Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Yaya kuwa za a yi mutum ya rayu rayuwa mai tsawo kamar yadda kuke kawowa game da jagoran wannan duniya na karshen zamani?


Daga cikin muhimman bahasosin da ake yi da suka shafi rayuwar Imam Mahadi (a.s) akwai lamarin tsawon rayuwarsa, saboda haka ne ma wasu suke tambayar cewa yaya za a yi mutum ya yi wannan rayuwa mai tsawo?! [1] Wannan tambaya ta taso ne sakamakon a yau ana ganin rayuwar mutane tana da iyaka daga 80 zuwa 100 ne [2], wasu suna ganin da wannan yanayi ba mai yiwuwa ba ne mutum ya rayu rayuwa mi tsawo hakan, ko kuma abu ne mai wahala. Amma a hankalce da kuma ilimin dan Adam sun nuna cewa zai yiwu mutum ya rayu rayuwa mai tsayi kuma ba tare da koda tsufa ba.
Barnard show yana cewa: Yana daga asasin ilimi gun malaman bayaloji cewa; ba yadda za a iya sanya iyaka ga rayuwar dan Adam, kuma hatta da mas'alar jinkirin rayuwa (dadewa a Duniya) abu ne wanda ba shi da iyaka". [3]
Parfesa Atingar yana rubutawa yana cewa: "a ganina ci gaban takanoloji da kuma ayyukan da muka fara a yau mutumin karni na ishirin da daya zai iya rayuwa tsawon dubunnan shekaru. [4]
Domin haka ne masu ilimi suka yi kokairn gano hanyoyin da za a iya maganin tsufa da kuma kai wa gashekaru masu yawa, wannan kuwayana nuna yiwuwar wannan al'amari da kuma yin wani taki domin cimma wannan al'amari. Kuma har yanzu a Duniya akwai mutane masu yawa da sakamkon wani yanayi na musamman da nau'in abinci da kuma ayyuka da suka dace da jiki da tunani da wasu ayyukan daban dasakamakon hakan sukan yi shekaru samada dari da hamsin kosama da hakan, mafi hummimmanci ma shi ne an jarraba wannan a tsawon tarihin dan Adam kuma akwai wannan a littattafai saukakku, cewa wasu mutanen sun yi shekaru masu yawa da tsawo fiye da rayuwar mutane a yau. Kuma saboda haka ne ma akwai makaloli masu yawa da aka rubuta da zamu yi bayanin wasu daga ciki a matsayin misali:
1-Akwai ayar Kur'ani mai girma da ba kawai tana maganar tsawon rayuwa ba ne, har ma tana bayar da labarin yiwuwar mutum ya dawwama ne, wannan aya game da Yunus (a.s) tana cewa: "ba don ya yi tasbihi a cikin kifi ba, to da ya zauna a cikinsa har ranar da za a tashi kiyama". [5]
Don haka wannan ayar tana nuna yiwuwar rayuwa tun daga lokacin Annabi Yunus (a.s) har zuwa ranar kiyama wanda a ilimin rayuwa ake kira rayuwa madawwamiya. [6]
2-Kur'ani yana fada game da Annabi Nuhu (a.s) cewa: Mu mun aika Nuhu (a.s) zuwa ga mutanesa sai ya zauna a cikinsu shekaru dubu ba hamsin. [7]
Abin da muka iya gani a wannan aya shi ne tsawon shekarun annabta na Annabi Nuhu (a.s) wanda wasu ruwayoyi sun kawo tsawon rayuwar sa gaba daya da cewa ta kai 2450. [8] Wani abin kayatarwa an karbo daga ruwayar Imam Sajjad yana cewa: Imam Mahadi (a.s) yana da sunnar Annabi Nuhu (a.s) ta tsawon shekaru. [9]
3-Haka nan game da Annabi Isa (a.s) yana cewa: Sam ba su kashe shi kuma ba su tsire shi ba, sai dai an rikitar musu ne a al'amuransu… ba su kashe shi ba bisa yakini, sai dai Allah ya daga shi zuwa gareshi ne…". [10] Kuma bisa dogaro da wannan ne dukkan musulmi suka yi imani da cewa Annabi Isa (a.s) a raye yake a sama, kuma a lokacin bayyanar Imam Mahadi (a.s) zai zo domin taimaka masa.
Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: "Imam Mahadi (a.s) yana da sunnoni biyar daga sunnonin annabawa (a.s)… da sunna daga Isa (a.s), wannan kuwa fadinsu cewa ya mutu, alhalin yana raye. [11]
Bayan Kur'ani zamu ga Attaura da Injila su ma sun yi bayani game da mutane masu tsawon rayuwa.
Ya zo a cikin Attaura: "…ranakun da "Adam" (a.s) ya yi ya mutu su ne dari tara da talatin da uku… kuma dukkan rayuwar "Kainan" shekaru dari tara da goma ne yayin da ya mutu… haka ma "Mutushalih" ya rayu dari tara da sittin da tara ne sannan sai ya mutu. [12] Saboda haka Attaura a fili tana bayanin samuwar wasu mutane masu shekaru sama da dari tara.
A cikin Injila ma akwai maganganu da suka zo da suke nuna isa ya rayu bayan kashe shi da tsire shi, kuma ya tashi sama. [13] Idan muka duba tun ranar da ya tashi sama harzuwa yau rayuwarsa tawuce shekaru dubu biyu.
Da wannan bayanin zamu gani a fili yake cewa masu bin addinin yahudanci da kiristanci bisa dogaro da littafi mai tsarki to dole ne su yarda kuma su yi imani da tsawaitar rayuwa.
Ta bangaren magangar ilimi da hankali wannan lamari abu ne karbabe da ya wuce a tarihi kuma ya wakana, wannan kuwa idan muka duba ikon Allah da karfinsa maras iyaka to duk yana iya tabbatuwa.
A cikin akidar ma'abota addinai saukakku daga Allah (S.W.T) dukkan kwayoyin zarra na Duniya suna karkashin ikon Allah ne, kuma tasirinsu da su da sabubansu duk suna da alaka da shi ne kuma duk daga gareshi ne, shi ne ya samar da komai da sabubansu, Shi ne Ubangiji mai ikon fitar da rakumi daga cikin dutse kuma ya sanya wuta ta zamanto mai sanyi ga Ibrahim (a.s) kuma ya busar da kogi ga Musa (a.s) da mabiyansa, kuma ya sanya su tsallake tsakanin katangu biyu koraye. [14] Shin duk wanda ya yi wannan ga annabawa da waliyyansa sai ya kasance ya kasa tsawaita rayuwar karshen ajiyar Allah a bayan kasa wanda dukkan burace-buracen 'yan Adam ya dogara kan samuwarsa da zuwansa?!
Imam Hasan (a.s) yana cewa: Ubangiji zai tsawaita boyuwar Imam Mahadi babba, sannan sai da ikonsa ya bayyanar da shi a cikin surar saurayi dan kasa da shekaru arba'in, domin mutane su sani cewa Allah mai iko ne a kan komai. [15]
Saboda haka maganar tsawaituwar rayuwar Imami na goma sha biyu (a.s) al'amari ne mai yiwuwa ta fuskancin hankali da ilimi da tarihi, kuma abu ne karbabbe, kuma fiye da haka ma akwai nuna nufin Allah da girmansa a ciki.


1. A yanzu yana da shekaru: 1170 kenan.
2. Ana samun sama da dari ma.
3. Raze tule umre Imam zaman (a.s), Ali akbar Mahadi pur, shafi: 13.
4. Majalleye danishmand, shekara: 6, lamba 6, shafi: 147.
5. Saffat, aya: 144.
6. An gano kifi a gefen madagaskar wanda ya yi shekaru miliyan 400, kaihan: lambata: 6413 – 1343/8/22
7. Ankabut, aya: 14.
8. Kamaluddin, j 2, babi 46, h 3, shafi: 309.
9. Kamaluddin, j 1, babi 21, h 4, shafi: 591.
10. Nisa'ai:aya: 157.
11. Biharul anwar, j 51, shafi: 217.
12. Zandeye ruzgaran, shafi: 132.
13. Zandeye ruzgaran, shafi: 134.
14. Suna da yawa a Kur'ani mai girma: anbiya: 69, shu'ura: 63.
15. Biharul anwar, j 51, shafi: 109.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
5+7 =