Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

AYATUL-LAHI MUHAMMAD JAWAD ALBALAGI (R)Nasabarsa

Sheikh Muhammad Jawad dan Hasan dan Dalib, dan Abbas albalagi, annajafi, arrab'i. An haife shi a Najaf shekarar 1282 H / 1865 M, a cikin gidan ilimi da tsoron Allah da takawa.
Ya taso inda aka haife shi wato; Najaf, kuma ya yi karatun Fikihu da Usul da Palsapa a can, da kuma adadi da waka da sauran ilimomi daban-daban.
Ya karanta mukaddimat a gun malaman Najaf, sannan sai ya tafi Kazimiyya, sannan sai ya sake dawowa Najaf a shekara 1312 ya sake yin karatu gun malamai kamar; Ali sheikh Muhammad Daha Najaf (T 1323) da sheikh Ridha Hamdani (T 1322), da sheikh Akhund Khurasani (T 1329) da sayyid Muhammad alhindi (T 1323).
Ya yi hijira zuwa Samarra shekara 1326, ya yi karatu gun Muhammad Taki Shirazi (T 1326) shugaban juyin halin nan na Iraki, kuma a nan ya wallafa wasu littattafai, ya bar ta kafin sojojin Ingila su mamaye ta sai ya tafi Kazimiyya ya zauna can shekaru masu yawa yana mai taimaka wa malamai wajen ganin cin nasara juyi da dauki ba dadi kan Ingilawa, da neman 'yanci.
Sannan sai ya dawo Najaf ya ci gaba da koyarwa da wallafawa har sai da mutuwa ta zo masa.

Ya kasance mutum ne wanda yake kogi a kowane fage na ilimi da sani, kuma daga cikin mutane 'yan kadan da suke sadaukar da rayuwarsu saboda hidimar addini da mazhaba, koda yaushe imma dai yana amsa tambayoyi ko kuma yana rubuta wasika domin amsa wata shubuha ko kuma yana rubuta littafi.
Ya tsaya kyam da kafafunsa wurin ganin ya hana yaduwar ‘yan mishan da suka durfafo Iraki da sauran garuruwan larabawa da addinai har sai da ya kasance yana da matsayi babba mai daraja hatta da a tsakanin malaman Kiristanci.

Kamar yadda ya tsaya kyam wurin ganin karkatattun addinai da mazhabobin kin allah ba su yi galaba ba, kamar kadiyaniyya, da albabiyya, da wahabiyanci, da musun samuwar Allah, don haka ne ya rubuta littattafai kan batansu da dasisosinsu, kuma ya nuna raunin lamarinsu da rushe duk wani dalili ko wata hujja da suka dogara da ita.

Kuma daya daga cikin abin da ya sanya shi samun wannan dammar shi ne kwarewarsa a harshen Farisanci, da Ibaraniyanci, da Ingilishi hada da yaren larabci.
Ya kasance yana da kyakkyawar niyya da Ikhlasin aiki har sai da ya kasance bai yarda a rubuta sunansa a littafin da ya wallafa ba, ya kasance yana cewa nib a komai nake so ba sai kariya ga gaskiya, ba bambanci a rubuta sunana ko sunan wani a kai.

Hatta da Ilyan Sarkis ya fada a littafinsa cewa; Littafin nan na “alhuda Ila Dinil Mustapah” a cikin talifofin Balagi ne. kamar yadda wasu suka ambaci wasu talifofin, kuma wani lokaci yakan yi kinaya da sunansa a littafi ne. amma duk da haka sunansa ya kasance kamar wuta ce da aka hura a kan tuta tana haskakawa.

Ya shahara matuka har sai da ta kasance ana kawo masa warwarar mas’alolin ilimi har tun daga nesa, hatta da malaman Turai suna koma masa ne a cikin matsalolinsu na ilimi masu wahalar warwara, kamar yadda aka fassara wasu talifofinsa zuwa Ingilishi.

Ya kasance yana yin sallar jam’I da mutane a kofar gidansa, sai kowa masu daraja da zababbun mutane da sauransu su yi koyi da shi, kuma bayan y agama salla sai ya koyar da littafinsa “Ala’ur Rahman”.

Ya kasance mai saukin hali, mai saukin ruhi, mai yalwar tafi, ba ya raha kuma bay a son yin raha da wani a gabansa, yana da kwarjini, kuma siffar masu takawa tana bayyana a fuskarsa.

Abin Da Ya Bari

Daga cikin abubuwan da suka wanzu da ya bari akwai juyayin ashura a tituna saboda irin soyayyar da yake da ita ta musamman ga Imam Husain (a.s) da yin fito na fito da masu gaba da shi masu kiyayya da juyayin ashura. Ba don shi ba da masu hanawa sun ci galabar hanawa, da ba a samu wannan matsayin na yin juyayi ba, sai dai shi ya yi riko da su kam.

Wannan gwarzo ya kasance duk da tsufansa da raunin jikinsa amma ya kasance yana tafiya babu ko takalma a cikin taron masu juyayin ashura da kafafunsa yana mai dukan kirjinsa, a bayansa ana shelata sha'a'ir, a gabansa kuwa ana buga bandiri. Kuma wannan ya ci gaba har zuwa wannan rana tamu ta yau. Kuma yana daga abubuwan da ya bari akwai kwadaitar da mutane wurin kariya ga gaskiya da shan gaban karkatacciyar akidar nan ta Baha'iyya a Bagadaza da kuma kai kara domin hana su mallakar abubuwan da suka mamaye a garin Mahallar Sheikh Basshar a Karh, wanda suka mayar da shi wurin bukukuwansu domin tsayar taken bata na dagutanci, don haka ne kotu ta yi hukunci da a kwace shi daga hannunsu, sai ya mayar da wurin masallaci da ake salloli biyar a cikinsa, kuma ana yin zaman koken Imam Husain (a.s) da sauran Ahlul Baiti (a.s).

Malamai da yawa masu ilimi ne suka ya ba masa da cewa shi gwarzo ne mai takawa, da ilmi, da baiwa, da kyauta, da mujahada, da sarrafa rayuwa wurin yin talifii da sannafa littattafai, da kyawawan halaye. Kamar sayydi Khu'I, da Muhsin al'amini, da sheikh Abbas Kummi, da Muhammad Ali Tabrizi da malamai masu yawa wadanda ba mu kawo su ba saboda tsoron tsawaitawa.

Yana da wakoki masu yawa game da haihuwar imamai Hasan da Husain (a.s) da kuma Imam Mahadi (a.s), da wakokinsa kan raddi ga masu musun samuwar Imam Mahadi (a.s) da sauran wakoki a kan fagage masu yawa.

Dalibansa

Yana da dalibai masu yawa wadanda suka yi karatu a wurinsa da masu ruwaya daga gareshi wadanda yawancinsu sun shahara da suka hada da:
Sheikh Murtadha almuzahiri Annajafi (wafati: 1414)
Sayyid Abulkasim Khu'I (wafati: 1413)
Sayyid Shihabuddin Muhammad Husain Mar'ashi (wafati: 1411)
Sayyid Mujtaba Lankarani annajafi (wafati: 1406)
Da sauran malamai masu yawa da ba mu kawo sunansu ba a nan.

Ya wallafa littattafai masu yawan gaske da risaloli a fagen ilimomi daban-daban da 'yan baya suke amfana daga garesu da wadanda ma zasu zo bayansu da zamu yi nuni da wadannan kamar haka; amma abin takaicin har yanzu wasu ba a buga su ba don haka muka rasa albarkacin amfanuwa daga garesu, wadanda aka buga sun hada da:

Al'aurRahman fi tafsiril Kur'an
Risalatun fi takzibi ruwayatut tafsiril mansub ilal Imam Hasan askari (a.s)
Alwajiz fi ma'arifatil kitabil aziz
Alhuda ila dinil Mustapha
Alhuda ila dinil Mustapah
Da'il islam, wa Da'in Nasara
Da sauran littattafai masu yawa da ba mu kawo su a nan ba saboda tsoron yawaitawa.

Wafatinsa

Ya rasu a sakamakon rashin lafiya a daren litinin 22 sha'aban 1352, daidai da 9 ga watan 12, 1933. ana yada labarin rasuwarsa sai ga garin Najaf mai daraja ya cika da kukan rashin wannan tauraro da ya kisfe. Wanda aka yi wa musulunci fuju'a da mutuwarsa. Kuma malamai manya daga mujtahidai da kuma jama'a masu yawa dubunnai ne suka raka shi zuwa masaukinsa. Allah ya gafarta masa.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+1 =