Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Duba zuwa ga muhimmancin al'amuran wayarwa da kuma al'adun al'umma na gari, wane irin tsari da shir ne Daular jagoran Duniya ta yi domin cimma wannan burin?


Bayan sanin hadafin hukumar Jagoran Duniya (a.s) sai mu yi kokarin sanin tsarin da zai gudanar domin kaiwa ga wannan hadafin. Idan mun duba ruwayoyi masu yawa da suka zo game da tsarin hukumarsa (a.s) zamu ga sun kasu gida uku ne kamar haka: tsarin wayewa da al'adu, tsarin zamantakewar al'umma, da, tsarin tattalin arziki.
Sanannen abu ne cewa sakamakon nisanta da koyarwar Kur'ani da Ahlul Baiti (a.s) duniyar dan Adam ta samu matsaloli da fadawa cikin rushewa a wadannan janibobi na rayuwarta, amma da koma zuwa ga Kur'ani da Ahlul Baiti (a.s) togyara da cigaba da aminci zai mamaye dukkan wadannan janibobi muhimmai a rayuwar dan Adam.
Bayan mun kawo bayanai kan tsarin hukumarsa to zamu yi bincike game da su a ruwayoyi dalla-dalla don haka ne yanu zamu fara binciken mafi muhimmancin tsare tsarensa (a.s).

A Daular Imam Mahadi (a.s) akwai tsari na habakar ilimi da kuma aiki na gari da al'umma zata durfafi yinsa, kuma zasu sanya wando daya da jahilci da rashin ilimi. Mafi muhimmanci a wannan janibi sun hada da:

Bayan tsawon lokaci da aka dauka da wurgar da littafin Allah da sunnar Annabisa, za a samu dawowar littafin Allah da sunnar Annabinsa a aikace da zarar an kafa hukumar Imam Mahadi (a.s).
Game da siffanta wannan hukuma ta Kur'ani ta Jagoran Duniya Imam Mahadi ce Imam Ali (a.s) yake cewa: A lokacin da son rai yake shuganbanci sai Imam Mahadi (a.s) ya bayyana ya mayar da aiki da gaskiya mai makon son rai, kuma a wannan zamani da ake gabatar da ra'ayin mutum a kan Kur'ani sai ga shi ya mayar da tunanin mutane kan Kur'ani, kuma ya sanya shi mai hukunci a kan al'umma. [1]
A wata ruwayar yana cewa: Kai ka ce ina ganin mutane yanzu a masallacin Kufa, an sanya hema, kuma ana koyar da mutane Kur'ani kamar yadda ya sauka. [2]

Kur'ani mai girma da koyarwar Ahlul Baiti (a.s) sun karfafi kiyaye kyawawan halaye domin wannan shi ne babban abin da zai haifar da ci gaban dan Adam zuwa ga kaiwa ga hadafin halittarsa. Kuma hadafin ma'aiki mai tsira da aminci shi ne kammala kyawawan halaye [3], domin haka ne Kur'ani yana sanar da mu cewa shi ne ya fi kowa kyawawan halaye. [4] Don haka hukumar Imam Mahadi (a.s) hukuma ce ta ubangji da a kan tsarinta kyawan halaye su ne suke gaba a dukkan Duniya.
Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: "Idan Imam Mahadi (a.s) ya zo zai sanya hannunsa a kan bayi sai ya tara hankulansu, kuma ya cika kyawawan halayensu. [5]
Wannan al'amarin yana nuna mana cikar kyawwan halaye da zai wakana sakamakon kafa hukumar adalci ta Imam Mahadi (a.s), da kuma kamalar hankalin dan Adam, a lokaci guda kuma ga Kur'ani da sunnar Allah suna jagorantar mutane zuwa ga shiriya da aikata kyawawan halaye.

Kawo juyin ilimi yana daga cikin tsarin hukumar Imam Mahadi (a.s) wanda shi kansa shi ne malamin wannan zamani gaba daya [6] da yake makomar ilimi. Manzon rahama ya yi nuni da wannan lamarin game da zuwan Imam Mahadi (a.s) yana cewa: "…kuma dukkan Duniya zata amfana daga iliminsa, bayan ta cika da jahilci da rashin ilimi…”. [7]
Sannan kuma wannan lamarin bai bar mata a baya ba kamar yadda zamu iya ganin a cikin ruwayar hadisin Imam Muhammad Bakir (a.s) da yake cewa: A zamanin Imam Mahadi (a.s) za a ba ku ilimi da zai kai ga mace a cikin gidanta tanan yin hukunci daidai da abin da yake a littafin Allah da sunnar Manzonsa. [8] Wannan lamarin yana nuna mana ilimi mai zurfi na wannan zamani domin kuwa mun san hukunci da Kur'ani da ruwayoyi al'amari ne mai wahalar gaske.

Bidi'a tana sabanin sunna ce kuma tana nufin kawo sabon abu da shigar da shi cikin addini, kamar sanya ra'ayin mutum a addini. Imam Ali (a.s) yana fada game da bidi'a: "Bidi'a hanya ce tawanda yake sabawa da umarnin Allah da na Manzonsa, kuma yana aiki bisa ra'ayi da son ransa…". [9] Don haka bidi'a sabawa ne da littafin Allah da Manzonsa da kuma sanya hukunci na son rai da aiki bisa ra'ayin mutum. Bidi'a wata abu ce da take kashe sunna da kuma tafarkin Allah (s.w.t).
Imam Ali (a.s) yana fada: Ba abin da ya rusa addini kamar bidi'a. [10] Don haka ne ma ya zama wajibi a kawar da bidi'a, kuma a nuna wa mutane hanya tagaskiya.
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Duk sa'adda bidi'a ta bayyana a tsakanin al'ummata, to yana kan malami ya bayyanar da iliminsa, duk wanda bai yi haka ba, to Allah ya nesantar da shi! [11] Amma abin takaici duk da wannan fadin na Manzon rahama da haskaka hanyar gaskiya ga al'umma, wace irin bidi'a ce ba a kawo ta cikin addini ba?! kuma wace irin karkacewa ce ba a kawo ta ba?! wane irin bata ne ba a ja mutane a kansa ba?! Kuma duk da irin kokarin da imamai (a.s) suka yi da su da malaman da suka biyo bayansu amma sai ga bidi'a ta cika addini!.
Sai ga shi har yanzu Duniya ba ta gushe ba tana sauraron mai tseratarwa wanda Kur'ani ya yi bayanin zuwansa wanda a karkashin hukumarsa za a tsige bidi'a gaba daya.
Imam Muhammad Bakir (a.s) yana siffanta Imam Muhammad Mahadi (a.s) da cewa:… ba zai bar wata bidi'a ba sai ya kawar da ita, kuma ba zai bar wata sunna ba sai ya tsayar da ita…[12]


1. Nahajul balaga, huduba: 138.
2. Nu'umani, babi 21, h 3, shafi: 333.
3. Mizanul hikima: j 4, shafi: 1530.
4. Ahzab: 21.
5. Biharul anwar, 52, shafi: 336.
6. Gaiba, nu'umani, babi 13, h: 1.
7. Biharul anwar, j 36, shafi: 253.
8. Nu'umani: 239. biharul anwar, j 52, shafi: 352.
9. Mizanul hikima, h: 1632.
10. Biharul anwar, j 78, shafi: 91.
11. Mizanul hikima, h 1649.
12. Biharul anwar, j 58, h 11, shafi: 11.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
5+5 =