Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

A lokacin bayyanar jagoran juyin duniya (a.s) yaya duniya zata kasance? Kuma shin wannan yanayin har yanzu bai faru ba?


Mun yi nuni da boyuwar Imami na sha biyu (a.s) da kuma hikimar hakan a bangaren da ya gabata, sannan bayan an samu yanayin da ya dace da bayyanarsa sai ya bayyana domin mutane su amfana daga shiriyarwarsa kuma Duniya ta iya amfana daga sumuwarsa. Amma dole ne mutane su yi aiki wanda zai iya samar dawannan yanayi domin ya bayyana da gaggawa. Amma sakamakon biyayya ga shedan da kaucewa koyarwar Kur'ani da kuma karkacewa daga tafarkin gaskiya na jagorancin imamai (a.s) masu tsarki sai ga shi bayyanar Imami (a.s) ta tsawaita, kuma a sakamakon zabar wadancan hanyoyi sai ga shi mummuna ya haifu (faru).
Sai ga shi Duniya a yanzu wacce take cike da zalunci da fasadi ta kai ga rashin aminci da kyawawan halaye da kuma nisanta daga kyawawa da ayyuka na gari da kuma ketare iyakar da danne hakkokin dan Adam da suke faruwa a wannan yanayin na boyuwar Imam Mahadi (a.s). Wannan kuwa al'amari ne da imamai (a.s) suke yi hasashen faruwarsa.
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana gaya wa daya daga sahabbansa: "A lokacin da ka ga zalunci ya mamaye ko'ina an mance da Kur'ani kuma an bi son zuciya, kuma mabarnata sun wuce gaban masu gaskiya, masu imani sun zabi yin shiru, kuma an yanke zumunci, an yawaita roko, hanyoyin alheri sun zamanto ba tare da mai jagoranci ba, kuma an bayar da hankali wajen hanyoyn sharri, haram ta zama halal, halal kuma ta zama haram, kuma an kashe kudi masu yawa wajen barna da fushin Allah, an yada cin rashawa tsakanin ma'aikatan daula, kuma an samu dimuwa mai yaduwa kuma babu wani wanda zai iya shan gabanta, jin gaskiyar da take cikin Kur'ani ta kasance mai nauyi ga mutane, amma jin barna ya kasance mai sauki garesu, kuma suna tafiya hajji ba domin Allah ba, kuma zukatan mutane sun kekashe, idan kuma wani ya yi umarni da kyakkyawa sai su yi masa nasiha cewa wannan ba aikinka ba ne, kuma kowace shekara sabuwar fasadi da bidi'a sai bayyana suke dada yi! To ka yi hattara da kanka ka kuma nemi hanyar mafita wajen Allah madaukaki kuma ka nemi fita daga wannan hanya domin bayyanar Imam Mahadi tana kusa. [1]
Wannan lamari kuwa yana bayani game da yanayin da yake aukuwa a wannan zamani kafin bayyanar Imam Mahadi (a.s), kuma a wannan zamanin ne masu biyayya ga tafarkin gaskiya suke dada karfin imani da riko da tafarkin imaman shiriya masu tsarki, kuma wadannan su ne mafifita daga bayin Allah masu daukaka, wadanda aka yabe su a ruwayoyi masu yawa da suka zo daga imaman haske da shiriya (a.s). Sun yi rayuwa mai tsarki kuma suna kiran wasu su zo domin su rayu rayuwa mai tsarki, domin samar da yanayi mai kanshi da hasken imani da kuma bayyanar kyawawan halaye da kuma share fagen samuwar tsayuwar hukumar kyawawa da adalci da kawar da munana wanda wannan al'marin zai taimaka wa mai gyara da aka yi alkawarin zuwansa. kuma wannan tunani na tsayawa kyam domin ganin an kawo karshen barna da fasadi ba domin komai ba ne sai domin neman gaggautar bayyanarsa (a.s), kuma ta haka ne za a iya samu bayyanarsa (a.s).
Wajabcin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna yana daga ayyukan tilas kuma nauyi ne da suka hau kan kowane musulmi wadanda ba za a taba daina su ba a kowane zamani a kowane wuri, don haka yaya za a yi wani ya kawo tunanin cewa domin samun gaggauta bayyanar Imam Mahadi (a.s) dole ne a yada zalunci da barna da fasadi?
Manzon Allah (s.a.w) ya cewa: A karshen zamanin al'ummata za a samu wasu mutane da suke kamar musulmi a farkon zuwana, suna umarni da kyakkyawa suna hani ga mummuna kuma suna yakar ma'abota fitina. [2]
Sannan akwai ruwayoyi da suka zo da bayanin cikar Duniya da zalunci da danniya amma wannan ba tana nuni da nufin dukkan mutane ba, sai dai akwai kuma wasu mutane da suke kan tafarkin Allah kuma suka dade a kai.
Domin haka ne za a samu wani yanayi mai dacin gaske da wahla da tsanani kafin bayyanar jagora (a.s) amma zai tuke kuma da zakin bayyanarsa, duk da cewa kuwa akwai fasadi da zalunci mai mamaya amma tsarkakar wasu mutane da kuma kiransu zuwa ga kyawawan halaye yana daga cikin ayyuka na wajibi da suka hau kan masu sauraro, kuma da wannan ayyukan nasu ne za a iya samun tasiri wajen gaggauta bayyanar Imam Mahadi (a.s).


1. Kafi, j 7, shafi: 28.
2. Mu'ujam ahadisul Imam Mahadi, j 1, shafi: 49.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
4+3 =