Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


AHMAD HUSAIN YA’AQUB
(Jordan – Bashafi’e)An haife shi a Jordan garin “Jarsh” shekara ta 1939 M. a cikin gidan da suke riqo da shafi’iyya, kuma ya samu karatun sakandare a misira, sannan sai ya yi karatun Law a jami’a a Damaskus ya samu shedar karatu ta Law a jami’ar Labanon a matsayinsa na lauya kuma mai huxuba a jumma’a kuma shugaban masu kula da gari.

Rushewar tunanina na farko game da tarihin musulunci

Malam Ahmad yana cewa: “Na yi tafiya zuwa Bairut domin tattaunawa kan wani rubutu da na yi ga jami’ar labanon kan jagorancin halifanci a shari’a da tarihi, kuma na yi rubutun ne game da abin da aka sani na gado, kuma ya yi daidai ne da abin da aka saba na rubutu game da tunanin al’umma, ina Bairut sai na karanta littafin “Aban’ur rasul fi karbala” na Halid Muhammad Halid, kuma duk da cewa mai littafin yana tausaya wa ga masu kisan yana ba su uzuri, sai dai na samu karaya matuka game da abin da ya samu imam husain (A.S) da sauran ahlin gidan Annabi (S.A.W) da sahabbansu.

Ana iya cewa ciwon zafin kisan imam husain (A.S) shi ne abin da ya sanya ni samun canji a rayuwata gaba xaya, kuma ina cikin Bairut sai na karanta littafin “Shi’a ko gaskiya ko wahami” na Muhsin Amin, da kuma littafin Muraji’at na sharafuddin Amuli, sai na cigaba da duba littattafai game da mazhabar ahlul bait (A.S) da masoyansu sai na samu canji a tarihi gaba xaya, na fitar da duk wani tunani na kuskure daga qwaqwalwata.

Haka ne na san ahlul bait (A.S)

Ustaz Ahmad yana cewa haka nan ne ya bayyana gare ni cewa ahlul bait (A.S) da waxada suka yi biyayya garesu su ne muminai na gaskiya, kuma jama’ar tsira, kuma masu shaida da gaskiya a tsawon tarihi, kuma ba yadda za a yi a fahimci musuluinci mai tsarki tatacce sai ta hanyarsu, kuma su ne xayan nauyaya biyu, kuma jirgin Annabi nuhu (A.S), kuma qofar gafara, taurarun shiriya, ba don su ba da musuluinci na haqiqa ya vace, da kuma ba a samu wanda zai gane gaskiya ba, kuma su ne suka xaga tutar qalu-bale a tsawon tarihi, suka xaukai nauyin wahalhalu a tafarkin Allah fiye da yadda wani xan’adam zai xauke, har sai da suka kai wannan addini zuwa ga wannan yanayi na tsarki kammalalle mai albarka.

A taqaice haqiqa na shiriya na san cewa ahlul bait suna da haqqi akan duk duniya kuma na yi alqawarin zan kare wannan haqqin matuqar ina raye, sai duk talifofina suka kasance domin kariya ga wannan haqqi nasu, kuma na tashi domin agazawa hankali da tunanin musulmi a keve da kuma duniya a gaba xaya domin fita daga duhun vata zuwa ga hasken shiriya.

Talifofinsa (Littattafansa)

1- Tsarin siyasa a musulunci (ra’ayin shia da na sunna)
2- Nazarin adalcin sahabbai da makomar siyasa a musulunci (ra’ayin shia da na sunna)
3- Madogarar tunanin siyasa (musulunci, jari-hujja, da gurguzu)
4- Matakan siyasa domin haxe kan al’ummar musulmi
Da wasu masu yawa da ba mu ambata ba, kamar yadda ya rubuta maqaloli masu yawa kan fagagen daban-daban.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
4+10 =