Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Muhimmancin tsarin zamantakewar al'umma ba kasa yake da na tsarin al'adunsu da tattalin arizikinsu ba a muhimmanci, don haka muke son mu ji wane irin tsari ne Daular imam Mahadi (a.s) zata yi wannan lamari mai muhimmnaci?


Kula da tsarin zamantakewar al'umma yana daga mafi muhimmancin gyara a cikin al'umma, don haka a tsarin hukumar Imam Mahadi (a.s) an bayar da muhimmanci matuka ga koyarwar Kur'ani da sunnar ma'asumai (a.s) wajen ganin an gudanar da tsarin zamantakewar al'umma maras misali a Duniya. Wadannan tsare-tsare za a yi nuni da su kamar haka:

A hukumar Imam Mahadi (a.s) za a gudanar da umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, kuma wannan wajibi ne da aka karfafa shi a cikin Kur'ani mai girma a matsayin siffar al'ummar musulmi ce domin ganin an samu kurbutar al'umma daga rushewa. [1] Shi wajibi ne kuma umarin Allah da sauran wajibai ba sa daidaituwa sai da tsayar da shi [2], kuma an shar'anta shi ne domin kawar da duk wani abu da zai iya halaka al'umma da zai bice da kyawawanta.
Sannan yana daga cikin mafi tsarin horo da kyakkyawa da hani ga mummuna shugaban hukuma da ma'aikatansa su kasance sun siffantu da kyawawa da kuma nisantar munana. Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: Mahadi da shabahbbansa suna umarni da kyakkyawa suna kuma hani gamummuna. [3]

Daular Ubangiji ba zata takaita ga magana da harshe ba kawai; kawar da dukkan munkari da miyagun halaye daga cikin al'umma da kuma tsarkake al'umma daga dukkan wani mummuna yana daga cikin aibn da zata aiwatar. A cikin addu'ar nuduba ya zo cewa: Ina mai yanke igiyoyin karya da kage, ina mai tsige dukkan kufai na karkata da bata da son rai!? [4]

Yakar fasadi a al'umma yana da hanyoyi mabambanta, kuma hukumar Imam Mahadi (a.s) ta wani bangare tana koyar da mutane ilimi na akida da imani da koyar da al'adun musulunci domin ganin an gyara fasikai an dora su zuwa ga hanyar shiriya da gyara. Ta wani bangare kuma tana samar da abubuwan bukata na hankali da shari'a domin gudanar da adalcin zamantakewar al'umma kuma tana toshe duk wata kafa ta fasadi da barna. Amma duk da haka akan iya samun wasu masu ketare iyaka da take hakkin mutane da na Ubangiji wanda dole ba zata yarda da hakan ba, don haka irin wadannan dole ne daula ta dauki mataki kwakkwara a kansu, kuma ta gudanar da hukuncin Allah a kansu domin kawar da dukkan wata barna kamar yadda dokokin musulunci suka tanada.
A wata ruwaya daga Manzon rahama (s.a.w) da kuma Imam Muhammad Jawad (a.s) ya zo cewa: Imam Mahadi (a.s) zai tsayar da haddodin Allah. [5]

Gwamnatin Imam Mahadi (a.s) zata zo domin ta gudanar da adalci a dukkan Duniya ta kuma cika ta da shi kamar yadda aka cika ta da zalunci, amma daya daga mafi girman hanyar kawo adalci shi ne hukunci da gaskiya na adalci, kuma wannan shi ne bangaren da mafi yawancin zalunci a Duniya yake wakana daga gareshi, ta haka ake zubar da jini kubutacce, kuma a ba wa maras hakki hakkin mai hakki, sannan kuma a kawo wasu dokoki da suke taskace wasu amfani ga masu karfi da dukiay domin amfaninsu na kashin kansu.
Hukumar Imami Jagora (a.s) zata kawo karshen dukkan irin wadannan zalunci da kawo gaskiya da adalcin Allah a kowane fage, zata samar da kotun adalci da alkalai masu gaskiya masu tsoron Allah, ta yadda babu wani waje a Duniya da wani mutum zai kasance karkashin zalunci.
Imam Ridha (a.s) yana fada game da siffanta Imam Mahadi (a.s): Idan ya bayyana sai Duniya ta haskaka da hasken Ubangijinta, kuma a sanya ma'auni na adalci tsakanin mutane, babu wani da zai zalunci wani. [6]


1. Ali imrana: 11.
2. Mizanul hikima, tarjama j 8, shafi: 3704.
3. Biharul anwar: j 51, shafi: 47.
4. Mafatihul jinan: Nudba.
5. Biharul anwar: 52, babi 27, h 4.
6. Biharul anwar, j 52, shafi: 321.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+3 =