Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Kamar yadda yake sanannen abu ne babu wani motsi da ba shi da hadafi tare da shi, mene ne babban hadafin daular da imam Mahadi (a.s) zai kafa


Bayan tafiyar gajimare mai duhu sai hasken rana ya haskaka domin ya bayyana a idanuwan masu sauraro. Don haka ne bayan yaki da kawar da ma'abota barna da karya da masu ashararanci, sai a samu batun tabbatar hukumar adalcin Allah da kowa da komai zai zauna a matsayinsa, kuma kowane rabo ya zama a mahallinsa. Daga karshe Duniya da 'ya'yanta zasu ga hukumar adalci ta gaba daya, kuma ba zasu sake ganin mafi kankantar zalunci ba. Daula ce ta bayyanar siffofin Allah (s.w.t) da kyawunsa, kuma a nan ne dukkan mutane zasu manta da gurace-guracensu. A wannan fasali zamu yi bayanin abubuwan hudu ne:
1. Hadafin hukumar Duniya ta Jagora Imam Mahadi (a.s)
2. Tsarurrukan hukumar Jagora (a.s) a fagage daban-daban
3. Abubuwan da hukumar Allah zata samar da fadadarta
4. Siffofin wannan hukumar ta Jagora Imam Mahadi (a.s)

Mutum yana da hadafofi guda biyu da yake son cimma a cikin rayuwarsa ta Duniya da suka hada da hadafin zahiri da na badini domin kai wa zuwa ga kamalar da yake bukata, don haka hadafin hukumar Imam Mahadi (a.s) duk ya shafi duka bangarorin biyu ne, wadanda zamu kawo su a nan gaba.

A hukumar dagutanci zamu ga dan Adam yana mancewa da kyawawan dabi'u gaba daya, maimakon kyawawan halaye kamar; gaskiya da taimakekeniya da sadaukarwa da kirki, sai ya maye gurbinsu da munanan halaye kamar; son zuciya, laifi, rashin mutunci, karya da son kai, daga karshe sai kimar rayuwa da alherinta ya tafi, sai dan Adam ya fada cikin rushewa. Amma hukumar Imam Mahadi (a.s) zata zo domin raya zukatan mutane da ruhuinsu da ba su sabuwar rayuwa mai kanshi da kyau.
"Ya ku wadanda kuka yi imani ku amsa wa Allah (s.w.t) da Manzo (s.a.w) zuwa ga abin da suke kiran ku na abin da yake raya ku…". [1]
Mu sani rayuwar badinin mutum ita ce take ba wa mutum bambanci tsakninsa da dabbobi, kuma domin wannan rayuwar ne ake kiran sa "Adam", kuma da ita wannan rayuwar ne yake samun kusanci zuwa ga Allah (s.w.t).
A lokacin Imam Mahadi (a.s) rayuwar badini da kyawawan halaye zata mamaye ko'ina na samuwar dan Adam, kuma za a samu tsarkakar badini, da kaunar juna, da sadaukarwa, da cika alkawari, da gaskiya, da duk wani abu da ake kira kyau, amma mu sani kaiwa zuwa ga wannan hadafi mai girma yana bukatar tsari mai zurfi sosai.

Zalunci shi ne mafi munin abu da ake fama da shi a cikin al'ummmu, kuma al'ummu a karnoni masu yawa sun cigaba da zama cikin rashi da fatara da take hakkinsu, kuma ba a taba raba baiwar da Allah ya yi wa dan Adam ta arziki bisa daidaito ba. Don haka ne sai ka ga sun cika cikinsu dam da abinci a gefe kuma ga wasu suna fama da yunwa, wasu a cikin dogayen binaye da gine-gine alhalin wasu suna kwana a kwararo mai kunci a kusa da wadannan gidaje. Karfin da ake amfani da shi ya sanya mutane sun koma masu rauni kuma sun zama tamkar bayi ne, sannan kuma ga kabilanci na farar fata da bakar fata wanda ya isa a kashe mutum domin laifinsa shi ne shi bakar fata ne.
Wadannan abubuwa da wasunsu da suka cika duniyar dan Adam sun kai shi ga burin da yake dauke da shi tilo shi ne ya kai ga samun adalci da daidaito, don haka sai ya kasance wannan shi ne abin da yake jira a kodayaushe. Amma karshen sauraro zai kai ga samuwar hukumar ni'ima ta Imam Mahadi (a.s) a matsayinsa na babban jagoran adalci domin yada adalci a Duniya a dukkan bangarorin rayuwa, kuma wannan wani abu ne da aka yi bayaninsa a cikin ruwayoyi.
Imam Husain (a.s) yana cewa: Idan da Duniya babu abin da ya rage sai wuni daya, da Allah ya tsawaita wannan har sai wani daga 'ya'yana ya zo kuma ya cika Duniya da adalci kamar yadda aka cikata da zalunci. Kuma haka nan na ji daga Manzon Allah (s.a.w). [2] Da wasu gomomin ruwayoyi da suka zo game da adalcin Duniya da kuma kawar da zalunci a wannan hukuma ta Imam Mahadi (a.s).
Wani abin kayatarwa kuwa shi ne; adalci da kuma hukunci bisa gaskiya suna daga cikin mafi bayyanar siffofin Imam Mahadi (a.s) da suka zo wasu addu'o'i kamar haka:
"ya Ubangiji kuma ka yi tsira ga masoyin lamarinka mai tsayuwa (da adalci) wanda ake burin (zuwansa) kuma adalci da ake sauraro. [3]
Haka nan ya sanya adalci ma'auninjuyinsa, domin idan babu adalci to rayuwar daidaiku da ta al'umma da kuma Duniya damutanenta zasu kasane kamarmatattu ne da ba su da rai.
Imam Musa Kazim (a.s) yana fada game da tafsirin ayar nan "Ku sani Allah yana raya kasa bayan mutuwarta". [4] Sai ya ce: Ba ana nufin cewa ana raya kasa da ruwan sama ba, amma abin nufi shi ne; Ubangiji zai tayar da wasu mutane [5] domin su raya adalci don haka sakamakon yaduwar adalci sai ya raya kasa.
Wannan yana nufin cewa adalcin Imam Mahadi zai mamaye dukkan Duniya ba wani bangare nata ba kawai.


1. Anfal: 24.
2. Kamaluddin, h 1, babi 30, h 4, 584.
3. Mafatihul jinan, du'a'I iftitah.
4. Hadid: 17.
5. Burhan, j 7, shafi: 446.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
2+7 =