Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

Alkur'ani Mai Girma A Ruwayoyin Ahlulbaiti (a.s)

Wanda duk ya yi bitar ruwayoyi da hadisan da suka zo ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) ya kuma karanci tarihin rayuwarsu da alakarsu da Littafin Allah, ba zai sami muhimmanci da kulan da Ahlulbaiti (a.s) suke bayarwa fiye da wanda suke bai wa Littafin Allah, Mai Girma da Daukaka ba, ko a yanayin rayuwarsu ko cikin abin da suka ruwaito da maganganunsu ko cikin abin da suka yi wasiyya ko suka tarbiyyantar ko suka fuskantar da mabiyansu da almajiransu da daukacin 'ya'yan musulmi.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ya ku mutane, lalle kuna gidan dako ne, kuma kuna kan tafiya, tafiyar kuwa tana sauri da ku, kun ko ga dare da yini da rana da wata suna tsufar da kowane sabon abu, suna kuwa kusanto da kowane manisanci suna kawo kowane abin alkawartawa, to ku tanadi shiri wa tafiyar nan mai tsawo".
Ya ce: sai Mikdad bn Aswad ya mike, ya ce: Ya Manzon Allah! Mene ne gidan dako?, sai yace masa:
"Gidan isarwa da yankewa, to idan fitinu kamar yankin dare mai duhu sun rikitar da al'amurra a kanku, na hore ku da Alkur'ani, domin shi, mai ceto ne abin karbawa ceto, mai jayayya abin gaskatawa. Duk wanda ya sanya shi gabansa zai ja-gorance shi zuwa aljanna, wanda ko ya sanya shi a bayansa zai iza shi zuwa wuta. Shi kuwa ja-gora ne mai shiryarwa zuwa mafi alherin hanya. Kuma shi littafi ne wanda a cikinsa akwai rarrabewa da bayani da riba (ko karuwa) shi ne rarrabewa kuma ba kakaci ba ne, yana da baya da ciki. Bayansa hukumci ne, cikinsa kuwa ilmi ne, bayan nasa gwanin kyau ne da shi, cikin nasa kuwa zurfi ne da shi. Yana da taurari, bisa taurarinsa ma akwai wasu taurarin. Ba a iya kididdigar ababen ban mamakinsa, abubuwan ban sha'awarsa kuma ba sa tsufa. Akwai fitilun shiriya da hikima cikinsa, kuma mai shiryarwa ne zuwa ga masaniya ga wanda ya san sifa. To mai yawo ya yi yawo (cikin Alkur'ani) da ganinsa, kuma dubinsa ya riski sifar domin ya tsira daga halaka ya kuma kubuta daga tsanani. Domin kuwa tunani rayuwar zuciya mai gani ne, kamar yadda mai tafiya cikin duhu yake haskaka hanya da haske. To na hore ku da kubuta mai kyau da karancin dako[98] ".
Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Mahaddacin Alkur'ani, mai aiki da shi yana tare da Mala'iku Marubuta, Masu daraja, Masu da'a ga Allah[99]".
Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Wanda Allah Ya ba shi Alkur'ani, sai ya ga cewa an bai wa wani mutum fiye da abin da aka ba shi, to hakika ya rena babban abu, ya kuma girmama karami[100]".
Ya zo kuma daga wajen Imam Muhammadu Bakir (a.s.) cewa ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ya ku jama'a makarata Alkur'ani! Ku ji tsoron Allah Mai Girma da Daukaka cikin abin da Ya dora muku na LittafinSa domin ni abin tambaye ne, ku ma abin tambaya ne. Ni za a tambaye ni kan isar da sako, ku kuma za a tambaye ku ne kan abin da aka dora muku na Littafin Allah da Sunnata [101]".

Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Ya kamata mumini kada ya mutu har sai ya koyi Alkur'ani, ko kuwa ya zama cikin koyonsa([102]".
Imam Sadik (a.s.) kuma yana cewa:
"Alkur'ani alkawarin Allah ne da bayinSa, to hakika ya kamaci mutum musulmi ya yi dubi cikin alkawarinsa, ya kuma karanta ayoyi hamsin daga ciki a kullum[103] ".
Imam Sadik din dai yana cewa:
"Abubuwa uku za su kai kuka zuwa ga Allah Madau-kakin Sarki: masallacin da aka kaurace masa ba a salla a cikinsa, malamin da ke tsakanin jahilai da kuma Alkur'anin da aka rataye shi kura tana hawa kansa don ba a karanta shi[104] ".
Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Lalle Alkur'ani rayayye ne ba matacce ba, kuma yana gudana kamar yadda dare da yini suke gudana, kuma kamar yadda rana da wata suke tafiya. Yana kuma tafe ne kan na karshenmu, kamar yadda yake tafe a kan na farkonmu".
Amirul Muminina (a.s) ya ce:
"Sannan Allah Ya saukar masa da Littafi, haske ne fitilunsa, ba su mutuwa, fitila ce da haskenta ba ya bishewa, kogi ne da ba a risko zurfinsa; tafarki ne wanda salonsa ba ya bacewa; haske ne wanda ba ya yin duhu, mai rarrabewa wanda karfin hujjarsa ba ya raguwa, bayani ne wanda ba a rusa ginshikinsa, waraka ce wadda ba a tsoron cuta a tare da ita, daukaka ce wacce ba a rinjayar masu taimakon ta; gaskiya ce wadda ba a tabar da masu taya ta. Shi ne taskar imani, kuma tsakiyar shi, shi ne mabubbugan ilmi da kogunan shi; shi ne koraman adalci da tabkunan shi; shi ne murhun Musulunci da ginin shi; shi ne kwazazzabon gaskiya da mafakarta; shi tekun ne da masu kwarfa ba sa iya kwarfe shi; idanuwar ruwa ne masu kwarfa ba su iya karar da shi; wuraren sha ne masu taho masa ba sa kafar da shi; masaukai ne da matafiya ba sa bacewa da hanyarsa, alamu ne wadanda matafiya ba sa makance masa; tsaunuka ne da wanda ya nufe su ba zai wuce su ba. Allah Ya sanya shi mai kashe kishin ruwan malamai; bazaar (mai rayawa) ga zukatan fukaha'u (masana ilmin fikihu); gwadabe mai tara hanyoyin mutanen kwarai; waraka wadda babu wata cuta bayanta; hasken da babu wani duhu tare da shi; igiya ce mai karfi; mafaka ce wadda kololuwarta karerriya ce; daukaka ga wanda ya jibince shi; aminci ga wanda ya shige shi; shiriya ga wanda ya yi koyi da shi; uzuri ga wanda ya yi riko da shi; hujja ga wanda ya yi magana da shi; shaida ga wanda ya yi amfani da shi wajen jayayya; nasara ga wanda ya kafa hujja da shi; mai daukar duk wanda dauke shi; abin hawa ga wanda ya yi aiki da shi; alama (aya) ce ga wanda ya sa lura; garkuwa ga wanda ya nemi kariya da shi; ilmi ga mai kiyayewa; abin fadi ga mai ruwaya; kuma hukumci ne ga mai hukumtawa [105] ".
Haka nan dai muke fahimtar kimar Alkur'ani da darajarsa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da kuma tafarkinsu. Ita ce kuwa kima ta hakika wacce Alkur'ani ya yi furuci da ita, wahayi kuma ya siffanta shi da ita
"Hakika wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa hanya da tafi daidai". (Surar Isra'i, 17: 9)
Alkur'ani shi ne hanyar rayuwar al'umma, mabubbu-gar ilmi da shiriya, taskar ma'arifa da wayewa, tafarkin fahimta da tunani, ma'aunin ci gaba da halaye na kwarai, shi ne doka ta ilmi wajen tsara rayuwar dan'Adamtaka, kuma shi ne ma'aji mai tattara al'adun rayuwar mutumtaka da dokokinta.

98. Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 598.
99. Kamar na sama, shafi na 603.
100. Kamar na sama, shafi na 605.
101. Kamar na sama, shafi na 606.
102. Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 607.
103. Kamar na sama, shafi na 609.
104. Kamar na sama, shafi na 613.
105. Nahjul Balagah, huduba ta 198.