Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

Sunnar Annabi (s.a.w.a) A Mazhabar Ahlulbaiti (a.s)

"Allah Ya ni'imta bawan da ya ji maganata sannan ya haddace ta ya kiyaye ta ya kuma bayar da ita (ga wasu) kamar yadda ya ji ta. Sau da yawa ana samun mai daukar ilmi, amma ba malami ba, sannan kuma sau da yawa ana samun mai daukar ilmi ya zuwa wanda ya fi shi sani [117] ".
Baicin Littafin Allah, Sunna ita ce mabubbuga ta biyu daga mabubbugan shari'a, wadanda musulmi suke dogara da su wajen fitar da hukumce-hukumce da dokoki da ka'idojin Musulunci. Ita Sunna tana daukar nauyin bayani da faiyacewa da kuma tafsirin Littafin Allah da furuci da abubuwan da ya kunsa da kuma abubuwan da ya tattara na shari'a da tunani da kuma tarbiyya. Shi nassi na Alkur'ani yana dauke da wata wadata da arziki na tunani da shari'a, mai girma kuma dauwamammiya, ita sunna kuwa ta dauki nauyin bayyana wannan arziki da gamar da shi. Lalle hankula ba za su iya riskar Littafin Allah tamkar yadda Sunna take riskar shi tana bayyana shi ba. Manzon Allah (s.a.w.a.) shi aka yi wa zance da wahayi, shi ne kuwa masanin abin da ke cikin Littafin Allah mai girma na daga abin da suka shafi hukumce-hukumce da ababen fahimta daga ciki da kuma manufofin da yake da su.
Don haka ne ita Sunna mabubbuga ce wacce ba ta kafewa, kuma gaskiya ce wacce barna bata taho mata a bayanta ko a gabanta. Sunna ita ce amintacciya mai ayyana dokokin rayuwa da kuma tsarin jin dadin dan'Adam, kuma ita madawwamiya ce dawwama irin ta Alkur'ani mai girma. Allah Ta'ala Ya ce:
وما آتَاكُمُ الرَّسولُ فَخُذُوهُ وَما نَهاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا

"Abin da Manzo ya zo muku da shi, ku karba, abin da kuma ya hane ku, to ku hanu...". (Surar Hashr, 59: 7)
لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرجُو اللهَ وَاليَومَ الآخِر

"Hakika abin koyi mai kyau ya kasance muku daga Manzon Allah, da duk wanda yake kaunar Allah da kuma ranar lahira...". (Surar Ahzab, 33: 21)
فإنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ الى اللهِ وَالرَّسُولِ

"Idan kuka yi jayayya a wani abu to ku mai da (hukumcinsa) ga Allah da Manzo...". (Surar Nisa'i, 4:59)
Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) da wadanda suka dauki tafarkinsu wajen tafsiri da hadisi da fikhu da shari'a da akida, sun lizimci wannan hanyar, sun kuma yi gwagwarmaya, sadaukarwa, daurewa cutarwa, shiga kurkuku, kisa, azabtarwa da kuma kora duk a dalilin kare sunna mai tsarki da kira zuwa ga dacewarta da Littafin Allah mai girma.
Hakika an bijirar da Sunna tsarkakakkiya ga coge da karkatarwa da jirkitarwa wanda masu yi wa Musulunci dasisa, karya da kiyayya suke yi domin muzanta wannan dawwamammen sako na Ubangiji, domin kuma su karkatar da tafarkin al'ummar Musulunci.
Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna fagen kan gaba wajen kiyaye Sunna tsarkakakkiya da daukar ta da kuma isar da ita da gaskiya da amana, da kuma bayyana abubuwan da ta tattara na bayani mai zurfi.
Don aka ne suka yaki bidi'oi da bata, suka yi kira da a lizimci Littafin Allah da Sunna da sanya Littafin Allah ya zama shi ne ma'aunin Sunnar Annabi (s.a.w.a). Sun yi hakan ne domin Littafin Allah abin kiyayewa ne daga karkatarwa da jirkita - Alhamdu lillahi - kiyayye ne kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya isar da shi ga Annabi Amintacce Muhammadu (s.a.w.a).
"Lalle Mu muka saukar da Ambato (Alkur'ani) kuma lalle Mu Masu kiyaye shi ne".
Saboda haka, babu hannun jirkitawa ko coge ko wasa da ya taba shi. Domin haka ne ma muke samun Amirul Muminina (a.s) yana cewa:
"Ya ku mutane! Farkon aukuwar fitinu (na daga) son zuciya wadanda ake bi da hukumce-hukumce fararru (wato na bidi'a) wadanda ake sabawa Littafin Allah wajen binsu, mutane suna jibintar wasu mutane wajen bin wadannan hukumce-hukumce. Da dai ita bata tsantsarta take, da ba ta buya ba ga mai hankali, da kuma gaskiya tsantsarta take, da sabani bai samu ba. Amma ana daukar wani abu a nan, a dauki wani a can, sai a cudanya su, sannan su zo tare. A nan ne Shaidan ya rinjaye majibantansa, wadanda kuwa kariya ta gabata gare su daga Allah suka tsira[118] ".
Abu Basir, daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa: "Na ce da Abu Abdullahi (a.s.) cewa: Wadansu abubuwa suna taho mana, mu ba mu san su cikin Littafin Allah ko Sunna ba, to za mu dube su? Sai ya ce: "A'a, amma kai ko ka dace ba za a sakanta maka ba, idan kuwa ka yi kuskure to ka yi wa Allah Mai Girma da Daukaka karya[119] ".

Sannan ya ce (a.s.): Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata cikin wuta take".
Abdullah bn Abi Ya'afur ya ce: "Wata rana na tambayi Abu Abdullah (a.s.) game da sassabawar hadisai, wadanda muke amincewa da wadanda ma ba mu amince musu suna ruwaitowa", sai ya ce:
"Idan hadisi ya zo muku kuma kuka sama masa wata shaida daga Littafin Allah ko wata magana ta Manzon Allah (s.a.w.a.), (to ku karba) idan kuwa ba haka ba to wanda ya kawo muku hadisin ya fi cancanta da shi[120] ".
An samu daga Ayyub bn Al-Hurr ya ce: "Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana cewa:
"Duk wani abu ana iya masa raddi in ban da Littafin Allah da Sunna, to duk hadisin da bai dace da Littafin Allah ba, to kyalkyali ne kawai [121]".
An samu daga Ayyub bn Rashid daga Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ya ce:
"Abin da bai dace da Alkur'ani ba daga cikin hadisai kyalkyali ne kawai [122]".
An samu daga Imam Sadik (a.s.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Wanda ya yi riko da Sunnata yayin sassabawar al'umma, yana da ladan shahidai dari [123]".
Wani mutum ya taho wa Amirul Muminina (a.s) ya ce: "Ka ba ni labari (mece ce) Sunna da bidi'a da jama'a da kuma rarraba", sai Amirul Muminina (a.s) ya ce da shi:
"Sunna ita ce abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sunnanta, bidi'a kuma ita ce abin da aka fare shi a bayansa. Jama'a ita ce wadanda suke tare da gaskiya ko da su kadan ne, rarraba kuwa ita ce wadanda suke tare da bata, ko da kuwa suna da yawa[124]".
Har ila yau, Imam Ali (a.s) yana cewa:
"Sunna biyu ce: Sunna ta wajibci, riko da ita shiriya ce, barinta kuwa bata ce. Da kuma Sunna cikin abin da ba wajibi ba, riko da ita falala ce, barinta kuwa kure ne([125]".
Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Ita Sunna ba a yi mata kiyasi, to ya ya za a yi kiyasin Sunna alhali mace mai haila tana rama azumi, amma ba ta rama salla[126]".
An samu daga Abu Abdullah, Imam Sadik (a.s.) daga Mahaifansa, daga Imam Ali (a.s.) cewa:
"Kowace gaskiya tana tare da wata hakika, kuma kowace dacewa tana tare da wani haske. To abin da ya dace da Littafin Allah ku karbe shi, abin da kuwa ya saba da Sunnar Manzon Allah, to ku bar shi[127]".
Sannan kuma yana cewa:
"Allah Ya ji kan mutumin da ya kawo hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ba tare da ya yi masa karya ba, ko da kuwa mutane sun guje shi[128]".
Sannan Amirul Muminina Ali (a.s) ya ce: "Na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Idan hadisi ya taho muku (sashinsa) yana daidaita, (sashi kuma) yana sassabawa, to abin da sashinsa yake karyata sashe ba daga gare ni yake ba, kuma ban fade shi ba, ko da an ce na fada. Idan kuma hadisi ya taho muku, sashensa yana gaskata sashe, to shi daga gare ni yake, kuma ni na fade shi. Wamda kuwa ya ganni bayan rasuwata, kamar wanda ya ganni a raye ne, wanda kuwa ya ziyarce ni to zan kasance masa mai shaida a ranar kiyama[129]".

An samu daga gare shi (a.s.) ya ce wa Muhammad bn Muslim cewa:
"Ya Muhammad! Abin da ya taho maka na wata ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya dace da Alkur'ani to ka dauke shi, abin da kuwa ya taho maka na ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya saba da Alkur'ani to kada ka karbe shi[130]".
Haka nan ake sanya iyakoki wa abin da ake daukarsa Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) ne a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da tafarkinsu da kuma alakar wannan Sunna mai tsarki da Littafin Allah, da kuma rawar da take takawa cikin shari'a da sanya dokoki da gina rayuwar zamantakewa da ta ibada, wa al'ummar Musulmi.
Muna iya tsamo wadansu abubuwa daga wannan tsarin mazhabi kamar haka:
1. Cewa kowane fadi ko aiki ko tabbatarwar da aka danganta ga Manzon Allah (s.a.w.a.), to wajibi ne a gwada su da Alkur'ani, a tabbatar da ingancinsu bisa hasken Alkur'ani, abin da ya dace da Littafin Allah, to daga Sunnar Manzo (s.a.w.a) yake, abin da kuwa ya saba da shi to ba kome yake ba wajen Sunna.
2. Alkur'ani da Sunna su ne tushen shari'a da doka, su ne ma'aunin hukumce-hukumce da halaye da tsarin rayuwa. Abin da duk muka samu na hukumce-hukumce na fikihu ko ma'anonin da ake riska na akida, to wajibi ne mu tabbata sun dace da Littafin Allah da Sunna. Duk abin da muka samu daga cikinsu ya dogara bisa asasin Littafin Allah da Sunna da shari'a, to doka ce ta Allah, mu yi aiki da shi, mu rike shi da karfi. Abin da kuwa ya saba da Littafin Allah da Sunna to shi bidi'a ce, bata ce.
3. Idan aka samu Sunna tabbatacciya, wacce an tabbatar da fitowarta daga Manzon Allah (s.a.w.a.) tana kuwa yin daidai da Litttafin Allah, to wajibi ne mu dauke ta a matsayin ma'auni kuma abin da za a yi amfani da ita wajen ruwayoyi da hadisan da muke shakkar su, ko muka sami rikitarwa wajen ingancinsu. Sai mu tabbatar da abin da ya dace da Littafin Allah da tabbatacciyar Sunna, mu yarfar da abin da ya saba da su. Ta wannan hanyar ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta ke iyakance tafarkin da za a bi wajen mu'amala da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.).
Rabe-Raben Sunnar Annabi (s.a.w.a):
Malamai suna raba Sunnar Annabi (s.a.w.a) zuwa gida uku:
1. Maganganu: Su ne dukkan abin da suka taho daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na daga zantattuka, hudubobi, wasiyyoyi, wasiku da dai sauransu.
2. Ayyuka: Abin nufi shi ne duk wani aiki da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wajen mu'amalarsa da mutane, ko wajen yin ibadoji, ko wanin wannan daga abin da yake bayyana halalci. Duk aikin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aikata to za mu gane halalcinsa a tushen al'amarin domin Ma'aiki (s.a.w.a.) abin tsarakake-wa ne daga aikata haramun.
Saboda haka muna iya cewa abin da ya fito daga Ma'aiki (s.a.w.a.) na aiki ya kasu kashi biyu:
• Wajibci: Sashin abin da ya fito daga Manzo (s.a.w.a) kamar salla, hajji, adalci tsakanin mutane da dai sauransu, yana bayyana wajibcin wannan aiki, da kuma cewa shi takalifi ne kuma farilla ne, wadda lizimtar su yana wajaba a kanmu, kuma dole ne mu gudanar da hukumce-hukumcensu.
• Akwai wasu ayyukan Manzon Allah (s.a.w.a.) wadanda ba su nuna wajibci, suna nuna halalci ne. Dukkan wannan yana karkashin halal, wanda aikatasu ja'izi (ya halalta) ne.
Don haka, aikin Manzo (s.a.w.a.) yana bukatar tafsiri domin mu gane wajibi da mustahabi da kuma ja'izi. Malamai wadanda suka kebanta da wannan fannin suna rarrabewa cikin fahimta da tafsirin 'aiki' a cikin Sunna, ta hanyar hujjoji da alamomi da tafarkin bincike na ilmin Usulu.
3. Yarda (Takriri): Shi ne yin shirun Manzo (s.a.w.a) kan wani aikin da sahabbansa suka aikata, ya gani kuma bai hana su ba, kamar mu'amalolin zamantakewa da aikin mutum shi kadansa. To hakan ikirari ne da kuma yarda daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.), yana kuma shiga karkashin Sunna.
To kamar haka ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta iyakance yadda ake mu'amala da Sunna mai tsarki da tafarkin tabbatar da ingancinta da tafsirinta.

Tafarkin Bincike da Tabbatarwa:
Malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suna da hanyar bincike da tabbatar da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wacce Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka iyakance kuma suka bayyana tushenta da alamominta. Mun riga mun yi nuni ya zuwa ga ruwayoyin da suka zo kan hakan a baya.
Bisa wannan tushen malaman fikhun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka kafa tafarkin gyara (nakdi) cikin aikin bincike na ilmi. Babu wata sunna da suke mika wuya wajen ingancinta tun farko, sai dai su dauki matakin shakka kan ingancin sunnar, sannan su ci gaba da kokkofi da binciken ruwayar da tabbatar da ingancinta, idan har ingancinta ya tabbata sai su yi riko da ita da kuma daukanta a matsayin hujja da kuma fitar da hukumce-hukumce daga cikinta. Idan kuwa rashin ingancinta ya tabbata musu, sai su yi jifa da ita, ba za su yi aiki da ita ba. To kamar haka ne tafarkin binciken ruwayoyi da tabbatar da ingancin Sunna yake.
Bisa ga wannan bayani, malaman mazhabar Ahlul-baiti (a.s) ba su yi ikrari da samuwar wasu littattafan hadisai masu inganci, sake ba tare da wani kaidi ba. Sai dai kowane littafi dole ya rusuna wa bincike da gwaji kafin a tabbatar da ingancinsa.
Misalin littattafai mashahurai a ruwaya wadanda suka tattara abin da ya taho ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) su ne:
1. Al-Kafi na Shaikh Kulayni.
2. Al-Istibsar na Shaikh Dusi.
3. Al-Tahzib na Shaikh Dusi.
4. Man la Yahdhuruhul Fakih na Shaikh Saduk.
5. Wasa'il al-Shi'a na Hur al-Amuli.
6. Biharul Anwar na Allama Majlisi.
Da dai sauran littattafan hadisi.
Babu shakka malaman Imamiyya wadanda kuma suke lizimtar tafarkin Ahlulbaiti (a.s) a fikihu da shar'antawa da ilmomin Musulunci sun sanya hadisan da suka zo cikin wadannan littattafa a bisa ma'aunin bincike wanda ya kubuta daga son rai, inda bayan binciken suka zubar da adadi mai yawa na hadisan saboda rashin ingancinsu.
Kamar yadda wadannan malumma suka binciki wadannan littattafa na hadisi, haka kuma suka gudanar da bincike kan wasu littattafan kuma, kamar su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunan Abi Dawud, Kanzul Ummal da dai makamantansu daga cikin littattafan hadisai da ruwayoyi, suka kuma auna su da wannan ma'auni na ilmi, kamar dai yadda suka gudanar akan wadancan, suka dauki na dauka da kuma zubar da ba zubarwa.
Su wadannan malamai kuwa, su kan yi wannan bincike nasu ne a bisa wadannan asasai:
(A). Bincike Kan Isnadi: Abin nufi da isnadi kuwa shi ne silsilar maruwaita wadanda suke ruwaito hadisi. A nan malaman su kan tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiyar maruwaitan, suna masu dogaro da ilmul Rijal, wanda yake gabatar musu da sanarwar abin da ya jibinci mutanen da suke maruwaita ne, yana shaidar gaskiya ko rashin gaskiyarsu, ba tare da la'akari da mazhabar da maruwaicin ya fito ba. Idan ya zama abin dogaro kuma gaskiya, sai su karbi ruwayarsa, idan kuwa an yi suka cikin al'amarinsa sai su ture ruwayar tasa. Su ba sa duba kome sai gaskiyar mai ruwaya da kubutarsa a bisa ginshikai tabbatattu.
(B). Binciken Matani: Abin nufi da matani shi ne asalin nassi. A nan malamai suna bincike ne kan luggar matani da ma'anarta, kuma suna bincike domin su tabbatar da cewa abin da ya taho a hadisin bai sabawa Littafin Allah ko tabbatacciyar Sunna ko wata hakika tabbatacciya wacce Mai shar'antawa Matsarkaki (Allah) Ya tabbatar da ita a matsayin tabbatacciyar hakika a hankalce ba.
Yayin da ingancin isnadi da na matani suka tabbata wajen malamai sai su karbi ruwayar, idan kuwa ba haka ba sai su ture ta, ba ruwansu da cewa a wani littafi daga cikin littattafan hadisi ta zo.
Saboda haka a tafarkin malaman fikihu da malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) Imamiyya ba a samun:
1. Rikon wani littafi na hadisi a matsayin sahihi daga dayansa ko kuma kore shi gaba dayansa.
2. Su suna karbar ruwayar maruwaici ne bisa sharadin gaskiyarsa da amincinsa ba tare da lura da mazhabarsa ko bangaren da ya fito ba.
Wanda duk yake bitar littattafan Usulu da fikihu da Ilmul Rijal , zai samu wannan hakikar a bayyane.
Da haka ne wannan hanyar bin diddigi ta ilmi ta kiyaye asalin shari'a da tsarkin ta, da kuma hadin kan musulmi da nisantar nuna bangaranci, jahilci da ganin girman wani tun da ba a ba da dama wa wadannan abubuwa a tafarkin bincike, don kuwa a yayin bincike kowa daya ne.
Kuma da wannan tafarkin bincike da ilmin bin diddigi, wanda ya kafu a bisa asasin neman gaskiya da bincike a aikace, da rashin mika wuya da yarda da ingancin kowace ruwaya ba tare da lura da kowane ne maruwaicin ta ba, ko littafin da aka ruwaito ta ba, ne ake gudanar da binciken hadisi.

117. Al-Diraya na Zainuddin al-Amuli, shafi na 113.
118. Sahihul Kafi na Muhammad Bakir Bahbudi, juzu'i na 1 shafi na 8.
119. Kamar na sama, shafi na 9.
120. Sahihul Kafi na Muhammad Bakir Bahbudi, juzu'i na 1 shafi na 11.
121. Kamar na sama.
122. Kamar na sama.
123. Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.
124. Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.
125. Kamar na sama.
126. Kamar na sama.
127. Kamar na sama.
128. Kamar na sama.
129. Kamar na sama.
130. Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.