Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

HADISAN IMAM BAK'IR (A.S)1. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: ما شيعَتُنا إلّا مَنِ اتَّقَى اللّهَ و أطاعَهُ؛ . (تحف العقول، ص 295)
1. Imam Bak'ir (a.s): Ba kowa ne shi'armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shi. (Tuhaful uk'ul, shafi 295)

2. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: تَبَسُّمُ الرَّجُلِ في وَجهِ أخيهِ المُؤمِنِ حَسَنَةٌ . (مشكاة الأنوار، ص 316)
2. Imam Bak'ir (a.s): Murmushin mutum a fuskar d'an'uwansa lada ne. (Mishkatul Anwar: shafi: 316)

3. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: يَقولُ اللَّهُ: ابنَ آدمَ! اجتَنِب ما حَرَّمتُ عَلَيكَ تَكُن مِن أورَعِ النّاسِ. (الكافى، ج 2، ص 77)
3. Imam Bak'ir (a.s): Allah mad'aukaki yana cewa: ya kai mutum! Ka nisanci abin da na haramta maka ka kasance mafi tsentsenin mutane. (Al'kafi, j 2, shafi 77)

4. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: اَلحَياءُ والإيمانُ مَقرونانِ في قَرَنٍ فَإذا ذَهَبَ أحدُهُما تَبِعَهُ صاحِبُهُ . (الكافى، ج 2، ص 106)
4. Imam Bak'ir (a.s): Kunya da imani a had'e suke a cikin wuri d'aya, idan d'ayansu ya tafi, sai d'ayan ya bi shi. (Al'kafi, j 2, shafi 106)

5. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: مَن عَلَّمَ بابَ هُدىً فَلَهُ مِثلُ أجرِ مَن عَمِلَ بِهِ ولايُنقَصُ اُولئِكَ مِن اُجورِهِم‏شَيئاً . (تحف‏العقول، ص 297)
5. Imam Bak'ir (a.s): Wanda ya koyar da wani babi (abu) na shiriya, to yana da ladana wanda ya yai aiki da shi, kuma ladan wad'annan (wad'anda suka yi aikin) ba zai tawaya da komai ba.(Tuhaful Uqul: shafi: 297)

6. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: إيّاكَ وَالتَّفريطَ عِندَ إمكانِ الفُرصَةِ، فَإنَّهُ مَيَدانٌ يَجري لِأهلِهِ الخُسرانَ . (تحف العقول، ص 286)
6. Imam bak'ir (a.s): Na hana ka yin tak'aitawa gun kowace dama, ka sani ita wuri ne da ake samun hasara ga masu ita.(Tuhaful Uqul: shafi: 286)

7. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: ما مِن شَى‏ءٍ يُعبَدُ اللَّهُ بِهِ يَومَ الجُمُعَةِ أحَبَّ إلَىَّ مِنَ الصَّلاةِ عَلى‏ مُحَمَّدٍ و آلِ مُحَمَّدٍ . (وسائل الشيعه، ج 7، ص 388)
7. Imam Bak'ir (a.s): Babu wani abu da za a bauta wa Allah da shi a ranar juma’a mafi soyuwa gareni fiye da yin salati ga Muhammad da alayen Muhammad. (Wasa'ilus Shi'a: j 7, shafi: 388)

8. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: لامُصيبَةَ كَاستِهانَتِكَ بِالذَّنبِ ورِضاكَ بِالحالَةِ الَّتي أنتَ عَلَيها . (بحارالأنوار، ج 75، ص 165)
8. Imam Bak'ir (a.s): Babu musibar da ta kai k'ank'antar da zunubinka da yardar da nutsuwa da halinka da yake a kai. (Biharul Anwar: j 75, shafi: 165)

9. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: تَزَيَّن للَّهِ‏ِ بِالصِّدقِ فِي الأعمالِ . (تحف العقول، ص 285)
9. Imam Bak'ir (a.s): Ka yi wa Allah ado da gaskiya cikin ayyukanka.(Tuhaful Uqul: shafi: 285)

10. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: قُولُوا لِلنّاسِ أحسَنَ ما تُحِبّونَ أن يُقالَ لَكُم . (الكافى، ج 2، ص 165)
10. Imam Bak'ir (a.s): Ku gaya wa mutane mafi kyawun abin da kuke so a gaya muku. (Al'kafi, j 2, shafi 165)

11. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: اِستَشِر في أمرِكَ الَّذينَ يَخشَونَ اللَّهَ . (تحف العقول، ص 293)
11. Imam Bak'ir (a.s): Ka nemi shawarar wad'anda suke jin tsoron Allah a cikin al’amuranka. (Tuhaful Uqul: shafi: 392)

12. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: إنَّ اليَمينَ الكاذِبَةَ وقَطيعَهَ الرَّحِمِ لَيَذَرانِ الدِّيارَ بَلاقِعَ مِن أهلِها . (تحف‏العقول، ص 294)
12. Imam Bak'ir (a.s): Hak'ik'a rantsuwar k'arya da yanke zumunci suna wawashe gida su bar masu shi fanko. (Tuhaful Uqul: shafi: 294)

13. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: فَأنزِل نَفسَكَ مِنَ الدُّنيا كَمَثَلِ مَنزِلٍ نَزَلتَهُ ساعَةً ثُمَّ ارتَحَلتَ عَنهُ . (بحارالأنوار، ج 75، ص 165)
13. Imam Bak'ir (a.s): Ka sanya zamanka a duniya kamar wani gida ne da ka sauka cikinsa awa d'aya sannan sai ka tafi ka bar shi. (Biharul Anwar: j 75, shafi: 165)

14. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: اَلصَّلاةُ تَثِبيتٌ لِلإخلاص، تَنزيهٌ عَنِ الكِبرِ. (الأمالى، طوسى، ص 296)
14. Imam Bak'ir (a.s): Salla tana tabbatar da ikhlasi, kuma tana kawar da girman kai. (Amali, D'usi: shafi: 296)

15. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: لافَضيلَةَ كَالجِهادِ، ولاجِهادَ كَمُجاهَدَةِ الهَوى‏. ( تحف العقول، ص 286)
15. Imam Bak'ir (a.s): Babu wata falala da ta kai jihadi, babu wani jihadi da ya kai yak'ar son zuciya. (Tuhaful Uqul: shafi: 286)

16. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: تَعَرَّض لِرِقَّةِ القَلبِ بِكَثرَةِ الذِّكرِ فِي الخَلَواتِ .( تحف العقول، ص 285)
16. Imam Bak'ir (a.s): Ka sami taushin zuciya da yawaita ambaton Allah a cikin keb'ewa. (Tuhaful Uqul: shafi: 285)

17. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: كانَ الحَسَنُ (المجتبى عليه السلام) كَثيرَ الاِجتِهادِ فِي العِبادَةِ و التَّصَدُّقِ . (نظم دررالسمطين، ص 196)
17. Imam Bak'ir (a.s): Imam Hasan (a.s) ya kasance mai yawan k'ok'ari a ibada da sadaka. (Nazmu Durarul Simd'ain: shafi; 196)

18. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: لَقَد أعطاني اللَّهُ عِلمَ ما كانَ و ما هُوَ كائِنٌ إلى‏ يَومِ القِيامَةِ. (بحار الأنوار، ج 46، ص 296)
18. Imam Bak'ir (a.s): Hak'ik'a Allah ya ba ni ilimin abin da ya kasance, da wanda zai kasance har zuwa ranar k'iyama. (Biharul Anwar: j 46, shafi: 296)

19. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: اَلصَّدَقَةُ يَومَ الجُمُعَةِ تُضاعَفُ لِفضَلِ يَومِ الجُمُعَةِ عَلى‏ غَيرِهِ مِنَ الأيّامِ. (ثواب الأعمال، ص 220)
19. Imam Bak'ir (a.s): Ladan sadakar ranar juma’a yana nunkawa, saboda falalar ranar juma’a a kan sauran ranaku. (Sawabul A'amal: shafi: 220)

20. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: الخَيرُ وَالشَّرُّ يُضاعَفُ يَومَ الجُمُعَةِ). (ثواب الأعمال، ص 143)
20. Imam Bak'ir (a.s): Alheri da sharri duk ana ninka su ranar juma’a. (Sawabul A'amal: shafi: 143)

21. الإمامُ الباقِرِ عَليهِ السَلامُ: الحَجُّ تَسكينُ القلُوبِ). (الأمالى، طوسى، ص 296)
21. Imam Bak'ir (a.s): Hajji yana sanya zukata nutsuwa. (Amali, D'usi: shafi: 296)Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
2+2 =