Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Yaya Duniya zata kasance kafin bayyanar Imam Mahadi (a.s)? kuma shin bayyanar tasa tana da wasu sharudda kuwa ko kuwa? Kuma shin akwai wani taimakon Allah a kan hakan ko kuwa sunnar dokoki ce kawai take aiki?


Bayyanar Jagoran Juyin Duniya Imam Mahadi (a.s) tana da sharudda da alamomi wadanda suke almanta yanayin bayyanarsa da tasiri mai karfi da cikarsu yana daga cikin abin da zai kawo bayyyanarsa, wadanda idan babu su to bayyanarsa ba zata wakana ba. Amma kafin mu shiga bayanin alamomin bayyanarsa zamu fara da kawo yanayi da sharuddan da zasu gabaci bayyanarsa, sannan kuma sai daga karshe mu kawo takaictaccen bayani game da alamomin bayyanarsa.

Dukkan wani abu yana da sharudda da yanayin share fagen bayyanarsa wadanda idan babu su to ba yadda zai wakana. Kamar shuka ce da take bukatar ruwa da iska da iri da suka dace da ita, da kuma lokaci da kasa mai kyau da suke sharadi ne na dole domin samun kaiwa ga sakamako mai kyau.
A bisa wannan asasi duk wani juyi na al'umma yana da yanayi da sharudda da suke damfare da shi, kamar juyin Iran na musulunci da kuma sauran juyi da suke tare da gabatarwa domin su kai ga cin nasara. Haka nan ma mafi girman juyi a tarihin dan Adam na Imam Mahadi (a.s) kuma motsi mafi girma na Duniya yake, idan babu wadannan gabatarwa babu yadda zai wakana, domin shi ma juyi ne da yake kan sunnar Allah da kuma sabubba.
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Ubangiji ya ki yarda sai dai al'amura su kasance bisa sabubansu. [1]
A wata ruwayar Imam Muhammad Bakir (a.s) da yake amsa jawabin wani mutum da yake cewa da shi: Ana cewa zamanin da Imam Mahadi (a.s) zai bayyana komai zai kasance bisa nufinsa ne. Sai Imam (a.s) ya ce: Ba haka ba ne. Na rantse da wanda raina yake hannunsa da Ubangiji zai yi wa wani mutum hakan to da ya yi hakan ga Manzon Allah. [2]
Amma wannan ba ya nufin cire taimakon Allah a cikin harkar Imam Mahadi ba, abin da ake nufi shi ne bayan taimakon Allah kuma akwai sharudda da yanayi da zai yi riko da su. Mafi muhimmancin yanayoyin da zasu gabaci juyin juya halin Duniya na Imam Mahadi (a.s) abubuwa hudu ne da zamu kawo bayaninsu kamar haka daya bayan daya:

1-Samar da tsari gamamme wanda zai yi fada da rashin kyawawan halaye da miyagun dabi'u;
2-Doka mai dacewa da zata lamunce dauke bukatun al'umma da hakkokin daidaikun mutane a bisa tsari guda daya na adalci na hukuma da kuma samar da wani motsi na cigaban al'umma domin samar da yanayi mai dacewa;
Koyarwar Kur'ani da sunnar ma'asumai su ne musulunci na gaskiya kuma su ne dokoki tabbatattu wadanda suke hannun Imam (a.s) kuma a bisa asasinsu ne zai yi hukunci da adalci a daularsa. [3] A cikinsu akwai duk bukatu na Duniya da lahira, kuma wannan yana nuna cewa juyin Duniya zai kasance mai dokoki da babu kamarsu, kuma ba za a iya kwatanta wani juyi da shi ba. Babban dalili kan haka shi ne; muna iya ganin Duniya a yau ta shaida bayan jarraba tsari iri-iri cewa tsari da dokoki da take a kai masu rauni ne da ba zasu iya warware matsalar dan Adam ba.
Alwin Taplar masani mai shawara kar harkokin siyasa ba'amurke yana fada game da matsalolin al'umma da kuma hanyar gayara a Duniya a nazarin "guguwa ta uku" [4] ya yi furuci da hakan yana cewa: "Matsalolin yammacin Duniya ba zasu kare ba, da ganin abin da yake faruwa na cigaban masana'atu da gurbacewar badinin dan Adam da halayensa da fasadi da rashin samun kosar da bukatunsa, da rushewar kyawawan halaye, da guguwar rashin yarda, da kuma takurawa domin kawo canji. Kuma saboda amsa wadannan al'amura an yi tsari masu yawa da suke da'awar warwara ta asasi hatta ma ta juyin juya hali kuma a lokuta masu yawa an sanya dokoki da tsare-tsare, da sababin dokoki da gyaran fuska da kwaskwarima garesu, amma duk da haka matsaloli sai daduwa suke yi kuma ana dada samun gajiyawa da yanke kauna, wannan tsari kuwa ga kowace irin demokradiyya tana da hadari…".

Da akwai bukatar jagoranci mai tasiri a kowane irin juyi, kuma shi wani abu ne wanda yake dole domin samara da juyi kuma duk sa'adda hadafi ya kasance mafi girma kuma juyi ya kasance mafi fadi to bukatar jagora mafi karfi da iko tana karuwa daidai girman wannan hadafin. Don haka domin samun jagora mai adalci da hukunci wanda zai yi jayayya da zaluncin Duniya dole ne ya kasance jagora ne mai karfi da iko da kuma iya tafiyar da al'amura kuma mai yanke hukunci yanke, kuma wannan asasi ne na asali a kowane juyi.
Imam Mahadi shi ne ragowr ajiyar Allah a Duniya kuma jagoran wannan juyi, a sakamakon alakarsa da Allah da dukkan halittunsa ne yake da cikakkiyar masaniya da abin da zamaninsa yake bukata; Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: "Ku sani cewa; Imam Mahadi (a.s) shi ne mai gadon dukkan ilimomi, kuma shi yana da masaniya game da dukkan ilimomi". [5]


1 Mizanul hikima, j 5, h 8166.
2 Gaiba, nu'umani, babi 15, h 2.
3 Biharul anwar, j 51, shafi: 141.
4 Juyi na farko da na biyu: na Noma da na Sana'a, na uku kuma shi ne na Kayan Wuta da Iliktrik.
5. Najamus sakibi, shaif: 193.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
7+9 =