Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

AYATUL-LAHI ALLAMA SAYYID ADIL ALAWI (D.Z)An haife shi a garin Kazimiyya mai tsarki a tsakanin alfijir da bullowar rana, shida ga watan Ramadan na shekarar 1375 H. wato; 1955 M. a kasar Iraki. Nasabarsa tana tukewa zuwa ga Imam Sajjad da hula 38 daga abdullahil Bahir dan'uwan Imam Bakir (a.s), kuma babarsu ita ce Fadima 'yan Imam Hasan mujtaba (a.s) dan Imam zainul'abidin wato; Ali dan Husain (a.s) dan Ali (a.s) dan Abu Dalib (a.s).
Mahaifin Allama shi ne Ayatul-Lahi Ali dan Husain al'alawi (k.s) yana daga malaman Kazimiyya da Najaf da BAgadaza da Kum, kuma an binne shi a laburaren masallacin Alawi a Kum, kuma yana da laittattafai da ayyukan jama'a da ya assasa.
Ya yi karatu a Iraki da Najaf da Bagadaza a hannun mahaifinsa marigayi da waninsa, da Kum a hannun manyan malamai masu daraja kamar sayyid Mar'ashi Najafi, da sayyid Gulfaigani, da Fadil lankarani, da jawad Tabrizi da sauransu.
A yau yana daga cikin malamai a hauzar Kum da yake koyar da karatun Fikihu da Usul, da Falsafa, da Akida, hada da laccocin da yake gabatarwa a cikin tafsiri, da kyawawan halaye ga jama'ar da ta hada malamai da sauran masu sauraro, da kuma Intanet, yana koyarwa da wallafe-wallafe, da laccoci tun ranar farko da ya kai shekarun balaga kuma ya sanya rawani a hannun mahaifinsa mai daraja, kuma yanzu haka an samu daruruwan malamai da ya yaye su a karatunsa wadanda suke daga kasashe daban-daban, da wasunsu suka kai matsayi babba a cikin al'ummarsu, da ilimi mai zurfi, a sama da shekaru talatin da ya yi yana koyarwa.
Wasu daga manyan mar'ja'ai sun yi sheda da kaiwarsa matakin ijtihadi da fifiko, kuma yayin da ya rubuta littafinsa mai suna "Zubdatul afkar fi najasati au daharatil kuffar" sai ya samu shedar Dakta digiri a shari'ar musulunci a makarantar Hauzar garin Kum.
Hakika ya shahara da wallafe-wallafe masu amfani masu yawa kuma yana kokarin samara da wani insakulipidiya mai girma da yake magana kan dukkan wani nau'I na ilimin musuliunci a cikin sama da littattafai da risaloli 200, kuma an buga sama da 130 daga cikinsu, hada da makaloli a jaridu da mujallu.
Kuma ya shahar da hidimar al'umma ta hanar gidan wurin shan magani na Imam Sajjad (a.s), da cibiyar musulunci don isar da sakon musulunci da shiryarwa, mai suna "Al'mu'assasatul islamiyyatul amma littablig wal'irshad" da "Jama'atul ulama wal khudaba" a garin Kazimiyya da Bagdaza, da kuma "Darul muhakkikin, da "Maktabatul Imam Sadik" a Kum, da "wata laburare" da kafa mutane masu kula da wasu husainiyyoyi kamar ta "kazimain" da makarantar "Imamain aljawadain" a garin Kum, da Husainiyyar "Ahalil Kazimiyya" a Tehran, da husainiyyar "Ummul banin" da garin Karjak, da Husainiyyar "Ahalil kazimiyya" a Ispahan, da Ahwaz, da Kashan, da sauransu, kamar yadda ya kafa jaridar "Sautul kazimain" da ya kafa tun shekarar 1410 da take futowa duk wata da harshen larabci, da mujallar "Kausar" mai fitowa sau biyu duk shekara da larabci, da mujallar "Usshaku Ahlil Bait (a.s)" da yaren Urdu.
Kuma sama da malamai ishirin suka ba shi damar yin ruwaya kamar manyan malamai da suka hada da: Sayyid Najafi, da Sayydi Gulfaigani, da Sheikh Araki, da Sheikh Lankarani, da Sayyid Abdullahi Shirazi, da sayyid Muhammad Shahrudi, da sayyid Muftis Shi'a, da sayyid Muhammad Hasan Langurudi, da sauransu.
Hakika ya zo daga manzon Allah (s.a.w) cewa: "Ilimi uku ne; Aya muhkama, da sunna tsayayya, da farilla madaidaiciya, amma waninsu kari ne" wannan kuwa yana nuna cewa manyan ilimomin musulunci guda uku ne: Akida, da Kyawawan halaye, da Fikihu, waninsu dadi ne da kari.
Don haka ne dogaro da wannan hadisi sai muka ga Insakulifidiyar da malaminmu Allama sayyid Ustazu yake rubutawa ta hada da Akida, Kyawawan halaye, da Fikihu, sannan sai kashi na hudu da ya hada da wayewar al'umma. Amma wadanda aka buga su daga littattafansa suna hada da:
Baganren Akida littattafai guda 43
Baganren Halaye littattafai guda 45
Baganren Fikihu littattafai guda 13
Baganren Wayewa littattafai guda 28
Baganren Rubutattu littattafai guda 47
Amma bayan an samu buga wasu daga littattafan mausu'arsa "Insakulifidiyarsa" mai suna Risalatun Islamiyya da suka hada wani bangaren Akida, da Halaye, da Fikihu, da Wayewa da suka kai kusan mujalladi 24 zuwa yanzu.

Intanet disa shi ne: http://www.aadel-alavi.blogfa.com
Email kuwa: Aadel-Alabi@Yahoo.comRa'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+5 =