Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


IBRAHIM WATARA
(Ivory cost – Bamalike)An haife shi a garin “Soko” qarqashin garin Bondoko a Ivory cost a shekarar 1980 a gidan da suke bin malikiyya, kuma ya samu fahimtar mazhabin ahlul bait (A.S) a 1993 a garinsa bayan ya samu gaskiya ta bayyana gareshi ta hanyar bincike.

Farkon karkata zuwa ga gaskiya

Ibrahim yana cewa: har yanzu ina tuna ranar da na ji ambaton kalmar Shi'a a lokacin ina xalibi a makarantar tarbiyya da koyarwar musulunci, kuma na kasance ina matuqar son tarihi, wata rana ana karatu game da umayyawa sai malaminmu ya kawo babban abin da ya faru a lokacin na al’amarin ashura, ya ambaci cewa halifan musulumi ya kashe Imam husain (A.S). da ahalin gidansa ta mummunar hanya mai firgitarwa, sannan kuma sai ya nemi ganin bayan Shi'a a wannan lokacin, sannan sai ya kawo wasu ayyukan da waxanna runduna suka yi na dabbanci da rashin imani da tausayi a kan Imam husain da ahlin gidanda da sahabbansa.

Sanin Shi'a

Sai na samu tasirantuwa mai qarfi a rayina game da wannan lamarin na al’amarin ashura da aka kashe xan ‘yar Manzon Allah (S.A.W) a cikinta, kuma na samu tambayoyi suna ta tashi a qwaqwalwata na cewa; yaya yazidu zai iya wanna jur’ar waxannan munanan ayyukan alhalin shi ne halifa a wannan lokacin!
Sai tambayoyi suka yi ta faxo mini a cikin raina: kuma su waye Shi'a da malaminmu ya kawo da yake cewa yazid ya kashe su? Mece ce alaqarsu da husain (A.S)?

Yayin da darasi ya qare sai na zo wurin malamin domin in smau bayanai kan Shi'a da ya kawo, sai na ce masa: su waye Shi'a kuma mene ne alaqarsu da husain (A.S), kuma domin me halifa yazid ya kashe su kuma ya kashe xan ‘yan Manzon Allah (S.A.W)?

Sai malamin ya amsa mini da cewa: Shi'a wasu jama’a ce ta musulmi da suke imani da cewa Imam Ali (A.S) da ‘ya’yansa su ne suka fi cancantar halifanci bayan Annabi (S.A.W) kuma waxannan aqidu ne vatattu, kuma waxannan sun sava da abin da musulmi suke a kansa gaba xaya, kuma su mutane ne masu Magana babu dalili ko hujjar hankali kan abin da suke cewa.

Sannan sai ya qara da cewa: kuma kana iya ware waxannan mutane ta hanyar yadda suke salla, kuma suna sujada a kan turba, sannan sai ya ce da ni: kuma kana iya sanin abubuwa da yawa a wurinsu idan ka tafi wurin Adamu Taraware domin shi ma yana cikinsu, ina fatan da zaka haxu da shi domin ka ji irin vatansu da kanka, ka san vatansu a fili.

Kwatsam sai xayan dangina ya zama Shi'a

Na yi mamaki yayin da malamin ya ba ni labari cewa adam ya zama xan Shi'a! sai na faxa a raina cewa lallai shi ne wand azan san al’amarin mutanen nan gunsa fiye da kowa game da mutanen nan da suka haxu da wannan bala’I a ranar ashura.
Sai na tafi wurinsa na ba shi labarin abin da yake faruwa tsakanina da malamina game da lamarin Karbala, kuma na nemi ya gaya min abin da ya sani kuma ya gaya mini dalilin da ya sanya shi shiga cikin waxannan mutane? Sai ya yarda kuma muka yi alqawarin wurin da zamu haxu mu yi Magana kan lamarin.

A lokacin da muka haxu, sai xan’uwa Adam y afara Magana yana mai cewa: Abubuwan da suka faru bayan wafatin Annabi (S.A.W) suna da yawa, kuma yana da kyau ga mai bincike ya fara tun daga farko a bahasin.
Sai na ce masa: yana da kyau mu fara daga farko tukuna domin abubuwan su bayyana sosai, sai ya fara da batun rashin lafiyar Annabi (S.A.W) d akuma yadda wasu sahabbai suka tuhume shi da sumbatu na rashin hankali, da kuma abin da ya faru bayan wafatin Annabi (S.A.W) na saqifa, da kuma yadda aka keta alfarmar gidan faxima (A.S) da … har dai ya zo kana bin da ya shafi al’amarin sanya yazid halifanci.

Da wannan ne muka shiga Magana kan yazid da varnarsa ga al’ummar musulmi da siffofinsa da yadda aka karvi bai’ar mutane da qarfin tsiya tare da cewa ba shi da wata tarbiyya in bada farauta da shaye-shaye da maye da kallon kixa da rawar mata da sauran fasiqanci. Shi mutun ne wanda ba ya voye fasadinsa a fili savanin sauran munafukai, wannan kuwa domin ya rayu ne a cikin kiristanci.

Sai ya karvi mulkin da ya fara da kashe zuriyar Manzon Allah (S.A.W). sai kashe dubunnan musulmi waxanda daga cikinsu akwai wasu sahabbai a Madina da halartawa rundunarsa matan mutanen Madina, har sai da aka kawar da budurcin sama da budurwa dubu xaya, kuma aka sha giya kan mimbarin Annabi aka hana salla kwana da kwanaki.
Haka nan binciken tarihin Yazid ya sanya ni ganin abubuwa masu yawa da rashin imani da ya yi, haxa da waqoqin qiyayya da isgili da musulunci da Annabi (s.a.w) da ya yi da musun saukar wahayi da saurarn varnace-varnace, amma duk da haka sai na ga wasu suna neman kariya ga cewa; duk abin da shugaba ya yi to dole a bi shi a kan hakan. Haxa da xaukar kafirai da sauran fasiqai a matsayin masu ba shi shawarar yadda zai tafiyar da hukumarsa, da riqon sauran maqiya Allah makusantansa, da qiyayyarsa ga alayen Manzon Allah (a.s), da yin wasa da kan 'yar Manzon Allah (s.a.w) kuma jikansa (a.s), da yin dukkan nau'in fasiqanci a fili. Ta wani vangaren kuma sai ga malamai masu adalci sun bayyanar da cewa; Yazidu la'ananne ne kuma kafiri ne mai fasadi a duniya waxanda suka haxa da manyan malaman Sunna.

Samun canji da fahimta

Bayan dukkan waxannan abubuwan da suka gabata sia na ximauce na samu gaskiya ta fito mini a fili, hijabi ya yaye mini, na ga cewa; ba yadda za a yi wanda zai yi wannan aiki ya fito daga wuri wanda yake mai halayen kirki balle ya kasance mai tsarki domin ya rasa duk wani alheri da Manzon Allah ya siffanta muminai da shi, balle ya kai ga samun matsayin halifancin Manzon Allah (s.a.w).
Don haka sai muka shiga bahasosin halifanci bayan Annabi da jagorancin al'umma a kwanaki masu yawa da ni da Adam yana kuma ba ni hujjoji gamsassu, sannan kuma ina komawa wurin malamin nan ina tattaunawa da shi amma ba ya iya ba ni amsa, sai ya fara qyamata ta yana kuma nuna mini in yi hattara sannan yana ba ni adreshin wasu cibiyoyin addini domin in samu littattafai da zasu sanya ni tabbata kan koyarwar Sunnanci, kuma yana ba ni wasu littattafai da zasu taimaka mini kan hakan.

Sai dai ina mai godiya ga Allah sai na fara sanin haqiqa kamar yadda take duk da na fuskanci wahalhalu masu tsanani kan tunanin ganin shin zan bar mazhabina na da kenan? Yaya zan bar aqidata? Sai na cigaba da tunani har sai da na haxu da wani abokina da yake karatu a Ghana makarantar Ahlul bait (a.s) na yi masa magana kan hakan sai ya ba ni littafin "Summah tadaitu" da "Li akunanna minassadiqin" da "mu'utamu Bagdad" sai na samu gaskiyar da take qarfafa mini abin da Adam ya gaya mini a cikinsu. Don haka a sannu-sannu sai na samu duhu ya fara yayewa haske yana bayyana a zuciyata sai na karkata zuwa ga riqo da taurarin da Allah da manzonsa (a.s) suka bar mana wato alayen Annabi (a.s). sai na shelanta sabon mazhabina na Ahlul bait (a.s) a "Aburi kost" a shekarar 1993.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
7+7 =