Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Mene ne malaman addinin musulunci suke fada game da Imam Mahadi (a.s)?


Bayani kan Imam Mahadi (a.s) da kuma kafa hukumarsa ta Duniya wani abu ne wanda bai kebanta da littattafan Shi’a ba, al’amarin imani da shi ya hade dukkan mazhabobin musulmi. Kuma sun yi bayaninsa da fadi, kuma sun yi imani da bayyanar Mahadi (a.s) daga zuriyar Manzon Allah (s.a.w) daga ‘ya’yan Zahara [1] (a.s), mai son karin bayani yana iya komawa littattafan Sunna. Tafsirai da dama kamar Kurdabi [2] da Fakhrur razi [3] sun yi nuni da ayoyi masu yawa game da Imam Mahadi (a.s).
Haka nan marubuta hadisai na Sunna suka ruwaito hadisai masu yawa game da Imam Mahadi (a.s) kamar Sihahus sitta da kuma masnad Ahmad bn Hanbal. Wasu malaman nasu sun yi littattafai na musamman game da Imam Mahadi (a.s) kamar Abu Na’im Asfahani, a littafinsa na Arba’una Hadis, da Suyudi a littafinsa na Al’urful wardi fi akhbaril Mahadi (a.s). Da yawa malaman Sunna sun rubuta makaloli da bayanai masu yawa domin raddi kan masu musun bayyanar Imam Mahadi (a.s).
Ga wasu misalai daga ruwayoyin da suka zo ta hanyarsu:
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Da ya kasance sauran kwana daya ya rage daga Duniya, da lallai Allah ya tsawaita wannan rana har sai ya tayar da wani daga zuriyata mai suna irin nawa. [4] Abin sani shi ne; imani da wanda zai bayyana a karshen zamani domin kawo gyara da tseratar da al’umma da cika Duniya da adalci wani abu ne wanda dukkan mabiya addinan sama suka yi imani da shi bisa dogaro da koyarwar addinansu da dukkaninsu suna sauraron zuwan wannan abin alkawari mai girma ne. A littattafai masu tsarki Zabura, Attaura, Injila da littattafai irin na Hindu da Zartush da Barahma duk an yi nuni da bayyanar mai tseratar da Duniya. Sai dai kowace al’umma tana da lakabi da take ambatonsa da shi, misali; Zartush suna kiransa da “Sushyanus” ma’ana mai tseratarwa, Kiristoci suna kiransa “Masih”, Yahudawa suna kiransa da “Surur mika’ili”.
Haka ya zo a cikin littafi mai tsarki na Zartush mai suna “Jamasb Nameh” kamar haka: “Annabin larabawa shi ne Annabin karshe wanda zai bayyana a tsakanin duwatsun Makka… zai rika cin abinci tare da bayinsa, kuma zai rika zama irin na bayi… addininsa shi ne mafi daukakar addinai, kuma littafinsa shi ne zai shafe dukkan littattafai… kuma daga ‘ya’yan ‘yar Annabin da take ranar Duniya kuma mai suna sarauniyar zamani, wani sarki zai fito (ta tsatsonta) da zai yi hukunci a Duniya da hukuncin Allah, wanda yake shi ne kuma halifa na karshe na wannan Annabi… kuma daular da zai kafa zata tuke har zuwa tashin kiyama. [5]


1 - Almustadrik alas sahihaini: j 4, shafi 557.
2 Tafsirul kurdabi: j 8, shafi 121.
3 - Tafsirul kabir: j 16, shafi 40.
4 - sunan abu Dawud: j 2, h 4282, shafi: 106.
5 - Adyan wa mahdawiyyat: shafi: 21.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
6+3 =