Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Muna son cikakken bayanin siffofin mataimakan Imam Mahadi (a.s) domin mu samu dammar kyakkyawan koyi da wadannan siffofin ko Allah zai sanya mu cikinsu?


Samuwar mataimaka wadanda suka dace da juyi da kuma daukar nauyin ayyukan hukuma yana daga cikin abin da zai tabbatar da sharuddan samuwar tabbarar juyin Imam Mahadi (a.s), wannan kuwa sananne ne cewa juyi mai jagora daga Ubangiji yana bukatar mataimaka da suka dace da shi. Don haka ne daya daga shi'ar Imam Ja'afar Sadik (a.s) mai suna Sahal dan Hasan Khurasani yana cewa da shi:
Me zai hana ka kwatar hakkinka na jagoranci alhalin kana tare da daruruwan dubunnan shi'a wadanda suna iya zare takubba karkashin umarninka? Sai Imam ya yi umarni aka hura wuta, kuma ya ce da Sahal: kai Khurasani tashi ka shiga wannan kaskon wutar. Sahal da ya yi tsammanin Imam (a.s) ya yi fushi ne sai ya ki shiga yana bayar da uzuri da hakuri, yana cewa: ka yi mini afuwa, kada ka kona ni da wuta! Imam yana cewa da shi wannan ya wuce (wato; wuta ake so ka shiga ba wani abu ne na fushi ba). Sai ga wani mabiyan Imam na gaskiya mai suna Harun Makki yana shigowa ya yi sallama. Ba tare da wata mukaddima ba, sai Imam Ja'afar Sadik (a.s) ya ce da shi: shiga cikin gidan kaskon wutar nan.
Babu wata tsayawa ko jinkiri ko tambaya sai Harun Makki ya aikata hakan! Sai Imam (a.s) ya ci gaba da tattaunawa da mutumin nan Khurasani, ya ci gaba da ba shi labari kamar kai ka ce shi ya ga hakan. To bayan wani dan lokaci sai Imam ya ce da Sahal: tashi kai Khurasani ka shiga wannan kaskon ka ga ni! Sai Sahal ya tashi ya duba, ya hango Harun a tsakiyar wuta tana ci, shi kuma yana zaune!
Sai Imam (a.s) ya kalli Sahal ya tambaye shi: a Khurasan mutum nawa ne kamar Haruna da ka sani?! Sai Khurasani ya ce: Na rantse da Allah ko mutum daya kamar haka ban iya gani ba. Sai Imam (a.s) ya ce: ka sani mu muna zamani ne da hatta mutum biyar masu taimakawa ba mu da su domin mu yi juyi, mu mun sani wane lokaci ne lokacin juyinmu. [1]
Don haka ne akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo game da siffofin sahabbai mataimaka Imam (a.s) da ya kamata kafin mu cigaba mu yi nuni da wasunsu:

Mataimakan Jagora suna da masaniya mai zurfi game da Ubangiji da shugabansu, kuma suna halartar fagensa tare da masaniya cikakkiya, Imam Ali (a.s) yana fadi game da su cewa: Mutane ne da suka san Allah kamar yadda yake. [2] Wannan sanin ya wuce na sanin suna da siffofinsa na zahiri da kuma nasabarsa. Sanin Imami sani ne na hakikanin wilayar Imam (a.s) da matsayinsa a duniyar halittu, kuma wannan shi ne irin sanin da ya mamaye su da soyayya ga imaminsu.
Manzon rahama (s.a.w) yana siffanta su da cewa: Su masu kokari ne wajen biyayya ga jagoransu. [3]

Mataimakan Imam Mahadi (a.s) suna daga cikin abin koyi na ibada da ambaton Allah da dare da rana, kuma Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana fada game da su: suna kai darensu safiya da ibada [4], kuma suna kai ranar su dare da azumi. A wani fadin yana cewa: suna masu tasbihin Allah (s.w.t) suna kan dawakai. [5]
Game da kuwa kafewarsau yana cewa: su mutane ne wadanda kai ka ce; zukatansu wani yanki ne na karafa. [6]

Saninsu mai zurfi game da Imam ya samar musu da zukata masu cike da kaunarsa, don haka ne ma a wajen yaki sai suka kasance kamar wani ado ne a cikin al'umma kuma suna jefa kansu cikin bala'oli.
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Mataimakan Imam Mahadi (a.s) a fagen yaki suna gewaye a gefensa, kuma suna kare shi. [7]
Kuma yana cewa: suna fatan yin shahada a tafarkin Allah. [8]

Mabiya Imam Mahadi (a.s) mutane ne masu sadaukantaka da jarumtaka; Imam Ali (a.s) yana siffanta su da cewa: Dukkansu zakuna ne wadanda suka fito daga kogunansu, kuma idan sun so sai su kawar da duwatsu daga wurinsu. [9]

Kafa hukumar adalcin Duniya tana tare da wahala mai tsanani kuma domin kawar da matsalolin Duniya da tabbatar burin Imam Mahadi (a.s) akwai matsaloli masu yawa da suke bukatar hadawa da ikhlasi da kaskan da kai da kuma juriya mai karfi.
Imam Ali (a.s) yana cewa: Su mataimakan Imam Mahadi (a.s) mutane ne da ba sa yi wa Allah gori saboda juriyar da suka yi, kuma ba sa yin takama saboda abin da suka bayar na rayukansu, kuma ba sa ganinsa wani babban aiki ne suka yi. [10]

Imam Ali (a.s) yana cewa: Su zuciya daya suke kuma masu hadin kai ne. [11] Wannan hadin kai ya kasance ne sakamakon babu wani son rai da maslaha ta kashin kai da take tare da su, don haka sai suka hada karfi karkashin tuta daya, kuma wannan yana daga cikin dalilan cin nasararsu.

Imam Ali (a.s) yana siffanta mataimamkan Imam Mahadi yana cewa: shi zai karbi bai'a daga mataimakansa cewa ba zasu sanya zinare ko azurfa ba, kuma ba zasu ajiye alkama ko sha'iri ba. [12] Wannan kuwa yana nuna hadafi mai girma da yake tare da su na nisanta daga Duniya da kawarta, don haka idanuwan su ba sa farin ciki da ganin kyalekyalin Duniya da kawarta, kuma wadannan abubuwa ba su da mazauni a cikin mataimakan Imam Mahadi (a.s).
Wadannan abubuwa da suka gabata wasu siffofi ne na mataimakan Imam Mahadi (a.s), sannan akwai wasu da suka zo daga zantuttukan ma'asumai (a.s) kamar haka:
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Wadannan su ne fiyayyun zababbun al'ummata. [13]
Imam Ali (a.s) yana cewa: Ina fansa da uwata da ubana ga wasu jama'a 'yan kadan wadanda aka jahilce su a Duniya. [14]
Koda yake mataimakan Imam Mahadi (a.s) suna da darajoji mabambanta, akwai mutane 313 na musamman da ruwayoyi suka yi magana game da su, sannan kuma akwai bataliya ta mutane dubu 10, hada da kuma dubunnan muminai masu yawa da suke jiransa.


1. Safinatul bihar, j 8, shafi: 681.
2. Muntakhabul asar, fasali 8, babi 1, h 2, shafi: 611.
3. Yaumul khalas, shafi: 223.
4. Abin da ya gabata, shafi: 224.
5. Biharul anwar, j 52, shafi: 308.
6. Abin da ya gabata.
7. Abin da ya gabata.
8. Abin da ya gabata.
9. Yaumul khalas, shafi: 224.
10. Abin da ya gabata, shafi: 224.
11. Abin da ya gabata, shafi: 223.
12. Muntakhabul asara, fasali 6, babi 11, h 4, shafi 581.
13. Yaumul khalas, shafi: 224.
14. Mu'ujamul ahadisul imamul Mahadi, j 3, shafi: 101.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+1 =