Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


TANIYA BOLING
(Jamane – Kirista)Ta samu musulunta a shekarar 1999 da karbar mazhabar Ahlul Baiti (a.s) tana mai barin kiristanci tana da shekaru ishirin da biyu bayan tsawon lokaci cikin duhun gafala da bata, sai ta samu wannan haske da ikon Allah madaukaki.
Wanda ya fi kowa sanin al'umma shi ne wanda ya tashi cikinta a matsayin daya daga cikinta, Toniya tana bayar da labarin yanayin da yake cikin rayuwar Turai a kasar da take wato; Jamus, ta ce: Ban kambama ba idan na ce kowannenmu yana rayuwar da hatta da kansa ya kaurace mata balle sauran mutane da suke tare da shi. Ta ce: Ba mu kasance muna hangen komai ba hatta da rayuwarmu ta nan gaba, kai babu wata tambaya da take fado mana game da don me muke rayuwa? Don me aka haife mu, kuma daga ina muke? Kuma ina zamu?!!
Kowa ya dimauce yana mai tafiya a kan fuskarsa ta hanyoyi mabanbanta da karkata da halaka, kamar dai dabbobin da aka yi wa tsawa suka tarwatse. Ga sama da kashi 60% cikin dari na samari da 'yan mata suna rayuwar kadaitaka duk da kuwa rayuwar kawance tsakanin 'yan mata da samari, domin suna yin yawancin rayuwarsu a cikin daki a rufe a daki daya ko wani falo ba tare da suna da alaka da wasu ba.
Wannan lamarin ya kawo kawar da yanayin gina badini da ruhi, sai kowa ya mayar da hankali kan biyan bukatun sha'awarsa da duniyarsa.
Ta ce: Gashi muna rayuwa tare, amma kowa yana da nasa yanayin da yake rayuwa, kuam ba ya kula bukatun waninsa, kowa yana rayuwa don kansa ne kawai.

Barin addini

Ta yiwu a ce dalilan da suka sanya barin addini a yammancin duniya shi ne ayyukan malaman Coci da kuma karkatar da ta samu addinin kiristanci wacce suka kasa bayar da mafita ga rayuwar dan Adam, suka sanya dokokin da babu inda zasu kai shi, sabanin abin da Annabi Isa (a.s) ya zo da shi.
Kuma wadannan malamai na Coci suka yi tsammanin sun bayar da duk wata mafita da sa'ada ga dan Adam a duniya da lahira alhalin lamarin sabanin haka ne. Ga akidar da ta saba wa hankali wacce take mai surkukiyar tunani, hada da dukkan abin da muke iya ganin na lalacewar dabi'u a Coci.
Al'amarin yamma ya kai ga mutane sama da kashi 50% cikin dari a bisa zahiri suna rayuwar kadaici ne, kuma sama da kashi 60% na samari ne ko 'yan mata suna cikin irin wannan halin ne, wannan kuwa duk da alaka ta kawance ta zahiri da ake gani, wasu ba sa iya daukar wani lokacin kirki suna wasanni da annashuwa sai wasu 'yan lokuta na awowin rana ko dare, yayin da yawancin rayuwarsu suna yin ta ne a cikin dakuna.

Farkon samun haske

Toniya ta rayu kusan shekaru ishirin a cikin wannan duhun har dai Allah (s.w.t) ya yi mata ludufi da samun hasken shiriya, kuma farkon wannan ya faru ne yayin da suke tafiya da kawayenta sai ta ga wata budurwa da hijabi sai ta yi mata isgili, tana mai cewa da ita wane ciwo ya same ki kike rufin jikinki hakan. Ta ce: sai ta ba ni amsa cikin nutsuwa da magana mai taushi da take nuna tunani mai zurfi da dalili mai karfi, da cewa wannan shi ne mutuncin mace da 'yancinta.
Ta ce: sai na ki yarda da maganarta duka, sai dai na rika tunaninta da yadda na ga ta yarda da gamsuwa da abin da take a kai, sai dai na tafi da kawayena, har dai wata rana abin ya dame ni sai na tafi masallacin Imam Ali (a.s) da yake garin "Hamborg" na samu yin tambayoyi kan abin da suke yi, sai na samu amsa mai cike da hankali da dalili mai karfi, don haka sai na karfafa alaka ta da su, har dai na samu yaye gaskiya mai yawa da na kasance a da ina jahiltarta, a hankali sai hankalina ya fara ba ni karkata zuwa ga tunaninsu da akidojinsu, har da na samu kaina na karbi musulunci na kasance kamarsu kwabo da kwabo.

Dalilan shiriya

Toniya tana ganin mafi girman dalilan da suka sanya ta shiriya suna hada da: na daya; alakar musulmi da ubangijinsu, a koda yaushe suna da alaka da shi. Na biyu: Alakar 'yan'uwantaka da take tsakanin musulmi kansu da karfin 'yan'uwantakar cikin iyali tsakanin miji da mata da 'ya'ya. Na uku: Samun bayyanannen hadafi a fili a rayuwarsu, don haka babu wani dar-dar ko dimuwa a ciki. Na hudu: Rashin iyaka da take ga al'ummar musulmi, ta yadda ba a la'akari da jinni ko kabila. Na biyar: Suna yin rayuwarsu ba tare da kadaici ba kamar yadda koyarwarsu ta koyar, su suna cakuda da kowa domin addininsu na kowa ne.

Sakamakon haka

Ta ce: Da na kasance ina da komai ban da Allah sai na fada cikin dimuwa da firgici da raurawar rai da tunani da jin tozarta, amma sai ga shi yau na samu kaina yayin da na samu Allah madaukaki bayan tozarta da rashinsa kusan shekaru ishirin, kuma saboda falalar musulunci a yau na samu komai.
Wanna kuwa shi ne 'yancin gaskiya da na samu, sannan duk wani abu da ya shafi samar da ma'ana mai kyau da bayan da ruhi mai karfi ga mutum a badini shi ne komai a duniya. Kuma lallai musulunci ne mabubbuga kuma mashayar duk wata daukaka da matsayi da dan Adam yake bukata.
Babbar sa'ar da Toniya ta yi shi ne ba ta san musulunci ta hanyar mushtashrikun ba, wadanda suka shahara wurin karkatar da musulunci da ba shi mummunar fassara da kawo mugalada da rufe gaskiya a ciki, da kawo rudu da shakku domin kawo karkatarwa ga tunanin mutane domin kada su fahimci gaskiya.
Mustashrikun sun yi wa musulunci fassarar da suka ga dama ne, suna kawo mas'alolinsa ne sannan sai su yi bayanin tasu mahangar su gabatar da ita ga mutane a matsayin musulunci. Wannan lamarin kuwa ya kasance ne sakamakon alaka mai karfi da take tsakanin kiristanci da ishrakanci da hadafi iri daya. Me kuwa za a yi tsammani daga mutanen da suke da irin wannan tunanin in ba abin da suke yi ba.
Toniya ta ci gaba da cewa: Daya daga abubuwan da suka ba ni sha'awa game da musulunci shi ne, alakar musulmi da ubangijinsu da kuma alakarsu tsakaninsu a junansu, da soyayyar da take tsakanin 'yan gida daya, da kuam kawar da batun bambancin kasa da kabila da al'umma. Wannan kuwa musulmi duk sun same shi ne sakamakon shi kansa musuluncin da koyarwarsa.
Ta ce: Da na hadu da musulmin da ba addininsu suke yi ba da ban samu wannan shiriyar ba.

Gudummuwar Ahlul Baiti (a.s)

Karanta littattafai kan koyarwar Ahlul Baiti (a.s) yana daga cikin abin da ya ja hankalin Toniya, sai ta karanta Kur'ani sannan kuma ta karanta hadisai da suka zo daga Ahlul Baiti (a.s) wanda ba domin Ahlul Baiti (a.s) ba da mafi yawan hadisai masu daraja ba su zo mana ba.
Tana cewa: Ni na samu duk abin da nake burin samu a cikin hadisan manzon Allah (s.a.w) da Ahlul Baiti (a.s) da dukkan abin da mutum yake bukata a addininsa, kuma da zan rasa komai saboda musulunci ne da zan ce na samu kaina, kuma na samu komai. Hakika na samu 'yancin tsarkin badini da ruhin da nake bukata, kuma na samu komai kamar yadda nake ji.
Ta ci gaba da cewa; Duk da na samu matsaloli masu tarin yawa da dangina musamman iyaye saboda na musulunta, duk da wahalhalu na zahiri da na fuskanta da tattaunawa mai zafi da na samu da iyayena, sai dai har yanzu ina rayuwa tare da su, kuma lokacin da suka ga da gasket nake sai suka kyale ni, suka koma suna kyautata mini, musamman ganin halina ya fi kyautatuwa nesa ba kusa ba fiye da dacan. Da wannan lamarin ne na samu ketare duk wata wahala mai wuya, da na samu a kan hanyar musulunci, da kuma samun ci gaban tunani da sani ilimomin koyarwar Ahlul Baiti (a.s). na samu dagewa a kan duk wani waigi da yake kan hanya, ta kuma samu dagewa a kan ayyukanta domin ta kasance mutum 'yantacce mai riko da addininsa ba tare da jin tsoron zargin mai zargi ba.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+9 =