Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Duba zuwa ga muhimmancin rawar farko da Tsarin tattalin arziki yake takawa wajen tafiyar da duniyar yau, sannan kuma a daya bangaren akwai sukurkucewarsa da lalacewarsa da ta sabbaba wahalhalun rayuwa a duniya, wane irin tsari ne Imam Mahadi (a.s) zai yi


Daga cikin alama ta al'umma mai kwanciyar hankali da yalwa shi ne dukiyar kasa ta kasance ba a hannun wasu jama'a kebantattu take ba, kuma al'umma gaba daya ta kasnace tana amfana daga wannan arziki. A cikin Kur'ani da ruwayoyin ma'asumai (a.s) an bayar da muhimmanci mai girma da yawa ga yanayin rayuwar mutane da tattalin arzikinsu. Don haka ne ma ya zo cewa Imam Mahadi (a.s) zai bayar da muhimmanci ga wannan al'amari kuma a bisa wannan asasin ne zai fuskanci haifar da kayan masarufi da kuma amfani da kayan ma'adinai da albarkatun kasa, sannan kuma dukiyar da aka samu zai raba wa al'umma bisa daidaito da zamu yi kokarin duba wasu daga ruwayoyi game da hakan.

Rashin amfana daga albarkatun kasa ta hanyar kwarai yana daga matsalolin da suka mamaye tattalain arziki, ba a amfana daga kasa ko ruwa, kuma ba a amfana ta hanyar raya kasa. Amma a hukumar Imam Mahadi (a.s) saobda albarkar hukumar adalci da gaskiya wannan hukumar zata kasance ta baiwa da kyauta, sannan kuma kasa zata fitar da komai na arzikinta. Imam Ali (a.s) yana cewa: …da Imam Mahadi (a.s) ya bayyana da Duniya ta saukar da ruwanta, kuma da kasa ta fitar da tsironta…. [1] Kuma Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: za a nade masa kasa, kuma taskokinta zasu bayyana gareshi…. [2]

Taskace dukiya da arzikin kasa a hannun wasu jama'a daidaiku –da kowane irin dalili ne kuwa- domin amfanin kashin kansu shi ne daya daga cikin matsalolin al'umma mafi girma, don haka ne ma Imam Mahadi (a.s) zai yi yaki da wannan kuma zai sanya dukiyar kasa a hannun mutane bisa daidaito. Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: idan mai tsayar da hukumar Ahlul Baiti (a.s) ya bayyana to zai raba dukiya bisa daidaito, kuma ya yi adalci a cikin al'umma.... [3] A wannan zamanin za a gudanar da asalin asasin daidaito, kuma kowa zai amfana daga hakkokinsa na 'yan'adamtaka kuma da wanda Allah ya huwace masa na arzikin kasa.
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Ina yi muku bishara da Imam Mahadi da zai zo cikin al'ummata… kuma zai raba dukiya da daidaito. Sai wani mutum ya tambaya me ake nufi da wannan ? Sai ya ce: zai yi rabo tsakanin mutane da gudanar da daidaito. [4] Da wannan ne za a kawar da talauci da fatara daga cikin al'umma kuma a kawar da bambancin dabakoki cikin al'ummu. Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: Imam Mahadi (a.s) zai yi hukunci da daidaito tsakanin mutane, har sai an rasa wani mabukaci da zai karbi zakka.[5]

Saudayawa raya kasa yakan kebanta da masu jin dadin kasa da masu mulki da mahukumta a dauloli da hukumomi, amma dabakar talakawa da miskinai su kam sukan zama abin mantawa ne, amma hukumar Imam Mahadi (a.s) zata game kowane mutum a tsarinta na raya kasa. Game da hukumar Imam Mahadi (a.s) Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: …babu wata kasa da zata rage sai ya raya ta…[6]


1. Biharul anwar, j 10, shafi: 104. khisal: 626.
2. Kamaluddini, j 1, babi 32, h 16, shafi: 603.
3. Nu'umani, babi 13, h 26, shafi: 242.
4. Biharul anwar, j 51, shafi: 81.
5. Abin da ya gabata, shafi: 390.
6. Kamaluddini, j 1, babi 32, h 16, shafi: 603.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
2+1 =