Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

Tawassuli Kamar Yadda Kur’ani Ya Zo Da Shi [27]

Allah madaukaki ya kwadaitar da bayinsa muminai a kan tawassuli ya kuma halatta tawassuli nau’i daban-daban, daga ciki zamu zo da wani nau’in daga cikin:

A- Tawassuli Da Sunayen Allah (S.W.T)

Fadinsa mai girma da daukaka; “Sunaye kyawawa na Allah ne, ku kira shi da su, ku bar wadannan da suke shisshigi a cikin sunayensa, da sannu za a saka musu da abin da suke aikatawa” [28]. Wannan aya tana siffanta mana sunayen Allah dukkansu da kyawawa ba tare da bambanci ba, sannan sai ta umarci da a yi addu’a da wadannan sunaye.
Yayin da bawa yake ambaton sunayen Allah da suke dauke da dukkan alheri da kyau da rahama da gafara da izza, sannan sai ya gabata zuwa ga Allah yana mai neman gafara daga zunubbansa da neman biyan bukata, sai Allah ya amsa addu’ar mai tawassuli da sunayensa.

B- Tawassuli Da Kyawawan Ayyuka Na Gari

Aiki na gari yana daga abin da ake tawassuli da shi a shar’ance wanda ta hanyarsa bawa yake samun kusanci zuwa ga Allah (S.W.T), tunda tawassuli yana nufin sanya wani abu gaba zuwa ga Allah domin neman yardarsa, to ba makawa aiki na gari yana daga mafi girman tsani da bawa yake riko da shi domin biyan bukatunsa. Allah madaukaki ya ce: “Yayin da Ibrahim yake daukaka ginshikan gini da Isma’ila (suka ce): Ya Ubangiji ka karba daga garemu hakika kai mai ji ne masani. Ya Ubangiji ka sanya mu masu mika wuya gareka daga kuma zuriyarmu a samu wata al’umma mai mika wuya gareka, ka kuma nuna mana wurin ibadarmu, ka karbi tubanmu kai ne mai karbar tuba mai jin kai” [29]. Ayar a nan tana karfafa dangantaka tsakanin aiki na gari da kuma addu’a da Ibrahim (A.S) yake neman a biya masa na zuriyarsa ta zama al’umma ta gari.
Kamar yadda yake karfafawa da fadinsa Allah (S.W.T): “Wadannan da suke cewa ya Ubangijinmu mu mun yi imani, ka gafarta mana zunubbanmu ka kuma kare mu azabar wuta” [30]. Sai a nan ya gwama tsakanin neman gafara da imani da nuna alakar imani da neman gafarar.

C- Tawassuli Da Addu’ar Manzo (S.A.W)

Kur’an ya yi nuni zuwa ga wannan matsayi da daukaka da manzo yake da ita wajan Allah, da kuma bambancinsa da sauran mutane, da fadinsa; “Kada ku sanya addu’ar manzo tsakaninku kamar addu’ar sashenku ga sashe” [31]. Kuma ya yi nuni da cewa manzo (S.A.W) shi ne dayan aminci biyu a duniya, da fadinsa: “Allah ba zai azabtar da su ba alhalin kai kana cikinsu, kuma Allah ba mai azabtar da su ba ne alhalin suna masu istigfari” [32].
Sannan mun samu Kur’ani a wurare masu yawa yana gwama ambatonsa da manzo yana mai raba musu aiki daya, yana cewa: “Da sannu Allah da manzonsa zasu ga ayyukanku sannan sai a mayar da ku zuwa ga duniyar boye da sarari” [33]. Yana kuma cewa: “Ba su saba ba sai domin Allah da manzonsa sun arzuta su daga falalarsa” [34]. Da sauran ayoyin da sunan annabi ya zo tare da sunan Allah a hade, idan wannan matsayi ne wanda manzo yake da shi a wajan Allah kuma ba a mayar da addu’arsa ana kuma amsa ta, to riko da addu’arsa riko ne da wani rukuni mai karfi.
Shi ya sa zamu ga Allah (S.W.T) yana umartar masu zunubi na daga musulmi da su yi riko da addu’arsa da yin istigfari a majalisinsa, suna tambayarsa ya nema masu gafara domin istigfarinsa yana zama sanadin saukar rahama da kuma karbar tubansu, Allah ya na cewa; “Ba mu aiko wani manzo ba sai domin a bi shi da izinin Allah, da dai cewa su yayin da suka zalunci kawukansu sun zo maka sai suka nemi gafarar Allah sai annabi ya nema musu gafara da sun sami Allah mai karbar tuba mai rahama” [35].
Da fadinsa madaukaki: “Idan aka ce da su ku zo manzon Allah zai nema muku gafara sai su karkata kawukansu ka gan su suna masu juyawa suna masu girman kai” [36].

D- Tawassuli Da Addu’a Ga Dan’uwa Mumini

Madaukaki ya ce: “Wadanda suka zo bayansu suna cewa ya Ubangijinmu ka gafarta mana da kuma ‘yan’uwanmu da suka rigaye mu da imani, kada ka sanya mugun kuduri a zukatanmu ga wadanda suka yi imani, ya Ubangijinmu kai ne mai tausayi mai rahama” [37].
Wannan aya tana nuna cewa muminai masu zuwa suna neman gafara ga ‘yan’uwansu, wannan kuwa yana nuna yi wa dan’uwa addu’a mustahabbi ne.

E-Tawassuli Da Annabawa Da Salihai Kansu

Wannan nau’in ya bambanta da maganar da ta gabata ta tawasssuli da addu’ar annabi, domin a nan tawasuli ne da zatin su annabawa da salihai da sanya su tsani domin amsa addu’a da kuma nuni zuwa ga matsayin da suke da shi wajan Allah madaukaki.
Idan mun kasance muna tsani da addu‘ar manzo a wajan Allah to a nan zamu sanya shi kansa manzo da karamarsa su zama tsani zuwa ga Allah ne. Sanannan abu ne cewa tawassuli da addu’ar da ta zo daga wannan mutum mai daraja da Allah ya daukaka ya girmama kamar yadda yake fada: “Mun daukaka maka ambatonka” [38]. Ya kuma umarci musulmi da su girmama shi da daukaka shi, da fadinsa: “Wadanda suka yi imani da shi suka kuma karfafe shi suka taimake shi, kuma suka bi hasken da aka saukar tare da shi, wadannan su ne masu rabauta” [39].
Idan ya kasance madogarar amsa addu’arsa shi ne shi kansa manzo (S.A.W) da yake da matsayi mai girma wajan Allah, to ashe kenan shi ya fi cancanta mutum ya yi tawassuli da shi kamar yadda yake tawassuli da addu’arsa, wanda ya yi furuci da halaccin na farko ya haramta na biyu, to ya raba tsakanin abu biyu da suke lizimtar juna. Wannan nau’in tawassuli akwai ruwayoyi da suka zo da suke karfafarsa da sanadai masu inganci da masu ruwayar hadisai suka yarda da shi[40].

F-Tawassuli Da Darajar Salihai Da Alfarmarsu Da Matsayinsu

Wanda ya bi tafarkin musulmi zai same su suna da wannan nau’i na tawassuli da matsayin salihai da kuma darajarsu gun Allah.
Muslim ya rawaito daga Mu’azu Dan Jabal ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin ka san hakkin Allah a kan bayi? Sai ya ce: Sai na ce Allah da manzonsa su ne mafi sani, sai ya ce: Hakkin Allah a kan bayi su bauta masa kada su tara wani abu da shi, sannan sai ya tafi kadan sai ya ce: Ya Ma’azu! Sai na ce: Amsawarka ya manzon Allah! Sai ya ce: Kasan hakkin bayi a kan Allah idan suka yi hakan? Sai na ce: Allah da manzonsa su ne mafi sani, sai ya ce: Kada ya azabtar da su” [41].
Ya bayyana cewa Kur’ani ya riga ya kawo mana tarihin annabawa da salihai daga bayinsa game da tawassuli, sannan sai ya kawo mana wasu nau’i na tawassuli da ya halatta, kuma bai kebanta da addu’a ba, ballantana a rarrabe tsakanin zatin annabi da addu’arsa, domin ya hada da zatin annabi kuwa.

Na Hudu: Tawassuli A Hadisan Annabi


Hadisai da yawa sun zo da suke halatta tawassuli da annabi (S.A.W) da kuma waliyai da salihai.

1- Daga Usman dan Ahnaf ya ce: Wani mutum makaho ya zo wajen annabi (S.A.W) sai ya ce: Ka yi mini addu’a Allah ya ba ni lafiya sai ya ce: Idan ka so in jinkirta maka shi ya fi maka, idan kuwa ka so in yi maka addu’a. Sai ya umarce shi da ya yi alwala ya kuma kyautata alwalar, ya yi salla raka’a biyu sannan sai ya yi addu’a da wannan: “Ya Ubangiji ni ina rokonka ina kuma fuskantarka don Muhammad annabin rahama, ya Muhammad ni ina fuskanta gareka zuwa ga ubangijina a kan wannan bukata tawa domin a biya mini ita, Allah ka ba shi cetona[42].
Wannan hadisi ba shi da wata matsala a ingancinsa har ma Dan Taimiyya yana ganinsa sahihi ne, ya ce: Abin da ake nufi da Abi Ja’afar a cikin sanadin wannan hadisi shi ne Abu Ja’afar Alhudami kuma shi amintacce ne.
Amma Rufa’i yana cewa: Ba makawa wannan hadisi ingantacce ne kuma mash’huri ne, kuma ya tabbata cewa makahon ganinsa ya dawo da addu’ar annabi (S.A.W) [43]. Nisa’i da Baihaki da Tabrani da Tirmizi da Hakim a Mustadrik duk sun rawaito shi[44].
A wannan hadisi akwai karfafawa a kan halaccin tawassuli, yayin da muka ga manzo ya sanar da makaho yanda zai yi tawassuli zuwa ga Allah da annabinsa annabin rahama, ya kuma ba shi cetonsa domin biyan bukatarsa, abin da ake nufi da annabi shi ne ainihin annabi ba addu’arsa ba da kuma fuskantar Allah da alfarmar annabi da sanya shi tsani.

2- Atiyya Al’aufi ya rawaito daga Abu Sa’idul Huduri cewa manzo (S.A.W) ya ce: “Wanda ya fita daga gidansa domin salla sai ya ce: Ya Ubangiji ina rokonka don girman masu rokonka, ina kuma rokonka domin tafiyata wannan, ka san ni na fito ba mai ashararanci ba, ba mai takama ba, ba riya ba, ba domin jiyarwa ba, na fito ina mai neman tsari da fushinka, da kuma neman yardarka, ina rokonka ka kiyaye ni daga wuta ka kuma gafarta mini zunubaina, domin ba mai gafarta zunubbai sai kai, Allah zai fuskanto zuwa gareshi kuma mala’iku dubu saba’in zasu nema masa gafara[45].
Wannan hadisi yana nuna halaccin tawassuli zuwa ga Allah da girman waliyyansa na gari, da matsayinsu gunsa (S.W.T) sai mai tawassuli ya sanya su tsakiya da tsani masu ceto domin biyan bukatunsa da amsa addu’arsa.

3- Daga Anas dan Malik ya ce: Yayin da Fatima ‘yar Asad ta rasu sai manzo (S.A.W) ya shiga wajanta ya ce: Allah ya ji kan ki ya babata bayan babata, ya kuma yabe ta ya kumayi mata likkafani da bargonsa, sannan sai manzo (S.A.W) ya kira Usama dan Zaid da Abu Ayyubal ansari da Umar dan khaddabi da wani yaro bakar fata domin su haka kabari, sai suka haka kabarinta, yayin da suka kai ga lahadu sai manzo (S.A.W) ya haka shi da hannunsa ya kuma rika fitar da kasarsa, yayin da ya gama sai ya shiga ya kwanta a ciki sannan ya ce: Allah shi ne yake rayawa kuma yake kashewa, shi rayayye ne ba ya mutuwa, ka gafarta wa babata Fatima ‘yar Asad, ka yalwata mata mashigarta, saboda girman annabinka da kuma annabawan da suke gabanina[46].

4- An rawaito cewa Sawad dan Karib ya yi waka ga manzo (S.A.W) a kasidarsa wacce yake tawassali da annabi a cikinta yana mai cewa:
Na shaida babu wani abin bauta bayan Allah
Kuma kai amintacce ne ga dukkan fakakke
Kuma kai ne mafi kusancin manzanni tsani
Zuwa ga Allah ya dan masu girma tsarkaka
Umarce mu da abin da ya zo maka ya fiyayyan Manzo
Koda kuwa a cikinsa akwai wahala mai kwankwatsa
Ka zama mai ceto ranar da babu wani mai ceto
Mai wadatarwa ga Sawad dan Karib in ba kai ba[47]

Na Biyar: Tawassuli A Tafarkin Musulmi


Dabi’ar musulmi ta gudana a kan tawassuli da Manzo lokacin rayuwarsa da bayan mutuwarsa (S.A.W), haka ma da waliyyan Allah, da neman ceto ta hanyar matsayinsu gunsa, misalai a kan hakan su ne:
A- Abubakar yana fada bayan wafatin manzo (S.A.W) ya ce: Ka tuna mu wajan ubangijinka kuma mu kasance a zuciyarka[48].
B- Hafiz Abu Abdullahi Muhammad bn Musa Annu’umani a littafinsa Misbahuz zulam ya ce: Hafiz Abu Sa’id Assum’ani ya fada a cikin abin da muka rawaito daga gareshi daga Ali dan Abu Dalib (A.S) ya ce; “Yayin da wani balaraben kauye ya zo bayan mun binne manzo (S.A.W) da kwana uku, sai ya fadi a kan kabarin annabi (S.A.W) ya kuma zuba kasa a kansa, ya ce: Ya RasulalLahi! Ka fada mun ji maganarka, ka kiyaye daga wajan Allah mun kiyaye daga wajanka, kuma daga cikin abin da aka saukar akwai fadin Allah: “Da cewa su yayin da suka zalunci kawukansu sun zo maka suka nemi gafarar Allah…” Kuma ni na zalunci kaina na zo maka ka nema mani gafara sai aka kira shi daga cikin kabarin an gafarta maka” [49].
C- Manzo (S.A.W) ya kasance ya sanar da wani mutum addu’a da zai yi ya kuma roki Allah sannan sai ya yi wa annabi magana yana mai tawassuli da shi, sannan sai ya roki Allah ya karbi cetonsa, sai ya ce: “Ya Allah ni ina rokonka ina kuma tawassuli da annabinka annabin rahama “Ya Muhammad ya RasulalLah ni ina tawassuli da kai zuwa ga ubangijinka ga bukatata wannan, Allah ka ba shi cetona” [50].
D- Ya zo a cikin littafin Sahihul Buhari cewa Umar dan Khaddabi ya kasance idan aka yi fari sai su nemi shayarwa da Abbas dan Abdulmudallib, ya ce Ubangiji muna tawassuli zuwa gareka da annabinmu sai ka shayar da mu, mu yanzu muna tawassuli zuwa gareka da ammin annabinmu ka shayar da mu. Ya ce: Sai a shayar da su” [51].
E- Mansur Al’abbasi ya tambayi Maliku dan Anas shugaban malikiyya yanda zai yi ziyarar annabi (S.A.W) da kuma tawassuli da shi, ya ce: “Ya kai Abu Abdullahi in fuskanci alkibla in yi addu’a ko kuma in fuskanci kabarin annabi (S.A.W), sai Malik ya ce masa: Me ya sa zaka juya fuskarka gabarin annabi (S.A.W) alhalin kuwa shi ne tsaninka kuma tsanin babanka Adam (A.S) har zuwa ranar kiyama? Ka fuskance shi ka nemi cetonsa sai Allah ya ba shi cetonka, Allah ya na cewa; “Da dai cewa su idan suka zalunci kawukansu…”[52].
F- Shafi’i ya ambaci wadannan baitoti biyu na waka yana mai tawassuli da Alayen annabi (S.A.W):
Alayen annabi su ne hanyata
Kuma su ne wasila ta gareshi
Ina kaunar dominsu gobe a ba ni
Takardata a hannun dama[53]
Da wadannan hujjoji da kuma dalilai na tarihi, da muka ambata baya zamu iya cewa: annabawa da salihai daga bayinsa suna daukar dukkan wani abu da Allah ya sanya kiyayewarsa da ludufinsa a kai, abin da za a iya tawassuli da shi da fadinsa madaukaki: “Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku kuma nemi tsani zuwa gareshi[54]”. Tsani kuma ya hada har da mustahabbai, bai takaita da wajibai ko nisantar haram ba.

Na Shida: Tawassuli Gun Ahlul Baiti (A.S)


Imamai (A.S) sun kwadaitar da yawa kan yin tawassuli da Kur’ani da waliyyai da sauransu, wanda ya koma wa littattafan imamiyya da hadisansu da littattafan addu’o’insu zai samu wannan ala’mari a wajansu a bayyane yake ta yadda babu wani kokwanto a cikinsa, ga wasu misalai daga ciki:
A- Haris dan Mugira ya rawaito cewa: Na ji Abu Abdullahi (A.S) yana cewa: “Na hana ku wani ya tambayi ubangijinsa wani abu na bukatun duniya har sai ya fara da yabon Allah da kuma salati ga Annabi (S.A.W) sannan sai ya roki Allah bukatunsa” [55].
B- Daga Abu Ja’afar (A.S) ya ce: “Jabirul Ansari ya ce; Na tambayi manzon Allah (S.A.W) me zai ce game da Ali dan Abu Dalib? Sai ya ce: “Wannan shi raina ne, sai na ce: me zaka ce game da Hasan da Husain? Sai ya ce: Su ruhina ne, Fatima babarsu ‘yata ce, duk abin da yake munana mata yana munana mini kuma abin da yake faranta mata yana faranta mini, na shaida har ga Allah ni mai gaba ne ga wanda yake gaba da su, mai aminci ne ga wanda ya aminta da su, ya Jabir, idan kana so ka yi addu’a a amsa maka ka roki Allah da sunayensu, su ne mafi soyuwar sunaye a wajan Allah (S.W.T).
C- Daga annabi (S.A.W) ya ce: “Ya Ubangiji ni ina fuskanta zuwa gareka da Muhammad da alayen Muhammad ina kuma neman kusanci da su zuwa gareka, kuma ina gabatar da su ga bukatuna” [56].
D- Imam Ali (A.S) yana fada a cikin addu’arsa: “Saboda darajar Muhammad da Alayen Muhammad a wajanka, da kuma girmanka mai girma a wajansu ka yi tsira garesu kamar yadda kake ma’abocinsa ka ba ni mafificin abin da ka ba wa masu tambayarka daga bayinka da suka gabata na daga muminai, kuma mafificin abin da kake bayar wa ga wadanda suka ragowa na daga muminai” [57].
E- Imam Husain (A.S) a addu’ar Arfa yana cewa: “Ya Ubangiji ni ina fuskanta zuwa gareka a wannan yammacin da ka halitta, ka girmama, don Muhammad annabinka manzonka, kuma mafificin halittarka” [58].
F- Imam Zainul abidin (A.S) yana fada a addu’arsa don gane da bayyanar watan Ramadan; “Ya Ubangiji ina rokonka don girman wannan wata da kuma girman wanda ya yi bauta a cikinsa -tun farkonsa har zuwa lokacin karewarsa- na daga mala’ika da ka kusantar, ko kuma wani annabi da ka aiko, ko wani bawa na gari da ka zabe shi” [59].

Na Bakwai: Amsa Wa Masu Musun Halaccin Tawassuli


A- Suka ce: Bai kamata ba a yi tawassuli da matattu, wannan aiki ne mummuna a hankalce, saboda matacce ba shi da iko a kan amsawa, tawassuli da shi magana ce da rasasshe[60].
Amsa: Wannan magana tasu ba daidai ba ce saboda ta ci karo da Kur’ani mai girma, ga kuma misalai kan hakan daga ayoyin da suke kore cewa mutuwa rashi ce.

1- Fadinsa: “Suna da arzikinsu (abincinsu da abinshansu) safe da yamma” [61]. Wannan aya ta sauka game da muminai domin tana bayyana nau’in kiyaye wa garesu duniya da lahira.

2- Wacce ta fi wannan aya karara: “Wuta ce da ake bujiro da su gareta safe da yamma, kuma a ranar kiyama (sai a ce) ku shigar da alayen fir’auna mafi tsananin azaba” [62]. A nan Allah yana bayyana abin da masu sabo da kafirai suke ciki na azaba a duniyar barzahu, wanda wannan yake nunawa cewa su rayayyu ne bayan mutuwa kafin alkiyama. Domin ambaton ranar kiyama ya kasance ne bayan bujuro da su ga wuta safe da yamma.
B- Suka ce: Idan ma ya tabbata cewa mutuwa ba karewa ba ce ita ma rayuwa ce, shin zai yiwu a yi alaka da matacce ko ba zai yiwu ba? Domin rayuwar barzahu zata hana iya samun alaka da shi.
Amsa: Abin da yake nuna yiwuwar alakar mutum rayayye a wannan duniya da mutum da yake rayayye a duniyar barzahu ya zo a cikin Kur’ani mai grma daga ciki akwai:

1- Kiran Annabi Salihu (A.S) mutanensa zuwa ga bautar Allah, ya kuma umarce su da kada su taba mu’ujizarsa -taguwa- da sharri, bayan sun soke taguwa sun yi shisshigi kan al’amarin ubangijinsu Allah ya ce: “Sai tsawa ta rike su sai suka wayi gari suna masu gurfanawa a cikin gidajensu. Sai ya juya ga barinsu ya ce: Ya ku mutane na isar da sakon ubangijina na yi muku nasiha sai dai ku ba kwa son masu nasiha” [63].
Sai muka ga Allah yana bayar da labari yanke da cewa al’ummar Annabi Salihu (A.S) ta wayi gari a gidajensu a gurfane, bayan nan kuma Annabi Salihu yana juya musu baya yana mai magana da su yama mai cewa: “Na isar da sakon ubangijina na yi muku nasiha sai dai ku ba kwa son masu nasiha” [64].
Magana ta zo ne daga Salihu (A.S) bayan an halakar da mutanensa da mutuwarsu, da karina ta cewa sai ya juya ga barinsu.

2- Annabi Shu’aibu (A.S) ya yi wa mutanensa magana bayan halakarsu da fadin Allah (S.W.T): “Sai ya juya ga barinsu ya ce: Ya ku mutane hakika na isar da sakon ubangijina gareku na kuma yi muku nasiha, to yaya zan yi bakin ciki a kan (abin da ya samu) mutane kafirai” [65].
Maganar Annabi Shu’aibu (A.S) ga mutanensu ya zo ne bayan halakarsu, wannan kuwa yana karfafa yiwuwar haduwa da su, ba don masu halaka da wannan tsawa sun kasance suna jin maganar Annabi Shu’aibu (A.S) ba to menene ma’anar yi musu magana’.
Kuma ba yadda za a yi a fassara cewa maganar kaico da ya yi, magana ce ta nuna jin zafinsa domin wannan ya saba wa zahirin abin da ya kunshi dokokin tafsiri.
Amma hadisai madaukaka masu yawa sun zo suna nuna yiwuwar alakar kamar haka:

1- Abin da aka rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa ya tsaya a gefen rijiyar kalib a Badar ya yi magana da mushrikai da aka kashe aka kuma jefa jikunkunansu a kalib.
Daga Anas dan Malik ya ce: Sahabban manzon Allah (S.A.W) sun ji shi a cikin dare yana cewa: “Ya ku mutanen Kalib, ya Utba dan Rabi’a! Ya Shaiba dan Rabi’a! Ya Umayya dan Khalaf! Ya Aba Jahal dan Hisham! Sai ya kirga duk mutanen da suke cikin Kalib; Shin kun sami abin da ubangijinku ya yi muku alkawari gaskiya ne? Ni na samu abin da ubangijina ya yi mini alkawari gaskiya ne. Sai musulmi suka ce: Ya manzon Allah! Kana kiran mutanen da sun zama mushe? Sai ya ce: Ku da kuke nan ba ku fi su jin abin da nake fada ba, sai dai su ba sa iya amsa mini[66].

2- Musulmi dukkaninsu sun tafi a kan yin sallama ga manzo (S.A.W) a salla, a yayin karewa suna cewa: Aminci ya tabbata gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarsa. Wannan sallama tana nuna yiwuwar alaka da ruhinsa (S.A.W) kai tana nuna wajabcin faruwarsa ne.

3- Ya zo daga gareshi (S.A.W) cewa: “Wanda ya ziyarce ni bayan wafatina ya yi mini sallama zan amsa masa sallama goma, kuma mala’iku goma zasu ziyarce shi suna masu yi masa sallama, wanda ya yi mini sallama a cikin gida to Allah zai mayar mini da raina har sai na amsa masa” [67].

4- Manzo (S.A.W) ya ce: “Wanda ya ziyarce ni bayan mutuwata kamar ya ziyarce ni ne a rayuwata” [68].
C- Suka ce: Idan yiwuwar alaka da mutumin da yake a duniyar barzahu ya tabbata shin ya halatta a nemi wani abu daga gareshi a kuma yi tawassuli da shi domin biyan bukatu, ko kuma wannan shi ma shirka ne da Allah saboda dalilin fadinsa madaukaki: “Hakika al’amari dukkansa na Allah ne” [69].
Amsa: Hakika dukkan al’amari na Allah ne kuma da nufinsa, da yardarsa ne al’amura suke faruwa, sai dai wannan ba ya kore tabbatar ceto ga annabawa da waliyyan Allah a duniya da lahira bayan samun izinin Allah, kamar yadda muke gani a tabbatar halitta da rayar da matacce da warkar da marasa lafiya da Isa (A.S) ya yi da izinin Allah (S.W.T).
Tunda komai yana tafiya bisa dokar sababi da dalilai sai mu ga Musa (A.S) yana cewa: “Ita sandata ce ina dogara a kanta kuma ina kakkabar ganye ga dabbobina da ita kuma ina da wasu bukatu na daban da ita” [70].
Annabawa tare da ismarsu amma sun nemi taimako da wanin Allah har sai da aka saukar da aya ga manzon Allah (S.A.W) cewa: “Ya kai Annabin Allah da wadanda suke tare da kai na daga muminai sun isar maka” [71].
Zahirin aya yana nuna cewa Annabi abin taimaka wa ne daga Allah da muminai kamar karfafa Isa (A.S) da hawariyyun yayin da ya ce: Waye zai taimake ni zuwa ga (aikin) Allah” [72]. Da kuma karfafa Musa da Haruna (A.S) kuma Allah ya amsa masa da cewa: “Zamu karfafe ka da dan’uwanka” [73] [74].
Sannan mun gani cewa Allah (S.W.T) yana neman taimakon bayinsa da cewa: “In kun taimaki Allah, zai taimake ku” [75]. Da fadinsa: “Wadannan da suka bayar da masauki kuma suka yi taimako wadannan su ne muminai” [76].
D- Suka ce: Idan muka yarda da halaccin neman taimako da tawassuli da wanin Allah domin ya kasance da izinin Allah da nufinsa, to menene dalilin neman taimako da mamaci tare da cewa abin da ya tabbata da dalili shi ne tawassuli da neman taimako da annabi ko waliyyi a rayuwarsa ba bayan mutuwarsa ba?.
Amsa: Sahabbai ba su musa tawassuli da Annabi ba a lokacin rayuwarsa da bayan wafatinsa.

27. Attawassuli Na Subhani: Daga 21-68.
28. A’arafi: 180.
29. Bakara: 127-128.
30. Ali Imran: 16.
31. Nur: 63.
32. Anfal: 33.
33. Tauba: 94.
34. Tauba: 74.
35. Nisa’i: 64.
36. Munafikun: 5.
37. Hashar: 10.
38. Inshirahi: 4.
39. A’arafi: 157.
40. Tirmizi Kitabud Da’awati, Babi 119, 3578: 5\531. Da Masnad Ahmad: 4\138, H 16789.
41. Sahih Muslim Sharhin Nawawi: 1\230, 231, 232.
42. Ibn Majah: 1\441. Hadisi 1385. Da Masnad: 4\138 H 16789.
43. Tawassuli Na Subhani: 79.
44. Tirmizi: 5\531, H 3578.
45. Ibn Majah: 1\256, H 778.
46. Kashful Irtiyab: 312.
47. Addurarus Sunniyya: 27. Da Tawassul Ila Hakikatut Tawassul: 300. Da Fatahul Bari: 7\137.
48. Addurarussunniyya Fir Raddi Alal Wahabiyya: 36.
49. Wafa’ul Wafa: 2\1361.
50. Majmu’atur Rasa’il Wal Masa’il: 1\18.
51. Sahihul Buhari: Babu Salatil Istiska’i: 2\32, H 947.
52. Wafa’ul Wafa: 2\1376.
53. Sawa’ikul Muhrika: 274.
54. Ma’ida: 35.
55. Biharul Anwar: J 93, Babi 17 H 19.
56. Biharul Anwar: J 93, B 28.
57. Sahifatul Alawiyya: 51.
58. Ikbalul A’amal Na Ibn Dawus: 2\85.
59. Sahifatus Sajjadiyya: Addu’a 44.
60. Minhajussunna Na Ibn Taimiyya.
61. Maryam: 62.
62. Gafiri: 46.
63. A’araf: 78-79.
64. A’araf: 93.
65. A’araf: 93.
66. Sahihul Buhari: 5\76, Da Sirar Ibn Hisham: 2\639.
67. Sunan Abi Dawud: 2\218. Da Kanzul Ummal: 10\38.
68. Kanzul Ummal: 5\135, H 12372.
69. Ali Imran: 154.
70. Daha: 18.
71. Anfal: 64.
72. Ali Imran: 52.
73. Kasas: 35.
74. Albarahinul Jaliyya: 42.
75. Muhammad: 7.
76. Anfal: 74.