Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

AYATULLAHI UZMA ASSAYYID ALI AL-HUSAINI SISTANI ( A J Z )SIFFOFINSA

Ya amfana daga sayyid khu’I kusan rabin karni amfani mai yawa wanda yake babu kamarsa a fagen tunani na musulunci da kuma fagage daban daban na ilimomi da mahangai na musulunci masu muhimmanci . wanda malamai da dama suka fita daga makarantarsa da mujtahidai manya masu daraja , wadanda suka dauki nauyin isar da sako da tunani na musulunci da dukkan abinda suke da shi don hidimar ilimi da al’umma ,suka dauki nauyin isar da sakon da yake kunshe da shi da tunani da sadaukarwa . wadanda mafi yawancinsu a yau malamai ne na hauza musamman ta birnin Najafa mai girma da garin Kum mai tsarki daga cikinsu akwai wadanda suke da matsayi mai girma wanda suna iya daukar nauyin tarbiyyatarwa da ilmantarwa da jagoranci na al’umma da marja’anci da kuma shiryar da al’umma a wannan zamani namu. Daga manyan fitattu a cikin wadannan gwaraza a kwai shugabanmu Ayatul-Lahi uzma assayyid Ali Al-Husaini sistani .wanda yana daga manyan futattun daliban sayyid al-khu’I marigayi Allah ya ji kansa wanda suka shahara a ilmi da falala da daukaka da cancanta na matsayi mai girma , wannan maganar tamu zata kasance game da shi nekamar haka:

Haihuwarsa da rayuwarsa

An haife shi a Rabi’ul awwal shekar ta 1349 hijira a Mashhad a cikin gida mai ilimi da addini da tsoron Allah . ya yi karantu a firamare sannan ya karanta mukaddimat da marhala matsakaiciya . ya bi ta da karatun ilmin hankali da sanin Allah a gun manyan malamai har ya kware a kai sosai.
Ya halarci karatun bahasul harij a Mashhad yana mai amfana daga ilimin Al-allama Almuhakkik Mirza Al-isfanhani Allah ya ji kansa. Sannan ya cirata zuwa birnin Kum a lokacin marja’in nan mai girma Assayyid Burujardi Allah ya ji kansa a shekarar 1368 hijira. Ya halarci bahasin ilimi na malamai manya a wannan lokaci kamar sayyid Burujardi a fikihu da usul . ya kuma samu da yawa da ga iliminsa da tajribarsa da nazarinsa kan ilimin rijal da hadisi , kamar yadda ya halarci karatu wajan malami assayyid alhujja al-kuhmari Allah ya ji kansa. Sannan sai ya bar garin Kum ya fuskanci cibiyar ilimi da falala wato birnin Najaf mai girma a shekarar 1371 ya kuma halarci karatun manyan malamai kamar Al-imam Al-hakim da Asshaikh Hasan hilli da imam Al-khu’I Allah ya kara musu yarda gaba daya. Kamar yadda ya lizimci sayyida khu’I ya yi karatu a wajansa na fikihu da usul sama da shekara goma kamar yadda ya lizimci karatu wajan Asshaikh Hilli na usul cikakkiyar daura .
Ya shagaltu da koyar da bahasul hariji a fikihu a shekara ta 1381 hijira a cikin littafin nan na Makasib na sheikh Al-ansari Allah ya ji kansa .ta haka aka samu littafin nan nasa na sharhin littafin tsarki da mafi yawan hukunce hukunce fur’ua na salla sannan ya biye shi da sharhin littafin urwatul wuska na sayyid Diba’diba’I ta haka ya samu fitar da sharhin littafin tsarki da salla da wani bangare na littafin humusi kamar yadda ya fara bayar da karatu a bahasul hariji na usul a watan sha’aban na shekarar 1384 hijira ya kuma kammala daura ta uku daga usul din a sha’aban na shekarar 1411 hijira mutane da yawa sun yi rikodin din(dauka a rikoda) wannan karatu na sa.

Hazakarsa ta ilimi

Assayyid sistani fifikonsa akan sauran dalibai ya bayyan a cikin bahasin karatu da yake da malamansa ta hanyar karfin ishkali da saurin fahimta da yawan bincike da bibiyar littafan fikihu da na Rijal da ci gaban bincike na ilimi da nacewa da bayar da mahanga a fage daban daban na ilimin Hauza . wanishaida akan haka shi ne shaidar sayyid khu’I gare shi a rubuce da wata shaidar ta Asshaikh Alhilli . wanda sun shaida da matsayin ijtihadinsa har sau biyu masu tarihin 1380 hijira suna cike da yabo akan fifikonsa da iliminsa al’amarin da aka sani ko daga sayyid khu’I ba ya shaidawa ga daliban da ijtihadi a rubuce sai kadai ga sayyid sistani da kuma Asshaikh Ali Aal-falsafi daya daga shahararrun malaman Mashhad. Kamar yadda Asshaikh Al-allama masani hadisi a zamaninsa Aga buzurg Attehrani Allah ya ji kansa ya shaida masa a shekara ta 1380. yana mai yaba masa akan kwarewarsa ta ilimi a rijal da hadisi. Haka nan ya rabauta da shaida daga malamai yana dan shekara talatin da biyar a rayuwarsa.

Baiwar tunaninsa da talifansa

Tun kusan shekara 34 daga rayuwarsa ya fara bayar da karatu a bahasul hariji na fikihu da usul da rijal ya kuma fitar da sakamako na ilimi mai yawa ya yi bincike a bahasin makasib da tsarki da salla da hukunci da humusi da wasu sashen ka’idodin fikihu kamar riba da takiyya da ka’idar ilzam ya kuma koyar da usul daura uku . wasu daga cikin wadannan bincike a shirye yake don bugawa. Malamai da yawa sun fito daga makarantarsa ne kamar Allama Asshaikh Mahadi Marwaridi da Allama assayyid Habib Hhusainiyyan da Allama assayyida Murtada al-asfahani da Assayyid Ahmad Almadadi da Asshaikh Bakir Al-irawani da sauran manyan malaman Hauza . kamar yadda ya shagaltu da wallafa littafai masu muhimmai da risaloli domin yalwata laburaren ilimin addini da littafai masu gamsarwa . hade da abin da ya wallafa na bahasin malamansa na fikihu da usul. Wanda ya hada da ;

1- Sharhin littafin urwatul wuska
2- Albuhusul usuliyya
3- Kitabul kada’I
4-Kitabul bai’I
5-Risala fil libas wal mashkuk
6-Risala fi ka’idatul yad
7-Risala fi salatil safar
8-Risala fi kai’datij tajawuz wal farag
9-Risala fil kibla
10-Risala fit takiyya
11- Risala fi ka’idatil ilzam
12-Risala fil ijtihad wattaklid
13-Risala fi kaidati la darar wala idrar
14-Risala fir riba
15-Risala fi hujjiyyati marasili ibn abi umair
16-Nakdi risalati tashihil asatiz lil ardabili
17-Sharhi mashyakhatiz tahzibaini
18-Risaltun fi masalikil kudama’a fi hujjiyatil akhbar.

Hada da sauran littafai da dama rubutattu da risala amaliyya ta hukunce hukunce saboda masu taklidi.

Hanyar bahasinsa da koyarwarsa

Hanyar koyarwarsa tana da bambanci da yawa da ta sauran malamai na Hauza da masu bahasil hariji misali a fagen usul hanyar koyarwarsa ta kasance kama r haka :

1-Bayar da labarin tarihin bahasi da sanar da asasinsa da farinsa : da yana iya kasancewa daga falsafa kamar bahasin mushtak da tarkibat ko daga Akida ko Siyasa ko bahasin ta’adil da tajrih ko kum a abin ya shafi yanayi n Siyasa da Akida da imamai suka samu kansu a ciki . irin wannan hanya ta binciken tarihin mas’ala ita kan kai mu ga sanin hakikanin abin da ya faru da kewaye wa ga masa’ala da kai wa zuwa ga hakikanin ra’ayoyin da aka yi binciken mas’alar akansu.

2- Kokarin damfara tunanin Hauza da wayewar duniya ta wannan zamani ; kamar a bahasinsa na bambancin da yake tsakanin ma’anar Harafi da Suna da cewa menene hakikanin bambancinsu na zati ne ku na la’akari ne da bambancin hangen da ake yi wa ma’anoni yayin amfani da su ? Anan ya zabi ra’ayi ne na mai littafin Kifaya dacewa bambancin na yanayin yadda ake duba ma’anonin ne ba bambnci ne na zatin ma’anonin ba . kuma ya yi gini ne akan mahangar falsafa sabuwa wato it ace mahangan nan ta yawaitar riska ta mariskai a kwakwalwar mutum da dabi’arsa ta yadda yana iya yuwuwa ga kwakwalwa ta hangi abu daya da mahanga daban daban wani lokaci a matsayin mai zaman kansa wani lokaci kuma a matsayin yana damfare da waninsa . haka ma yayin da ya shiga maganar mushtak da jayayyar malamai kan ismuz zaman sai ya shiga maganar zamani a mahangar falsafa sabuwa haka ma a mahangar sigar umarni da kalmarsa da bahasin tajarri ya shiga nazarin malamai kan yadda malaman zamantakewa suka kasa umarni da nema da cewa sakamakon shi mai nema ya siffantu da neman ta hanyar kasancewar sa yana ganin shi ne sama ko daidai yake da wanda ya nema wajansa ko kuma yana ganin kansa kasan wanda yake nema a wajansa ne. haka nan ya sanya ma’aunin azabtar da mai sabo da cewa saboda shi bawa ya yi tawaye ga umarnin ubangijinsa ne kuma haka yake bisa kashe kashen matsayi da darajojin al’umma a zamantakewarsu ta yadda zaka ga akwai bawa da uban gida da na sama da na kasa da sauransu .wannan kuma bahasi ne kan dabakokin a al’umma ba magane ce ta doka ba wacce ta ginu bisa masalahar al’umma .

3-Himmantuwa da usul da yake da alaka da fikihu :Saudayawa dalibi yakan ga malamai sun dulmiya cikin usul dulmiya da bahasin da ba ya kai wa ga komai sai tsantsar nazari da ba ya bayar da wani sakamako na fikihu a tafarkin ilimin fikihu kamar bincike game da cewa sanya wa ma’ana lafazi shin alamari ne na dabi’ar samuwa ta halitta ko kuma abu ne na la’akari na tunani wanda irin wannan bincike ba shi da wani sakamako na a zo a gani a fikihu amma shi malamin da muke Magana akansa ya shagaltu da bincike na usul ne mai zurfi wanda yana da alaka da sakamako na fikihu kamar bahasin amm da khas da ta’adul wat tarjihi da usulul amaliyya.

4- Canji da sabuntawa :Malamin ya kasance yana dauke da ruhin neman canji ba kamar wasu malamai ba da yawa zaka same su ba sa dauke da ruhin kawo canji , suna sa himmarsu ne kawai wajan ganin kayen bahasi ba hakikanin asalinsa ba. sai ya shagaltar da kansa wajan warwarar wasu jimloli da ishkalin da aka yi akansu.

5-Shagaltuwa da al’amuran zamani :kamar bahasi kan halarcin auren kafira mushrika da ka’idar tazahum da malamai suke bincike akanta a matsayin ka’ida ta hankali kadai , amma shi ya shigar da ita karkashin ka’idar iddirari wato abu na larura da ba makawa gare shi wacce ita ka’ida ce ta shari’a ba ta hankali ba kamar yadda nassi hadisai da ayoyi sun yi nuni zuwa gare ta. Haka nan ka’idar latu’adu a cikin salla ya sanya ta akan duk wata farilla da sunna da suka hadu ko a salla ko ba a salla ba saboda karshen ruwayar yana cewa ba a sake farilla saboda sunna ai sunna ba ta iya rusa farilla . shi ya sa ya gabatar da lokaci da alkibla akan yanke yanken salla, saboda lokaci da alkibla farilla ne ba sunna ba.

6-Duban nassi ta fuskacin zamantakewar al’umma :Wasu malamai suna duba nassi ruwaya ne ba tare da neman fidda ma’anarta ba da kallonta ta mahanga daban daban. Amma wasu malamai kamar shi Ayatul lahi sistani suna duba ruwaya ta kowane bangare kamar yanayin zamantakewar al’umma domin fahimtar ruwaya. Kamar hadisin da yake cewa manzo (SAW) ya hana cin naman jakin gida a khaibar, a nan zamu ga yanayin lokacin ana yaki ne kuma ana daukar kaya akan jakuna ne idan aka cinye su to wannan yana nufin raunin kayan sufuri da daukar kayan yaki saboda haka anan ba wani abu da yake fahimtar da haramci ko karhanci na cin naman jakin gida domin hanin ya zo da bayanin masalahar da ta sanya hana cin naman jakin na yanayi da ake cikin.

7-Cikakkiyar masaniya da ilimomin ijtihadi da fitar da hukunci :Sayyid sistani ya kasance yana dagewa ko da yaushe kan cewa malami ba ya zama malami sai idan yana da cikakkiyar masaniya game da maganar larabawa da wakokinsu da hudubobinsu domin ya zama zai iya gane ma’anar Magana ta maudu’iyya ba zatiyya ba ya kuma zama yana da cikkakken sani kan littafan lugga da mawallafanta da hanyar rubuta ta wannan duk yana daga abubuwa da za a dogara da su wajan karbar maganar ma’abocin littafin lugga. Haka nan ya zama yana da cikken sani game da hadisan Ahlul bait (AS) da masu rawaito hadisan dalla dalla domin ilmul rijal larura ne kuma dole ne saninsa ga mujtahidi. Wasu malamai sukan dogara ne da zuhuru shakhsi na akhbar ba tare da ya hada ta da zuhurur maudu’I ba. ko ya dogara kan maganar mawallafa littafan luga ba tare da bincike ba na kashin kansa.

8- Kwatantawa tsakanin makarantu daban daban :Sanannen abu ne ga wanda suka halarci karatunsa sun san cewa baya kayyade tunaninsa da makaranta daya ko mahanga daya. Yana hada bincikensa ne tsakanin makarantar Mashhada da ta Kum da ta Najaf yana bincike a ra’ayoyin mirza isfahani da na sayyid burujardi da na sayyid khu’I da asshaikh Husain hilli Allah ya ji kansu.

TAFARKINSA NA FIKIHU

Tafarkinsa na fikihu yana da kasu kashi uku ne:
1- Hadawa da kwatantawa tsakanin fikihun shi’a da na sunna
2- Amfana da ga ilimin kanun (dokoki) a fikihu domin samun fadada wajajan amfani da ka’idojin fikihu da kuma buda tunani kan dokokin zamani da taimakawa wajan bayanin dokokin fikihu da wuraren amfani da ita.
3- Sabunta yanayin yanda ake bayar da darasi, kamar mahangarsa ga ka’idar ilzami ta wata fuska kamar ta fuskacin girmamawa shi ya sa ma yake kiranta da ka’idar girmamawa.

SIFFOFINSA

1- Girmama ra’ayin wasu da yi musu adalci ya kasance mai binciken ra’ayin mutane har da na abokansa mai yawan bin littafai da kwadayin ilmi da cimma gaskiyar lamari, yana binciken har ra’ayin abokansa da na wasunsu wadanda ba malamansa ba ne ya kuma yi munakasha da tattaunawa akan ra’ayin da girmamawa.

2-Lladabi cikin tattaunawa ba kamar yadda wasu dalibai kan yi ba shi ya kasance yana tattaunawa da ladabi ne da girmamawa ga malami kuma yana nisantar duk wata jayayya kumayana amsawa ga dalibi tambayarsa da tattaunawarsa da girmamawa ta fuskacin kamar luraswa da shiryarwa ga mafifici. Idan dalibi ya dage ya mayar da shi jayayya to yanaamsawa ne amma idan ya sake dagewa, sau da yawa yakan fifita shiru kan magana

3- Dabi’arsa : Yana ganin koyarwa aiki ne da ya hau kansa domin shiryar da al’umma( ba kamar aiki ne na gwamnati ba da sauransu) da kuma tausayawa ga dalibi. Haka kyawawan dabi’unsa suka yi tasiri akan dalibansa kamar yadda ya kasance ga Ayatul- lahi assayyid Hakim da kuma sayyid khu’i (RA)

4-Tsantseni : Ya kasance mai lizimtar shiru da tsantseni da nisantar duk wata hargowa ta kabilanci ko hassada da mugun kudiri da neman amfanin kashin kai. Ya kasance yana mai nisantar duk wani neman matsayi da suna da mukami da sabani kan al’amura na duniya. Kuma ya kasance mai zuhudu da tufafi na takawa da kaskantar da kai. Da dan karamin gidansa da ‘yan kayansa.

5- Kawo sabon tunani : Assayyid sistani ba kawai malami ba ne , shi mutum ne mai wayewa da masaniya kan al’amuran zamani kuma mai budadden tunani kan wayewa da al’adu daban daban kuma yana da mahanga da ra’ayoyi game da tattalin arziki da siyasa da nazarce nazarce sababbi da tunani kan zamantakewa da faffadan tunani game da yanayin wannan lokaci ta yadda fatawowinsa suka kasance domin masalahar al’ummar musulmi.

Marja’ancinsa

Wasu malaman Najaf madaukakiya sun nakalto cewa bayan wafatin Ayatul Lahi Assayyid Nasrullah Allah ya ji kansa sai malamai suka ba wa sayyid khu’I shawarar cewa ya fitar da wani mutum da ake nuni zuwa gare shi ake girmamawa da ya cancanci mar’ja’anci da kuma kiyaye hauzar Najaf , sai ya zabi sayyid sistani saboda falalarsa da daukakarsa ta ilimi da tsarkin zuciyarsa da kyawun dabi’unsa. Bayan wafatin sayyida khu’i ya kasance cikin mutane shida da suka raka jana’izarsa kuma shi ne ya yi masa salla, bayan haka ne ya daukin nauyin marja’anci da jagoranci Hauza da aikawa da izini da raba dukiyoyi da koyarwa akan minbarin sayyid imam Al-khu’iAllah ya ji kansa a masallacin Khadra’a kuma takalidi da shi ya yadu da gaggawa a kasar Irak da Khalij da sauran yankunan duniya kamar Indiya da Afrika da sauransu musamman tsakanin malamai a Hauza da kuma tsakanin samari da wayayyun mutane wadanda suke da tunani na wayewa , har yanzu yana cikin mutane ‘yan kadan da malamai manya da yawa suka yi musu shedar a’alamiyya a Najaf da Kum madaukaka Allah ya ja zamaninsa ya tsawaita rayuwarsa.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
9+8 =