Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

Ahlulbaiti (a.s.) Cikin Sunnar Annabi

Dukkan wanda ya bibiyi sunnar Manzon Allah (s) da tarihinsa na aikace da kuma alakarsa da mutanen gidansa wadanda nassin Alkur'ani ya kawo, sannan shi (Manzo) kuma ayyanasu (Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu ), zai san cewa mutanen wannan gida suna da wata rawar da za su taka a bangaren nauyin rike sako da kuma wayewar wannan al'umma. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mai tsare-tsare domin al'ummar tasa da kuma shirya da ita domin ta karbi wannan ni'ima ta Ahlulbaiti (a.s), da umurnin Allah (S.W.T.).
Hakika wannan yanki mai haske na tsare-tsaren Annabi (s.a.w.a), wadanda ya yi da umurnin Allah, ya soma ne da aurar da Fadima (a.s.) ga Imam Ali (a.s.), da dasa wannan itaciya mai albarka, domin rassanta su mamaye sansanin wannan al'umma, tsawon rayuwarta.
An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) yayin da ya aurar masa da Fadima (a.s.) cewa:
"Lalle Allah Madaukakin Sarki Ya umurce ni da in aurar maka da Fadima bisa sadaki gwargwadon nauyin miskalin azurfa dari hudu, shin ka yarda da hakan". Sai Aliyu (a.s.) ya ce: "Lalle na yarda da hakan, Ya Manzon Allah". Anas bin Malik ya ce: Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Allah Ya hada kanku, Ya arzurta kokarinku, Ya albakace ku, Ya kuma fitar da zuriya mai albarka". Sai Anas ya ce: "Wallahi, hakika kuwa Allah Ya fitar da zuriya mai albarka daga gare su ".
An ruwaito cewa yayin da Annabi (s.a.w.a) ya aurar da Fadima ga Aliyu (a.s.), sai ya shiga wajenta ya kira ta sai Ummu Aiman ta kawo kasko da ruwa a ciki, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi tofi a ciki sannan ya yayyafa a kanta da tsakanin nononta, sannan ya ce:
"Ya Allah! Ni ina nema mata tsarinKa da zuriyarta daga shaidan jefaffe". Sai kuma ya ce wa Ali (a.s.): "Miko min ruwa", sai Aliyu (a.s.) ya kawo masa, sai ya zuba a kansa da kuma tsakanin kafadunsa (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ina nema masa tsarinKa da zuriyarsa daga shaidan jefaffe".
A wata ruwayar kuma cewa aka yi, sai ya bukaci a kawo masa ruwa, bayan ya yi alwala da shi sai ya zuba a kan Aliyu da Fadima (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ka albarkace su cikin zuriyarsu[54] ".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana neman uzuri ga duk wani daga cikin sahabbai da ya zo neman a ba shi Fadima (a.s.), yana mai cewa:
"Hukumci bai sauko ba tukunna[55] ".
Hakika wannan kula ta Ubangiji da AnnabinSa ta aurar da Fadima (a.s.) ga Aliyu (a.s.) ta sanya aurar da ita bai faru ba face da umurni daga Allah (S.W.T.) domin wannan ya yi nuni ga matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kuma alherin al'umma da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake nufi da alakarsa da su. Wannan matsayi na su kuwa shi ne Alkur'ani mai girma ya fassara, haka nan ma sunnar Annabi (s.a.w.a) mai daraja.
Watakila hasken da muke tsinkaya daga ruwayoyi da hadisai Manzon Allah (s.a.w.a.) da Ahlulbaiti (a.s) (wadanda kuwa masu yawa ne) suna riskar da mu ne irin zurfaffar kula ta Allah da ManzonSa (s.a.w.a) wajen gina wannan gida, da yawaita soyayya da albarka da kula gare shi. Domin mutanen wannan gida su zama ja-gororin al'umma cikin rayuwarsu da kuma hanyoyin tsirarsu daga bala'u da kuma kasancewa tsari da makomat hadin kanta yayin da ta rarraba, kamar yadda ruwayoyi da hadisai suka yi nuni da hakan.
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana danganta zuriyar Aliyu da Fadima (a.s.) da kansa, yana cewa: "Lalle su zuriyata ne 'ya'ya ne, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana hakan da cewa:
(فَمَنْ حاجَّكَ فيهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءكَ ك مِنَ الْعِلْمِ فَقُل تَعالَوا نَدْعُ أبْنَاءَنَا وأبْنَاءَكُمْ ونِسَاءَنَا ونِسَاءَكُمْ وأَنْفُسَنَا أنْفُسَكُمْ )

"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku". (Surar Ali Imrana, 3: 61)
Abin nufi da 'ya'yansa a wannan aya su ne Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda maganganun malaman tafsiri da ma'abuta tarihi suka sanar da mu.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karfafa wannan ma'anar wa al'ummarsa sau da yawa, bari mu ambaci kadan daga cikinsu. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Allah Ya sanya zuriyar kowane Annabi daga tsatsonsa, (ni kuma) Ya sanya zuriyata cikin tsatson wannan", yana nufin Aliyu (a.s.) [56] .
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana rungumar Hasan da Husaini (a.s.), yana cewa:
"Dukkan 'ya'yan wani uba dangantakarsu ta ubansu ce, ban da 'ya'yan Fadima, ni ne ubansu, da ni ake dangantasu". Imam Ahmad ya fito da wannan hadisin cikin al-Manakib[57] .
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) yana karfafa matsa-yin Ahlulbaiti (a.s) a kowani muhimmin lokaci, domin al'umma ta koma gare su, ta lizimci tafarkinsu, ta kuma yi riko da soyayyarsu. A ruwayoyi da dama, muna samun cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya nuna mana su a matsayin tudun tsira ga wannan al'umma, yana gwama su da Alkur'ani, yana kuma sanya rawar da za su taka a fagen akida da rike sakon Musulunci, mai lizimtar Littafin Allah ne, ba sa rabuwa da shi. Hakan kuwa don al'umma ta fuskanto su wajen fahimtar Alkur'ani mai girma, da ciro ma'anoninsa da hukumce-hukumcensa.
Littattafan hadisi da tarihi sun taru bisa kawo hadisin Annabi (s.a.w.a) da ake kira da Hadisin Nauyaya Biyu (Hadith al-Thakalain). Musulmi sun ruwaito wannan hadisi duk da bambance-bambancen mazhabobinsu na siyasa da fikihu. Za mu ambace shi a nan tare da sashin isnadinsa (maruwaitan da suka ruwaito shi), kamar yadda masu ruwaya da malaman hadisi suka nakalto
1- Hadisus Sakalain (Nauyaya Biyu):
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Na kusata da a kira ni in kuma amsa, amma ni mai bari muku abubuwa masu nauyi guda biyu ne, su ne kuwa: Littafin Allah Mai girma da Daukaka, da kuma zuriyata. Littafin Allah wata igiya ce da aka sako ta daga sama zuwa kasa, zuriyata kuwa su ne mutanen gidana (Ahlulbaiti). Allah Mai tausasawa Ya ba ni labari cewa su biyun ba za su taba rabuwa ba har abada har sai sun iske ni a bakin tafki. To ku lura da yadda za ku rike su a bayana[58] ".
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto cikin littafinsa mai suna al-Ithafu bi hubbil Ashraf, cewa:
"Muslim da Tirmizi sun kyautata shi (hadisin), haka ma Hakim shi ma ya ruwaito shi, lafazin Muslim kuwa daga Zaid bn Arkam cewa ya yi: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya mike a cikinmu domin ya yi mana huduba

sai ya yi godiya ga Allah ya yi yabo gare Shi, sannan ya ce:
"Bayan haka, Ya ku mutane, ni dai mai mutuwa ne, kuma zan amsa kiran manzon Ubangijina. To amma na bar muku wasu nauyayan abubuwa guda biyu tare da ku; na farkonsu Littafin Allah, shiriya da haske na cikinsa, to ku kama Littafin Allah ku yi riko da shi". Sannan sai ya ce: "Da Ahlulbaitina, ina gama ku da Allah dangane da Ahlulbaitina[59] ".
Al-Shibrawi din kuma ya nakalto cewa: "A wata ruwayar kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa ya yi: "Ni mai bari muku al'amurra guda biyu , ba za ku bata ba idan har kun bi su, su ne kuwa; Littafin Allah da Ahlulbaitina". A wata ruwayar kuma (aka cika da cewa) "ba za su rabu ba har sai sun iske ni a bakin tafki, to ku kula da yadda za ku rike su a bayana[60]".
Ya kara da cewa: "Ibn Hajar ya fada cikin Sawa'ikul Muhrika cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya ambaci Alkur'ani da zuriyarsa da cewa "Nauyaya Biyu" ne saboda nauyin dukkan wani mutum shi ne abu mafi muhimmanci a gare shi, kuma wadannan guda biyu haka suke. Domin kuwa kowane daga cikinsu taska ce ta ilmummukan addini da sirrorin hankali irin na shari'a, domin haka ne ma aka kwadaitar da koyi da su. Wani kaulin kuma ya ce an ambace su da "Nauyaya Biyu" ne domin wajibcin kiyaye hakkokinsu. Sannan kuma wanda kwadaitarwar ta tabbata a gare su, su ne masana Littafin Allah masu riko da sunnar ManzonSa (s.a.w.a), domin su ne wadanda ba su rabuwa da Littafin har zuwa tabki[61] ".
Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya nakalto cikin tafsirinsa Ala'u al-Rahman fi tafsiril Kur'an cewa:
"Haka nan ma kamar hadisin Sakalain wanda yake an tabbatar da ingancinsa kamar yadda 'yan'uwanmu Ahlul Sunna suka ambace shi cikin littattafansu suka kawo ruwayarsa daga sahabbai wadanda suka ji shi daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.):
"Ni mai bari muku Nauyaya guda biyu ko kuma halifofi guda biyu, Littafin Allah da zuriyata, Ahlulbaitina, wadanda idan kun yi riko da su ba za ku bata ba har abada, su ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".
(1). Imam Ali bn Abi Talib (a.s) (2). Abdullahi bn Abbas.
(3). Abu Zar Giffari (4). Jabir al-Ansari.
(5). Abdullahi bn Umar (6). Hudhaifa bn Usaid.
(7). Zaid bn Arkam. (8). Abdurrahman bn Awf.
(9). Dhamratul Aslami. (10). Amir bn Laili.
(11). Abu Ra'fi'. (12). Abu Huraira.
(13). Abdullah bn Handab (14). Zaid bn Thabit.
(15). Ummu Salama. (16). Ummu Hani.
(17). Khazima bn Thabit. (18). Sahl bn Sa'ad.
(19). Adi bn Hatam. (20). Ukba bn Amir.
(21). Abu Ayyub Ansari. (22). Abu Sai'd al-Khudri.
(23). Abu Shuraih Khuza'i. (24). Abu Kadama Ansari.
(25). Abu Laili. (26). Abu Haitham bn Al-Tayhan.
Allama al-Balagi ya ci gaba da cewa: Wadannan su ne muka riga muka ambaci sunayensu bayan Ummu Hani. Kowannensu ya ruwaito shi, shi kadai, kamar wadanda suka gabace shi, sun tsaya a dandalin Kufa tare da mutum bakwai Kuraishawa, suka tabbatar da cewa sun ji wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.), adadinsu kuwa shi ne talatin da uku.
Kuma abu Nu'aim Al-Isfahani ya ruwaito shi cikin littafin Munkabatu al-Mudahharin da isnadi daga Jabir bn Mad'am da kuma wani isnadin daga Anas bn Malik da Al-Barra'u bn Azib, haka nan Muwaffak bn Ahmad ya ruwaito shi daga Amr bn al-As.
Da wuya a sami wani littafin hadisi babba ko karami ko littafin falaloli da Ahlussunna suka rubuta wanda bai kawo wannan hadisin ba, daga farkon wadanda suka kawo hadisin daga hadda da kuma zukatan mahaddata har zuwa takardun malaman hadisi. Kuma bai gushe ba ana ruwaito shi daga sahabbai guda ko masu yawa. Ta yiwu ma a ruwaito shi daga sama da sahabbai ashirin a littafi guda, ko dai a game kamar yadda ya zo cikin littafin Sawa'ikul Muhrika, ko kuma da isnadi rarrabe kamar yadda ya zo cikin littattafan al-Sakhawi da Suyudi da Samhudi da dai sauransu".
Sannan sai ya ce:
"Malaman Imamiyya sun ruwaito shi cikin litattafan-su da isnadinsu masu maimaita juna daga Imam Bakir, Ridha da Kazim da Sadik (a.s.) daga iyayensu (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma wadansu isnadan na daban daga Amirul Muminina (a.s) da Umar da Ubayyu da Jabir da Abu Sa'id da Zaid bn Arkam da Zaid bn Thabit da Huzaifa bn Usaid da Abu Huraira da sauransu, dukkanninsu sun ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) [62].
A cikin Musnad na Ahmad bn Hambal, ya ruwaito ta hanyar Abi Sa'id al-Khudri daga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ni na kusanta da a kira ni in amsa, ni kuma mai barin nauyayan abubuwa ne guda biyu tare da ku, Littafin Allah Mai Girma da Daukaka da kuma Ahlulbaitna, shi Littafin Allah igiya ce da aka sako daga sama zuwa kasa. Kuma lalle Mai Tausasawa Masani, Ya ba ni labarin cewa ba za su taba rabuwa da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki, don haka ku kula da yadda za ku rike su a bayana[63]".
Haka nan kuma idan muka duba za mu ga kusan dukkan maruwaita sun ruwaito wannan hadisi da ke gwama Ahlulbaiti (a.s) da Littafin Allah Mai Tsarki. Daga wannan ne musulmi za su fahimci cewa Ahlulbaiti (a.s) su ne makoma baicin Littafin Allah kuma su ne aka bar wa amanar Littafin har su isa ga tabki.
2- Hadisus Safina (Hadisin Jirgin Ruwa):
Yayin da Hadisus Sakalain yake gwama Ahlulbaiti (a.s) da Alkur'ani waje guda domin nauyin da aka dora musu na bayyana Alkur'anin da kwaranye boyayyun abubuwansa da asirorinsa da abubuwan da ke kewaye da shi, to wannan hadisi na Safina kuwa yana bayyana wa al'umma ne cewa su Ahlulbaiti (a.s) su ne jirgin tsira, kuma hanyar kubutar wannan al'umma bayan Manzon Allah (s.a.w.a.). Domin haka, lallai rashin riskan wannan jirgin da rashin hawansa, zai ja wadanda suka ki shiga jirgin zuwa ga nutsewa da halaka. Domin kin binsu, kin bin ja-gora zuwa gabar shiriya da tsira ne.
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto daga Rafi Maulan Abu Zarri, ya ce:
"(Wata rana) Abu Zar (r.a.) ya hau dokin kofar Ka'aba, ya kama marikin kofar ya dogara da shi, sai ya ce: "Ya ku mutane, wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuma bai sanni ba, to ni ne Abu Zar, na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ahlulbaitina tamkar jirgin Nuhu suke, wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya ki hawa ya fada wuta".

Na kuma ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ku sanya Alayena (a gareku) matsayin da kai yake da shi a jiki, kuma matsayin idanu ga kai. Domin shi jiki baya shiryuwa sai da kai, shi kuma kai ba ya shiryuwa sai da idanu[64]".
Abu Nu'aim[65] ya ruwaito ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin (Annabi) Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawa ya nutse (ya halaka) [66]".
An ruwaito ta hanyar Anas bn Malik, cewa, ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Abin sani kawai shi ne cewa, misalin Ahlulbaitina a cikinku, kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka[67]".
Suyudi ma ya ruwaito wannan hadisin cikin littafinsa Durrul Mansur karkashin tafsirin fadin Allah Madauka-kin Sarki cewa:
(وإذ قُلنَا آدخُلوا هَذِه القَرْيةَ فَكُلُوا مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ رَغَداً وادْخُلُوا البابَ سُجَّداً وقُولوُا حِطَّة نَغْفِر لكُمْ خَطاياكُمْ)

"Kuma lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alkarya, sa'an nan ku ci daga gare ta, inda kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga kofa kuna masu tawali'u, kuma ku ce: "Kayar da zunubai" Mu gafarta muku laifukanku".
Inda ya ce: "Ibn Abi Shaiba ya fitar da hadisi daga Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya ce:
"Abin sani dai, misalinmu (Ahlulbaiti) cikin wannan al'umma kamar misalin jirgin Nuhu ne, kuma kamar Kofar Yafuwa (Hidda) ce[68]".
Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin littafin Kanzul Ummal (juzu'i na 6 shafi na 216) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka, kuma tamkar kofar Hidda ne ta Bani Isra'ila". Sannan ya ce Dabarani ma ya ruwaito wannan hadisi daga Abu Zarri[69].
3- Hadisin Aminta Daga Sassabawa:
A cikin wannan hadisin, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) ke takawa a fagen akida da siyasa. Domin mafi hadarin abin da yake samun al'umma shi ne rarraba da sabawa cikin ra'ayi da akida da kuma fuskantarwa ta siyasa. Don haka ne ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana tsoratar da al'ummarsa wannan fitinar, ya kasance yana tsare-tsare saboda hadin kanta da riko da juna ta bangaren tunani da siyasa. Kana kuma yake fuskantar da al'ummar tasa zuwa ga lizimta da riko da Ahlulbaitinsa da komawa gare su. A saboda hakan ne kuma, ya siffanta su da cewa su masu lizimtar Alkur'ani da kiransa ne, kuma ba za su rabu da juna ba har ranar tashin kiyama. Ya kuma siffanta su da cewa su jirgin tsira ne, kuma kofar yafuwar zunubbai. To a nan kuma yana siffanta su ne da cewa su ne mattara, kuma su ne madogara mai hada kan wannan al'umma ta musulmi ne, da kuma cewa riko da su da rayuwa bisa tafarkinsu lamuni ne daga rarraba da sabawa.
Al-Dabarani ya kawo hadisi daga Ibn Abbas (r.a.) cew, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Taurari aminci ne ga mazauna kasa daga nutsewa (halaka), Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazauna kasa daga sassabawa (rarrabuwa) [70]".

Muhibbuddin Dabari ya ruwaito daga Aliyu (a.s.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Taurari aminci ne ga mazowa sama, idan taurari suka tafi, mazowa sama sai su tafi, Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazowa kasa, idan Ahlulbaitina sun tafi, mazowa kasa sai su tafi".
Sai al-Dabarani ya ce: "Ahmad bn Hambal ya ruwaito wannan hadisi cikin al-Manakib[71] .
4- Hadisul Kisa'i (Hadisin Mayafi) [72]:
Hadisin Mayafi shi ne hadisin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) yayin da Ayar Tsarkakewa ta sauka. Mun riga da dai mun gabatar da wannan hadisi kuma mun yi magana a kan shi tare da kawo ra'ayuyyukan wasu malaman tafsiri, da kuma ruwayoyin da suka yi batun wadannan wadanda aka tsarkake a cikin babin "Ahlulbaiti (a.s) Cikin Alkur'ani". To amma a nan za mu kawo wasu ruwayoyi ne daban domin karfafa wannan fikirar da kuma kafa wannan manufar da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake da ita wajen yin hakan (wato lullube su da mayafinsa da kuma yi musu addu'a).
Hanyoyin da wannan hadisi ya zo suna da yawan gaske cikin littattafan hadisi da ruwaya da tafsiri, to amma za mu ambaci wasu daga cikinsu ne kawai:
"Dangane da abin da aka ruwaito daga Ummu Salama, matar Annabi (s.a.w.a), Imam Ahmad ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa har ya zuwa ga Ummu Salama, inda ta ce: "Wata rana Manzon Allah (s.a.w.a.)

yana dakina, sai wani hadimi ya zo ya ce: 'Aliyu da Fadima na nan bakin kofa', sai ta ce: sai Annabi (s.a.w.a) ya ce da ni: "Ki tashi ki kauce wa Ahlulbaitina". "Sai na tashi na kauce gefe guda. Sai Aliyu da Fadima da Hasan da Husaini suka shigo. A yayin nan Hasan da Husaini suna yara kanana, sai Annabi (s.a.w.a) ya dauke su ya dora su a kan cinyarsa, ya sumbace su, ya rungume Aliyu da hannunsa, Fadima kuma da dayan, sannan ya lullube su da wani bakin mayafi, ya ce:
"Ya Allah! Zuwa gare Ka ba zuwa wuta ba, ni da Ahlulbaitina". Sai Ummu Salama ta ce: 'Da ni ya Manzon Allah', sai ya ce: "Na'am da ke[73]".
Al-Wahidi ya ruwaito cikin littafinsa Asbabun Nuzul marfu'i ta hanyar Ummu Salama (r.a.) ta ce: (Wata rana Annabi (s.a.w.a) ya kasance a dakinta sai Fadima (a.s.) ta zo da tukunya da wani abinci na alkama a ciki, sai ta shiga da shi. Sai yace da ita: "Ki kira mini mijinki da 'ya'yanki biyu". Sai Ali da Hasan da Husaini suka zo, suka shiga suka zauna suna cin abincin, Annabi (s.a.w.a) kuma yana zaune a kan wani benci, a kan wani mayafi wanda aka saka a Khaibara. Sai Ummu Salama ta ce: Ni kuma ina cikin dakin, kusa da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya kama mayafin ya lullube su da shi, sannan ya ce:
"Ya Allah! Mutanen gidana, kebantattuna (kenan), to Ka tafiyar da kazanta daga gare su Ka tsarkake su, tsarkakewa".
Sai ta ce: Sai na shigar da kaina, na ce: "Ni ma ina tare da ku, Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "Ke kina tare da alheri, ke kina tare da alheri". Sai Allah Mai girma da Daukaka Ya saukar da ayar:
إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً

"....Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa[74]". (Surar Ahzabi, 33:33)
5- Hadisin Soyayya:
Mun riga da mun yi magana kan Hadisin Soyayya wajen tafsirin Ayar Soyayya, kuma mun ambaci wasu masu ruwaya da suka ruwaito shi da kuma daga wajen wadanda suka ruwaito shi. A nan za mu sake ambaton hadisin ta hanyoyin daban ne, kuma zai kasance mai amfani mu ambaci sashin abin da ya taho daga Annabi (s.a.w.a) a kan son Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu a wasu ruwayoyin na daban.
(Imam Ahmad da Dabarani duk sun ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da Ayar Soyayya, wato "Ka ce: "Bana tambayarku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka, sai mutane suka ce: Ya Manzon Allah, su wane ne makusanta wadanda soyay-yarsu ta wajaba a kanmu?, sai yace:
"Aliyu da Fadima da 'ya'yansu guda biyu".
Al-Bazzaz da Dabarani sun ruwaito cewa Hasan dan Aliyu (a.s.) yayi huduba wata rana yana cewa: "Wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuwa bai sanni ba, to ni ne Hasan dan Muhammadu (s.a.w.a). Ni ne dan Mai albishir, ni ne dan Mai gargadi, ni ne dan mutanen gida wadanda Allah Ya farlanta son su a kan kowane musulmi, Ya kuma saukar a kansu (da ayar), "Ka ce: Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa". To aikata kyawawan shi ne soyayyarmu, Ahlulbaiti[75] ".
Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa:
"....wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".
Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa:
"...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".
Inda ya ce: "Soyayyar ta Alayen Muhammadu (s.a.w.a) ce [76]".
Hadisan da suka zo game da so da kaunar Ahlulbaiti (a.s) da kuma yin musu da'a da lizimtarsu, ba za su kirgu ba cikin wannan dan karamin littafi, sai dai mun zabi sashi ne daga cikinsu kawai, don kuwa kowanne daya daga cikinsu (Ahlulbaiti) (a.s.) rana ce mai haske a cikin littattafan hadisi da ruwayoyi.
To amma domin a kara arzurta mai karatu da kara karfafa abin da zai kara masa sanin Ahlulbaiti (a.s) da kuma karfafa dangantaka da su, da mai da shi mai ta'allaka da su, mai rayuwa bisa tafarkinsu, don ya samu nasarar samun cetonsu, bari mu sake ambaton wasu daga cikin hadisan da suka zo game da su:
(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin al-Awsad daga ibn Hajar (r.a.) cewa; "Karshen abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya furta shi ne: "Ku wakilce ni cikin Ahlulbaitina[77] ").
(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin Al-Awsad daga Jabir bn Abdullah (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba, na ji yana cewa:
"Ya ku mutane! (Duk) wanda ya fusata mu, mu Ahlulbaiti, Allah Zai tashe shi ranar kiyama yana bayahude[78]".
(Muslim da Tirmizi da Nasa'i duka sun ruwaito daga Zaid bn Arkam cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Ina tunatar da ku Allah game da Ahlulbaitina[79] ".
Alkhatib ya fitar a cikin littafin Tarihinsa daga Aliyu (r.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Cetona ga al'ummata, na ga wanda ya so Ahlulbaitina[80]".
6- Wasu Ruwayoyi Na Daban
Kamar dai yadda muka bayyana, hadisai da ruwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) game da Ahlulbaitinsa (a.s.) suna da yawan gaske, kuma ba za su kidayu ba a wannan karamin littafin. Malamai da masu hadisi sun kebance musu litattafai, ko kuma fasulla a littattafan hadisai, ko kuma sun ambata a wuraren da suka dace cikin litattafan tafsiri da ruwaya. Ga kadan daga ciki:
"Mu Ahlulbaiti ba a gwada mu da kowa[81]".
A cikin wannan hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mukamin Ahlulbaiti (a.s) ne, da kuma matsa-yinsu madayanci, domin ya sanar da al'umma mahal-linsu, ya kuma shiryar da ita zuwa ga riko da su da lizimtar hanyar su a bayansa, domin a auna su da wasu wadanda ba su ba, don a gani.
A cikin wani hadisi na daban kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana magana ne kan Ahlulbaitisa (a.s.), inda yake cewa:
"Mu Ahlulbaiti, Allah Ya zaba mana lahira bisa ga duniya, kuma lalle Ahlulbaitina za a nuna musu son kai da tsanani da kora cikin garuruwa, har wasu mutane za su zo ta nan - sai ya yi nuni da hannunsa ta gabas - ma'abutan bakar tuta, za su tambayi hakki, ba za a ba su ba, za su yi yaki kuma su yi nasara. Za a ba su abin da suka so kuma ba za su karbe shi ba har su mika ta (tutar) ga wani mutum daga Ahlulbaitina, har sai ya cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. To duk wanda ya riski wannan ya taho musu ko da da jan ciki ne a kan kankara[82] ".
(Dailami ya kawo hadisi daga Abu Sa'id (r.a.) cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Fushin Allah ya tsananta kan wanda ya cutar da ni dangane da Ahlulbaitina[83]".
(Daga Aliyu (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ku yi wa 'ya'yanku tarbiyya kan halaye guda uku: son Annabinku da son Ahlulbaitinsa da kuma karatun Alkur'ani, domin mahaddatan Alkur'ani na cikin inuwar Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa, tare da AnnabawanSa da ZababbunSa[84]").
(Dabarani ya ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an tambaye shi abubuwa hudu: Kan rayuwarsa, yadda ya karar da ita; da jikinsa, yadda ya tsufar da shi, da dukiyarsa, yadda ya kashe ta da inda ya same ta da kuma soyayyarmu, Ahlulbaiti [85]").
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana shiryar da al'ummarsa zuwa ga Ahlulbaitinsa, yana kuma bayyana matsayinsu na ilmi, da kuma fuskantar da al'ummar zuwa gare su yayin da fitinu suka tsananta, ra'ayoyi kuma suka sassaba. Yana gwama su da Littafin Allah, domin su ne malamai masu bayyana abin da Alkur'ani ya kunsa, masana hakikaninsa da abubuwan da ya tattara.
(Dabarani ya fitar da hadisi daga Al-Mudallabi bn Abdullahi bn Handabi daga babansa, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba a Juhfa, ya ce:

"Ashe ban fi ku cancanta ba a kan kanku", sai suka ce: "Haka nan ne Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "To ni mai tambayar ku ne kan abubuwa biyu: kan Alkur'ani da Ahlulbaitina [86])").

Alkur'ani Mai Girma A Wajen Malaman Mazhabar Ahlulbaiti (a.s)
"Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika masu kiyayewa ne gare shi". (Surar Hijr, 15: 9)
Alkur'ani littafin Allah ne da wahayinSa abin saukarwa a kan AnnabinSa mai daraja, Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w.a). Littafin da Allah Ya kiyaye shi daga jirkita da gurbata. Wannan wahayin Allah tsarkakakke, wanda hannun mai jirkitawa bai taba shi ba, duk wata barna bata samunsa, ko ta baya ko ta gaba. Shi a yau yana nan kamar yadda ya sauko wa Manzo Amintacce (s.a.w.a), ba tare da wata tawaya ko kari ba. Shi ne mabubbugar shari'a, daga gare shi ake fitar da hukumce-hukumce, shi ne ma'auni sunna, magwajin fahimta da tunani, shi ne mabubbugar wayewar ilmomin Musulunci kana kuma tushen alherin dan'Adam da tsirarsa.
Hakika musulmi sun zazzaga da Alkur'ani tsakanin-su, daga tsara zuwa wata tsarar, suna nakaltar sa da kiyayewa da kula da shi kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya saukar da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.). Wannan kuwa shi ne abin da musulmi suka dace a kai, kamar yadda suka hadu a kan karyata ruwayoyi raunana na karya wadanda suka sabawa wannan ijma'i na malamai kan rashin gurbatan Alkur'ani ta kowane bangare.
Babban malamin tafsirin nan wanda ya rubuta shahararren littafin tafsirin nan na Majma'ul Bayan fi (65)

Tafsiril Kur'an, Allama Shaikh Abu Ali al-Fadhl bn Hasan Dabrisi[87] (Allah Ya daukaka mukaminsa), wanda ake daukar tafsirinsa a matsayin mabubbuga kana abin komawa ga malamai da masu tafsiri, ya ce:
"Akwai irin wadannan maganganu (marasa tushe) kan kari ko ragi cikin Alkur'ani, da ba sa ma bukatan magana a kansu. To amma dangane da kari, an hadu kan cewa rashin ingancin hakan, amma batun ragi, wasu jama'a daga cikin abokanmu da wasu mutane daga cikin 'yan Sunna sun ruwaito cewa akwai canji ko tawaya a cikin Alkur'ani. To amma ingantacciyar magana a gurinmu ita ce sabanin hakan (wato babu wata tawaya ko ragi a cikin Alkur'ani), hakan kuwa shi ne abin da Murtadha[88] (Allah Ya tsarkake ruhinsa) ya bayyana ya kuma yi bayani a kai. A wurare da dama ya ambata cewa ilimin da ake da shi kan ingancin nakalto Alkur'ani kamar ilmin da ake da shi kan garuruwa, manyan abubuwan da suka faru, shahararrun littattafa da rubutattun wakokin larabawa, lallai an sami kula mai tsanani, bukata kuwa ta tabbata kan nakaltar Alkur'ani da kiyaye shi. Bukatar da kular sun kai matsayin da nakalto shahararrun littattafa da wakokin da muka ambata ba su samu ba, domin Alkur'ani mu'ujizar annabta ne, a nan ake daukar ilmomin shari'a da hukumce-hukumcen addini. Malaman Musulunci sun kai matuka wajen kiyaye shi da kare shi har sukan san duk abin da a ka saba cikinsa game da li'irabinsa, kira'arsa, haruffa da kuma ayoyoyinsa, to ya ya zai yiwu a ce an jirkita shi ko kuma an tauye shi duk da wannan kula mai tsanani da kuma tsarewa matsananciya..."
Ya kuma kara da cewa: "Lalle ilmi a kan tafsirin Alkur'ani da sassaninsa da kuma ingancin nakalto shi kamar ilmi ne a kan jumlarsa, kuma hakan yana bisa tafarkin abubuwan da aka sani ne bisa larura cikin littat-tafai wallafaffu, kamar littafin Sibawaihi da Al-Mazanni. Masu kula da wannan sha'ani (nahawu) sun san littattafan nan a fasalce tamkar sanin da suka yi musu a jumlace, ta yadda da wani zai shigar da wani babi na nahawu cikin littafin Sibawaihi, wanda da baya ciki, to da sun gane da kuma fahimtar cewa an sanya shi ne cikin littafin daga baya, ba daga cikin asalin littafin yake ba, haka nan ma yake game da littafin Al-Mazanni. Kuma sananne abu ne cewa kula da nakalin Alkur'ani da tsare shi, yafi gaskata bisa kula da tsare littafin Sibawaihi da kuma Diwanin mawaka".
Ya kuma sake cewa: "Shi Alkur'ani ya kasance a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) a tare yake a wallafe kamar yadda yake a yau. Ya kafa hujja da cewa Alkur'ani ya kasance ana darasinsa ana kuma haddace shi a wancan zamani har aka ayyana wata jama'a cikin sahabbai da cewa sun haddace shi, da kuma cewa ana bijiro da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) ana karanta masa, sannan kuma wata jama'a daga cikin sahabbai kamar su Abdullahi bn Mas'ud da Ubayyu bn Ka'ab da sauransu, sun sauke Alkur'ani gaba ga Annabi (s.a.w.a) sau da yawa. Duk wannan yana nunawa cewa shi Alkur'ani ya kasance tararre ne jerarre, ba yankakke ba, ba kuma a watse yake ba. Ana riskar wannan hakika kuwa ba tare da bukatar wani dogon tunani ba. Sayyid Murtadha ya ci gaba da cewa wanda ya saba wa wannan ra'ayi daga cikin Imamiyya da Hashawiyya, to ba a dogaro da wannan sabawa ta su domin sabawa da wannan ra'ayi abin dangantawa ne ga wasu mutane daga cikin ma'abuta hadisi wadanda suka nakalto hadisai masu rauni, amma suna zaton ingantattu ne. Kuma ba a barin abin da aka tabbatar da ingancinsa domin irin wadannan raunanan hadisai[89] ".
Sannan kuma sai ya ce:
"Abin da ya shahara a wajen malaman Shi'a da masu bincikensu, kai ba ma kawai shahara ba har ma babu jayayya a cikinsa, shi ne rashin ragi ko kari cikin Alkur'ani[90]".
Shaihin malaman hadisi Muhammad bn Ali bn Husain bn Babawaihi al-Kummi, wanda ake wa lakabi da "Saduk" (ya rasu a shekara ta 381), kuma mawallafin littafin Man La Yahdhuruhul Fakih da kuma dimbin muhimmman littattafai, ya fada cikin littafinsa mai suna I'itikadatul Saduk cewa:
"Akidarmu game da Alkur'ani mai girma wanda Allah Ya saukar wa AnnabinSa Muhammadu (s.a.w.a) shi ne abin da yake cikin bangwayen nan biyu, shi ne wanda yake hannun mutane bai wuce wannan ba - har ya zuwa inda yake cewa - kuma duk wanda ya danganta gare mu cewa muna fadin wai Alkur'ani ya fi haka to shi makaryaci ne". Sannan ya shiga kawo hujjoji kan hakan, mai son karin bayani yana iya duba cikamakin maganan tasa[91].
Shugaban jama'ar Shi'a, Abu Ja'afar Muhammad bn Husain al-Dusi (wanda ya rasu a shekara ta 460 hijiriyya), mawallafin littafin Al-Khilaf da Al-Mabsud da Al-Tahzib da Al-Istibsar da sauransu, ya fada cikin littafinsa na tafsiri mai suna Al-Tibyan cewa[92]:

"Amma zancen kari (cikin Alkur'ani) da tawaya, suna daga cikin abubuwan da su ma ba su dacewa da shi domin kari cikinsa, abu ne wanda aka yi ijima'i kan batacce ne. Tawaya kuwa, bisa zahirin ra'ayin musulmi, babu shi, hakan kuwa shi yafi dacewa da abin da ya inganta a mazhabarmu, shi ne kuwa abin da Al-Murtadha ya goyawa baya, shi ne kuma zahirin ruwayoyi, - har zuwa inda yake cewa - ruwayoyinmu kuma suna karfafa juna kan kwadaitar da karanta shi da riko da abin da yake ciki, da dawowa da duk wata sassabawar hadisai masu magana kan rassa (furu'a) zuwa ga Alkur'ani. Hakika an ruwaito wani hadisi da ba wanda yake musa shi, daga Annabi (s.a.w.a) cewa, Annabi (s.a.w.a) ya ce:
"Ni mai barin Nauyayan Abubuwa guda Biyu ne tare da ku, wadanda idan kuka yi riko da su ba za ku bata a baya na ba: (su ne) Littafin Allah da Zuriyata, Ahlulbaiti, don ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".
Wannan yana nuni da cewa shi Alkur'ani samamme ne a dukkan zamani, domin ba zai yiwu ya yi umurni da riko da abin da ba za mu iya riko da shi ba, kamar yadda Ahlulbaiti (a.s) da wanda bin fadarsa yake wajibi samammu ne a duk lokaci. To idan wanda yake tare da mu an hadu a kan ingancinsa to ya kamata mu shagaltu da tafsirinsa da bayyana ma'anoninsa, mu bar komawa bayan wannan).
Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya tabbatar da wannan hakika cikin tafsirinsa Ala'ur Rahaman fi Tafsiril Kur'an, wato dawwamar Alkur'ani da kubutarsa daga jirkita da gurbata, inda yace:
"Haka Alkur'ani ya ci gaba a kan wannan gagarumin tafarki daga wannan al'umma zuwa wancan, kana iya ganin duban dubata na littattafa da mahaddatansa, kuma haka aka ci gaba da buga wasu Kur'anan daga wasu, wasu daga cikin musulmi suna ji da karanta shi daga wasunsu……ko da yake muna cewa dubbai ne kawai, amma fa daruruwan dubbai ne ko ma a ce dubban dubbai. Babu shakka, babu wani al'amari na tarihi da ya sami irin wannan inganci da wanzuwa wacce take a sarari tamkar abin da Alkur'ani ya samu, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawari cikin Surar Hijr:
"Lalle Mu ne Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika, Masu kiyayewa ne a gare shi".
Da kuma fadinSa Ta'ala cikin Surar Kiyamati:
"Lalle ne wajibi ne a gare Mu, Mu tara shi, Mu (tsare maka) karatunsa".
To idan ka ji wani abu kan jirkitar Alkur'ani da bacewar sashensa, daga bakaken ruwayoyi, kada ka ko kula su sannan ka fadi duk abin da ilmi yake yarda da fadinsa na daga sassabawar su da rauninsu da raunin masu ruwaitosu da sabawarsu wa musulmi, da kuma raunin da abin ruwaitowarsu - rusashshe - ya zo da shi[93] ".
Shehin malamin ya ci gaba da cewa cikin tafsirinsa karkashin fasalin: "Maganar Imamiyya Kan Cewa Babu Tawaya Cikin Alkur'ani", inda yace: "Ba a boye yake ba cewa Shaihin masu hadisi wanda aka san shi da kula da abin da yake ruwaitowa, wato Shaikh Saduk (Allah Ya kyautata makwancinsa) ya fada cikin littafinsa al-I'itikad cewa: "Akidarmu ita ce cewa Alkur'anin nan da Allah Ya saukar wa AnnabinSa (s.a.w.a) shi ne dai wanda yake cikin bangwayen nan biyu (wanda kowa ya sani) bai kuma wuce haka ba, wanda kuwa ya danganta mana cewa mun ce ya fi haka, to shi makaryaci ne".
Shaikh al-Mufid a littafinsa na al-Makalat ya kawo cewa wasu jama'a daga cikin Imamiyya sun ce shi Alkur'ani ba a tauye ko da kalma ko aya ko sura daga cikinsa ba, amma an shafe abin da yake tabbatacce cikin Mus'hafin Amirul Muminina (a.s) na tawili da tafsirin ma'anoninsa bisa hakikanin saukarwa.
A cikin littafin Kashful Gida'i fi Kitabil Kur'an, a fasali na takwas, kan tawayar Alkur'ani an ce: Babu shakka cewa an kiyaye shi daga tawaya da kiyayewar Sarki Mai sakamako, kamar yadda Alkur'ani ya yi nuni da hakan a sarari, kuma malamai suka hadu a kai.
Shaikh Baha'i yana cewa: "Kuma haka nan an yi sabani kan aukuwar kari da tawaya cikinsa, abin da ya inganta shi ne shi Alkur'ani mai girma kiyayayye ne daga hakan, kari yake ko ragi, kuma lalle fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "Kuma lalle Mu, hakika Masu kiyayewa ne gare shi" yana nuni da kuma tabbatar da hakan.
Al-Mukaddas al-Bagdadi cikin Sharhin al-Wafiya yana cewa:
"Hakika sanannen zancen Imamiyya kan ragi a cikin Alkur'ani shi ne rashin hakan a cikinsa", har ila yau ya ce an samu daga Shaikh Ali bn Abdul Ali cewa shi ya wallafa littafi na musamman kan kore tawaya cikin Alkur'ani daga hadisai, inda ya ce idan hadisi ya zo bisa sabanin dalili na Littafin Allah da Sunna ingantacciyar ko kuma ijma' (abin da malamai suka hadu a kai amma da sharadin akwai wani Imami a cikinsu), kuma ba zai yiyu a yi masa wani tawili ba ko kuma daukansa da wasu ma'anoni ta wasu fuskoki ba, to wajibi ne a jefar da shi[94]".
Marigayi Allama kana Mujahidin zamani Shaikh Muhammad Husain Kashif al-Ghida ya fada cikin littafinsa mai suna Aslul Shi'a wa Usuluha cewa:
"Lalle wannan Littafin da yake hannu musulmi shi ne Littafin da Allah Ya saukar masa (Annabi) domin gajiyarwa da kalubale, da kuma cewa babu nakasi a ciki, babu jirkita, babu kuma kari, a kan hakan ne (malamai) suka hadu a kai".
Sharifi mai kira zuwa ga gyara, Sayyid Abdul Husain Sharafuddin ya fada cikin littafinsa Fusulul Muhimma fi Talifil Umma cewa:
"Alkur'ani mai hikima, barna bata zuwa masa a zamaninsa ko a bayansa. Abin sani dai shi ne a cikin bangwaye biyun nan, shi ne kuma a hannun mutane, ba a kara ko da harafi ko kuma a rage wani ba, babu musayyar kalma da wata, ko harafi da wanin harafin. Kuma ko wani harafi cikin haruffan Alkur'ani tabbatacce ne a kowani zamani tun daga zamanin da aka saukar da shi. Sannan ya kasance a tare a wancan zamani mafi tsarkaka, yana rubuce kamar yadda yake a yau. Mala'ika Jibrilu (a.s.) ya kasance yana kawo shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) sau da yawa, dukkan wannan yana cikin al'amurra sanannu wajen masu bin diddigi cikin malaman Imamiyya. Don haka ba a dogara da maganan 'yan Hashawiyya, domin su ba su da fahimta".
Haka nan kuma malamin nan mai yawan bincike, babban mutum, Sayyid Muhsin Amin Husaini Amili ya fadi cikin littafinsa A'ayanu al-Shi'a cewa:
"Babu wani daga cikin 'yan Imamiyya, dadadde ko na yanzu da yake cewa akwai kari, babba ne ko karami, cikin Alkur'ani, face ma dai dukkansu sun hadu a kan rashin kari, hakika wadanda ake dogaro da maganarsu daga cikin masu bin diddigi sun hadu a kan cewa babu abin da ya ragu daga cikin Alkur'ani".
To wannan dai shi ne Alkur'ani mai girma da kuma ra'ayin Imamiyya dangane da shi, shi ne kuma dai a yanzu yake hannu musulmi, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya zo da shi. Kuma shi mai wanzuwa ne da wanzuwar dan'Adam a kan doron kasa, yana haskaka wa dan'Adam hanyar rayuwa, ya kuma rike hannun al'umma zuwa ga shiriya.
Malamai da masu bincike da masu bin diddigi, suna ganin cewar abin da ke yawo tsakanin wasu mutane na ruwayoyi da zantattuka (marasa tushe) da suke maganar tawayar Alkur'ani, cikin da'irar Ahlussunna da Shi'a, ba kome ba ne face sanyawa ce ta makaryata, wacce babu makawa dole a yi jifa da su.
Haka nan ana samun wasu ruwayoyi wadanda ana yiwa zahirinsu wata fahimta ba tare da zurfafa nazari wajen karanta su da fahimtar su ba, wacce kuma ta sa ake cewa da akwai tawaya cikin Alkur'ani ko kuma samuwar wani Mus'hafi daban kamar yadda al'amarin ya rikitar da wasu mutane, masu muzanta Musulunci kuma suka dauki hakan wata dama ce gare su ta musguwa wa Musuluncin da kuma musulmai da kuma kokarin kawo rarrabuwa tsakaninsu. Kamar abin da aka ruwaito daga Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.), ba tare da kula da ingancin ruwayar ko rashin sa ba. Ga abin da ya ce:
"....amma wallahi - sai ya mika hannunsa zuwa kirjinsa - akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da mu, takobinsa da sulkensa, kuma wallahi, muna da Mus'hafin Fadima tare da mu, babu wata ayar Littafin Allah a cikinsa, shi dai shifta ce daga shiftar Manzon Allah (s.a.w.a.) Aliyu kuwa shi ne ya rubuta shi da hannunsa[95]".
Hakika wasu sun shiga wahami kan cewa Imam Sadik (a.s.) - wal iyazu billahi - yana ba da labarin samuwar wani Alkur'ani ne ban da wannan Alkur'anin da ke hannunmu, sai wadansu suka dauki wannan waha-mi a matsayin wata hujjar shuka barna tsakanin mutane.

To amma abin da hadisin nan yake nufi a sarari yake, ga mafi raunin mutane, wanda dai ya san harshen larabci. Domin shi Imam Sadik (a.s.) yana cewa ne: "Wallahi muna da Mus'hafin Fadima".
Idan muka koma ga kalma Mus'haf cikin harshen larabci zai sa mu fahimci ma'anar wannan magana ta Imam (a.s.).
Ragib al-Isfahani yana cewa:
"Sahifa ita ce duk wani abu shimfidadde, kamar shimfidar kunci, ganye ko wani shafi da ake rubutu a kansa, jam'inta kuwa shi ne Saha'if ko kuma Suhuf. Allah Ta'ala Yana cewa:
"Suhufin Ibrahima da Musa", "Suna karanta Suhufai tsarkakakku, cikinsu akwai litattafai masu kima".
An ce abin da ake nufi da Suhufan shi ne Alkur'ani, sai Ya sanya su takardu da litattafai a cikinsa domin tara wani abu bayan abin da yake cikin sauran littattafan Allah.
Shi kuwa Mus'hafi shi ne abin da aka yi shi mai tattara takardu rubutattu, jam'insa kuwa shi ne Masahif [96] ).
Saboda haka kalmar Mus'haf, a ma'anonin da muke amfani da su a yau, tana nufin littafi ba suna ne wanda ya kebanta da Littafin Allah (Alkur'ani) ba. Shi suna ne na kowane littafi da ya tattara takardu ko fatu (kamar yadda ake rubutu a jikin fata a zamanin da). Ana kiran Alkur'ani da sunan Mus'haf ne domin shi mai tattare ne da takardu.
Alkur'ani mai girma yana da sunaye daban-daban kamar haka: Alkur'ani, al-Zikr, al-Furkan da kuma al-Kitab[97] , wahayi dai bai kira shi (Alkur'ani) da sunan Mus'haf ba, kai dai musulmi su suka ba shi wannan suna yayin da suka tara shi, don bayan tarawan ya zamanto wani tari ne na takardu (suhuf).
Saboda haka, lallai tushen rudanin shi ne batun isdilahi (yadda ake amfani da kalmomi) da ma'ana ta lugga a wancan zamanin, wadda ma'anar da mutane suke dauka a cikinsa, yanzu ba a daukar ta a wannan zamanin.
Sannan kuma Imam ya bayyana ma'anar wannan Mus'haf din domin ya kau da rikitarwar da ka iya faruwa, inda ya ce: "Babu wata aya ta Littafin Allah a cikinsa".
Ma'ana, shi ba Alkur'ani ba ne, ba kuma daga Alkur'ani yake ba, ba kuma wahayi ne ba, (shi dai shifta ce ta Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma (rubutun Imam Ali).
Wasu malumma suna cewa wannan Mus'hafin wasu tarin addu'oi da shiryarwa ne wadanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi shiftar su ga Fadima al-Zahra (a.s.) domin tarbiyyarta da kuma ilmantar da ita.
To wannan yana bayyana mana kuskure, rudani da jirkitarwa da wasu daga cikin musulmi suka yarda da shi a dalilin mummunar fahimta da mugun nufi.

54. Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Abdullah bn Muhammad bn Amir al-Shabrawi al-Shafi'i, shafi na 21.
55. Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30.
56. Zakha'irul Ukba na Dabari, shafi na 67.
57. Dabari ya ruwaito wannan hadisi da dan bambancin lafazi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 24, haka nan cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 220, Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 121, da Suyudi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 29, da wannan lafazi" "Dabarani ya fitar da shi daga Umar, cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Dukkan wani mutum, to danganta-karsa tana komawa ne ga mahaifinsa, in ban da 'ya'yan Fadima, don dangantakarsu tana komawa ne gare ni, ni ne mahaifinsu".
58. Tirmizi ya ruwaito shi cikin Sahihinsa juzu'i na 2, shafi na 380 da isnadinsa daga Zaid bn Arkam, haka ma Hakim ya ruwaito shi cikin Al-Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 109, shi ma daga Zaid bn Arkam, haka nan ma Ahmad bn Hambal ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa daga Abu Sa'id al-Khudri, juzu'i na 3 shafi na 17, kamar yadda kuma Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir juzu'i na 1 shafi 129 ya ruwaito, haka ma Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba daga Ahmad shafi na 16.
59. Al-Ithafu bi hubbil Ashraf, shafi na 22.
60. Kamar na sama.
61. Kamar na sama, shafi na 22-23.
62. Al-Balagi cikin Ala'ur Rahman shafi na 44.
Allama Faiz Abadi ya nakalto cewa: " Muslim ya ruwaito Hadisus Sakalain cikin sahihinsa, haka ma Ahmad bn Hambal cikin Musnad dinsa, juzu'i na 4 shafi na 366, da Baihaki cikin Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 148, juzu'i na 7 shafi na 30, haka ma Darimi ya ruwaito shi Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 431, Al-Muttaki cikin Kanzul Ummal, juzu'i na 1 shafi na 45, da juzu'i na 7 shafi na 102, haka ma Dahawi cikin Mishkilul Athar juzu'i na 4 shafi na 368, Tirmizi ma ya ruwaito shi cikin Sahihinsa, juzu'i na 3 shafi na 109, haka Nisa'I cikin Khasa'is shafi na 21. Haka nan ma cikin al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3 shafi na 148.
63. Musnad Ahmad bn Hambal, juzu'i na 3 shafi na 17.
64. Shabrawi al-Shafi'I cikin littafinsa na al-Ittihaf bi hubbil Ashraf, mukaddimar mawallafi, shafi na 26.
65. Abu Nu'aim cikin littafin Hilliyat al-Awliya juzu'i na 4 shafi na 306, ya nakalto daga Firuz Abadi cikin littafin Fadha'il al-Khamsa min al-Sihah al-Sitta juzu'i na 2 shafi na 64, Ibn Hajar ma ya ambato shi cikin Zawa'id babin Ahlulbaiti wal Azwaj shafi na 277, haka ma Haithami ya nakalto shi daga Ibn al-Bazzar cikin Majma' al-Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163, kamar yadda kuma Dabarani ya kawo cikin Mu'ujamul Kabir juzu'i na 1 shafi na 125, haka ma Dabari cin Zaka'ir shafi na 20, haka ma Hakim cikin al-Mustadrak tare da karin lafuzza, juzu'i na 2 shafi na 343, haka ma cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 216.
66. Hakim cikin al-Mustadrak ya ruwaito wannan hadisi a juzu'i na 2 shafi na 343, inda ya ce: wannan hadisi ne ingantacce a bisa sharadin Muslim, haka ma Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 216, da kuma Haithami cikin Majma'ansa, juzu'i na 9 shafi na 168, haka ma Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir dinsa shafi na 20, haka ma Khadib al-Bagdadi cikin Tarihinsa, juzu'i na 12 shafi na 19.
67. Fadha'il al-Khasa na Firuz Abadi, juzu'i na 2 shafi na 65.
68. Kamar na sama.
69. Kamar na sama.
70. Al-Ittihaf bi Hubbil Ashraf na Al-Shabrawi shafi na 20, Hakim ma ya fitar da shi cikin al-Mustadrak, juzu'i na 3 shafi na 149, inda ya ce wannan hadisi ne ingantacce sai dai kuma bai (Muslim) ruwaito shi ba, kamar kuma al-Muttaki ya fitar da shi cikin littafinsa Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 217, haka ma Ibn Hajar ya kawo shi cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika shafi na 140.
71. Fadha'il Khamsa, juzu'i na 2 shafi na 68.
72. An kira wannan hadisi da sunan Hadisin Mayafi ne saboda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tara Ahlulbaitinsa guda hudu (Aliyu, Fatima, Hasan da Husaini) ya rufe su da mayafi.
73. Ma'ana E kema ba kya zuwa wuta.
74. Al-Fusulul Muhimma fi Ahawalul A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 25-26.
75. Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Shaikh Shabrawi, shafi na 17-18.
76. Al-Fusulul Muhimma fi Ahawalul A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 29.
77. Suyudi ya ruwaito shi cikin littafin Ihya'ul Mayyiti daga Dabarani daga Umar, shafi na 20, kamar yadda Haithami kuma ya fitar da shi cikin littafin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163, kamar yadda kuma Ibn Hajar ya kawo shi cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika shafi na 90.
78. Suyudi ya ruwaito shi cikin littafin Ihya'ul Mayyiti daga Dabarani daga Jabir bn Abdullah, shafi na 22, kamar yadda Haithami kuma ya fitar da shi cikin littafin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 172.
79. Muslim ya ruwaito shi cikin littafin Fadha'il al-Sahaba (Falalar Sahabbai) cikin babin falalar Aliyu bn Abi Talib daga Yazid bn Hayyan, juzu'i na 4 shafi na1873, haka ma Ahmad bn Hambal ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa ya yi kuma daidai da abin da Muslim ya ruwaito, juzu'i na 4 shafi na 366-367, kamar yadda kuma Muttaki ya ruwaito cikin Kanzul Ummal juzu'i na farko shafi na 158, da kuma cikin juzu'i na bakwai shafi na 102, haka ma Suyudi ya ruwaito shi cikin tafsirinsa Durrul Mansur juzu'i na 6 shafi na 7, ya ce daga gare shi: Muslim, Tirmizi da Nasa'i sun ruwaito shi daga Zaid bn Arkam, haka ma Suyudi ya ruwaito shi cikin littafinsa Ihya'ul Mayyit shafi na 11.
80. Khadib ya ruwaito shi cikin tarihinsa, juzu'i na 2 shafi na 146 da kari cikin matanin, kamar yadda kuma Al-Muttaki ya kawo hadisin cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 217 karkashin lamba ta 3800, sannan Suyudi ma ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti bi Fadha'il Ahlulbaiti, shafi na 37.
81. Tabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 17.
82. Kamar na sama.
83. Suyudi ya fitar da shi cikin Ihya'ul Mayyit daga Dailami daga Abi Sa'id, shafi na 43, haka ma Al-Manawi ya ambace shi cikin Faizul Kabir juzu'i na 1 shafi na 515, ya ce: Dailami ya fitar da shi cikin Firdausi.
84. Suyudi ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 40-41, yana cewa: "Dailmai ya fitar da shi daga Aliyu, kamar yadda kuma Al-Muttaki ya ambato shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 8, shafi na 278, kamar yadda kuma Ibn Hajar ya ambato shi cikin Sawa'ikul Muhrika, shafi na 103.
85. Suyudi ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 39, daga Dabarani daga Ibn Abbas, haka ma Al-Muttaki ya ambato shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 8, shafi na 212, yana cewa: "Dabarani ya nakalto shi daga Ibn Abbas, sannan kuma Haithami ma ya ambace shi cikin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 10 shafi na 346, ya ce: "Dabarani ya ruwaito shi cikin Al-Kabir da Al-Awsad.
86. Ihya'ul Mayyiti na Suyudi shafi na 38, Majma'ul Zawa'id na Haithami juzu'i na 5 shafi na 195, Usudul Gaba na Ibn Athir juzu'i na 3 shafi na 137, Hilyatul Awliya na Abu Na'im juzu'i na 9 shafi na64 daga Aliyu (a.s.).
87. Shaikh Tabrisi yana daga cikin shahararru kana manyan malaman mazhabar Shi'a Imamiyya a qarni na shida hijiriyya.
88. Sayyid Murtadha: shi ne Aliyu bn Husain, yana daga cikin manya-manyan malaman Shi'a Imamiyya na qarni na hudu hijiriyya, kuma yana daga cikin daliban Shaikh al-Mufid kuma malamin Shaikh al-Tusi, Mu'assasin Jami'ar birnin Najaf al-Ashraf, ya rasu a shekara ta 437 Hijiriyya.
89. Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an na Shaikh Dabarasi a mukaddimar tafsirin.
90. Kama na sama.
91. Ma'al Khatib fi Khututihi al-Aridha na Shaikh Lutufullah Safi, shafi na 42.
92. Tafsirul Tibyan Shaikh Dusi juzu'i na 1shafi na3.
93. Ala'ur Rahaman na Shaikh Al-Balagi, juzu'i na 1 shafi na 18
94. Kamar na sama, Mukaddima.
95. Biharul Anwar na Allama Majlisi juzu'i na 47, shafi na 271.
96. Mu'ujam Mufradat Alfaz al-Kur'an na Ragib Isfahani, wajen kalmar Suhuf.
97. Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an na Allama Dabrisi, a mukaddimar littafin.