Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Wane irin ci gaba ne da kayan more rayuwa da walawala da kuma yanayi mai tsarin da zai gina ruhi da badinin dan Adam hukumar Imam Mahadi (a.s) zata samar?


Masu son hawa kan karagar mulki sukan yi bayanin hadafin hukumarsu, amma ba kasafari sukan isa kaiwa ga wannan hadafin ba, wannan kuwa yakan kasance ne saboda hadafinsu ba na hakika ba ne ko kuma tsarin da aka dauka yana da matsalar da ba zai iya kaiwa ga nasara ba, ko kuma rashin sa'ar samun masu gudanarwa marasa dacewa. A hukumar Imam Mahadi (a.s) hadafinsa na gaskiya ne, kuma tsari ne mai kamala karkashin Kur'ani da sunnar Ahlul Baiti (a.s) a dukkan fagagen gudanarwa, don haka ne ma za a samar da wani juyi mai girma da Duniya zata fuskanto zuwa gareshi, kuma a samu cikar hadafofi da dukkan kamala ta Duniya da ta lahira. A nan zamu ga wasu ruwayoyi da suke nuna wasu daga sakamakon da aka cimma na nasara a daular Imam Mahadi (a.s).

Ya zo a cikin Kur'ani mai daraja da ruwayoyi masu yawa cewa babban hadafin hukumar Imam Mahadi (a.s) shi ne samar da adalci a ko'ina a Duniya a dukkan fagen rayuwa. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: na rantse da Allah, adalci zai kutsa cikin gidajen mutane, kamar yadda sanyi da zafi suke kutsawa cikin gidaje. [1] Wannan yana nuna yaduwar adalci da hatta a cikin gidajen mutane daidaikun 'ya'yan gida daya ba sa zaluntar junansu, kuma suna zama tsakaninsu da adalci, kuma wannan adalci ne da zai tsayu a karkashin koyarwar Kur'ani da kyautatawa.

An yi bayanin cigaban tunani da kyawawan halaye da tsaro a hukumar Imam Mahadi (a.s)a wasu ruwayoyi.Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: a zamanin da Imam Mahadi zai bayyana zai sanya hannunsa a kan bayin Allah sai da albarkacin hakan hankulansu su kammala. [2] Kuma mun sani cewa dukkan kyawawan ayyuka suna karkashin cikar hankalin dan Adam ne, hankali shi ne ma'aikin badini mai hukunci kan rayuwar mutum, da gyaruwarsa ne ayyuka da tunanin mutum zasu gyaru. An tambayi Imam Ja'afar Sadik (a.s) mene ne hankali? Sai ya ce: hankali shi ne abin da ake bauta wa Allah madaukaki da shi, kuma da shi ne ake shiryuwa zuwa ga hanyar aljanna. [3]
Amma a wannan al'umma yau da muke gani wacce take ba tare da Imami ba muna ganin yadda sha'awa ta yi galaba kan hankali, da yadda aka manta da kyawawan halaye na shari'ar Allah.

Ya zo a cikin ruwayoyi masu yawa cewa; a hukumar Imam Mahadi (a.s) mutane zasu kansane cikin soyaya da kaunar juna kuma a kawar da duk wata gaba daga zukantasu Imam Ali (a.s) yana cewa: "Idan mai tsayawar cikinmu (da juyinmu) ya bayyanar… kuma gaba da juna zata tafi daga zukatan bayi…". A wannan zamani babu wani hakki na wani da zai tafi, kuma hankali shi ne mai tafiyar da rayuwa ba son rai da sha'awa, don haka babu wata gaba da ta yi saura a cikin zukata, kuma za a samu hadin kai da kaunar juna a zukata karkashin hukumar 'yan'uwantaka ta Kur'ani da koyarwar Ahlul Baiti (a.s). Imam Ja'afar Sadik yana fada game da hakan: a wannan zamani Ubangiji zai sanya haduwa da kauna a tsakanin zukata masu rarraba da kiyayya. [4]
Ba don ludufin Allah da taimakonsa ba, da dan Adam da yake cikin wannan yanayi da kiyayya da gaba da rufewar idon son Duniya bai kai ga hakan ba. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: A lokacin da Imam Mahadi (a.s) zai tsayar da hukuma za a samu abota ta kauna ta gaskiya, kuma duk mabukaci yana iya daukar gwargwadon abin da yake bukata daga aljihun abokinsa, kuma shi abokin nasa ba ya hana shi. [5]
Cututtuka hatta da masu wahalar magani a Duniya suna daga cikin mafi girman matsalar dan Adam a Duniya, wadannan kuwa sun faru ne sakamakon rashin yanayi da mahalli mai lafiya da kayan nukuliya, da atom, da maikrob, da kuma alaka ta haram tsakanin mutane, da kawar da dazuzzuka, da ruwa da kuma abubuwa masu jawo cututtukan da suka hada da kuturta, da annoba, da shan inna, da bugawar zuciya da gomomin cututtuka na zahiri da badini wadanda suka gurbata rayuwar mutane kuma ba zasu juru ba.
A cikin daular jagora kuma limamin al'umma, wasiyyin Annabi na karshen Imam Mahadi (a.s) yaduwar adalci da kuma hukuma madaidaiciya zasu sanya kawuwar wadannan cututtuka na jiki da na ruhi. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: yayin da Imam Mahadi (a.s) zai tsayar da hukuma, Allah zai kawar da dukkan wasu cututtuka daga muminai, kuma lafiya zata dawo musu. [6]
Da wannan ne duk wata cuta maras magani zata kau, kuma lafiya da koshin lafiya su mamaye ko'ina albarkacin samuwar Imam Mahadi (a.s). Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: duk wanda ya riski Imam Mahadi (a.s) idan ba shi da lafiya to zai warke, kuma idan yana da rauni to zai yi karfi. [7]

Da kafuwar hukumar Imam Mahadi (a.s) ne alheri mai yawa zai cika al'umma kuma kasa da sama kowanne zai kawo albarkatunsa. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Allah zai gudanar da albarkar sama da ta kasa saboda Imam Mahadi (a.s), sama ta yi ruwa, kasa kuma ta futo da shuka. [8] Wannan juyi mai albarka maras misali na halifana na goma sha biyu, kuma wasiyyin karshe na Annabi kuma jagoran duniya Imam Mahadi a wannan zamanim zai kai mutane ga tsarkaka da takawa da imani, kuma mutane dukkaninsu zau kasnade karkashin tarbiyyar Allah, kuma alakarsu zatakasance a bisa kyawawan halaye ne, a irin wannan yanayi ne Allah yake bayar da albarkarsa. Kur'ani mai girma yana cewa; da mutanen alkaryu (garuruwa) sun yi imani kuma sun ji tsoron Allah da mun bude musu albarkatu daga sama da kasa; [9]

A lokacin da sama da kasa suka bude albarkatunsu kuma aka cika Baitul mali, kuma aka raba dukiya da daidaito, to babu wani wuri da talauci zai samu, kuma al'umma har abada zata rabu da talauci kenan. [10] A wannan lokacin za a samu 'yan'uwantaka da kaunar juna da nisantar bin amfani da maslahar kai, kuma kowa ya zama tamkar dan uwa ga dayansa, don haka ne sai a samu yanayin na hadewa a dunkule.
Game da hukumar Imam Mahadi (a.s) ne Imam Muhammad Bakir (a.s) yake fada cewa: A kowace shekara yana bayar da kyauta sau biyu ga mutane, koma a kowane wata yana ba su sau biyu, kuma a wannan lokaci zai aiki da daidaito tsakanin mutane har sai an kai ga babu wani mai bukatar dukiyar zakka. [11] A wasu ruwayoyi ya zo cewa rashin bukatar mutane saboda wadatar zuci ne, sakamakon yarda da suka yi da abin da Allah ya ba su, kuma suna farin ciki da wannan, don haka ba sa bukatar dukiyar wasu. Manzon rahama (s.a.w) yana fada yana mai siffanta wannan daula da cewa: …Allah zai sanya rashin bukata a zukatan mutane. [12]
A dunkule muna iya cewa; a zamanin Imam Mahadi (a.s) za sa mun fitar rashin buata daga zukata, kuma za a raba dukiya da daidaito, wannan kuwa yana nuna cikar kyawawan halayen mutane. Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Ubangiji zai sanya rashin bukata a zukatan al'ummar Muhammad a wannan zamani, kuma adalcin Imam Mahadi (a.s) zai mamaye ko'ina, ta yadda Imam Mahadi (a.s) zai yi umarni ga mai shela ya shelanta cewa: waye yake bukatar dukiya? Amma ba mai tashi tsakanin mutane sai mutum daya, sai Imam (a.s) ya ce da shi: ka tafi wajen mai kula da Baitul mali ka ce masa: Imam Mahadi (a.s) ya ce ka ba ni dukiya. Sai ya tafi ya gaya masa. Sai mai kula da Baitul mali ya ce: kawo tufafinka. Da an cika masa tufafinsa da dukiay, da ya dauka sai ya yi nadama, ya ce: me ya sa na fi kowa kwadayi ne a cikin al'ummar Annabi… sai ya mayar da dukiyar ya ki karba, sai a ce masa ai ba ma karbar abin da muka riga muka bayar. [13]

Kur'ani madaukaki ya yi alkawari a wurare uku na cewa zai sanya addinin musulunci addinin Duniya gaba daya: "Shi ne wanda ya aiko Manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya dora shi a kan addini dukkanisa…". [14] Kuma babu kokwanto Allah ba ya saba alkawari. "Hakika Allah ba ya saba alkawari". [15] Duk da irin kokarin da Annabin rahama (s.a.w) da sauran waliyyan Allah suka yi sai dai har yanzu wannan rana ba ta zo ba [16], amma da sannu wannan rana da kalmar shahada zata filfila a kan tutar tauhidi zata zo, kuma za a kawar da kafirci da shirka har sai ya kasance babu wani kufai nasu da zai yi saura.
Imam Muhammad Bakri (a.s) yana fada game da ayan nan da take cewa: "ku yake su har sai ya kasance babu wata fitina kuma addini gaba daya ya kasance na Allah…[17]" cewa: Tawilin wannan aya har yanzu bai zo ba, duk wanda ya yi zamani da Imam Mahadi (a.s) zai ga tawilin wannan aya, a wannan zamani duk inda dare ya kai to addinin Muhammad (s.a.w) zai kai wurin, ta yadda babu wani kufai na shirka da zai yi saura a bayan kasa, kamar yadda Allah ya yi alkawari. [18]

A Daular jagoran zamanin karshe (a.s) za a samu aminci da tsaro mafi girma wanda yake daya daga ni'imomin Allah mafi daukaka da dan Adam yake burin samu. Matukar al'umma ta kasance mai hadafi daya, kuma ta kiyaye kyawawan halaye, kuma adalci ya mamaye dukkan rayuwa mutane a daidaiku da al'umma, to tabbas za a samu kawar da rashin tsaro da rashin aminci da zaman lafiya. Imam Ali (a.s) yana cewa: …yayin da mahadinmu zai zo sai gaba ta tafi daga zukata, dabbobi ma zasu daidaita da juna, (kuma za a samu aminci da) mace kyakkyawa da ado zata yi tafiya daga Iraki zuwa Sham… amma babu wani abu da zai tsoratar da ita. [19] Tabbas wannan lamari yana da wahalar sawwalawa ga mutumin yau sai dai idan mun duba abubuwan da zasu wakana to wannan mai saukin faruwa ne. Ubangiji madaukaki yana fada: Ubangiji ya yi wa wadanda suka yi imani alkawari cewa zai sanya su halifofinsa masu maye gurbinsa a bayan kasa kuma zai canja musu da aminci bayan". [20] Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Wannan aya ta sauka ne game da Imam Mahadi (a.s) da mataimakansa. [21]

A hukumar Imam Mahadi asiran ilimi masu yawa na ilimomin musulunci zasu bayyana, kuma ilimin mutane zai fadada ta yadda ba a tsammani. Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Ilimi haruffa ishirin da bakwai ne, kuma abin da Manzo (s.a.w) ya kawo daga ciki harafi biyu ne, mutane har yanzu ba su da ilimi sai na wadannan haruffa biyun, yayin da Imam Mahadi (a.s) zai zo zai futo da haruffa ishirin da biyar da suka rage, kuma ya yada su a cikin mutane, wadannan haruffan za a yada su tare da wadannan haruffa biyu ne. [22] Wannan ruwayoyi da wasu ruwayoyin ma suna nuni da cewa; ilimin dan Adam na masana'antu da kere-kere zai kasance yana da bambanci da na yau mai nisa kwarai da gaske. [23]
Imam Ja'afar Sadik yana cewa: idan Imam Mahadi (a.s) ya bayyana to mumini da yake gabas zai ga dan'uwansa mumini da yake yammacin Duniya. [24] Kuma yana cewa: yayin da Imam Mahadi (a.s) zai bayyana, karfin gani da ji na shi'armu zai karu, ta yadda Imam Mahadi zai yi magana da Shi'arsa daga nisan baridi daya (farsahi hudu) kuma su ma suna jin maganarsa suna kuma ganinsa alhalin yana wajensa. [25]
Game da saninsa da halin da mutane suke ciki a matsayinsa na shugaban hukuma ya zo cewa: Idan wani ya yi wata magana a gidansa to yana jin tsoron cewa; kada fa bangwayen gidansa su kai bayaninsa. [26] Idan mun yi la'akari da kayan sadarwa da ake da su fahimtar wadannan ruwayoyi yana da sauki, amma kuma ba wani abu ba ne fayyacacce, shin wadannan kayan su ne zasu fi hakan cigaba ko kuwa wani tsarin takanolaji ne sabo zai zo da shi wanda ya fi wannan da zai maye gurbin na yau.


1 Biharul anwar, j 52, shafi: 362.
2 Biharul anwar, j 52, h 71, shafi: 336.
3 Kafi, j 1, h 3, shafi: 58.
4 Kamaluddin, j 2, babi 55, h 7, shafi: 548.
5 Biharul anwar, j 52, h 164, shafi: 372.
6 Abin da ya gabata, h 138, shafi: 364.
7 Abin da ya gabata, h 68, shafi: 335.
8 Gaiba, Dusi, h 149, shafi: 188.
9 A'arafi: 96.
10 Muntakhabul asar, fasali 7, babi 403, shafi: 589 – 593.
11 Biharul anwar, j 52, h 212, shafi: 390.
12 Abin da ya gabata, j 51, shafi: 84.
13 Abin da ya gabata, shafi: 92.
14 Tauba: 33. fatahi: 28. saff: 9.
15 Ali imran, aya: 9
16
17
18 Biharul anwar, j 51, shafi: 55.
19 Khisal, j 2, shafi: 418.
20 Nur: 55.
21 Gaiba nu'umani, h 35, shafi: 240
22 Biharul anwar, j 52, shafi: 326.
23 Ta yiwu kuma ana nuni ne da mu'ujizarsa.
24 Biharul anwar, j 52, shafi: 391.
25 Abin da ya gabata, shafi: 336.
26 Abin da ya gabata, shafi: 390.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
9+2 =