinsa, kuma mai kiyayewa, kuma jagora kuma mai taimako, kuma mai shiryarwa kuma mai kulawa, har sai ka zaunar da shi (mai matsayi) a kasarka, kuma ka jiyar da shi dadi mai tsawo a cikinta [54].
Mai sauraro na hakika duk lokacin da zai bayar da sadaka to yakan fara tunawa ne da amincin samuwar imami madaukakiya, kuma shi mai yin tawassuli ne da shi a kowane hali, kuma mai begen ganin bayyanrsa da duba zuwa ga kyawonsa maras misali.
Yana yin tsanani gareni in ga halitta kai kuma ba a ganinka [55].
Mai sauraron imam Mahadi (A.S) kowane lokaci kuma kowace rana yana kai kawo ne a wurare kamar masallacin Sahala da Sardab da sauransu.
Masu sauraronsa kullum suna jaddada masa bai'a ne kuma suna daukar masa alkawari. Suna masu karanta addu'a suna masu fada: ya Ubangiji ni ina jaddada masa bai'a da alkawari a kan wuyana a wannan safiya ta ranata wannan matukukar ina raye, kuma ba zan juya gabarinta ba kuma ba zan gushe ba har abada, ya Ubangiji ka sanya ni cikin mataimakansa masu kare shi, masu gaggawa zuwa gareshi don biyan bukatarsa, kuma masu bin umarninsa masu kariya gareshi kuma masu rige zuwa ga nufinsa masu shahada a gabansa [56].
Idan da mun fahimci hakikanin abin da k cikin wannan addu'a ba zamu taba samun rauni ba wajen tabbatare da burinmu kuma ba zamu taba ja baya ba wajen ganin mun saurari zuwansa ba.
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: "duk wanda ya karanta wannan addu'a kwana arba'in a jeri to zai tashi cikin mataimakan imam Mahadi (A.S), idan ma ya mutu to Allah zai tashe shi daga kabarinsa ya taimaki imam Mahadi (A.S).

Hadin Kan Al'umma

Daga cikin ayyukan da suka hau kan masu sauraronsa shi ne hada hannu waje daya domin ganin an samu nasarar abin da yake shi ne hadafi na hujjar Allah.
Don haka ne dole ne a samu al'umma mai haduwa wuri daya domin samun kafuwar daular imam Mahadi (A.S).
Imam Mahadi (A.S) a cikin bayanansa yana cewa: idan shi'armu suka cika alkawarin da suka dauka, kuma suka yi niyya kan hakan to ni'imar haduwa da mu ba zata yi jinkiri garesu ba, kuma za a gaggauta musu dacewar haduwa da mu da saninmu cikakke na hakika [57].
Alkawarin ya zo a cikin littafin Allah da kuma maganar imamai masu tsarki da zamu yi nuni da mafi muhimmancinsu:
1-Kokarin biyayya ga imamai (A.S) da kuma son masoyansu da kuma nisantar makiyansu: imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: farin ciki ya tabbata ga wadanda suka riski imam Mahadi (A.S), a lokacin kafin bayyanarsa suka yi bayayya gareshi kuma suka so masoyansa kuma suka ki makiynasa, wadannan su ne abokaina a aljanna kuma abin so ne kuma masu daraja al'ummata, a ranar kiyama [58].
2-su masu tsayuwa ne kan kyawawan halaye kuma masu tsaya wajen yakar bidi'o'i da karkacewa a addini da kuma hana yada mummuna:
Manzon rahama (S.A.W) yana cewa: a karshen zamani za a samu wasu mutane daga al'ummata ladansu kamar ladan al'ummar musulumi ta farko ne, suna umarni da kyakkyawa suna hani ga mummuna kuma suna yakar ma'abota fitina [59].
3-su masu taimakon raunana ne kuma masu bin halayensu da taimaka musu. Wasu jama'a daga Shi'a sun nemi imam Muhammad Bakir (A.S) ya yi musu nasiha sai ya ce: duk wanda yake mai karfi a cikinku to ya taimaki mai rauni, kuma maras bukata ya taimaki mabukaci, kuma kowannenku ya yi wa waninsa aikin alheri [60].
4- Yada sanin imam a cikin al'umma, kuma da nuna halaye na imam da koyarwarsa cikin al'umma.
Daya daga cikin sahabban imam Muhammad Bakir (A.S) Abdul hamid wasidi yana cewa: a sauraron al'amarin farin ciki da bayyanar imam mu mun yi wakafin rayuwarmu ta yadda matsaloli zasu kasance tare da mu.
Sai imam (A.S) ya ce: Kai Abdul hamid shin kana tsammanin cewa Ubangiji bai sanya wa wanda ya yi wakafin rayuwarsa hanyar warware matsaloli ba, na rantse da Allah ya sanya masa hanyar mafita, kuma Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al'amarinmu [61].
Wannan yana nuna mana cewa masu sauraron imam Mahadi (A.S) dole ne su kansace wani bangare na al'ummarsu.

Alamomin Sauraro

Wasu mutane sun dauka cewa sauraro yana nufin zura ido a ga masu barna da fasadi suna yada barna ba tare da an yi umarni ko hani ga mummuna ba, amma a bisa abubuwan da suka gabatawannan yana nuna mana sabanin abin da wadannan suke gani.
Sauraron imam Mahadi na hakika shi ne yake kunshe cikin motsi domin kawo gyara, domin duk sadda gyara ya karu to wannan yana nufin kusantowar wanda ake sauraro domin samun alamar karbar gyara a cikin al'umma. Don haka ne massu sarauro sukan yi kokarin da zasu iya ne domin ganin an samu gyara da kafuwar gaskiya. Duk sadda aka samu yanayi wanda yake dauke da karbar gyara to a irin wannan al'umma ne za a iya samun rayuwa ta nishadin karbuwar gyarawa.
Kuma a nan ne za a samu damar habakar imani da karfafarsa da kuma kafuwar mahangar mahadiyyanci mai karfi mai cike da albarkar sauraro.
Kuma masu sauraro ba sa yarda su narke cikin fasadin da ya babaye al'umma, kai suna kokari ne ma na ganin sun kawar da wanda yake kewaye da al'ummu ne, suna masu jurewa domin yin shimfida ta tabbatar daular adalci ta imam Mahadi (A.S).

Ladan Sauraro

Farin ciki ya tabbata ga wanda ya tsaya a kan tafarkin kyautatawa da aiki mai girma na sauraron farin ciki da bayyanar imam (A.S) wanda aka yi alkawarin zuwansa a wata rana, kuma lallai wannan wani aiki ne na lada mai girma da daraja madauakakiya da matsayi na masu sauraro na hakika ga imam Mahadi (A.S).
Daga cikin misalan darajoji da lada na masu wannan aiki imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: farin ciki ya tabbata ga shir'ar imam Mahadi (A.S) wadanda suke sauraron bayyanarsa a lokacin boyuwarsa, kuma suke bin umarninsa yayin bayyanarsa, wadannan su ne masoya Allah da ba su da wani tsoro ko bakin ciki da zai same su [62].
Wace irin daraja ce da matsayi mai girma da suka kai matsayi da rarajar a sanya mutum cikin masoyan Allah (S.W.T).
Imam Sajjad (A.S) yana cewa: wanda duk ya tabbata kan wilayarmu a lokacin boyuwar imam (A.S) to Ubangiji zai ba shi ladan shahidai dubu na yakin badar da uhud [63].
Wannan yana nuna cewa masu sauraro a wannan lokaci kamar masu yaki ne da takubba a cikin rundunar manzon Allah (S.A.W) wadanda suka cakuda jikinsu da jinin shahada.
Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: Idan wani daga cikinku (Shi'a) ya mutu a halin sauraron bayyanar imam Mahadi s to kamrwanda yake gefen imam Mahadi (A.S) ne a hemarsa! Sannan sai ya saurara kadan ya ce: kai yana kamar wanda ya yi yaki tare da imam Mahadi (A.S) ne. sannan sai ya saurara ya kuma ce: kai yana kamar wanda ya yi yaki tare da manzon Allah (S.A.W) ne kuma ya yi shahada [64].
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: wata rana manzon Allah (S.A.W) a cikin sahabbansa ya ce: Allah ya nuna mini 'yan'uwana! Kuma ya fada sau biyu, sai shabbansa suka ce: ya ma'aikin Allah shin mu ba 'yan'uwanka ba ne?
Sai ya ce: Haka ne, ku sahabbaina ne, amma 'yan'uwana mutane ne da zasu zo a karshen zamani su yi imani da ni kuma alhalin ba su gan ni ba! Ubangiji ya nuna mini su da iyayensu kuma ya sanar dani su… tabbatarsu a kan addininsu ya fi zafin zage kayar karangiya, kuma ya fi zafin zama kan garwashin wuta.
Wadannan su ne hasken shiriya da Ubangiji ya tseratar da su daga fitinoni masu duhu [65].
Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: farin ciki ya tabbata ga wanda ya riski imam Mahadi (A.S) kuma ya yi koyi da shi kafin bayyanarsa, kuma ya so masoyansa kuma ya ki makiyansa, kuma ya yi imani da imaman da suka gabace shi, wadannan su ne abokaina masoyana a cikin aljanna, kuma su ne mafi daraja a guna [66].
Duba ka ga irin matsayi mai girma da suka samu wajen manzon Allah (S.A.W), kuma suka samu sunan masoya abokai daga baki mai tsarki na madaukaki (S.A.W).
Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: wata rana zata zo wa mutane da imaminsu zai boyu, farin ciki ya tabbata ga masu dagewa a kan soyayyarmu a wannan rana.
Kuma mafi karancin ladan wadannan mutane shi ne; Ubangiji zai yi kira wannan rana ya ce: ya ku bayina, kun yi imani da gaibi (imam Mahadi) ne kuma kun gaskata shi?! to ku yi murna da ladana mai yawa, lallai ku bayina ne, ayyukanku na karbe su, kuma na yafe kurakuranku, saboda ku ne nake saurakar da rana kan bayina, kuma nake kawar musu da bala'i, idan da babu ku a cikin mutane da azabata ta sauka kansu [67].
Mene ne ya fi wannan girma da kyawu da daraja gun masoya imam Mahadi (A.S) masu sauraronsa! lallai wannan al'amari nasu ya girmama kuma ya daukaka.
Imam Musa Kazim (A.S) yana cewa: Farin ciki ya tabbata ga shi'armu, su ne masu dagewa kan soyayyarmu a lokacin boyuwar imam Mahadi (A.S), kuma masu juriya kyam a kan cutarwar makiyanmu, wadannan su ne daga garemu kuma mu ma daga garesu. Su sun yarda da biyayyarmu, mu ma mun yarda da su a matsayin shi'armu, farin cikinsu ya tabbata!! Na rantse da Allah zasu kasance a matsayi da daraja irin tamu a ranar lahira [68].

Daga LIttafin: Imam Mahadi Adon Halitta
Mawallafa: Muhammad Mahadi Ha’iri Fuur-Mahadi Yusufiyan-Muhammad Amin Bolo Dastyan. Mafassari: Hafiz Muhammad Sa'id


1. Gaiba na Nu’umani, babi 10, h 3, sh 146.
2. Biharul anwar: j 25, babi 23, sh 152.
3. Kamalauddin, j 1, babin farko zuwa na bakwai, sh 254 – 300.
4. Biharul anwar, j 52, h 3, sh 90.
5. Kamaluddini, j 1, b 25, sh 536.
6. Abin da ya gabata: j 2, babi 44, h 11, shafi: 204.
7. Ilaluls shara'I'I, shafi 244, babi 179.
8. Kamaluddin, j 2, babi 44, h 4, shafi: 232.
9. Gaiba, Dusi, fasali 5, h 284, shafi: 237.
10. Kamaluddin, j 2, babi 44, h 7, shafi: 233.
11. Akwai misalign irin wannan sa hannun ya zo a littafin biharul anwar: j 53, babi 31, shafi: 151 – 197.
12. Gaiba, Dusi, fasali 6, h 319, shafi: 357.
13. Gaiba, Dusi, fasali 6, h 317, shafi: 355.
14. Gaiba, Dusi, fasali 6, h 365, shafi: 395.
15. Kamaluddin, j 2, babi 45, h 3, s:236.
16. Ihtijaj, j 1, h 11, s: 15.
17. Ihtijaj, j 2, s: 115.
18. Biharul anwar: j52, shafi 178.
19. Tauba: 105.
20. Jannatul ma'awa, da najamus sakib: muhaddis nuri.
21. Kamaluddin, j 2, babi 45, h 4, shafi: 239.
22. Bakara: 282.
23. Biharul Anwar, j 53, shafi: 315. Da kuma Najmus Sakib, Kissa: 31.
24. A yanzu yana da shekaru: 1170 kenan.
25. Ana samun sama da dari ma.
26. Raze tule umre imam zaman (A.S), Ali akbar Mahadi pur, shafi: 13.
27. Majalleye danishmand, shekara: 6, lamba 6, shafi: 147.
28. Saffat, aya: 144.
29. An gano kifi a gefen madagaskar wanda ya yi shekaru miliyan 400, kaihan: lambata: 6413 – 1343/8/22
30. Ankabut, aya: 14.
31. Kamaluddin, j 2, babi 46, h 3, shafi: 309.
32. Kamaluddin, j 1, babi 21, h 4, shafi: 591.
33. Nisa'ai:aya: 157.
34. Biharul anwar, j 51, shafi: 217.
35. Zandeye ruzgaran, shafi: 132.
36. Zandeye ruzgaran, shafi: 134.
37. Suna da yawa a Kur'ani mai girma: anbiya: 69, shu'ura: 63.
38. Biharul anwar, j 51, shafi: 109.
39. Biharul anwar, j 52, shafi: 122.
40. Gaiba nu'umani, babi 11, h 16, shafi: 207.
41. Abin da ya gabata, babi 13, h 26, shafi: 252.
42. Kamaluddin, j 1, h 15, shafi: 602.
43. Gaiba, nu'umani, babi 11, h 16, shafi: 200.
44. Bakara; 138.
45. Kamaluddin, j 2, h 12, babi: 171.
46. Usulul kafi 1, babi 84, h 5, shafi: 433.
47. Gaiba, nu'umani, babi 10, fasali 3, h 6, shafi: 170.
48. Duba fasali na farko na wannan littafin.
49. Za a yi maganar a fasali mai zuwa.
50. Kamaluddin, j 1, babi 25, h 3, shafi: 535.
51. Biharul anwar, j 53, shafi: 177.
52. Gaiba nu'umai, babi 11, h 16, shafi: 207.
53. Kamaluddini, j 2, babi 45, h 4, shafi: 237.
54. Mafatihul janan, ayyukan dare na 23 na Ramadan.
55. Mafatihul jinan, du'a'I Nudba.
56. Abin da ya gabata.
57. Ihtijaj, j 2, Lamba, 360, Shafi: 600.
58. Kamaluddini, j 1, babi 25, h 2, shafi: 535.
59. Dala'ilun nubuwwa, j 6, shafi: 513.
60. Biharul anwar, j 52, babi 22, h 5, shafi: 123.
61. Abin da ya gabata, j 16, shafi: 126.
62. Kamaluddini, j 2, babi 33, h 54, shafi: 39.
63. Abin da ya gabata, babi 31, h 6, shafi: 592.
64. Biharul anwar, j 52, shafi: 126.
65. Abin da ya gabata, shafi: 123.
66. Kamaluddini, j 1, babi 25, h 2, shafi: 535.
67. Abin da ya gabata, babi 32, h 15, shafi: 602.
68. Kamaluddin, j 2, babi 34, h 5, shafi: 43.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+5 =