Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

SAYYID SHIHABUDDIN MAR\'ASHI NAJAFI (K.S)Iyali

Malami ne da ya kare littattafan addini daga tozarta, masanin usul da hadisi da fikihu, kuma masanin adab, da tarihi, an haife shi a Najaf 20 ga Safar, 1315, H. daidai 21. ga watan 6, 1897. ya yi karatu a hannun malami babansa mai suna Shamsuddini Mahmudi Husaini Mar'ashi Najafi wanda ya rasu a (1338 H) wanda yake daya daga manyan malaman zamaninsa.
Kakanninsa sun kasance imma dai malamai ko likitoci ko masu mulki, har ma yankin Golistan na Arewacin Iran ya kasance a hannun kakanninsa kusa shekaru dari biyu.
Sayyid kiwamuddin mar'ashi wanda aka fi sani da almira alkabir ya kasance shugaban sarautar mar'ashawa, kabarinsa yana nan a Amul arewacin Iran wuri ne da mutane suke ziyararsa domin neman albarka.
Kuma nasabar sayyid mar'ashi Najafi tana komawa zuwa ga Imam zainul'abidin (a.s) da hula (33) tsakaninsu, kuma suna da nasaba mai karfi ta sharifai wacce aka kiyaye ta. Kuma yawancin sun zabi rayuwa a garuruwan Iran kamar; Kum, Ispahan, Mazandaran, Rafsanjan, Damawand, Kazwin, Khuzistan, da Azarbaijan.

Malamansa

Sayyid Mar'ashi ya yi karatu gun malamai masu yawa; kamar Sheikh Murtadha attalikani, da sheikh Muhammad Husain al'ispahani, da gun hajiya Bibi Shamsu Sharaf bijan attibatiba'I (kakarsa ta wurin Uwa), kuma ya koyi karatun Kur'ani da tajwidi da tafsiri gun Mirza Abulhasan almishkini, da sheikh Muhammad Husain asshirazi, da sayyid hibatullah asshahristani, da sayyid Ibrahim shafi'I Rufa'I Bagdadi, kamar yadda ya koyi ilimin nasabobi gun sayyid Ridha almusawi algarifi, da dan'uwansa sayyid mahadi algarifi.
Amma fikihu da Usul ya koya gun mahaifinsa da sheikh Murtadha talikani, da sayyid Muhammad Ridha Rafsanjani, da Sheikh gulam Ali kummi, da mirza abulhasan mishkini, da sayyid Aga shushtari, da mirza Ali kazimain, da sheikh Abulhusain arrashti, da mirza aga al'istahbanati, da sheikh Musa karmanshahi, da Ni'imtaullahi larijani, da sayyid Ali diba'tibatiba'I alyazdi.
Kamar yadda ya karanta ilimin taurari da lissafi gun malamai masu yawa kamar sheikh abdulkarim albushahri, da sayyid abulkasim almusawi alkhunsari, da Dakta andalib zadeh, da mirza mahmud al'ahari da Muhammad mahallati, da sheikh abdulhamid addashti, da mirza ahmad munajjam, da sayyid kazim al'asar.
Kuma ya karanta ilimomi masu yawa kamar likitanci da ilimin Rijal, da Diraya, da hadisi, da Fikihu mai zurfi, da Usul mai zurfi gurin malamai masu yawa da ambatonsa yakan iya daukar layuka masu yawa.
Ya zauna watanni uku a garin Samra'u da Kazimain domin kamala Fikihu da Hadisi, da Rijal a hannun malamai daban-daban. Sannan sai ya sake dawowa Najaf ya karanta ilmin kalama gun mahaifinsa da kuma gun Muhammad jawad albalagi da wasu malaman.
Da wannan muna iya gane cewa sayyid mar'ashi Najafi yana daga cikin malamai wadanda suke 'yan kadan irin wadanda suka yi karatu wurin malamai masu yawan gasket daga manyan malaman hauzar ilimin addini mai zurfi a Najaf.
Kuma ya samu shedar zama mujtahidi da wuri, kuma ya kasance fitacce a tsakanin abokansa wurin neman ilimi, kuma ijtihadi shi ne daraja mafi girma ta ilimi a cibiyoyin addini na Shi'a.

Hijira zuwa Iran

Bayan shekaru da samun darajar ijtihadi sai ya tafi ziyarar Imam Ridha (a.s) a mash'had shekara 1342H / 1924M. bayan ya dawo sai ya tsaya a Tehran yana mai ci gaba da bahasi da karatu gun manyan malamai kamar sheikh abdunnabi annuri, da sheikh Husain annajm abadi, da mirza dahir attankabuni.
Sannan sai ya sake tafiya zuwa Kum bayan shekara ya sauka gun Ayatul-Lahi uzma sheikh abdulkarim alha'iri alyazdi, wanda ya assasa hauza a birnin Kum. Sai ya zabi zama a Kum, ya fara koyarwa a Hauza ya zama daga malamai na farko a cikinta a lokaci kankani.
Ya ci gaba da koyarwa a Kum kusan shekaru 67 a jeer, kuma yana da zama kusan goma a kullum, kuma ya jagoranci limancin salla a haramin Ma'asuma kusan sama da rabin Karni babu yankewa.
Bai taba gajiyawa ba ko kiftawar ido a kan hidima ga hauza kuma wannan kokari nasa ya fitar da dubunnan malamai da a yau suka kasance daga mash'huran malamai a hauza, kuma ya gina cibiyoyin ilimi masu yawa da masallatai da husainiyyoyi da cibiyoyin kiwon lafiya, da laburori a Kum da sauran garuruwan Iran da ma wajen Iran. Kuma da kansa ya yi kokarin kiyaye littattafan magabata kuma ya kwadaitar da dalibai yin amfani da su.

Gadon iliminsa

Yalwar iliminsa tana iya bayyana ta hanyar ganin irin ilimiomin da ya yi rubutu a kansu da yawancinsu da larabci ne, daga ciki:
Mulhakatul ahkak a ilimin kalam da akida da falalar imamai masu tsarki (a.s) wanda ya duba sama da littattafai 5000 na ahlussunna kafin hada shi, kuma ya hada shi cikin shekaru 40: zuwa yanzu an buga mujallad 36 ne kawai daga ciki karkashin kulawar danda mahmud mar'ashi Najafi. Sannan akwai littattafai masu yawa da ya rubuta wadanda ambatonsu zai yi tsawo, kamar yadda ya hadu da manyan malamai na duniya da masa daga kasashe daban-daban a rayuwarsa su ma ambatonsu zai yawaita.

Cibiyarsa

Ya assasa mafi girman cibiya da laburare a duniyar musulmi gaba daya da ta hada duk wasu kayan tarihi na littattafan musulmi da yake nuna musulunci a cikin karnoni 12 da suka gabata. Da yada ilimi da bincike da rubutu da a yau amfaninsa ya bayyana fiye da lokacin da.
Wannan laburare tana da matsayi mai girma a matsayinta ta daya a cikin Iran ta uku a duniyar musulmi gaba daya. Sannan kuma ya tattara dukkan littattafan musulunci na da musamman na rubutun hannu domin gudun kada azzalumai su ci gaba da kawar da su kamar yadda ya faru ga mafi yawansu.
Ya sanya laburare wakafi tun 29,4,1968 M, a matakin farko.

Rasuwarsa

Bayan kusan karni guda da ya yi yana yada ilimi da wayewar musulunci da raya ilimin Shi'a'nci sai ya amsa kiran ubangijinsa yana mai shekaru 96, a ranar laraba, bakwai ga watan Safar, 1411, daidai 29 August 1990.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
8+8 =