Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

Tawassali Da Annabawa Da Salihai Bayan Mutuwarsu

Yana daga dabi’ar musulmi yin tawassuli da Annabi (S.A.W) bayan wafatinsa
1- Ya zo a Masnad Ahmad:
“Ya Ubangiji ni ina rokonka don darajar masu rokonka da tafiyata wannan, ni na fito ba domin ashararanci ba, kuma ba don takama ko riya ko jiyarwa ba, na fito ne domin neman tsari daga fushinka da kuma neman yardarka, ina rokonka da ka tseratar da ni daga wuta, ka kuma gafarta mini zunubaina domin ba mai gafarta zunubai sai kai” [77].
Wannan hadisi yana nunawa a fili a kan halaccin tawassuli da salihai su a kan kansu, ba da addu’arsu ba kawai, domin lafazin kalmar masu rokonka ya game dukkan mai rokon Allah tun daga Annabi Adam (A.S) zuwa yau, ya game dukkan mala’iku ma da muminan aljanu. Ba zai yiwu a takaita shi da masu rokon Allah a yau ba ko kuma rayayyu, domin a wannan hadisi babu dalili a kan hakan, kuma babu wani hadisin da ya zo daban ya kebance shi[78].

2- Ya zo a littafin Nisa’i da Tirmizi:
“Ya Ubangiji ina rokonka ina kuma tawassuli zuwa gareka da Annabinka Annabin rahama, ya Muhammad ya manzon Allah ina tawassuli da kai zuwa ga ubangijina a bukatata domin ya biya mini ita, ya Ubangiji ka ba shi cetona”. Wannan addu’a ce wacce musulmi suke tawassuli da annabi (S.A.W) da ita bayan mutuwarsa.

Raddi Ga Ibn Taimiyya A Kan Tawilin Wannan Addu’a

An samu sabani da Ibn Taimiyya da masu bin sa na salafiyawa da wahabiyawa a mas’alar tawassuli da annabawa da salihai bayan mutuwarsu, da suka tafi a kan cewa bai halatta ba a yi tawassuli da mamaci, ga abin da ya ce:
A Tawassuli babu addu’a domin bayi, ko neman taimako da bayi, ba komai sai addu’a da neman taimakon Allah, sai dai a cikinsa akwai rokon Allah don darajarsu, kamar yadda ya zo a cikin sunan Ibn Majah, daga Annabi (S.A.W) yana fada game da addu’ar wanda ya gama salla ya ce: “Ya Ubangiji ina rokonka don darajar masu rokonka…”.
A wannan hadisi ya roki Allah don darajar masu rokonsa, kuma Allah ya sanya wa kansa daraja (har zuwa inda yake cewa) wasu jama’a sun ce: Babu halaccin tawassuli da shi bayan mutuwarsa ko ba ya nan, kawai ana tawassuli da shi a lokacin rayuwarsa kuma a halartarsa.
Sannan sai ya fara karfafar ra’ayi na farko yana mai cewa: wannan tawassuli da shi, shi ne suke rokonsa da ya yi musu addu’a sai ya yi musu addu’a, suna tawassuli da cetonsa da addu’arsa, sai ya kawo hadisin balaraben kauye da yake cewa: “Ya manzon Allah! Dukiyoyi sun halaka, hanyoyi sun yanke, ka rokar mana Allah ya yanke shi haka daga garemu.
Ya ce: Wannan shi ne tawassulinsu da shi a neman shayarwa da makamantansu, yayin da manzo (S.A.W) ya mutu sai suka kasance suna tawassuli da Abbas. Haka nan Mu’awiya ya nemi shayarwa da Yazid dan Al’aswad Aljurshi, ya ce: Ya Ubangiji muna neman cetonka da zababbunmu, ya Yazid daga hannunka zuwa ga Allah.
Sannan sai ya kare maganarsa da fadinsa: “Babu wani daga malamai da ya halatta tawassuli da neman shayarwa da Annabi da Salihin mutum bayan mutuwarsa ko fakuwarsa, kuma ba su so hakan ba a neman shayarwa ko a wajan neman taimako da makamantan wannan na daga addu’o’i, addu’a kuwa ita ce bargon ibada[79].
A nan muna iya ganin magana mai karo da juna a fili a wajaje masu yawa na wannan magana da zamu fara nuna su kafin gabatar da dalili da ake bukata.
1- Cakuda tawassuli da Annabi (S.A.W) da kuma tawassuli da alfarma da daraja, alhali bambanci a nan a fili yake tsakanin fadinka: “Ya Muhammad ko ya manzon Allah ni ina fuskanta da kai zuwa ga Allah”, da kuma fadinka: “Ya Ubangiji ni ina rokonka domin darajar masu rokonka”, ko “Ya Ubangiji domin darajar Muhammad (S.A.W)”.
Na farko fuskanta ne da tawassuli da shi kansa.
Na biyu fuskanta ne da tawassuli da darajarsa da alfarmarsa da matsayinsa wajan Allah, A wannan nau’i na biyu na tawassuli ne annabawa da salihai suka shiga wannan kashin.
Ibn Taimiyya ya fassara ma’anar na farko a kan na biyu, wanda wannan kuskure ne.
2- Cakudawa kamar yadda ya cakuda a farko tsakanin fuskantar Allah da annabinsa da kuma neman addu’a daga gareshi, bambancinsu a fili yake, saboda haka zaka gan shi yana mai kafa hujja da hadisin balaraben kauye sai ya zo da wani bangare daga gareshi ya bar maganar da muka gabatar dazu: “Ya manzon Allah ina neman ceto wajan Allah da kai”. Wanda Annabi ya tabbatar da hakan.
3- Tanakudi da magana mai karo da juna wajan karbowa daga malamai, sannan sai ya koma ya kasa addu’a zuwa neman shayarwa da waninta domin rikita kwakwalen mutane ba wani abu ba, domin ya koma sai ya tara sauran nau’o’in addu’o’in yana mai cewa: Ba su so wannan ba a neman shayarwa ko a wajan neman taimako da makamantan wannan na daga addu’o’i.
Sannan kuma da farko ya karbo maganganun malamai na halaccin tawassuli da Annabi lokacin rayuwarsa da bayan mutuwarsa, sannan sai ya koma ya ce: Babu wani malami da ya ambaci cewa ya halatta a yi tawassuli ko neman shayarwa da Annabi ko Salihin mutum bayan mutuwarsa!
A nan zamu kawo abin da ya kai ga karo da juna a maganarsa da dalilin da shi da kansa ya yi furuci da ingancin wasusnsu da bai ambaci wani abu game da dayan ba.
Mun tabbatar mun kuma karfafa a kan cewa Dan Taimiyya bai samu wani nassi da zai yi amfani da shi ba da yake hana tawassuli da Annabi (S.A.W) sai ya rika dora ma’anar wasu hadisai a kan wasu wanda hakan ba daidai ba ne, zamu ga yadda yake dora zahirinsa a kan wani hadisin da ya inganta wanda babu wata matsala game da shi.
Yana mai karbowa daga Sahabi mai daraja Usman dan Hanif cewa: Yana sanar da mutane tawassuli da Annabi a lokacin Usman dan Affan, sannan sai ya biyo shi da wasu hadisai makamantan wannan daga magabata.
Yana cewa: Baihaki ya rawaito cewa wani mutum ya kasance yana zuwa wajan Usman dan Affan a kan wata bukatarsa, Usman ya kasance ba ya sauraronsa, ba ya kuma kallonsa a wannan bukatar, sai ya hadu da Usman dan Hanif ya kai kukan wannan wajansa, sai Usman dan Hanif ya ce da shi: Ka tafi wajan alwala ka yi alwala, sannan sai ka je masallaci ka yi salla raka’a biyu, sannan sai ka ce: “Ya Ubangiji ni ina rokonka ina kuma fuskanta zuwa gareka da annabinmu Muhammad (S.A.W) annabin rahama, Ya Muhammad ni ina fuskanta da kai zuwa ga ubangijina domin ya biya mini bukatata”. Sannan sai ka ambaci bukatarka ka tafi domin in tafi tare da kai.
Sai mutumin ya tafi ya yi abin da ya gaya masa, sannan sai ya zo wajan Usman dan Affan, sai mai tsaron kofa yazo ya kama hannunsa ya shigar da shi wajan Usman sai ya zaunar da shi a kan bargo, ya ce: Menene bukatarka? Sai ya fada, sai aka biya masa.
Sannan sai mutumin ya fito daga wajansa sai ya hadu da Usman dan Hanif ya ce masa: Allah ya saka maka da alheri, ba zai taba biya mini bukatata ba, ba ya ma kallona har sai da ka yi masa maganata, sai Usman dan Hanifi ya ce: Ai ban yi masa magana ba, sai dai ni na ji Manzo (S.A.W) wani mutum makaho ya zo wajansa ya kai kukan makancewarsa, sai Manzo (S.A.W) ya ce da shi ko ka yi hakuri…”. Sai ya ambaci hadisin har zuwa karshensa.
Baihaki ya ce: -In ji Ibn Taimiyya- Ahmad dan Shabib dan Sa’id ya rawaito shi daga babansa da tsayinsa, kuma Hisham Addistiwa’i ya rawaito shi daga Abu Ja’afar, daga Abu Umama dan Sahal, daga amminsa Usman dan Hanif, sannan sai Dan Taimiyya ya ambaci hadisin da sanadodinsa masu yawa, ya kuma inganta su, har zuwa fadinsa yana mai cewa:
Wasu magabata sun rawaito wani hadisi a kan haka, misalin abin da Ibn Abiddunya ya rawaito a littafin “Majanid Du’a” da sanadinsa: “Wani mutum ya zo wajan Abdulmalik dan Sa’id dan Abjar, sai ya dogari cikinsa ya ce: Kana da cutar da ba ta warkewa.
Sai mutumin ya ce: Menene?
Sai ya ce: Marurun ciki[80].
Sai mutumin ya juya ya ce: Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah! Ubangijina ba na shirka da wani abu da shi, Ya Ubangiji ni ina fuskanta zuwa gareka da Annabinka Muhammad Annabin rahama (S.A.W) Ya Muhammad ni ina fuskanta da kai zuwa ga ubangijinka ubangijina ya tausaya mini daga abin da ya same ni.
Ya ce: Sai ya dogari cikinsa yace: Ka warke daga ciwon.
Ibn Taimiyya ya kara da cewa: wannan addu’a da watanta an rawaito cewa magabata sun yi ta, kuma an karbo daga Ahmad dan Hanbal a “Mansak Almurzawi” game da tawassuli da Annabi (S.A.W) a cikin addu’a[81].
Wannan yana nuna bacin ra’ayinsa, da kuma bacin da’awar da ya yi a baya na cewa ba a karbo ba daga wani daga magabata da ya yi tawassuli da Annabi bayan mutuwarsa ba, wannan da’awa ce da ya dage a kanta ya kuma kawo ta a cikin littafinsa na “Attawassul Wal Wasila” [82].
Da wanann ne zai tabbata cewa abin da ya yi da’awarsa ba komai ba ne, sai dagewa a kan ra’ayi da yake batacce da dalilai suka tabbatar da bacinsa.
Gaskiyar magana ita ce; abin da ya tabbata cewa ya inganta daga magabata ya fi haka yawa sosai, ba su kuma takaita tawassuli da Annabi (S.A.W) bayan mutuwarsa ba kawai, sun yi tawassuli har da waninsa wanda suke ganinsa salihi suke kuma kudurce cewa yana da matsayi wajan Allah[83].

Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice

Mutuwa ba rashi ba ce, kuma akwai alaka tsakanin rayuwar barzahu a bisa hakika, kuma tafarkin musulmi a da, da yanzu ya gudana a kan tawassuli da annabawa da waliyyai rayayyu da matattu, ba bambanci tsakanin zatinsu da kuma addu’a. Don haka ra’ayi ingantacce shi ne mai cewa ya halatta a yi tawassuli, kuma ta bayyana cewa ra’ayin da ya hana tawassuli batacce ne.
Kamar yadda hanyar da bawa yake kusanta zuwa ga Allah da ita ba ta samuwa ta hanyar ijtihadi, shari’a ce ta dauki nauyin iyakance ta. Kuma zai yiwu a same ta daga dalilan shari’a, dukkan wata hanya ba wannan ba to bidi’a ce kuma bata ce.

77. Masnad Ahmad: 3\21. Da Sunan Ibn Majah: 1\356.
78. Azziyar Wat Tawassul Na Sa’ib Abdulhamid: 142.
79. Ziyaratul Kubur Wal Istinjad Bil Makbur: 37-43.
80. Dubaila marurun da yake bayyana a ciki kuma ya kan kashe maras lafiya.
81. Attawassul Wal Wasila: 97, 98, 101, 103.
82. Attawassul Wal Wasila: 18.
83. Azziyar Wattawassul: 148-152. Bugun Markazur Risala.