Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


ABUL KASIM MUHAMMAD ANWARUL KABIR
(Bangaladish – Bawahabiye)An haife shi a shekarar 1970 a Bangaladish kuma yana da shedar digiri a ilimin noma, da kuma wata a ilimin siyasa da al'adun musulunci.
Ya samu karbar mazhabin Ahlul Baiti (a.s) a shekarar 1991 a garin Daka na kasar Bangaladish yana mai barin wahabiyanci.
Abulkasim yana cewa; Na rayu a cikin gida mai riko da addini da shiriyar musulunci, don haka sai ya kasance na san duk wani hukunci na addinin musulunci wanda ya taimaka mini daga baya.
A sakamakon haka ne sai na samu kokarin karanta tarihin musulunci musamman wanda ya shafi rayuwar sahabbai da halifofi, sai na kasance ina jin dadin karanta tarihin rayuwar manzon Allah da halifofi da kuma kissoshin sauran annabawa (a.s). sai dai ina samun damuwa matuka idan na karanta wasu abubuwan.

Bayan Fahimtar Shi'anci

Yana cewa: bayan shekaru masu yawa da gama karatu kuma na fara tarjama a wasu jaridu na yaren bangal, sai na samu tarjamar nan na littafin almizan na allama Tibatiba'I, sai na samu ya hada tafarki tsoho da sabo, kuma ya saba da usulubin duk wani tafsiri da na karanta a baya.
Kuma shi ne farkon littafin Shi'anci da ya fada hannuna, kuma yayin da na duba bahasosinsa na tarihi sai wannan ya sanya ni canja tunanina na akida da ta rigaya, sannan kuma na samu amsar tambayar da ta dame ni a kwakwalwata wacce ta gamsar da ni, musamman game da lokacin Usman dan Affan.

Banu Umayya a tarihi

Banu Umayya mutane ne wadanda suka yi kokarin toshe duk wata falala ta alayen gidan manzon Allah (s.a.w) da dora wa kansu duk wata falala, don haka sun yi amfani da hanyoyi daban-daban domin cim ma wannan buri nasu, yayin da suka samu Usman a matsayinsa na daya daga cikinsu ya samu jagoranci sai suka yi kokarin shiga ta hanyarsa suna siffanta shi da ma'abocin haske biyu saboda aurensa ga agololin Annabi (a.s) da sauransu.
Wani abin mamaki sai ga Abuhuraira yana ruwaito wani hadisi da Rukayya take ce masa yanzu manzon Allah (s.a.w) ya fita daga nan na taje masa gashinsa har ya tambaye ni yaya na samu Usman sai na ce masa da alheri. Sai ya ce da ni: Ki rike shi, domin shi ya fi kowanne daga sahabbaina kama da ni a dabi'a.
Abin mamaki Rukayya ta rasu a shekara ta uku hijira, Abuhuraira ya musulunta ya zo madina shekara ta bakwai hijira, ko yaya aka yi suka hadu. Haka zaka yi ta samun irin wadannan jabon hadisai domin kokarin ganin an ba wa Banu Umayya dukkan falala.
Banu Umayya sun yi amfani da kasancewarsu kuraishawa suka yaudari mutanen Sham da wannan domin su nuna musu cewa su ne makusantan manzon Allah (s.a.w), domin suna kira da cewa sun hadu da shi a kakansa Abdulmanaf. Umayya bawa ne daga Rum da Abdusshams ya yi tabanninsa ta yadda duk wani abu da dansa yake da shi, shi ma Umayya da shi na daga hakkoki.
Kuma sun yi amfani da wannan damar domin su nuna suna daga kuraishawa, kuma su halatta duk wata barna da aikin masha'a da suke yi suka sanya gaba.
Sai dai yayin da musulmi suka duba ayyukan Usman suka kuma tabbatar da cewa; ba hukuncin Allah ba ne, kuma suka ga ya bar dukkan wani hukunci na littafin Allah da sunnar annabinsa, kuma ya wulakanta Kur'ani ta hanyar kona sauran mushafofi, sai wannan ya tayar da tawayensu gunsa. Kuma wannan yana daga abubuwan da ya sanya su yin tawaye gare shi da kashe shi daga karshe.
Usman ya bayar da dama ga dukkan wani murtaddi da munafuki wanda manzon rahama ya la'anta, kuma ya ba su mukamai, manyan sahabbai sun yi masa gargadin abin da yake yi amma ya ki sauraronsu. Sai ga dukkan wani wanda manzon Allah ya kusantar kuma an yi nesa da shi, hasali ma an kashe wasu daga cikin kamar Abdullahi dan Mas'adu, wasu kuma an kore su kamar Abuzar saboda fadin gaskiya. Wanda kuma manzon Allah ya kore ya la'anta sai dukkan fada ta koma a hannunsu kamar Hakam dan Asi, da Abdullahi bn Sa'ad bn Abi Sarha wanda manzo ya yi umarnin kashewa koda kuwa ya makale jikin Ka'aba da sauran munafukai da murtaddai.

Abulkasim ya ce: Irin wadannan abubuwan sun tayar mini da hankali, kuma abin takaici maimakon a nuna kuskuren da hadarinsu ga addini sai aka rika ba su kariya ana yi musu tawili, a nan ne na ga to wane tsarki ya rage wa musulunci matukar zai kasance barnar wasu jagororinsa abin karewa ce, wani abin mamaki da na dauka wasu abubuwan ana yi ne babu sanin Usman amma sai ta bayyana gareni a bincike cewa shi ne ma yake bayar da umarni.
Sai na ga Usman yana barin kisasi a kan wani mutum kamar Ubaidullah bn Umsar saboda kawai Amru dan Asi ya shiga ya nema masa afuwa, sai na ga hukunce-hukunce masu yawa da ya yi watsi da su, hada da kashe alayen Annabi (a.s) da lamarin karbala da suaran waki'o'I, a nan ne na san cewa; lallai babu wani tafarkin gaskiya sai na Ahlul Baiti (a.s) don haka na yi riko da su, wannan kuwa a garin Daka a shekara ta 1991 ne.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+1 =