Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Mece ce boyuwar Imam Mahadi (a.s) mai gajeren zango? Muna son mu samu bayanin wasu hikimomin da suke cikinta?


Idan mun yi la'akari da abin da aka fada a baya zamu ga cewa boyuwar Imam Mahadi (a.s) wani abu ne wanda yake tilas, amma idan mu ka duba dukkan na'uin wata gwagwarmaya da wani motsi da wadanda suka gabace mu suka yi zamu ga cewa an yi ta ne domin karfafa imani da akidar mutane ne. kuma akwai abin da ake jin torso na cewa kada buyan nasa ya haifar da wani miki da ba mai warkuwa ba ne a cikin addinin musulunci, amma al'amarin boyuwa zamu ga cewa al'amari ne da aka shirya shi ya farar da tsari da lura mai zurfi kuma a kan haka ne ya ci gaba.
Shekaru masu yawa kafin haihuwar Imami na goma sha biyu, maganganu da yawa game da shi sun zo daga harsunan manyan waliyyai kuma imamai (a.s) da sahabbansu. Haka nan nau'in alakar Imam Askari da Imam Hadi (a.s) da sahabbansu ya kasance ne bisa wani yanayi na musamman kuma sabo wanda ba a saba da shi ba kuma iyakantacce sosai, ta yadda shi'a suka saba da wani mai shiga tsakaninsu da imamai (a.s) wajen sanin addininsu ba tare da sun ga Imam (a.s) kai tsaye ba.
Haka nan bayan mutuwar Imam Hasan Askari (a.s) alakar Shi'a da imaminsu Imam Mahadi ba ta katse gaba daya ba, sai dai mutane suna samun alaka da shi ne ta hannun wakilansa. Ta haka ne Shi'a suka saba da cewa ba dole ne sai sun yi alaka da Imami (a.s) kai tsaye wajen sanin addininsu da aikace-aikacensu ba, kuma hakan ba sharadi ba ne garesu. A bisa wannan yanayi ne ya zama ya yi daidai Imam Mahadi (a.s) ya shiga boyuwa mai tsayi, kuma a yanke alakarsa da mabiyansa sabanin yadda aka saba a farko. Kuma zamu kawo wasu bayanai game da boyuwarsa mai tsawo da dogon zango.

Bayan shahadar Imam Hasan Askari Imami na goma sha daya (a.s) a shekarar hijira 260, daga wannan lokaci ne karamar boyuwa ta fara har zuwa shekara ta 329 kusa shekaru 70 kenan. Kuma mafi muhimmancin lamarin wannan lokaci shi ne alakar mutane da Imam Mahadi (a.s) tana kasancewa ne ta hanyar wakilai kuma ta hanyarsu ne ake aika masa da tambaya ana kuma karbar amsa. Kuma wani lokaci har da sa hannunsa ake samu ta hanyar su. [1] Wadannan wakilai na musamman dukkaninsu suna daga cikin malaman Shi'a wadanda Imam Mahadi (a.s) ya zaba daga cikin malamai domin su kasance 'yan sakonsa wadanda su hudu ne kamar haka:
1- Usman dan Sa'id Umari; wakilin Imam Mahadi daga farkon boyuwa kuma ya mutu a shekarar 265, kuma shi ne wakilin Imam Hadi da Imam Askari (a.s).
2- Muhammad dan Usman Umari; dan wakili na farko wanda ya samu matsayin wakilcin Imam Mahadi (a.s) bayan mutuwar dansa, shi kuma ya mutu a shekarar 305 hijira.
3- Husaini dan Ruhu Nobkhati ya mutu a shekarar 326, bayan ya yi shekara 21 yana wakilcin Imam Mahadi (a.s).
4- Ali dan Muhammad Samuri; ya mutu a shekarar 329, kuma da mutuwarsa ne karamar boyuwa lokacinta ya kare gaba daya, kuma aka shiga dogowar boyuwa. Wadannan wakilai na Imam Hasan Askari da Imam Mahadi (a.s) su ne suke zabarsu da hannunsu, aka kuma sanar da su ga mutane.
Sheikh Dusi yana rawaitowa a littafinsa na "Al'gaiba" cewa: wata rana mutane arba'in daga shi'a sun kasance tare da Usman dan Sa'id amari wakilin Imam Mahadi na farko a wajen Imam Askari (a.s) sai Imam (a.s) ya nuna musu dansa da yake gabansa ya ce: Bayana wannan yaron shi ne imaminku. Ku yi biyayya gareshi… ku sani cewa daga yau ba zaku sake ganinsa ba har sai shekarunsa sun cika. A boyuwarsa duk abin da Usman ya gaya muku ku yarda da shi ku karbi umarni daga gareshi, domin shi ne wakilin imaminku, kuma dukkan ayyuka suna hannunsa. [2]
A wata ruwayar ya zo cewa; Imam Hasan Askari da Imam Mahadi (a.s) sun yi magana suna masu fada karara game da wakilcin Muhammad dan Usman wakili na biyu na Imam Mahadi (a.s).
Sheikh Dusi yana cewa: Usman dan Sa'id yana tattara dukiyoyin shi'ar Yaman da umarnin Imam Hasan Askari (a.s) yana kawowa, wasu mutanen sun san abin da yake gudana sai suka zo suka gaya wa Imam (a.s), sai ya ce: Na rantse da Allah! Usman yana daga mafifitan Shi'a'rmu, kuma da wannan aikin da yake yi yana dada bayyana garemu a fili (cewa shi mutumin kirki ne).
Imam Hasan Askari (a.s) yana cewa: Haka ne; ku shaida Usman dan Sa'id wakilina ne, kuma dansa Muhammad wakilin dana ne. [3] Wannan ya kasance a lokacin kafin boyuwar Imam Mahadi (a.s) ne, kuma a tsawon wannan boyuwar tasa karama kowane daga wakilansa kafin mutuwarsa aka umarce shi da ayyana wani wakilin da umarnin Imam Mahadi (a.s).
Wadannan mutanen sun cancanci wakilci ne saboda siffofi na gare da suke da su, sun ada amana da tsarkaka da adalci a magana da aiki, da rike sirri, da boye sirrin Ahlul Baiti (a.s). Kuma su mutane ne da ake dogara da su da kuma yada mazhabar Ahlul Baiti (a.s).
Wasu daga cikinsu tun suna da shekaru 11 suke tare da tarbiyyantarwar imamai (a.s), kuma iliminsu yana tare da imani mai karfi a tare da su. Sunansu na gari ya yadu a harsunan mutane, tare da hakuri da juriya da dauke duk wata matsala da nauyi da wahalhalu da ya cakuda da samuwarsu, ga kuma cikakkiyar biyayyarsu ga imaminsu (a.s). Hada da dukkan wadannan siffofi na gari kyawawa kuma suna da karfin tafiyar da al'amuran Shi'a da cikakkiyar fahimta da kamala da sanin zamaninsu da amfana daga al'amura, da kuma shiryar da al'ummar Shi'a zuwa ga tafarki na Ubangiji na shiriya kuma suka wuce karamar boyuwa da aminci.
Binciken karamar boyuwa da kuma rawar da muhimmiyar gudummuwar da wakilai hudu suka bayar wajan samar da alaka tsakanin Imam Mahadi (a.s) da al'umma yana nuna wani bangare mai muhimmanci na rayuwar Imam Mahadi (a.s). Kuma samuwar wannan alaka da kuma samun damar ganin Imam (a.s) ga wasu jama'a na Shi'arsa a tsawon wannan boyuwa yana da tasiri mai yawa wajen tabbatar da tabbacin haihuwa da samuwar Imam Mahadi (a.s) Imam na goma sha biyu kuma karshen hujjar Allah a Duniya. Wannan ci gaba mai girma da aka samu ya faru ne a daidai lokacin da makiya suke kokarin ganin sanya shakku game da samuwar haihuwar dan Imam Hasan Askari (a.s), hada da cewa lokacin ya yi daidai da faruwar babbar boyuwa wanda a cikinta mutane ba su da wata alaka ta saduwa da haduwa da imaminsu ta hannun wasu mutane ayyanannu, amma da samuwar wannan nutsuwa ta zuciya a wannan lokuta da kuma amfanuwa daga albarkar samuwarsa sun share fagen boyuwarsa babba.


1 Akwai misalign irin wannan sa hannun ya zo a littafin biharul anwar: j 53, babi 31, shafi: 151 – 197.
2 Gaiba, Dusi, fasali 6, h 319, shafi: 357.
3 Gaiba, Dusi, fasali 6, h 317, shafi: 355.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+10 =