Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

BALA'IN RASHIN SANIN IMAM MAHADI (A.S)Kamar yadda duniya da kuma al'umma suke fuskantar matsalar rashin sanin addinan Allah madaukaki, haka nan akan samu matsalar rashin sanin mahadiyyanci, kuma wannan matsala ce mai girma da ya kamata mu yi bincikenta karshen wannan littafin.
Wannan al'amari suadayawa yakan sanya rauni game da sanin raunin imani musamman a tsakanin samari game da asalin samuwar imam Mahadi (A.S) da kuma janibobi daban-daban da suka shafi wannan imami (A.S) da zuwansa da ayyukansa.
Don haka a nan zamu yi nuni da mafi girman matsaloli da ake fuskanta game da hakan:

Kuskuren Fahimta

Da yawa wasu sukan yi kuskuren fahimtar wasu daga ma'anoni da suke zo a ruwayoyi da kuma yi musu fassara ta kuskure, daga ciki akwai :

1-kuskuren fahimtar ma'anar sauraro, ya sanya wasu suna tsammanin cewa: tun da gyara da kawar da fasadi zai kasance a hannun imam Mahadi (A.S) ne, to ba su da wani nauyi da ya hau kansu na gyara da kawar da fasadi a cikin al'ummarsu. Wasu ma suna ganin cewa dole ne su yada fasadi a bayan kasa domin imam Mahadi (A.S) ya bayyana! Irin wadannan miyagun tunanuka sun saba wa koyarwar Kur'ani da Ahlul Baiti (A.S) na umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna da suka dora su a wuyan dukkan musulmi gaba daya.
Imam khomaini jagoran juyin musuluncin Iran yana cewa: idan dai hannunmu zai iya kaiwa to hukuncin shari'a ya hau kanmu na wajabcin mu tafi ko'ina mu kawar da dukkan zaluncin da yake duniya, sai dai mu ba zamu iya ba. Amma kasancewar wannan aiki ne da imam Mahadi (A.S) zai yi shi a duk fadin duniya, ba yana nufin ku kawar da hannunku daga (yakar zalunci ba) na aikin da ya hau kanku na (umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna), wannan ba yana nufin ba ku da wani takalifi a kanku ba [1].
Ya ci gaba da cewa: shin mu zamu yi aiki ne sabanin Kur'ani ne mu bar hani ga mummuna da umarni da kyakkyawa domin kawai tunanin cewa imam Mahadi (A.S) zai zo [2]?!
Don haka ya zama dole mu yi bincike game da sahihiyar ma'anar sauraro.

2-Wasu ruwayoyi suna nuni da cewa duk wani motsi na gyara kafin bayyanar imam Mahadi (A.S) to abin mayarwa ne, don haka motsi da samar da juyi domin yakar dagutu wani abu ne mummuna kamar wanda ya faru a juyin musuluncin Iran.
Amma muna iya amsa wannan da cewa; gudanar da dokokin Allah wani abu ne wanda yake wajibi, amma ba zai iya samuwa ba sai da tsayar da hukuma mai adalci da zata tsayar da hukuncin Allah.
Na biyu wadansu ruwayoyin sun yi nuni da cewa: abin nufi irin wadannan motsi da babu hasken shari'a a cikinsu ko kuma wadanda ake yi ba tare da sharudda sun cika ba.
Kuma ana iya fassara wannan da irin kiraye kiraye da masu yinsu suke da'awar mahadiyyanci [3].

3-Daya daga mummunar fahimta game da imam Mahadi (A.S) shi ne nuna shi kamar wani mutum mai yawan fushi da aiki da karfin tuwo:
Sabanin yadda mutane da yawa suka dauka ne cewa; imam Mahadi (A.S) zai zo da takobin adalci ne mai yawan zubar da jini kamar tafkuna, amma duba zuwa ga abin da ya zo a ruwayoyi; imam Mahadi (A.S) shi ne hakikanin tausayi da rahamar Allah madaukaki, kuma shi ma kamar yadda Manzon rahama ya yi ne na kira da dalilai bayyanannu da kuma kiran mutane zuwa ga Kur'ani, don haka babu wani wanda zasu yi taho mu gama da shi sai masu gaba da Allah madaukaki.

Gaggauta Bayyana

Daya daga cikin matsaloli masu girma a game da mahadiyyanci shi ne mas'alar gaggauta bayyana. Domin gaggautawa yana nufin neman abu da sauri kafin lokacinsa ba tare da kammalar dukkan sharuddansa ba.
Mutum yana da gaggawa bisa dabi'arsa saboda raunin ransa da kuma karancin juriyarsa, saudayawa yakan rasa nutsuwar ransa, da neman gaggauta faruwar abu ba tare da cikar sharuddansa ba.
A bisa koyarwar mahadiyyanci al'amarin da ya shafi imami boyayye da mutum yake sauraaronsa, al'amari ne da aka yi umarni da addu'a gaggauta bayyanarsa, amma kuma ba a yi umarni da gaggawa ba, kuma duk tsawaitar boyuwarsa da nisantar bayyanarsa an yi umarni da aka sake cigaba da hakuri ne duk da kuwa akwai bege mai tsanani na neman bayyanar tasa. Kuma dole a mika wuya ga nufin Allah da sonsa, a yi kokarin ganin tabbatar sharuddan da suke wajibi kafin bayyanarsa.
Abdurrahaman bn Kasir yana cewa: Na je wajen imam Ja'afar Sadik (A.S) ina zaune sai Mahram ya shigo ya ce: ina mika gaisuwa! Labari ya zo mini cewa wannan al'amari da muke sauraro yaushe ne zai kasance? Sai imam (A.S) ya ce: Kai Mahram! Masu sanya lokaci sun yi karya, kuma masu gaggautawa sun halaka, masu mika wuya sun rabauta [4].
An hana gagautawa ne ta fuskacin cewa gaggawa takan sayna yanke kauna daga zuciyar mai sauraro, kuma ya rasa juriya da hakurin da syek da shi, kuma ya sanya kokwanto kan halin da yake ciki na mika wuya, kuma ya rasa nutsuwa sakamakon jinkirin sauraro, kuma wannan cutar tana iya smaun wasu mutane, kuma yakan iya kaiwa wani lokaci ga musun samuwar imam (A.S).
Mu sani cewa asalin gaggautawa yana faruwa ne sakamakon jahiltar bayyanar sunnonin Allah da cewa kamar sauran sunnoni ne da suke faruwa su tabbata a lokutan da sharuddansu suka kammala.

Ayyana Lokacin Bayyana

Daga manyan matsalolin da ake fuskanta game da al'amarin mahadiyyanci, shi ne ayyana lokacin bayyana, a ruwayoyi masu yawa an yi hani mai tsanani game da ayyana lokaci, kuma masu sanya lokaci sun yi karya.
Daga imam Muhammad Bakir (A.S) cewa an tambaye shi game da ayyana lokacin bayyana yaushe ne?
Sai ya ce: masu ayyana lokacin bayyana karya suke [5] (ya maimaita hakan sau uku).
Da yawa wannan yakan sanya yanke kauna ga wadanda suka yarda da maganar makaryata kuma daga baya ta bayyana ba haka ba ne.
Don haka masu sauraro su nisanci maganar masu karya da shaci fadi, su sanya wa nufin Allah da iradar ido game da lokacin bayyana.

Ayyana Alamomin Bayyana Kan Wasu Abubuwa Da Suka Faru (Ko mu ce; fassara wasu abubuwa da suka faru da cewa su ne alamomin bayyana)
A ruwayoyi an yi magana kan alamomin bayyana, amma yadda zasu faru da kuma hakikaninsu wani abu ne ba bayyananne ba, don haka masu bayani da fassara kan wannan suna yi ne bisa tsammani ne.
Saudayawa masu ayyana irin wadannan alamomin sukan kuma sanya kusancin lokacin bayyana game da hakan.
Wannan ma yana daga cikin matsaloli masu girma da suke fuskantar mahadiyyanci da suke sanya yanke kauna a zukatan mutane. Misali idan wasu suka nuna wani mutum da yake wani yanki a matsayin Sufyani, haka ma aka yi ta bayanai marasa dalili game da Dujal, sai kuma a nemi bayyanar imam Mahadi (A.S) a kusa, bayan an dade imam Mahadi (A.S) bai bayyana ba sai masu gaskatawa da wannan bayanai suka fada cikin karkata da bata, kuma suka samu shakku a imaninsu sahihi.

Kawo Bahasin Da Ba Dole Ba

A mahadiyyanci akwai abubuwa masu yawa da suke na tilas, wadanda bincikensu ya kasance wani abu na dole a matsayinsu na asasi game da al'marin da ya shafi mahadiyyanci.
Wani lokaci wasu mutane a tarurruka da jaridu da makaloli a mujallu sukan shiga bayani da bincike game da abubuwan da babu wata bukata game da su, wani lokaci ma sukan kawo shubuha da matsaloli ne kan al'amarin da ya shafi mahadiyyanci.
Milsalin wannan bahasi game da haduwar imam Mahadi (A.S) da wasu mutane, da kuma sanya wa mutane shaukin neman haduwa da shi da wuce gona da iri kan hakan, kuma saudayawa wannan al'amari ya kai wasu mutane zuwa ga shisshigi da yanke kauna daga karshe kuma musanta al'amarin mahadiyyanci. Alhalin abin da aka karfafa a ruwayoyi shi ne kokarin aiki domin samun yarda Allah da kuma aiki da imam Mahadi (A.S) da Ahlul Baiti (A.S) suka yarda da shi. Don haka muhimmi shi ne bayanin abubuwan da suka hau kanmu, a lokacin boyuwar imam (A.S) ko ma samu kanmu cikin wadanda imam (A.S) zai yarda da ayyukansu idan mun samu gamuwa da shi (A.S).
Wasu ma sukan shiga bincike game da auren imam, da 'ya'yansa da inda yake rayuwa da sauran bahasosi da ba su da wani muhimmanci ko amfani ga masu sauraro, wasu kuma da sun ga wasu ruwayoyi ba tare da ganin wasu ruwayoyin da suke fassara su ba, sai su shiga bayanai da ra'ayoyinsu.
Misali da sun ga ruwayoyi game da tsawon yakin imam Mahadi (A.S) sai su rika bayanin imam (A.S) kamar wani mai yawan zubar da jini ko mai kaushin hali da rashin tausayi, alhalin a ruwayoyi masu yawa an yi magana game da tsananin tausayinsa da tausasawarsa ga bayi da kuma dabi'arsa ta afuwa irin ta manzon Allah (S.A.W).
Mu sani cewa game da imam shi mai tausasawa ne ga dukkan masoyansa ko su waye, kuma mai tsananta wa kan azzalumai masu take hakkin Allah da na bayinsa.

Masu Da'war Karya Game Da Mahadiyyanci

Daya daga bala'in da ya mamaye al'amarin mahadiyyanci samuwar masu da'awa na karya game da mahadiyyyanci; a tsawon tarihi an samu mutane daban-daban da suka yi da'awar mahadiyyanci bisa karya ko kuma suka yi da'awar suna da alaka da shi, kuma shi ya umarce su da yin wasu ayyuka da makamantan wannan.
Imam zaman (imam Mahadi) (A.S) a wasikar karshe da ya aikawa wakilinsa na hudu ya bayyana cewa: Kai mai mutuwa ne nan da kwana shida, ka shirya al'amuranka, kuma kada ka yi wa kowa wasiyya game da mai maye gurbinka, lokacin boyuwa cikakkiya ya yi… kuma a nan gaba wasu daga shi'a na zasu yi da'awar ganina, Ku sani duk wanda ya yi da'awar ganina daga shi'ata kafin bayyanar Sufyani da tsawa to makaryaci ne [6]!
Da wannan bayani ya bayyana a fili cewa duk wani Shi'a ya san aikinsa, masu da'awar alaka da imam Mahadi (A.S) da da'awar wakilci na musamman daga imam Mahadi (A.S) to sun zama makaryata.
Wasu ma suna wuce gona da iri ne, bayan sun yi da'awar wakilci daga nan kuma sai su yi da'awar su ne imam Mahadi (A.S), daga nan sai su kafa mazhabobin bata da barna da karkatar da akidun mutane daga imani na gaskiya zuwa ga bata [7], wadannan irin kungiyoyi idan mai bincike ya koma tarihi zai gan su, kuma yawancinsu sun samu goyon baya daga 'yan mulkin mallaka ne.
A fili yake cewa wadannan kugiyoyin na bata da kuma mutane masu da'awar mahadiyyanci ko kuma wakilcin imam Mahadi (A.S) al'amarinsu tun farko yana da nasaba da jahilcinsu. Wasu kuma tsananin son su hadu da imam (A.S) da karancin saninsu da imam da shi, da gafala daga samuwar makaryata sai ya sanya su fadawa irin wadannan tarkuna na makaryatan mutane.
Don haka shi'a dole ne ya kasance yana da ilimi isasshe game da sanin imam Mahadi (A.S) domin kada su fada tarkon mayaudara da makaryata masu batarwa, kuma su lizimci biyayya ga malamansu a kan tafarkin tsira da hasken shiriya.

Daga LIttafin: Imam Mahadi Adon Halitta / Mawallafa: Muhammad Mahadi Ha’iri Fuur-Mahadi Yusufiyan-Muhammad Amin Bolo Dastyan. Mafassari: Hafiz Muhammad Sa'id1. Sahifeye nur, j 20, shafi: 196.
2. Sahifeye nur, j 20, shafi: 196.
3. Dod gustare jehan, shafi: 254 – 300.
4. Kafi, j 2, shafi: 191.
5. Gaiba, Dusi, j 411, shafi: 426.
6. Kamaluddin, j 2, babi 45, h 45, shafi: 294.
7. Kamar: "Babiyya" ta "Ali Muhammad Bab" da ya yi da'awar wakilcin imam Mahadi (A.S), sannan sai kuma ya yi da'awar shi ne Mahadi, sannan kuma ya yi da'awar annabta, ya kafa kungiya mai batar da mutane ta Baha'iyya.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+6 =