Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

Ahlulbait (a.s) Cikin Alkur'ani Mai Girma

Alkur'ani mai girma shi ne tushen dukkan tunani, shi ne mabubbugar shari'a da ka'idoji. Duk abin da Alkur'-ani ya zo da shi wahayi ne abin saukarwa, kuma magana ce tsarkakkiya daga Allah, yana furuci da tsarin rayuwa yana kuma ayyana dokokin rayuwar. Duk wani musulmi ya san cewa abin da Alkur'ani ya zo da shi shi ne shari'a da sakon da zai bi a rayuwarsa, sannan kuma an wajabta masa aiki da shi da yin tafiya bisa shiriyarsa. Abin lura kuma shi ne Alkur'anin nan ya yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s) da yanayi da tsari kamar haka:
1. Amfani da sunansu na isdilahi wanda shi Alkur'-anin ya sanya musu. Wani lokaci yakan ambace su da Ahlulbaiti kamar yadda ya zo cikin Ayar Tsarkakewa, wani lokaci kuma yana ambatonsu da al-Kurba kamar yadda ya zo cikin ayat al-Muwadda (ayar kauna). Ayoyi masu yawa sun sauka da wadannan ma'anoni sannan Sunna ta yi bayaninsu ga al'umma a lokacin da ayoyin suke sauka daga bisani kuma masu fassara da masu ruwaya suka nakalto bayanin cikin littattafansu manya da kanana.
2. Kiyaye da kuma rubuta dukkan ababen da suka kebanta ga Ahlulbaiti (a.s) bugu da kari kan saukan ayoyi da dama da suke ambaton falalar Ahlulbaiti (a.s), matsayinsu, yabo da fuskantar da al'umma zuwa gare su; wani zubin a ambaci darajojin a hade, kamar yadda ya zo cikin Ayar Mubahala (Surar Ali Imrana, 3: 61) da Ayar Ciyarwa cikin Surar Dahri da sauransu. Wani zubin kuwa a rarrabe kamar yadda ya zo cikin Ayar Wilaya (Surar Ma'ida, 5: 55).
Bari mu bijiro da sashen wadannan ayoyi - suna kuwa da yawa - wadanda suka yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s), domin bayani a kan falalarsu da matsayinsu, gami da kuma sharhi:
Ta Farko:Ayar Tsarkakewa
(إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً )

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa". (Surar Ahzabi, 33:33)
Hakika tafsirai da ruwayoyi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da Ahlulbaiti shi ne mutanen gidan Annabi (s.a.w.a) wadanda kuma su ne, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Bayani ya zo cikin littafin Durrul Mansur na Imam As-Suyudi cewa: (Al-Dabarani ya fitar da hadisi daga Ummu Salma cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da Nana Fadimatu cewa: "Taho min da mijinki da 'ya'yansa biyu", sai ta taho da su sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya lullube su da wani mayafi, sa'an nan ya sanya hannunsa bisansu ya ce:
"Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaitin Muhammadu (a wani lafazin zuriyar Muhammadu) to Ka sanya tsirarKa da albarkarKa wa zuriyar Muhammadu kamar yadda Ka sanya wa zuriyar Ibrahima, lalle Kai ne Abin godiya, Mai girma".
Sai Ummu Salma ta ce: "Sai na daga mayafin domin in shiga in kasance tare da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya janye shi daga hannuna ya ce: "Lallai ke kina tare da wani alheri"[1].
An ruwaito hadisi daga Ummu Salma, matar Annabi (s.a.w.a) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance a dakinta bisa wurin kwanciyarsa yana rufe da wani mayafi sakar Khaibara, sai Fadima ta zo da wata tukunya da abinci a cikinta. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ki kira mijinki da 'ya'yansa Hasan da Husaini". Sai ta kira su. Yayin da suke cin abincin sai aya ta sauko wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:
"…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkake-ku tsarkakewa"
Sai Annabi (s.a.w.a) ya kama gefen ragowar sashen mayafinsa ya rufe su da shi, sannan ya fitar da hannunsa daga mayafin ya nuna sama ya ce:
"Ya Allah! Wadannan su ne mutanen gidana, make-bantana, to Ka tafiyar da kazamta daga gare su kuma Ka tsarkake su, tsarkakewa".
Ya fadi hakan har sau uku. Ummu Salma ta ce: "sai na shigar da kaina cikin mayafin na ce: "Ina tare da ku Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "ke kina tare da wani alheri", ya fadi hakan har sau biyu [2].
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ci gaba da bayyana wa al'ummarsa ma'anar wannan aya mai girma, yana tsarkake fahimtarta ga wannan aya domin al'umma ta haskaka da ita ta kuma rayu a kan shiryuwarta. An ruwaito shi yana cewa:
"Wannan aya ta sauka ne a kan mutane biyar: Ni kaina, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini…."…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa [3] "
Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Ummul Muminina A'isha, tafsirin ayar da bayanin mutanen da ake nufi a ciki, kamar haka: (Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito wata safiya yana sanye da wani mayafi mai zane, wanda aka yi da bakin gashi, sai Hasan dan Ali ya zo, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya shigar da shi (cikin mayafin), sannan sai Husaini ya zo, ya shigar da shi, sannan Ali ya zo ya shigar da shi, sa'an nan sai ya ce:
"…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa [4] ".
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana wucewa ta kofar Fadima (a.s.) yayin da ya fito sallar asuba yana cewa:
"Salla! Ya mutanen babban gida (Ahlulbaiti), salla! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa " [5].
Hakan nan Alkur'ani yake magana a kan Ahlulbaiti (a.s) yana iyakance mutanen da suke ciki, tsarkaka manisanta daga dukkan dauda da sabo da zunubi da kuma son zuciya. Saboda haka halayen su abin koyi ne haka nan su kansu. Alkur'ani bai sanar mana da su irin wannan sanarwa ba, sai domin ya jaddada matsayi da mukaminsu ga al'umma, ya kuma ja hankulanmu zuwa ga koyi da su da komawa gare su domin fahimtar shari'a da karbar hukumce-hukumcenta daga wurinsu. Ta wannan hanyar, Alkur'ani ya ayyana mana mizani na aikace (wato ayyukan Ahlulbaiti) da ma'aunin da za mu koma gare shi yayin da ra'ayoyi suka sassaba, aka kuma sami bambancin fahimta da I'itikadi (wato abin da mutum ya yarda da shi).

Wannan kuwa a sarari yake idan muka duba yadda Alkur'ani ya jaddada cikin ayoyi da yawa ya kuma bijiro da Ahlulbaiti (a.s) a matsayin ja-gorori ga al'umman musulmi bayan Manzon Allah (s.a.w.a.).
Dogewar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi, wata da watanni bisa tsayuwa a bakin kofar Aliyu da Fadima (a.s.) yana kiransu da asuba zuwa salla, yana kiransu da Ahlulbaiti ba kome ba ne face sanar da al'umma mutanen da ake nufi da Ahlulbaiti, kana kuma yana fassara wa musulmi ayar tsarkakewa, yana sanar da su matsayin Ahlulbaiti (a.s) tare da jan hankulansu zuwa gare su da kuma wajabta musu kaunarsu da yi musu biyayya da jibinta al'amari gare su.
Dabarani ya ruwaito daga Abu Hamra' cewa:
"Na ga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa kofar Aliyu da Fadima tsawon wata shida yana cewa: "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa[6] ".
Fakhru al-Razi ya ambata a cikin tafsirinsa, Tafsir al Kabir, cewa bayan saukar ayar: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta", (Surar Daha, 20: 132), Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kan je (kofar) Aliyu da Fadima kowace safiya yana mai cewa: (lokacin) salla (ya yi), ya aikata hakan har na tsawon watanni.
Sannan kuma ya kawo hadisin Hammad bn Salma, daga Aliyu bn Zaid daga Anas cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana wucewa ta dakin Fadima koyaushe ya fito zuwa ga salla har na tsawon wata shida, yana mai cewa: "Salla! Ahlulbaiti! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa[7] ".

A cikin wannan akwai bayani da kuma nuni zuwa ga muhimmancin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya riki Ahlulbaiti (a.s) da shi, da kuma karfafawarsa wa musulmi cewa su (Aliyu, Fadima da 'ya'yansu) su ne mutanen gidansa (Ahlulbaiti), wadanda Allah Ya tafiyar da dukkan dauda ga barinsu, Ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Wannan muhimmancin an nuna shi ne bayan Allah Ya yi magana da ManzonSa cewa: "...kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta".
Sannan a sarari yake cewa daga abin da ayar: "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa", take nuni da shi da kuma amfani da lafazin maza ba lafazin mata ba da aka yi, wato (عنكم) da kuma (يطهِّركم), akwai nuni zuwa ga wadanda ake nufi, su ne wadannan mutane biyar din. Bayani ya zo a cikin Tafsirai cewa da Allah Yana nufin matan Annabi (s.a.w.) ne da Yayi amfani da kalmar (عنكنّ) da ta (يطهِّركنّ) da magana irin wacce ake yi wa mata.
A baya mun riga da mun ga Hadisin Mayafi lokacin da aka saukar da wannan aya ta tsarkakewa yayin da Ummu Salama taso shiga cikin wannan mayafi amma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata ke dai kina a matsayinka, kuma kina a kan alheri.
Hakan yana nuna mana rashin shigar matayen Annabi (s.a.w.a) cikin wannan aya ta tsarkakewa, kana kuma babu daya daga cikinsu da ta yi ikirarin saukar wannan aya a kansu, duk kuwa da cewa ayar ta falaloli da kuma matsayi mai girma ce.
Wannan ayar ta fitar da wata hanya wacce abin da take nuni da shi da abin da ta tattara suna da yalwar gaske. Tana jan hankulanmu zuwa ga batutuwa na asasi a rayuwar Musulunci domin kada mu sami rikitarwar fahimta balle ma manufofin Littafin Allah na gaskiya su tawaya. Allah Ya yi nufin gina al'umma bisa ginshikin tsarki da nisantar dauda da abin kunya sai Ya sanya Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani tushe abin dogara da kuma haske mai haskakawa. Lalle babu wani mutum da Alkur'ani mai girma ya siffanta shi da wannan siffa daga cikin musulmi, babu kuma wanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya siffanta shi da wannan siffar (siffar tsarki maras iyaka) face Ahlulbaiti (a.s).
Ta Biyu: Ayar Soyayya
(قُلْ لا أَسْألُكُم عَلَيْهِ أجْراً إلاّ المَوَدَّةَ في القُربى ومنْ يَقْتَرِفْ حسنةَ نزِدْ لهُ فيهَا حسْنًا إنّالله غفورٌ شَكُور)

"Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa, lallae Allah Mai gafara ne, Mai godiya". (Surar Shura, 42:23)
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana ko wane ne ake nufi da wannan aya mai albarka, kuma ko su waye kaunarsu da biyayya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu ya wajabta ga musulmi. Malaman tafsiri da hadisi da tarihi sun ruwaito cewa "Makusantar Annabi" wadanda ake nufi a wannan ayar su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).
Zamakhshari ya fada a cikin tafsirinsa al-Kashshaf cewa: "An ruwaito cewa mushrikai sun taru a wurin taronsu sai sashinsu ya ce wa sashi: "shin kuna ganin Muhammadu zai nemi wani lada a kan abin da yake kira gare shi? Sai aya ta sauka cewa: "Ka ce: "Ba ni tambaya ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta[8] ".
Sai Zamakhshari ya ce: "Kuma an ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka sahabbai sun tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda sonsu ya wajabta a kanmu". Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu".
A cikin Musnad na Imam Ahmad bin Hambal - da isnadinsa ambatacce -, daga Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da zance Allah Ta'ala cewa: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ya sauka, sai mutane suka tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Rasulallah! Su waye danginka wadanda sonsu ya wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'yayansu biyu[9] ".
Fakhrurrazi ya tabbatar da wannan zancen cikin Tafsirul Kabir bayan ya ambaci maganar Zamakhshari dangane da Alu Muhammad (dangin Muhammadu). Ga abin da yake cewa:
"Ni ina cewa dangin Muhammadu su ne wadanda al'amuransu suke tare da na shi (Annabi), to kuma duk wadanda kusancinsu yafi kusa da shi da kuma cika, to su ne aalu (dangin Annabi). Babu shakka cewa Fadima da Ali da Hasan da Husaini suna da mafi tsananin alaka da Manzon Allah (s.a.w.a.), wannan kuwa an nakalto ta hanyoyi daban. A saboda haka ya wajaba su kasance su ne Aalu".
Har ila yau an sassaba a kan ma'anar aalu, wasu sun ce su ne danginsa, wasu kuma sun ce su ne al'ummarsa. To idan mun dauke shi da ma'anar dangi, to su din dai su ne aalu din, idan kuma muka dauke shi da ma'anar al'umma[10] wadanda suka karbi kiransa to nan ma dai su ne aalu din. Don haka a bisa dukkan yanayi dai su aalu din ne dai.

To amma shigar waninsu cikin kalmar aal, a nan kan an samu sabani kan hakan. Marubucin al-Kashshaf ya ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka, mutane sun ce: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu, Fadima da 'ya'yansu biyu", sai ya tabbatar da cewa wadannan hudun su ne dangin Annabi (s.a.w.a), to idan kuwa hakan ya tabbata to ya wajaba su zama abin kebancewa da karin girmamawa. Ana iya tabbatar da hakan ta fuskoki kamar haka:
1. Fadin Allah (S.W.T) cewa: "face dai soyayya ga makusanta", kuma fuskar kafa hujja da ayar ya gabata.
2. Babu shakka cewa Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Fadima. An ruwaito shi yana cewa:
"Fadima yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita yana cutar da ni ".
Kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Aliyu, Hasan da Husaini (a.s.). To idan wannan ya tabbata, lallai kaunarsu ta zama wajibi a kan dukkan al'umma domin fadin Allah (S.W.T.) cewa:
"Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku...". (Surar Ali Imrana, 3:31)
"...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)
Da kuma fadinSa cewa:
"...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina....". (Surar Nur, 24: 63)
"Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah...." (Surar Ahzabi, 33: 21)
3. Addu'a ga dangin Manzo tana da wani matsayi mai girma, domin haka ne aka sanya wannan addu'ar ta zama cikamakin tahiya a cikin salla, wato: "Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kuma Ka yi jin kai ga Muhammadu da Alayen Muhammadu".
Ba a samun wannan girmamawa ga wani wanda ba su dangin ba. To duk wannan yana nuni da cewa kaunar alayen Muhammadu wajiba ce.
Imam Shafi'i yana cewa:
Ya kai mahayi tsaya a wannan kwari na Mina,
Ka kira mazaunin al-Nahidhi.
Da daddare yayin da alhazai suka wuce zuwa Mina,
Tamkar kogin Furatu mai yalwa da yawan ruwa.
Idan Rafdhu[11] shi ne son Zuriyar Muhammadu,
To mutane da aljannu su shaida ni Rafidhi ne[12] .
Ibn Munzir da ibn Abi Hatam da ibn Mardawihi da Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir daga Ibn Abbas sun ce: "Yayin da ayar: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka sai mutane suka ce: "Ya Manzon Allah su wane ne makusantanka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu[13] ".
A cikin Mu'ujam din dai ya inganta daga Imam Hasan dan Ali (a.s.) cewa wata rana yayin da yake huduba wa mutane ya ce:
"Ni ina daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya farlanta kaunarsu a kan kowane musulmi, inda Ya ce: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta".
(Ibn Abi Hatam ya fitar daga Ibn Abbas cewa: (lokacin da aka karanta wannan aya): (….ومن يقترفْ حسنة) "…kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau…) (Surar Shura, 42: 23), sai ya ce: "(hakan) shi ne kaunar Ahlulbaiti [14] ".
Alkur'ani mai girma ya tabbatar da tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da ayar tsarkakewa kuma ya fahimtar da al'umma matsayinsu da rawar da suka taka dangane da daukaka sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma. Da wannan ne kuma suka cancanci soyayya da riko zuciya daya wanda Alkur'ani ya yi umurni da shi a wannan ayar.
Abin da Alkur'ani yake nufi da wannan soyayya ba wai bege da doki da soyayya ta zuci kawai ba ne, domin babu wata fa'ida ga soyayya da kaunar da take cikin rai da zuciya, amma ba ta da wata bayyana a waje (a fili). Lallai tabbatar kauna da soyayya ga makusantan Manzon Allah (s.a.w.a.) yana samuwa wajen koyi da su da kuma rayuwa bisa turbarsu da lizimtar mazhabarsu da abin da ya fito daga gare su, da kuma daukar matsayinsu a al'umma matsayin shugaba kuma ja-gora.
Yayin da Alkur'ani yake sanya wannan ayar a bisa harshen Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma Yake umurtansa da cewa ya sanar da al'ummarsa da mutane bai daya cewa ba ya nufin samun wani lada ko sakayya daga gare su domin isar da sako da jure wahalhalun kira zuwa ga Allah da kuma shiryar da su, face soyayya ga makusantansa (s.a.w.a) da tsarkake zuciya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu, abin da kurum Alkur'ani yake nufi shi ne kiyaye tafarkin al'umma da tsare hanyarta ta akida da shari'a, domin al'umma ta fuskanci Ahlulbaiti bayan da Alkur'ani ya fuskantar da ita zuwa gare su.
Ba don lamuncewar da ake samu daga Ahlulbaiti (a.s) ba, da kuma ikon ja-gorancin al'umma a kan hanyar shiriya da lamunce hakan ba, da Alkur'ani bai saukar da soyayyar ba, kuma da ba a umurci Manzon Allah (s.a.w.a.) da ya sanya hakkinsa (ladansa) a kan al'umma shi ne kaunar Ahlulbaiti (a.s) ba.
Wannan tarin bayanai da muka kawo na maganganun malaman tafsiri da hadisi sun nakalto mana fassarar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wa wannan aya mai albarka, da sanya kaunar Ahlulbaiti (a.s) cikin zukata kuma ya sanya kaunar ta hakika ce mai tabbata cikin zuciyar ko wane musulmi, tana bayyana a cikin halayensa, tunaninsa da kuma begensa. Soyayyar nan tana kuma ayyana matsayarsa a kan Ahlulbaiti (a.s) da makiyansu da masoyansu da kuma bin tafarki da kuma abin da ya tabbata daga gare su na hadisi, fikihu, tafsiri, tunani, akida, shari'a da kuma tsarin aiki na jagoranci da siyasa.
Wannan lambar girma da daukaka tana da manufa da abin da take nuni da shi a kebance, wanda ya kamata musulmi su kiyaye shi kuma su riski zurfinsa.
Ta Uku: Ayar Mubahala
فَمَنْ حاجَّكَ فيهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءكَ ك مِنَ الْعِلْمِ فَقُل تَعالَوا نَدْعُ أبْنَاءَنَا وأبْنَاءَكُمْ ونِسَاءَنَا ونِسَاءَكُمْ وأَنْفُسَنَا أنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَةُ الله عَلى الكَذِبين

"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'an nan kuma mu kankantar da kai, sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". (Surar Ali Imrana, 3: 61)
Wani abu mai madauwamin tarihi wanda malaman tarihi da tafsiri sun ruwaito shi ya auku, wanda kuma yake nunawa al'umma irin girma da daukakan Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a.), su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) a wajen Allah (S.W.T.) da kuma matsayinsu a cikin wannan al'umma.
Wannan abin kuwa kamar yadda su malaman tafsiri da tarihin suka kawo shi ne cewa wata tawaga[15] ta kiristocin Najran ta zo domin ta yi jayayya da Manzon Allah (s.a.w.a.) don a gane waye yake kan gaskiya. Nan take sai Allah Ya umurce shi cikin wannan aya mai albarka da ya kira Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) ya fita da su zuwa wani kwazazzabo, ya kuma kira Kiristocin da 'ya'yansu da matansu su fito sannan a yi addu'ar Allah Ya saukar da azaba kan makaryata.
Zamakhshari a cikin Al-Kashshaf yana cewa:
"Yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kiraye su zuwa ga Mubahala[16] , sai suka ce: sai mun koma mun yi nazari. Da suka kebanta sai suka ce wa shugabansu; "Ya Abdul Masih! Me ka ke gani? Sai ya ce: "Wallahi, Ya ku jama'ar Nasara, kun sani cewa Muhammadu Annabi ne wanda aka aiko shi kuma hakika ya zo muku da bayani mai rarrabewa game da al'amarin sahibinku. Wallahi babu wata al'umma da ta taba yin mubahala da wani Annabi face babbansu ya halaka, karaminsu kuma ya gagara girma, to idan ko kun aikata hakan to lallai za mu halaka. Idan kun zabi riko da adddininku da zama bisa abin da kuke kansa to ku yi bankwana da mutumin na ku koma garinku.
Ko da gari ya waye sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito yana mai sammako, yana rungume da Husaini (a.s.) yana rike da hannun Imam Hasan (a.s.), Fadima (a.s.) kuwa tana biye da shi sannan shi kuma Aliyu (a.s.) yana bayanta, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu: "Idan na yi addu'a ku ce amin".
Ko da Kiristocin nan suka hango Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa da tasa tawagar, sai wannan Fadan da ke cikinsu ya ce musu: "Ya jama'ar Nasara! Wallahi ni ina ganin wasu fuskokin da idan Allah Ya so gusar da wani tsauni daga muhallinsa domin alhurmansu sai Ya yi. Don haka (ina shawartarku) da kada ku yi Mubahala da su don za ku halaka ya zamo babu wani kiristan da zai wanzu a bayan kasa har tashin kiyama".
To daga nan sai suka ce wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Abal Kasim! Mun yi shawara ba za mu yi mubahala da kai ba, mu bar ka a kan addininka, mu kuma mu tabbata a bisa addininmu".
Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu:
"Idan kun ki yarda da mubahala, to ku musulunta duk hakkin da musulmai ke da shi kuma kuna da shi, duk kuwa abin da yake kansu yana kanku". Amma sai suka ki, don haka sai ya ce musu: "To ni zan yake ku".
Sai suka ce : "Ba mu da karfin yaki da Larabawa, amma za mu yi sulhu da kai cewa ba za ka kai mana hari ba, ba za ka tsoratamu ba, ba za ka fitar da mu daga addininmu ba. Mu kuma za mu kawo riguna dubu biyu duk shekara, dubu daya cikin watan Safar dubu dayan kuwa cikin watan Rajab, da kuma sulken karfe guda talatin". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi sulhu da su akan hakan, sa'an nan ya ce:
"Na rantse da Wanda raina yake HannunSa, hakika halaka ta yi reto kan mutanen Najran, da sun yi mubahala (da mu) da an shafe su an mai da su birrai da aladu, da kuma kwazazzabon nan ya kama da wuta a kansu da kuma Allah Ya tuge Najran da mutanenta har tsuntsayen da ke bisa bishiyoyi, kuma da ba za a shekara ba face Nasara sun hallaka dukkansu".
Sannan Zamakhshari ya ci gaba da bayani kan tafsirin Ayar Mubahala da matsayin Ahlulbaiti (a.s) bayan da ya ba da shaidar matsayinsu mai girma da hadisin Ummul Muminina A'isha, ya ce:
"(Annabi) Ya gabatar da su (Ahlulbaiti) a kan kansa ne wajen ambato domin ya yi mana tambihi a kan taushin matsayinsu da kusancinsu (ga Allah), don ya nuna cewa su abin gabatarwa ne a kan kai kuma abin fansa da su. Wannan kuwa shi ne mafi karfin dalili a kan falalar Ashabul Kisa'i[17] (1).
Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi [18] (2).
Wannan yanayi (na fitowa domin Mubahala) yana nuna mana fitowar rundunar imani ne tana fuskantar rundunar shirka, sannan kuma wadanda suka fito (a sashin imani) su ne 'yan kan gaba wajen karbar shiriya, su ne magabatan al'umma kuma mafi tsarkin cikinsu, rayuka ne wadanda Allah Ya tafiyar da dauda ga barinsu kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa. Ba a mayar masu da addu'a, ba a kuma karyata wata maganarsu. Daga nan za mu fahimci cewa dukkan abin da ya zo mana daga Ahlulbaiti (a.s) yana gudana ne bisa wannan matsaya (ta tsarki da fifiko) sawa'un wani tunani ne ko shari'a ko ruwaya ko tafsiri ko shiryarwa da fuskantarwa. Domin su ne magaskanta cikin maganarsu da harkar rayuwarsu da kuma tafarkinsu.
Da Ahlulbaiti (a.s) ne Alkur'ani ya kalubalanci abokan gaba Musulunci, ya sanya masu jayayya da su su ne makaryata abubuwan bijirowar tsinuwa da azaba; "…sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata".
Shakka babu da ba don an lamunce mana tabbatuwa da kuma gaskiya cikin abin da yake fitowa daga gare su ba, da Allah bai ba su wannan daukaka ba kuma da Alkur'ani bai yi furuci da wannan ba.
Fakhrurrazi ya kawo cikin tafsirinsa Alkabir kwaton-kwacin abin da Zamakhshari ya ruwaito, inda tafsirinsu suka dace da juna a wannan matsayin. Sannan ya yi karin bayani a kan zancen Zamakhshari da cewa:
"Ka sani cewa wannan ruwaya daidai take da abin da aka daidaita a kan ingancinsa tsakanin ma'abuta tafsiri da hadisi[19] ".
Allama Tabataba'i ya ce wadanda ake nufi a wannan aya kuma wadanda Allah Ya yi nufin (amfani da su wajen) tsinewa abokan gabarsu, su ne Manzon Allah (s.a.w.a.), Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Ga abin da Allama Tabataba'in ya ce:
"Malaman hadisi sun hadu a kan ruwaito wannan ruwaya da samun karbuwarta, kuma ma'abuta manyan littattafai kamar su Muslim a cikin Sahihinsa da Tirmidhi a nasa Sahihin, sun tabbatar da wannan ruwaya, sannan malaman tarihi sun karfafa ta. Kana kuma malaman tafsiri sun hadu a kan kawo wannan ruwaya cikin tafsiransu ba tare da wata suka ba, ba kuma kokwanto. Haka nan kuma akwai malaman hadisi da tarihi kamar su Dabari da Abul Fida da Ibn Kathir da Suyudi da sauransu".
A cikin wannan aya mai albarka, Allah da ManzonSa Sun yi amfani da Ahlulbaiti (a.s) wajen yin Mubahala da abokan gaban Allah, to hakan kuwa yana sanar da al'umma matsayi da daukakan da suke da shi. Hakika ba don wannan kebantacciyar daukaka da suke da ita a wajen Allah ba, da kuma tsarki na musamman ma ba, da Manzon Allah (s.a.w.a.) bai kira wadannan taurari tsarkaka domin yin barazana ga makiya Allah da saukar da azaba da kuma lamunce amsa addu'arsu ba.
A cikin ayar akwai ma'anoni masu zurfi na harshen da aka yi amfani da shi cikin maganar wadanda lallai ne a yi la'akari da su, hakan kuwa shi ne danganta wadannan Taurari (Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini) da Annabi (s.a.w.a.), wato cewan da aka yi "'ya'yanmu" da "matanmu" da "kanmu".
Ba don faruwar wannan lamari da fitar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da wadannan Taurari tare da shi ba, da mai yiyuwa zukata su koma ga matan Annabi (s.a.w.a) wajen kalmar "matanmu", wajen kalmar "'ya'yanmu" kuwa zuwa ga Fadima da sauran 'ya'yan Ma'aiki (s.a.w.a.), sannan wajen kalmar "kanmu" kuwa zuwa ga zatin Annabi (s.a.w.a) mai tsarki shi kadai.
Amma fita da wadannan mutanen hudu da Annabi ya yi tare da shi koma bayan wasunsu, ya fassara mana cewa mafificiyar macen wannan al'umma kuma abin koyi gare ta ita ce Nana Fadima (a.s.), zababbun 'ya'yan musulmi kuwa su ne Hasan da Husaini (a.s.), don kuwa Alkur'ani ya dangantasu ga Annabi (s.a.w.a.) sai suka zama 'ya'yansa, kamar yadda aya ta nuna. Kana kuma Alkur'ani ya dauki Aliyu (a.s.) tamkar ran Manzo (s.a.w.a).

1. Tirmidhi juzu'i na 2 cikin "Manakib Ahlulbaiti" shafi na 308 daga Umar ibn Abi Salama, wanda ya ce: an saukar da ayar "…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" a gidan Ummu Salma. Daga nan sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kira Fadima, Hasan, Husaini da Ali ya rufe su da mayafi, ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaiti, don haka Ka tafiyar da kazamta daga gare su Ka tsarkake su tsarkakewa". Sai Ummu Salma ta ce: "Ya Manzon Allah shin ni ma ina daga cikinsu ne?, sai ya ce mata: "Ke dai kina a matsayinki, ke kina a kan alheri".
2. An ruwaito wannan hadisi cikin littafin Ghayat al-Maram daga Abdullah ibn Ahmad ibn Hambal ta hanyoyi uku daga Ummu Salama, haka nan ma cikin Tafsirin Tha'alabi…haka nan ma Ibn Mardawihi da Khadib daga Abi Sa'id Khudri da wannan ma'ana sai dai kawai 'yan canje-canje na lafazi. Haka nan kuma an ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram daga Abdullahi bn Ahmad bn Hambal daga babansa da isinadinsa zuwa ga Ummu Salama, dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i kan Ayar Tsarkakewa. Wanda kuma ya ke son karin bayani kan wasu masdarori na musamman kan tafsirin wannan aya da kuma gabatarwa kan Ahlulbaiti guda biyar (a.s.) to sai ya karin bayani da ke karshen wannan littafi.
3. Ibn Jarir da Ibn Abi Hatam da Dabarani sun ruwaito wannan hadisi daga Abi Sa'id Khudri, kamar yadda kuma aka ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram da Tha'alabi cikin tafsirinsa, a cikinsa Tirmidhi ya ruwaito shi kuma ya ingantar da shi, da kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Hakim, kuma duk sun ingantar da shi. Haka nan ma Ibn Mardawihi da Baihaki cikin Sunan dinsa ta hanyar Ummu Salma. Dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i.
4. Buhari da Muslim duk sun ruwaito ta hanyar A'isha/ Ghayat al-Maram, haka nan kuma Zamakhshari ya ambato shi cikin tafsirin al-Kashshaf ya yin da yake tafsirin Ayar Mubahala.
5. Ibn Mardawihi daga ibn Abi Shaibah da Ahmad da kuma Tirmidhi sun ruwaito kuma sun inganta shi, sannan kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Dabarani da Hakim, kuma sun inganta shi, da kuma ibn Mardawihi daga Anas. Mai son karin bayani sai ya duba Al- Mizan na Tabataba'i yayin da yake magana a kan Ayar Tsarkakewa.
6. Jami al Usul, juzu'i na 9, shafi na 156 ya nakalto daga Sahih Tirmidhi, haka nan ma Hakim ya ruwaito shi cikin Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 158, kuma ya inganta shi.
7. Fadhl Aalulbaiti na Takiyuddin Ahmad bn Aliyu al Makrizi (wanda ya rasu a shekara ta 845 bayan hijira), shafi na 21.
8. Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.
9. Ghayat Maram yayin tafsirin ayar.
10. Sanannen al'amari ga mai karatu cewa wannan fassara ta yi nisa ga hakikanin ma'anar kalmar, don kuwa ma'anar kalmar aal a cikin harshen Larabci a fili yake, babu yadda za a fassara kalmar aal da al'umma.
11. Rafdhu a wajen malaman Ahlussunna shi ne yarda da cewa Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) shi ne halifan Manzon Allah (s.a.w.a.) na farko bayan rasuwarsa. Kuma Rafidhi shi ne wanda ya yarda da hakan.
12. Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir, yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.
13. Ihya'ul Mait bi fadha'il Ahlilbaiti na Suyudi shafi na 8, kuma Suyudin ya ruwaito shi cikin Durrul Mansur , juzu'i na 6 shafi na 7 ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, sannan kuma Dabarani ma ya fitar da shi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 125. Haka ma Tabari ya ruwaito shi cikin Zakha'ir shafi na 25, yana cewa: "Ahmad ya fitar da shi cikin Munakib. Kamar yadda kuma Ibn Sabbag al-Maliki ya ruwaito shi daga Nabawiy daga Ibn Abbas, shafi na 29. Hakan nan kuma Kurdabi ya fitar da shi cikinsa Jami' al-Ahkam al-Kur'an da ruwayar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, juzu'i na 16, shafi na 21-22.
14. Tabataba'i daga Sheik Tusi.
15. Wannan tawaga ta kumshi manya-manyan shuwagabannin kiristocin Larabawa kamar haka: Abdul Masih, wanda ya kasance shugabansu, da kuma al-Ayhma, wanda ya kasance mai kula da al'amurran gudanarwa da ayyukan ibada, da kuma Abu Hatam ibn Alkama, wanda ya kasance bishof ne kana kuma kula da makarantunsu. Dubi Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki a sashin gabatarwar marubuci.
16. Yin 'yar kure tsakanin vangare biyu kan Allah Ya saukar da azaba a kan vangaren da ba ya kan gaskiya. A takaice dai yin la'ananneniya tsakanin vangarori biyu don gano wani vangare ne ya ke kan gaskiya.
17. Ashabul Kisa' (ma'abuta mayafi), suna ne da ake kiran mutanen da suka kasance tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) cikin mayafinsa inda daga baya aka saukar da Ayar Tsarkakewa a gare su. Su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda aka ambata a baya.
18. Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi.
19. Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a kan Ayar Mubahala.