Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

Tawassuli (Kamun Kafa)

Gabatarwa

Hakikanin tawassuli an riga an yi nuni da shi a kur’ani mai girma yayin da Allah madaukaki yake fada yana mai yi wa muminai magana: “Yaku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku nemi tsani zuwa gareshi ku kuma yi jihadi a tafarkinsa ko kwa rabauta” [3].
Wannan aya mai girma da watanta suna kirga takawa da jihadi daga hanyoyin da aka shar’anta da mutum zai iya rikon su tsani zuwa ga Allah madaukaki.
Shin da akwai wasu wasiloli da shari’ar ta kwadaitar da rikonsu ko kuwa al’amarin an bar shi a hannun mutum ne da kuma iyawarsa ya zabi wata wasila da zai nemi kusanci ta hanyarta?
Sanannen abu shi ne wasiloli da bawa zai iya kusanta zuwa ga Allah ta hanyarta ba ya yiwuwa ta hanyar ijtihadi, domin wadannan hanyoyi suna bukatar ayyanawa daga Allah, saboda haka ne ma shari’a ta daukar wa kanta bayaninsu, ta kuma ayyana su ta iyakance su a Kur’ani da Sunna, kuma dukkan wasilar da shari’a ba ta zo da ita ba a kebance ko a dunkule to ita bidi’a ce kuma bata ne.
Imam Ali (A.S) ya yi nuni da wannan wasilolin da bawa yake kusanta zuwa ga Allah da ita a fadinsa:
“Mafificin abin da masu tawassuli suke tawassuli zuwa ga Allah madaukaki da shi, shi ne imani da shi da kuma imani da manzonsa, da jihadi a tafarkinsa, domin shi ne kololuwar musulunci, da kuma kalmar ikhlasi domin ita fidira ce, da tsayar da salla, domin ita ce addini, da bayar da zakka domin ita wajibi ce, da azumin Ramadan domin shi garkuwa ne daga ukuba, da hajjin daki da kuma umararsa domin su suna kore talauci suna kuma kakkabe zunubi[4], da sadar da zumunci domin shi mai kara dukiya ne mai kuma jinkirta ajali, da kuma sadaka domin ita tana kakkabe kurakurai, da sadakar sarari domin ita tana kare mummunar mutuwa, da kuma aikata kyakkyawa domin shi yana kare fada wa rauni[5].
Kur’ani mai girma ya yi nuni zuwa ga dabi’a mai kyau da ake nema gun musulmi yana mai cewa: “Da dai cewa yayin da suka zalunci kawukansu sun zo wajanka sai suka nemi gafarar Allah sai manzo ya nema musu gafara, da sun sami Allah mai karbar tuba mai jin kai” [6]. Wannan kuma ba ya takaita da lokacin halin rayuwar annabi (S.A.W), domin Allah yana cewa: “Kada ku zaci wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne, su rayayyu ne ana azurta su a wajan ubangijinsu” [7]. Ashe kenan wannan yana gudana bayan wafatin manzo (S.A.W), kuma musulmi sun fahimci halarcin hakan hatta bayan wafatinsa kamar yadda sashen masu tafsirai suka yi bayani[8].
Ashe kenan ba abin da zai hana wannan alaka tare da Allah da neman gafarar zunubbai daga gareshi, ko neman biyan bukatun duniya da na addini ta hanyar tawassuli da annabi domin ya neman musu gafara da daukar sa a matsayin kusanci ga Allah da kuma kasancewarsa mai girma da daraja gunsa. Wannan hanya ce da shari’a ta kwadaitar da ita kuma Kur’ani mai girma ya ayyana ta.
Saboda neman Karin bayani muna iya bin bahasosi masu zuwa:
Na farko: Tawassuli a lugga da isdilahi.
Na biyu: Ra’ayoyi a kan hukuncin tawassuli.
Na uku: Halarcin tawassuli a Kur’ani.
Na hudu: Tawassuli a hadisan annabi (S.A.W).
Na biyar: Tawassuli a dabi’ar musulmi.
Na shida: Tawassuli gun Ahlul baiti (A.S).
Na bakwai: Tattaunawar masu tunani kan halarcin tawassuli da shar’anta shi.

Na Farko: Tawassuli A Lugga Da Isdilahi

A cikin littafin Lisanul Arab: Wasila gun sarki, wasila: daraja, wasila: kusanci, wane ya yi wasila zuwa ga Allah idan ya aikata wani aiki da yake kusantar da shi zuwa gareshi, wasila: mai kwadayi zuwa ga Allah, Lubaid ya ce:
Ina ganin mutane ba sa sanin darajar al’amarinsu,
Sai dai kowane ma’abocin hankali mai kwadayi ne zuwa ga Allah
Ana cewa: Wane ya riki wasila idan ya samu kusanci zuwa gareshi da wani aiki, wasila: isa da kuma kusanci, jam’inta su ne wasa’il wato wasiloli (ko tsanunnuka), Allah (S.W.T) ya ce: “Wadannan da suke kira suna neman wasila (tsani) zuwa ga ubangijinsu wanne ne ya fi kusanci” [9]. Da dai sauran littattafan lugga da suka yi bincike kan wannan kalma, domin ma’anarta tana daga cikin ma’anoni bayyanannu da hakikaninta ba ya ketare ma’anar rikon wani abu a matsayin tsani da zai kai ga wani abin da yake shi ne mafita da manufa da ake burin cimma sa, wannan kuwa yakan sassaba gwargwadon sassabawar manufofi.
Wanda yake neman yardar Allah sai ya nemi tsani da ayyuka na gari da zai samu yardar Allah da su, wanda kuwa yake son ziyarar dakin Allah mai alfarma sai ya nemi tsani da abin da yake iya kaiwa zuwa gareshi.
Ibn Kasir yana cewa: Tawassuli shi ne mutum ya sanya mai shiga tsaka, tsakaninsa da Allah domin biyan bukatunsa, ta hanyar wannan tsakanin[10].

Na Biyu: Ra’ayoyi Game Da Hukuncin Tawassuli

Kafin mu bijiro da dalilan tawassuli da hukuncinsa da kuma tattaunawa game da haka yana da kyau mu kawo wasu ra’ayoyi da suka zo game da tawassulin.

Ra’ayin Farko: Haramcin Tawassuli

Wannan shi ne ra’ayin Albani kuma yana ganin tawassuli bata ne, a littafin “Tawassuli; Nau’o’insa Da Hukuncinsa” a mukaddimar sharhin dahawiyya yana cewa[11]: Mas’alar tawassuli ba ta cikin mas’alolin akida.
Daga cikin wadanda suka tafi a kan haramci akwai Muhammad dan Abdulwahab yana mai cewa: “Idan wasu mushrikai (yana nufin musulmi da ba wahabiyawa ba) suka ce maka: “Hakika waliyyan Allah babu tsoro garesu ba kuma zasu yi bakin ciki ba” [12]. Ko suka ce maka ceto gaskiya ne, ko kuma annabawa suna da wani matsayi gun Allah, ko ya ambaci wata magana ta annabi domin ya kafa hujja a kan batansa (abin da yake nufi da bata shi ne ceto), kai kuma ba ka fahimta ba (ai ba ka iya ba shi amsa), sai ka amsa masa da cewa: Allah ya fada a littafinsa cewa: Wadanda suke da karkata a cikin zukatansu sai su bar bayyanannun ayoyi su bi ayoyi masu kama da juna” [13].
Daga cikin masu haramtawa akwai Abdul'aziz dan Abdullahi dan Baz, yana mai cewa: “Wanda ya roki annabi ya nemi ceto gunsa ya warware musuluncinsa” [14].

Ra’ayi Na Biyu: Halaccin Tawassuli

Shaukani Zaidi ya tafi a kan halaccin tawassuli a littafinsa “Tuhfatuz zakirin” da fadinsa: “Yana mai tawassuli zuwa ga Allah da annabawansa da salihai” [15].
Samhudi bashafi’e ya halatta shi yana mai cewa: “Tawassuli yana iya zama daga annabi (S.A.W) yana mai neman wani abu daga gareshi, da ma’anar cewa yana da ikon ya ba shi wannan abu da rokonsa da kuma cetonsa a wajan ubangijinsa, sai tawassuli ya zama wani nau’i na addu’a duk da nau’in maganganun da suke kunsa sun sassaba, yana daga tawassuli wani ya ce ina rokonka zama da kai a aljanna… ba kuma komai wannan yake nufi sai ya zama tsani kuma mai ceto” [16].
Ibn taimiyya ya nakalto daga Ahmad dan Hanbal a cikin “Mansak almarzawi” tawassuli da annabi da kuma addu’a gunsa, ya kuma karbo daga Ibn Abidduniya da Baihaki da Tabrani ta hanyoyi masu yawa da suke nuna ingancinsa[17].
Daga cikin masu halattawa akwai Shafi’i, yana mai cewa: “Ni na kasance ina neman tabarruki da kabarin Abu Hanifa ina zuwa kabarinsa kullum, idan wata bukata ta zo mini sai in yi salla raka’a biyu in zo kabarinsa in roki Allah bukata ta gunsa sai a biya” [18].
Daga masu halattawa akwai Abu Ali Alkhilal malamin hanbalawa, yana mai cewa: “Babu wani al’amari da zai zo min sai na je kabarin Musa dan ja’afar (A.S) in yi tawassuli da shi sai Allah ya saukake mini samun abin da nake so” [19].
Amma shi’a imamiyya suna cewa ne: “Ya halatta a yi tawassuli da annabi da imamai (A.S) domin biyan bukatu da kuma yayin bakin ciki bayan mutuwarsu, kamar yadda ya halatta a yayin rayuwarsu, saboda kasancewar wanda ake yin magana da shi ba rasasshe ba ne, kuma hakan ba shirka ba ne[20].

Ra’ayi Na Uku: Bambantawa Tsakanin Tawassuloli

Ra’ayi na uku: shi ne ra’ayin ibn taimiyya, sai dai mun samu magana mai karo da juna a ra’ayinsa, wani lokaci ya haramta wani lokaci kuma ya halatta, wani lokaci kuma ya rarraba, kamar yadda ya kasa tawassuli zuwa gida uku ya halatta nau’i biyu ya haramta na uku. Ya ce: Lafazin tawassuli ana nufin abu uku da shi:
Na daya: Tawassuli da biyayyar annabi da imani da shi, wannan kuwa shi ne asalin imani da musulunci, wanda ya yi musunsa, to zahirinsa ya kafirta gun malamai da sauran mutane.
Na biyu: Tawassuli ta hanyar addu’arsa da cetonsa, ai annabi ya yi addu’a ya ceci mutum kai tsaye, wannan kuwa yana yiwuwa a rayuwarsa ne, ko ranar kiyama da za a yi tawassuli da shi, wanda ya musa wannan kafiri ne mai ridda, a nemi ya tuba dole, in ya tuba shi ke nan, in ba haka ba, sai a kashe shi murtaddi.
Na uku: Tawassuli ta hanyar cetonsa bayan ya mutu, da kuma hada Allah da shi bayan ya mutu, wannan yana daga bidi’a da aka farar[21].

Na Uku: Halaccin Tawasuli A Kura’ani

Annabawa da salihai sun yi furuci da hakikanin tawassuli a matsayinsa na ibada ta shari’a ba wani kokwanto, kuma Kur’ani ya kawo wajaje masu yawa da annabawa suka yi tawassuli da annabawa da waliyai domin neman kusanci da Allah, sai ya zama ana amsa addu’ar su ana biyan bukatunsu, daga ciki akwai wannan misalai:
A- Allah (S.W.T) yana cewa: “Ina warkar da makaho da kuturu ina kuma raya matacce da izinin Allah” [22].
A nan zamu ga cewa sun yi tawassuli da Isa (A.S) sai dai wannan bai zama daga akidarsu ba da cewa Isa yana da wani karfi sabanin na Allah, wannan ya zo ne daga imaninsu da cewa Isa (A.S) yana da karfi da ikon warkar da cuta da izinin Allah saboda yana da matsayi a wajansa, wannan kuma ba shirka ba ce domin shirka shi ne ka kudurce ikon da yake ba daga Allah yake ba ga Isa (A.S) wanda babu wani daga musulmi da ya tafi a kan hakan.
B- Fadin Allah madaukaki: “Suka ce ya babanmu ka nema mana gafarar zunubbanmu” [23]. ‘Ya’yan annabi Yakubu (A.S) ba sun nemi gafara daga gareshi ba ne ba tare da ikon Allah da kudurarsa ba, sun sanya shi (A.S) a matsayin tsani ne na neman gafara saboda kusancinsa da Allah da matsayinsa, wannan kuma a fili yake idan muka duba amsar da ya ba wa ‘ya’yansa da cewa; “Zan nema muku gafarar ubangijina, hakika shi mai gafara ne mai rahama” [24].
C- Fadin Allah madaukaki: “Da cewa su, idan suka zalunci kawukansu, sun zo wajanka sai suka nemi gafarar Allah sai manzo ya nema musu gafara da sun sami Allah mai karbar tuba mai Rahama” [25].
Wannan aya tana nuna karbar neman gafarar manzo (S.A.W) ga musulmi masu tuba, domin manzo (S.A.W) yana da matsayi mai girma wajan Allah (S.W.T) a lokaci guda tana kuma karfafa muhimmancin zuwan musulmi wajan Annabi (S.A.W) saboda neman gafara garesu[26].

3. Ma’ida: 35.
4. Wankewa.
5. Nahajul Balaga Na Subhi Salih: Huduba 110\163.
6. Nisa’i: 64.
7. Ali Imran: 169.
8. Tafsirin Ibn Kasir: 1\532.
9. Tawassuli A Shari’ar Musulunci, Ja’afar Subhani: 17.
10. Tafsirin Ibn Kasir: 1\532.
11. Albishara Wal Ithaf Na Sakafi: 52, Daga Sharhin Dahawiyya: 60.
12. Yunus: 62.
13. Kashfusshubuhat Na Muhammad Abdulwahab: 60.
14. Mukhalaful Wahabiyya Lil Kur’ani Wassunna, Na Umar Abdussalam: 20.
15. Tuhfatuz Zakirin Na Shaukani: 37.
16. Wafa’ul Wafa Na Samhudi: 2\1374.
17. Attawassul Wal Wasila: Na Ibn Taimiyya: 144-145.
18. Tarihu Bagdad: 1\123. Ma Zukira Fi Makabiri Bagdad.
19. Tarihu Bagdad: 1\120. Ma Zukira Fi Makabiri Bagdad.
20. Albarahinil Jaliyya Fi Daf’i Tashkikatil Wahabiyya, Na Kazwini Alha’iri: 30.
21. Attawassul Wal Wasila: 13, 20, 50.
22. Ali Imran: 49.
23. Yusuf: 97.
24. Yusuf: 98.
25. Nisa’i: 64.
26. Mukhalafatul Wahabiyya: 22.