Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


AHMAD RASIM ANNAFIS
(Misra – Bashafi’e)An haife shi a shekarar 1377 a garin “Al’mansura” da misira, babansa ya kasance daga malamai, amma kakansa shi ne malamin nan na Azhar wanda yake yin huduba a masallacin alkarya, kuma yana da cibiya da ‘yan wannan alkarya suke haduwa suna koyon ilimomin addini da fikihu da adab a gunsa.
Dakta Ahmad yana cewa: Na tashi na yi wayo akan sunayen littattafai da ake bugawa sababbi, kuma sau da yawa aka zo gidanmu aka baje kolin littattafai masu yawa game da adabi da wakoki, kuma a lokacin garin Mansura cike yake da irin wadannan lamurran na ilimi, don haka sai na koyi son yin karatu wurin babana da kakana, na karanta duk wasu littattafansu tun ina yaro in banda wani littafi game da ‘ya’yan manzon Allah (s.a.w) a Karbala na marubuci mai suna Khali Muhammad Khalid mai suna “Abna’ur Rasul fi Karbala” wanda duk sa’adda na karanta shi sai hawaye su zo mini! Sai in kasa ci gaba da karanta shi...

Yanayin Karatu

Dakta Ahmad ya ci gaba da karatu bayan nan har sai dai ya samu shedar Sakandare a shekarar 1970 a garin Mansura da samsu shiga Koleji, sannan sai ya shiga cikin kungiyar dalibai domin ya samu dammar bayar gudummuwa a ayyukan wayarwa da al’adun musulunci, a nan ne tunaninsa ya bude game da gwagwarmayar tunani wacce take cike da kwakwalen dalibai a shekarun saba’in 1970s.
A nan ne aka samu tunanin kwaminis yana tafiya da karfi da sauri yayin da masu tunanin musulunci suna gefe a takure suna jin kunya, don haka ne ma aka samu taho-mugama tsakanin wadannan tunanin guda biyu, musamman ma yadda tunanin ‘yan kwaminis yake tafiya da tsokana da isgili. Dakta Ahmad yana karawa da cewa: a shekarar 1975 ne bayan wasu ayyukan shige gona da iri da ‘yan kungiyar kwaminis suka yi, sai muka mike tsaye domin shan gabansu, daga karshe muka tarwatsa su, kuma na samu jagorancin dalibai a kwalejin likitanci ta Mansura a shekaru biyu a jere.

Farkon Fahimta

An samu nasarar juyin musulunci a Iran a shekarar 1979, kuma wannan lamari ya samu tasiri mai girma a wurin bayar da mamakin gun Dakta Ahmad da cewar yaya wannan jama’a suka yarda su fuskanci duk wani harsashi da azabtarwa da shahada suna masu biyayya ga jagoransu! Ya ce; sai ya rika mamakin wadannan jama’a da wasu suka ce suna da muguwar akida amma suka sadaukar da kansu kamar haka, ya ce: a lokacin da muka so buga wasu littattafai na goyon bayan juyin musulunci a Iran sai wasu mutane suka ki yarda daga abokanmu, kuma ban a iya komai sai dai shiru a wannan lokaci, domin babu wani abu da zamu dogara das hi na sanin me yake faruwa a wannan lokacin.

Gaba Da Shi’anci

Sai Dakta Ahmad ya ci gaba da goyon bayan juyin musulunci, sai kuma yakin Iraki da Iran ya barke, sai ga littattafai masu yawa a shekarun 1982-1985 suna masu sukan musulmi Shi’a musamman wahabiyawa suka mike tsaye domin baje kolinsu a wurin, sai ga tunani wahabiyanci yana mai sukan Shi’anci da kagen cewa Farisanci ne da yake son mamaya kan larabci, wannan kuwa babu ko shakka tunani ne na ‘yan ba’as saddamawa masu yakar Iran.

Karkata Ga Mazhabar Ahlul bait (a.s)

Dakta Ahmad yana cewa: sai wata rana muka yi tafiya ta iyalinmu gaba daya a shekarar 1984: sai na samu wani littafi a wata laburare mai suna “Limaza akhtartu mazhabi ahlil bait?” wato me ya san a zabi mazhabar ahlul bait?. Sai na yi mamakin yadda wani malami mai girma kamar Sheikh Muhammad Mar’al Amin al’andaki mai wallafa wannan littafin zai zabi wannan mazhabar haka!? Sai dai sai na bar abin a zuciyata ban yi komai ba, sai n ace amma wannan malamin yana da tasa mahanga mai kima da ya cancanci girmamawa da ita.
Bayan shekara daya a wannan wurin dai sai na sake samun littafi na biyu mai suna “Khulafa’ur Rasul Isna Ashar” wato halifofin manzo goma sha biyu, sai na karanta littafin na fahimce shi sosai, sai na samu kaina ina kusantar mazhabar ahlul bait (a.s) a hankali a hankali.
Ya ce: bayan kwanaki sai na sake samun wani littafi mai suna “al’imam Ja’afar Sadik” wanda Abdulhalim aljundi ya rubuta tun kafin juyin musulunci wanda aka buga a 1997 a majma’al buhusu. Sai n ace da kaina wannan littafin game da imam Ja’afar sadik wanda bamisire ya rubuta shit un kafin juyin Iran kuma daula c eta buga shi bari in ga me yake kunsa, sai na dauka na karanta kuma ya girgizani sosai saboda abin da yake cikinsa na ilimomin Ahlul Bait as wacce azzalumai suka kawar da ita, kuma miyagun malamai suka boye shi, domin ba zasu iya jure jin ambaton alayen annabi Muhammad da alheri ba.
Sai na koma wa wadancan littattafai biyu sai nag a duk abin da yake ciki an ciro daga malaman Ahlussunna ne, sai n ace tayiwu ko shia sun yi wa sunnan karya ne, sai na koma wa littattafan asali sai na samu duk abin da aka fada kamar yadda yake.
Ya ce: kwanaki bas u tsawaita ba sai na tsaya na yi mukayasa tsakanin mazhabar sunna da ta shia sai nag a mas’ala ce mai girma ta fuskacin akida, kuma na hadu da daya daga abokaina na da sai na same shi a kan wannan halin da nake, sai muka fara binciken hukunce-hukuncen fikihu.
Kuma a lokacin na shagaltu da in kamala rubutun kamala karatun Dakta Digri dina, har na kolle ofishina domin in kamala wannan rubut, kuma na samu aka karbe ni a Afril 1986, na fara kuma shiryawa jarabawar karatun wani bangaren na likitanci day a shafi cikin jiki gaba daya, na fuskanci karatu matuka, sai dai kawai abin da nake yi shi ne idan na gaji sai na dauko littattafai mazhabar ahlul bait in ci gaba da dubawa.
Bayan fahimtar wannan mazhabin mai daraja sai ga tuhume-tuhume suna biyo baya da cewa ina da akida gurbatacciya domin bata suna, amma sai na rika tunanin wai mene ne laifin wanda ya yi riko da tafarkin alayen Muhammad saw? Daga nan ne aka samu wasu suak yi ta kokarin ganin sai an kore ni daga aiki a jami’a kai daga karshe dai sun samu an jinkirta ba ni shedar karatun Dakta Digiri nawa daga shekara 1987 zuwa 1992 kusan an jinkirta ni shekaru shida gaba daya da takurawa mai tsanani kan rayuwa domin a tilasta ni barin akida amma bas u ci nasara ba. Dakta Ahmad ya rubuta littattafai masu yawa da makaloli.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
7+3 =