Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

AYATUL-LAHI HASAN ZADEH AMULIHaihuwarsa

Aln haife shi a Amuli a shekara ta (1347) a garin Larijani (Amul) a yankin jahar Mazandaran.
Karatunsa
Ya yi karatu a hauza a masallacin Amul wanda ya dauke shi shekaru shida yana koyon darussan gun Ayatul-Lahi mirza abul kasim farsib, da Ayatul-Lahi garawi, da sheikh ahmad al'I'itimadi, da sheikh abul kasim raja'I, da azizullahi dabrasi, da marigayi ashraki.
Ya yi hijira zuwa birnin Tehran yana mai shekaru ishirin da biyu, sannan a shekarar (1369 H) ne, kuma ya samu damar yin karatu wurin malamai masu yawa kamar su mirza abul Hasan al'asha'ari, da ilahi kamshe'I, da taki amuli da rafi'I kazwini, da sauransu.
A shekara ta (1382) ne ya yi hijira zuwa kum, ya halarci karatuttukan allama sayyid Tiba'tiba'I, da dan'uwansa Muhammad Hasan, da kuma mahadi dukkansu Tiba'tiba'i.

Koyarwarsa

Har yanzu dai Hasan zadeh yana ci gaba da koyarwa a hauzar ilimi a birnin Kum mai tsarki.

Wallafe-wallafensa

Akwai littattafai da dama da ya wallafa da suka hada da: Talifofi, Sharhohi, Hawashi, Ta'alikoki, Tashihi, Risaloli.

Littattafai na musamman

Al'insanul kamil
Durusun fi ma'arifatun nafs
Risalatul fil ilahiyyat
Alfu nukta wa nukta
Alfu kalma wa kalma
Nahajul wilaya
Fi ittihadil akili wal'ma'akul
Alwahada fi nazaril arif
Ya rubuta sharhohin littattafai da dama, wasu kuma ya yi musu ta'aliki ne, wasu kuma ya yi gyare-gyare ne a cikinsu kamar yadda muka yi nuni a sam, wasu kuma ya yi musu hashiyoyi, wasu kuma risaloli ne da ya rubuta su.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
4+9 =