Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

AYATUL-LAHI UZMA SAYID MUSAWI ARDABILIHaihuwarsa Da Tasowarsa

An haifi Ayatul-Lahi Uzma Sayyid Musawi Ardabili a garin Ardabil 13 –Rajab-1344 BH. Wanda ya yi daidai da shekara 1926 Malamin ya kasance a gidan ilimi, Mahaifinsa shi ne marigayi Sayyid Abdurrahim ya kasance daya daga cikin manyan malamai a zamaninsa. Mahaifiyarsa kuwa ta kasance daya daga cikin jikokin Manzo ta rasu kuwa shekara ta 1928 sakamakon haka ne ya rayu a hannun yan uwansa mata. Maraici ya yi kyakkyawa tasiri a cikin rayuwarsa, ta yadda tun yana qarami aka fara ganin alamomin hazaka da kamalatare da shi.

Sayyid ya kasance yana cewa dangane da wani mafarki da ya yi, lokacin da ina yaro na kasance ina tsananin son haxuwa da Imam zaman (a.s) don haka ne na yi kokari na yi duk ayyukan da ake yi domin ganin Imam Mahdi (a.s) kamar yadda ya zo a cikin littafai, kamar yadda na yi qoqari wajen aikata wasu ayyukan mustahabbai, sakamakon haka ne na samu dace na ga Imam a cikin mafarki, yayin da na ga Imam (a.s) sai na rungume shi kamar yadda yara qanana suke yi wa iyayensu, sannan na riqe qafafunsa na neme shi da ya ba ni wani abu, nan take sai ya fitar da zobensa ya sanya mani a 'yatsana, a lokacin da na bai wa babana wannan labari, sai ya ce masa ban ji maka tsoron komai daga yau, domin kuwa zaka kasance cikin kiyayewa da kulawa ta Imam Mahdi (a.s).

Fara karatunsa na addini

Sayyid Musawi Ardabili (Allah ya yi masa tsawon rai )ya fara karatunsa na addini yana xan shekara shida, yayin da ya fara karatun kur’ani a makarantar Addini, bayan fara karatun kur’ani sai kuma ya fara karanta littafan fiqihu, Tanbihul gafilin, nisabus sibyan, Abwabul jinan, majalisul muttaqin, tarikhul mu’ujam, Addurun nadir, tarikhul wassaf da adabin harshen farisanci, da dai sauran littafai da ake karantawa a makarantun addini a wannan lokaci.
Bayan wannan ne sai ya fara karanta harshen larabci a shekara ta 1939 daga nan ne fa ya cigaba da karatunsa na hauza tukuru, yayin da shiga makarantar shehin mulla Ibrahim a garin Ardabil wannan kuwa ya farru a shekara ta 1940.
A wanna lokaci ya kasance makarantun karatun adddini guda uku ne kawai a garin Ardabil kamar haka:

1-Makarantar Mirza Ali Akbar wadda daga baya ta koma makarantar firamare.

2-Makarantar Salihin ita ma daga baya ta koma masaukin baqi wadan da suke zuwa daga Qafqaz, don haka sai ya kasance makaranta guda daya ta yi saura a wannan gari wannan kuwa ita ce;

3- Makarantar mulla Ibrahim, wadda xalibanta ba su wuce mutum huxu ba sakamakon rashin ganin qimar karatun addini a wannan lokaci. Amma duk da wannan mawuyacin halin Sayyid Musawi ya xauki xamarar ci gaba da karatunsa, yayin da ya kammala karatunsa na matakakin farko kamar abin da ya shafi suyuxi, Jami'u, Mutawwal, Hashitu Mulla Abdulla, shamsiyya da Ma'alim da shara’'u, wannan kuwa ya kasance a shekara ta 1943.

Bayan sarki "Ridha Sha" ya gudu ya sanya matasa sun samu sha’awa ga karatun addini, yayin nan suka kwararo zuwa makarantar Mulla Ibrahim, haxuwarsa da waxannan matasa ya qara qarfafa shi domin kuwa ya ci gaba da koyar da su abubuwan da ya karanta na matakin farko kamar abin da ya haxa da Nahwu, sarfu da Manxik. Sayyid Ardabili bai tsaya ba da wannan domin kuwa ya dukufa wajen ayyukan yaxa addinin musulunci wanda ya samu ci baya na kusan shekaru ashirin na tsananin mulkin azzalumin sarki Ridha Sha, kamar abin da ya shafi gabatar da wa’azi da sauran abubuwan da suka shafi addini a wannan yanki na Ardabil da kewayenta.

Hijirarsa zuwa Qum

Ayatul-Lahi Sayyid musawi Ardabili, ya yi hijira daga garin Ardabil zuwa Qum a cikin watan ramadan a shekara ta 1943 domin ci gaba da karatu mai zurfi a wannan gari na Qum, Shehin Malamin ya kasance a mashahuriyar makarantar nazarin addini mai zurfi ta "Faidhiyya" wacce ta yaye manyan malamai, a tsawon shekara uku ya yi karantu a wannan makaramta a hannun wasu manyan malamai, a wannan lokaci ne ya karanta kifaya da makasib a hannun Ayatul-Lahi Sayyid Muhammad Ridha Gulfaigani Allah ya jikans (a.s), sannan ya karanta kifaya da abin da ya shafi saye da sayarwa a cikin littafin makasib da sharhin hidaya a hannnn Ayatul-Lahi Khunsari, sannan ya karanta Rasa’il a wajen Ayatul-Lahi sheikh murtadha Ha’iri da Ayatul-Lahi Sultani, Sannan ya karanta Manzuma a wajen Ayatul-Lahi Hajj Mirza Mahdi.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+7 =